← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 91

Sashe 27

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin kalaman Shukra yasanya jikin Ziyada yin sanyi, hakan yasa ta juyar da kanta gefe, gaba ɗaya kalaman Shukra sun ɗaure mata kai, musamman ma inda tace wai "Idan kanason mutum zakana yawan tunaninsa, sannan zaina faɗowa ranka ako da yaushe"       "Me taimako" shine sunan data fara ambata acikin rai da zuciyarta.  Da sauri ta girgiza kanta,  sam bazata taɓa sakewa tasoma wannan banzan wasan dashi ba,  shi cikekken namiji ne, wanda haɗuwa da kyawunsa har sun wuce gaban kwatance,  tayama za'ayi tasoma wannan banzan wasan akansa, kawai dai saboda ya taimaketa ne, yasa takejinsa har acikin jikinta,  amma idan ba haka ba ita wacece  da har tunaninsa zaina damunta? duk wuya duk daɗi bazata taɓa manta wacece ita ba, Ƙasƙantacciya, wacce bata da wani gata, wacce tataso cikin talauci da maraici. Lumshe gajiyayyun idanunta tayi, tare da sanya hanu ta tallafi ƙuncinta.  Tanajin su Nasmah da Shukra suna hira, amma takasa sa musu baki, ahaka har Kamalu driver yazo ɗaukarta, cike da kewar juna tayi sallama da su Nasmah. Ko acikin mota jigum tayi gaba ɗaya damuwowi sun cika zuciyarta.

Lagos Nigeria.

Kuka sosai Alh.Mansur yayi alokacin dayaga yanda ɗansa Sooraj ya dawo,  gaba ɗaya ba abanbanceshi da gawa, domin kuwa har yanzu baisan inda kansa yake ba.  Gaba ɗaya yashiga damuwa, duk da cewa sosai likitotin suka dage wajen ganin sun bawa Sooraj ɗin kulawa.  Waya Alh. Mansur yayiwa babban abokinsa Dr.Mohd  dake aiki ababban asibitin Abuja, Dr.Mohd ƙwararren likitane wanda yasan aikinsa, domin kuwa aduk Abuja shine babban likita,   maganar da sukayi da Dr. Mohd ne yasanya Alh.Mansur yi musu booking flight,  ƙarfe 6 na yammaci daidai jirginsu ya ɗaga zuwa sararin samaniya.   
Koda suka isa Abuja Kamar gawa haka aka shiga da Sooraj Intensive Care Unit.

Jigum haka Abba ya zauna, tare da sanya hanu ya dafe kansa.  Gefensa Ummu ce wanda tabiyo flight daga Kaduna tazo, kuka take sosai, Abba yayi rarrashin duniya amma sam taƙiyin shiru.

Tafe yake yana tuƙa mota, amma gaba ɗaya hankalinsa baya tare dashi, tunani yake akan abunda zuciyarsa ke raya masa, har azahiri yana ganin hakan shine daidai.

Zaune take akan rug ta nannaɗe ƙafafunta, farcen ƙafanta take yankewa, amma azahiri hankali da tunaninta yana wani waje.  Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar falonne yasa ta ɗago kanta da sauri,  Dai dai lokacin Mas'oud ya buɗe ƙofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.  Ganin Mas'oud yasata tashi tsaye da sauri, murya asanyaye ta amsa sallaman nashi.  Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, yana mai ɗan ƙare mata kallo

Gaisheshi tayi cikin murya me sanyi,  fuskarsa aɗan sake ya amsa mata, kitchine ta shiga ta ɗauko cup, sannan ta buɗe fridge ta ɗauko masa ruwa,  akan glass stull ɗin dake gabansa ta ajiye ruwan. Tana shirin komawa ɗaki taji yaƙira sunanta "Ziyadah!"

Tsayawa tayi cak tare da É—an juyowa takalleshi "Na'am" ta amsa masa murya asanyaye.

"Ɗauko mayafinki kizo akwai inda zamuje" Yafaɗa yana mai ɗan kurɓan ruwan da ta kawo mai.

"To" tace murya asanyaye. Sannan ta wuce ɗaki, jigum tayi tana mai tunanin ina zasu, wata zuciyarne tasoma ƙoƙarin kawo mata wani mummunan tunani, hakan yasa tayi saurin ɗaukar lufayanta tasanya, tare da ɗaukan takalmi flat shoe ta zura aƙafafunta, lokacin da tafito falon a tsaye ta sameshi yana ta kaikawo da alama yana cikin damuwa.

