← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 91

Sashe 58

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Saida taga tafiyansu Oummu'n sannan takoma cikin gida, zama tayi akan gadonta tare da buɗe kwalin wayar,  dalleliyar iphone 9 plus grey colour ne ta bayyana acikin kwalin,  yayinda aƙasan kwalin aka shumfuɗe fararen ƴan dubu dubu wanda aƙalla zasu kai 8k, murmushi kawai tayi tare da ciro wayan kana ta maida kwalin ta rufe tasan Oummu tayi hakane saboda tasan idan ta bata kuɗin bazata amsa ba. Kasancewar komai arubuce yake kuma yanzu kanta awaye yake hakan yasa ta kunna wayar tare dayin downloading games ɗin da zasu ɗebe mata kewa. Koda tayi sallan Isha wajen Hajiya Arabi ta nufa, yau kam gyaran da akayi mata har ya zarce najiya, sai kusan wajen 10 sannan tayi bacci.

Wasa wasa yau kwananta 4 agidan Hajiya Arabi wani irin gyaran jiki ake mata na mussaman, acikin ƴan kwanakin huɗun jikinta ya soma sauyawa fatarta taƙarayin smooth yayinda face ɗinta ke shining, acikin  kwanki huɗunan  kullum da safe tatacciyar madaran shanun take fara sha kafun tayi break fast, wasu irin haɗaɗɗun magungana Hajiya Arabi ke bata, wanda har ƙarfinsu ya soma taɓa ta, don ayanzu takan yawan jin kanta acikin wani irin yanayi,, ɓangaren su Oummu kuwa shirye shiryen biki suke sosai hidima suka shiryawa bikin ba ɗan kaɗan ba.

*Singapore*

Kwance yake akan tangamemen gadonsa yayinda gaba ɗaya jikinsa ke lulluɓe da blanket, ahankali ya buɗe kyawawan idanunsa wanda suka kaɗa sukai ja, hannunsa yasanya ya dafe kansa dake masa masifar ciwo,  yau kwanansa uku kenan yana fama da wani irin zazzafan zazzaɓi, da zaran yayi tari kuwa saidai yaga jini ta bakinsa na fita,   wani irin ciwo yakeji sosai ajikinsa,  yau kwanansa uku banda ruwa baisa komai acikinsa ba, ahankali yaɗan tashi tare da jingina bayansa da saman gadon, rumtse idanunsa yayi tare sanya hannunsa ya riƙe saitin heart ɗinsa dake beating da sauri,  Numfashi  me ɗumi ya fesar, sai kuma ga tari ya biyo baya farin handkerchief yasanya yashiga goge jinin dake fita daga bakinsa, tsabar zafin zazzaɓin dake jikinsa har karkarwa laɓɓan bakinsa keyi, cikin dakiya ya zuro da ƙafafunsa ƙasa, ahankali ya sauƙo daga kan gadon, sanye yake da long jeans black colour, kasancewar baisanya riga ba hakan yasa murɗaɗɗun muscles and 6 packs ɗinsa suka bayyana, cikin dauriya tare da aro jarumta ya nufi toilet, agaban sink ya tsaya tare da kunna fanfo ya wanke bakinsa, lumshe idanunsa yayi tare da kifa kansa da jikin bango.

(am so sorry jia banyi update ba kuyi haƙuri Wallahi nashiga busy ne, zanbiyaku bashin najia gobe Insha Allah.)

*Vote and Comment*

fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

                *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                *WATTPAD*
          @fatymasardauna
#romance

               *Chapter 43*

Juyi take tayi akan ɗan madaidaicin gadon, yayinda gaba ɗaya nutsuwarta ke neman yin ƙaura daga gareta,   ahankali take buɗe idanunta har ta sauƙesu akan Nina wacce ke zaune akan gado tana faman lumshe idanunta, wayarta ƙiran iphone ne kare akan kunnenta, waya takeyi me ratsa zucia, kasancewar ɗakin ya ɗauki shiru, sannan ta ƙure volume ɗin wayan, hakan yasanya gaba ɗaya maganan da akeyi mata acikin wayan yake fitowa fili, kalaman soyayya saurayin nata ke zazzaga mata, yayinda gaba ɗaya maganganun nasu ya ƙare akan maganan aurensu da kuma ɗokin burinsu nason kasancewa tare daya kusa cika.
Ahankali ta janye idanuwanta daga kan Nina tare da ɗaura hannunta akan maranta dake yi mata ciwo, kusan kwana biyu kenan tanajin mararta na ɗaurewa, gawani irin baƙon yanayi da takejin kanta aciki,  idanunta ta sake lumshewa tana mejin daddaɗan ƙamshin jikinta na  cakuɗa da numfashinta, ita kanta yanzu ƙamshin da takeyi na matuƙar yi mata daɗi, gefe guda kuwa ga skin ɗinta daya ƙara kyau yayi santsi da laushi,  zuwa yanzu rabin rayuwarta cike take da kewa, wani irin son ganinsa takeyi, akullum gizo idanunta keyi mata na ganinshi, bata taɓa mantawa da kyakkyawar fuskarsa, kyawawan idanunsa masu ɗaukar hankali, harma da kyakkyawan nagartarsa, komai nasa me kyau ne, tanason komai daya dangance sa,, ahankali wasu siraran  hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, kana suka biyo ta gefen ƙuncinta, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da wani irin numfashi, bata iya seccond 1 batare da ta tunasa acikin ranta ba, da tarin tunaninsa acikin rai da zuciyarta bacci ɓarawo ya sace ta..