Yanaganinta yace "Yauwa muje ko"  haka suka fito yana gaba tana biye dashi abaya,  gani tayi ya tsaya yanawa me gadi magana , hakan yasa taɗan tsaya itama agefe.

Tafiya suke babu wani wanda yace da ɗan uwansa wani abu.   Har saida sukayi nisa da gidan kafun yaɗan rage gudun motar, kallonta yayi tare da cewa.  "Inaso daga yanzu ki fara amsa sunan ƙanwata,  SOORAJ baida lafiya yana asibiti yanzu haka, nasan yana da buƙatar kulawanki adaidai wannan lokacin, please Dan Allah  Ziyada ki kula da Sooraj, shiɗin mai rauni ne akowani ɓangare, kulawarki kaɗai yake da buƙata"

Ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, yayinda idanunta suka cicciko da ƙwalla, damuwa ƙarara ta bayyana akan fuskarta, duk da batasan asalin sunansa ba , amma jikinta ya bata cewa SOORAJ shine me taimakonta. Har suka isa babban asibitin bata sake cewa komai ba, saidai gaba ɗaya bata da natsuwa.  Haka suka shiga cikin asibitin jiki asanyaye, direct wani ɗan ɗaki suka nufa,  suna shiga Mas'oud ya durƙusa tare da  sake gaishe da su Abba da Umma, Abba ne kaɗai ya iya ƙarfin halin amsawa domin Ummu kam Kuka take har yanzu, cike da ladabi Ziyada ta durƙusa har ƙasa ta gaidasu,   Abba ya amsa yana me kallonta, sai alokacin Ummu dake kuka ta ɗago kanta ta kalli Ziyada.    Ganin irin kallon da Ummu keyiwa Ziyada yasa Mas'oud cewa.
  "Amm Abba dama wannan ƙanwatace ƴar Baffana ne dake Sokoto, tana karatune anan, sannan kuma suna da kyakkyawan alaƙa tsakaninta da Sooraj, shine nace mai zaihana tazo tana tayaku kula dashi tunda yanzu sunyi hutun makaranta"  Yaƙare maganar yana ɗan sosa bayan kanshi, domin shi kansa yasan ya shiryota.

Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da cewa "Tabbas hakan da kayi ka kyauta Mas'oud, domin dama kaga zaman Ummu'nku anan bazai yi wuba, saboda tunda tazo kuka take, nikuma banason kukannan!" Abba yafaɗi haka cike da damuwa.

Ɗan ɗagowa Ziyada tayi ta kalli wacce ake ƙira da Ummu, tsananin kaman da tagani na me taimako akan fuskar matar shiya sanya tayi tunanin ko mahaifiyarsa ce, to amma idan da yana da iyaye aida tasan bazai zauna agidansa shi kaɗai ba,  dole ne zai zamana iyayensa suna tare dashi.

Kallon Ziyada Ummu tayi sosai, wani tunanine yake ɗarsuwa  acikin ranta,  bazatace bata yarda da maganganun da Mas'oud ya faɗa ba, amma ita ta haifi Sooraj tasan kusan gaba ɗaya halayyarsa, mutumin da bayason mu'amala dako wacce irin mace yau shine za'ace wai akwai kyakkyawar alaƙa atsakaninshi da wata?.

*Vote Me 0n Wattpad *
   @fatymasardauna

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           *WATTPAD*
    @fatymasardauna

#romance

         *Chapter 23*

Abba da Mas'oud ne suka tashi suka fice daga cikin ɗakin, kasancewar alokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Magriba.  Ummu ne tafito daga toilet ɗin dayake cikin ɗakin, fuska da hannayenta duk ruwa da'alama alwala tayi.

Kallon Ziyada dake zaune jigum tayi.   "Jekiyi alwala" Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin shimfuɗa darduma akan tiles.  Sumu sumu haka ta wuce toilet ɗin ta ɗauro alwala,  hanu tasanya acikin hijab ɗin dake jikinta, ta zaro ɗan kwalin dake kanta, shimfiɗawa tayi akan tiles, sannan ta hau tare da daidaita tsayuwarta, akan ɗan kwalin ta gabatar da sallan Magriba, ko da ta idar da sallan, samun kanta tayi dayin shiru, tare da jingina kanta da jikin bango,  gaba ɗaya jin zuciyarta take babu daɗi,  babu wani abu da takeson gani sama da Helper ɗinta, sosai hankalinta yake atashe, sannan gefe guda kuma, ga kukan da taga mahaifiyar Sooraj ɗin nayi yasake ɗaga mata hankali. 

Dukansu daga ita har Ummu babu wacce tatashi daga kan abun sallanta, har aka ƙira sallan isha,   baga Ummu kaɗai ba hatta Ziyada saida tasanya Sooraj cikin addu'anta.    Ƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin kanta take, aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.   Alh.Mansur ne dakuma Mas'oud,  Mas'oud ne ya aje basket ɗin dake hanunsa, tare da kai dubansa gareta.

"Ziyada ki zubawa Ummu abinci taci, kema ki ɗebi naki kici, zuwa anjima likitotin sun tabbatar mana da cewa zamu samu ganinsa!"  Mas'oud yaƙare maganar cike da ɗan yanayi na damuwa.    Alh.Mansur kuwa kasa ma cewa komai yayi, zama kawai yayi akusa da Ummu tare dayin shiru.

Ɗaukan basket ɗin Ziyada tayi tare da zaro wasu plate,  kulan dake cikin basket ɗin ta buɗe tare da sanya spoon ta zuba lafiyayyar jalop rice wacce taji bushashshen kifi acikin plate ɗin. Cike da ladabi ta ƙarasa gaban Ummu, cikin muryarta dake rawa tace.  "Ummu ga abinci"

Kai Ummu tagirgiza cike da damuwa tace.
"Banajin zan iya cin abinci batare da na sanya ɗana a idanuna ba, kici kawai!" gaba ɗaya muryar Ummu rauni kawai take bayyanawa. 

Hanun Ummu Alh.Mansur ya kamo, cike da tsananin so da kuma nuna kulawa ga matartasa yace.   "Ki kwantar da hankalinki Sulaimiyya, Isha ALLAH Sooraj zai samu lafiya, addu'an mu kawai yake da buƙata bakomaiba,  kibar kukannan haka kuka banaki bane."   Kallon Ziyada yayi tare da cewa.

"Miƙomin abincin nan na bata"     karɓan plate ɗin abincin Abba yayi yashiga lallaɓa Hajiya Sulaimiyya akan taci, amma gaba ɗaya ta daburce taƙi ci, hawayene kawai ke silalowa daga cikin idanunta, shima kanshi Abban ƙarfin hali kawai yake amma damuwane ninke aƙasan ranshi. 

Gaba ɗaya itama Ziyada kasa cin abincin tayi,  lomanta uku ta ture plate ɗin abincin gefe, ji tayi ko kallon abincin batasonyi, hawayene suka ziraro daga cikin idanunta, da sauri tasanya gefen hijabinta ta share,  tausayin halin da taga Iyayensa aciki take, musamman yanda taga hawayen mahaifiyarsa ya kasa daina zuba,  jitayi gaba ɗaya zuciyarta ta karye.. 
Da ƙyar Abba yasamu Ummu taci 4 spoon na abincin.   Dr.Mohd ne dakanshi  turo ƙofar ɗakin ya shigo.   Cike da tausayawa ya dubi dukkaninsu, da sauri Alh.Mansur yataso daga zaunen da yake yana cewa.

"Dr.Mohd ya dai, akwai wani cigaba ko kanaga kawai gobe mu wuce Germany ɗin?"    Yanayin yanda Alh.Mansur yayi maganan kaɗai ya isa sanya zuciyar mai sauraro karyewa, domin kuwa kallo ɗaya zakayi masa kasan baya cikin wata nutsuwa, sosai rashin lafiyar Sooraj ɗin ke damunshi. 

Ajiyar Zuciya Dr.Mohd yayi tare da kama hanun Alh. Mansur suka fice daga cikin ɗakin, ganin haka yasa Ummu fashewa da kuka, domin atunaninta wani abunne ya kuma sake faruwa,  Mas'oud ne yayi ƙarfin halin fara rarrashinta.

"Calm down Alh.Mansur kazauna!" Dr.Mohd yafaÉ—i haka akaro na uku kenan, domin kuwa tun É—azu yaketa yiwa Alh.Mansur É—in tayin wajen zama, amma saboda ruÉ—un da Alhajin ke ciki, sam ya kasa zama.

"Bazan iya zama ba Dr.Mohd, hankalina amatuƙar tashe yake, kafaɗamin maiyasa ka kawoni office ɗinka? Shin wani abu yasake faruwa da SOORAJ ɗinne?" 
Chapter 27 · 0% Book details