Yau ta kama saura sati guda aurensu, sosai take shan gyara awajen Hajiya Arabi, zuwa yanzu idan kaga Zieyaderh sai kasha mamakin irin kyaun da tayi, fatarta tayi smooth yayinda duk wata halitta ta cikar ƴa mace dake jikinta suka sake ciccikowa, fatarta takoma milk colour wato kalan madara, ita kanta tasan ayanzu kyawunta ya ƙara bayyana, kuma ayanzune takejin kanta cikakkiyar mace.

Shirin biki ake sosai yayinda Oummu ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayawa amarya kayan da zata sanya alokacin biki, gaba ɗaya ahalin Oummu da Abba cike suke da farinciki saboda auren, kowa ka gani acikin Familyn burinsa shine yaga anyi auren lafiya.
***
Cike da masifa Inna Ma'u ke duban Malam Garba, cikin tsananin Mamaki tace.
"Kasan mekace kuwa? aure fa kake cewa zakayiwa Zieyaderh!"

Kallonta Malam Garba yayi cikin nutsuwa yace. "Ƙwarai Aure zanyi mata kuma saura kwanaki shida aɗaura mata aure inaso kisan da haka, yanzu ma na faɗa miki ne saboda karkice ban kyauta miki ba"

"Kam bala'i lallai Malam kacika butulu, yanzu ni Ma'u ni zakayi wa butulci? Har kasa auren ƴarka ka kuma karɓi kuɗin auren ka cinye batare da sanina ba? to wallahi bazai taɓa yiwuwa ba!" Cikin tsananin masifa Inna Ma'u ta faɗi haka.
Cikin nutsuwa Malam Garba yace "Ki kwantar da hankalinki Ma'u, auren Zieyaderh babu fashi Insha Allah za ayishi, yanzuma burina shine na saida gona ta don na saya mata ƴan abubuwan buƙata kama daga kan kayan ɗaki dadai sauransu"

Cikin mamaki Inna Ma'u tace "Gonarka kuma? Lallai ma Malam, akan auren wannan gantalalliyar yarinyarne har zakace zaka saida gonarka, to bazai taɓa yiwuwa ba!"

Kallonta kawai Malam Garba yayi tare da yin shiru, don acikin abun da yayi niyya babu wani wanda zai fasa, dole zai sauƙe haƙƙin Zieyaderh dake kansa amatsayinsa na uba.

Ganin yaƙi kulata yasanya tasa masa kukan munafurci tare da cewa.
"Nagode ae saboda banice na haifi Zieyaderh ba shiyasa kakemin haka"  
Shidai har yanzu idanu kawai ya zuba mata, don sarai yasan kukan munafurci takeyi, don ahalinta babu wani abu ɗaya wanda baisani ba, ganin da tayi cewa yaƙi kulata ne yasanya tasake taso da wani sabon borin inda tashiga haɗa kayanta wai lallai sai dai ya kaita birni ayi bikin da'ita.
Shidai ƙala baice mata ba baikuma sa aransa cewa zaikaita ba don yasan zuwanta bazai zama alkhairi ba.
***
Oummu ce zaune akan gado tana ta faman har haɗa kayan ɗinkin Zieyaderh wanda aka kawo mata ɗazun, Abba ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, Oummu naganinsa ta saki murmushi tare da ƙarasowa garesa, murmushin dake kan fuskar nata ne yaɗan gushe, ganin yanayin yanda fuskar Abba ta sauya, alamun akwai damuwa.
Cikin kulawa tare da ƙaunar mijin nata ta kamo hannayensa, haɗe da dubansa tace
"Lafiya kuwa?"

Ajiyar zuciya  Abba yayi tare da kamo hannun Oummu suka zauna akan gado, dubanta yayi tare da cewa.
"Sulaimiyya ina jin kamar Sooraj ba lafiya yake ba!"
Gaban Oummu ne ya faÉ—i take ta waro idanunta cikin yanayi na damuwa tace.
"Wani abu ya sameshi ne?"

Ajiyar zuciya yakuma sauƙewa tare da cewa. " Shine abun da bansaniba, amma ki kwantar da hankalinki nasan babu wani abu daya sameshi, kawai dai nine danakejin kamar bayacikin halin lafiya"
Cikin tsananin damuwa Oummu tace "Yace maka zaidawo ne?"
"Eh yace zai dawo jibi"
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Allah yadawo dashi lafiya"  da "Ameen" Abba ya amsa kana yace da Oummu takawo masa ruwa yasha.
Chapter 58 · 0% Book details