← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 91

Sashe 71

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hararan wayan Zieyaderh tayi tamkar suna ganinta, cikin gajiya da tsokanar tasu tace.
"Allah yashiryaki Shukra,nikam yanzu kinfi ƙarfina."

Fari da ido Shukra tayi tare da cewa.
"Naƙirane dama na tuna miki cewa next week zamu koma school, so sauran bayanin sai mun haɗu a school, nasan zuwa yanzu kin ƙara fresh, hope baki manta islamic lecture'n da akayi ranan a school ba?."

Kunyane ya rufe Zieyaderh, cikin ƙosawa tace.
"Allah yashiryaki Shukra, bazaki taɓa sanjawa ba."

Dariya suka saka atare, inda sukayi sallama akan cewa sai sun haÉ—u a school din.

Awannan rana haka Zieyaderh taƙare zamanta agidan ita kaɗai.

Dare nayi tana idar da sallan isha kuwa bacci ya ɗauketa anan falo kan kujera,  yauma baidawo gidanba sai ƙarfe 9, ganinta kwance afalo yasanyashi wucewa ɗaki kai tsaye, wanka yayi inda yashirya kansa cikin ƙananun kaya marassa nauyi,  kwanciya yayi akan gado tare da jawo blanket ya rufe jikinsa,  da tunani kala kala acikin ransa, haka bacci ya ɗaukesa. 

Yauma kamar jiya tun 6:00 am yafice daga cikin gidan,   haka ya wuceta kwance afalo tanata sharar bacci, koda ta tashi taganta kwance afalon baƙaramin mamaki tayi ba, nan tatuna da cewa baccine ya ɗauketa jiyan batare data shiryawa hakan ba,  kaitsaye bedroom ta nufa, sannu ahankali take ƙarewa cikin ɗakin kallo, komai dake ciki nead, da dukkan alama dai babu wani wanda ya kwana acikinsa, cikin zuciyarta tace.
"Kenan baidawo ba? ko yayi tafiya ne?."
Sanin bata dame amsa mata tambayoyin nata, yasanya ta wuce toilet, wanka tayi, yauma dai ta makara hakan yasa ta É—auro alwala tazo ta gabatar da sallah.
****
Wasa wasa yau kwananta 6 bata sashi acikin idanunta ba,   kullum batajin motsinsa, batasanin fitansa ba kuma tasanin dawowarsa,   daga gefe guda kuwa wani irin masifaffen kewarsa ne ke ɗawainiya da zuciyarta, sosai takejin wani abu na daban akansa, sannan kuma aduk sanda ta tuna da moment ɗinsu na ranan, saitaji wani irin feeling ya taso mata, sosai take buƙatan hakan daga garesa, sau ɗaya tak yashayar da ita yawun bakinsa, amma gaba ɗaya hakan ya zautar da ita.

Zaune take jigum akan gado, wata sleeping gown ne ajikinta me kalan light pink, sosai rigan tayi mata ɗas ajiki, wani ɗan madaidaicin hijab ta ɗaura akan rigan,  baccine cike a idanunta, amma haka take ƙoƙarin shanyewa, kasancewar gobe ne zasu koma school hakan yasa tun da yamma tagama kimtsa duk wani abu da zata buƙata, tuni har gugan uniform ɗinta tayi, kasancewar tagaji da zaman gidan, yasanya har Allah Allah take gobe tayi.
Yau ta ƙuɗurta aranta cewa bazata taɓa yin bacci ba harsai ta ganshi, takuma sanardashi maganan komawarsu makaranta gobe,don sunyi waya da Oummu, inda Oummu dakanta tace tasanar da shiɗin cewa gobene komawarsu school, saboda yanzu dole saida izininsa za take zuwa school ɗin.

Sama da mintuna talatin taÉ—auka zaune akan gadon har bacci yaÉ—an É—auketa batare da ta shiryawa hakan ba.
10 pm daidai ya shigo cikin gidan,  yana shiga cikin ɗakin yasoma rage kayan jikinsa batare daya kula inda take ba,  towel ya ɗaura akan waist ɗinshi inda ya nufi bathroom, kwana biyunnan baƙaramin azabtuwa yakeyi ba, sosai yakejin zafi azuciyarsa, shikansa yanajin kamar yana hora zuciyarsa da horo mafi girma, baisan meyasa abun dayakeji ajikinsa ke ƙara yawaita kullum ba,  ƙaran ruwan dake tashi daga cikin toilet ɗinne yayi sanadiar buɗe idanunta,  Ajiyar zucia ta sauƙe, tare da ɗan langwaɓar da kanta gefe, fargaba ne aranta don batasan daya zata fuskancesa da maganan ba.

Baiwani jima cikin toilet ɗin ba, yafito, farar bathrube ne ajikinsa, gaba ɗaya kansa jiƙe yake da ruwa, kaitsaye gaban mirror yanufa, da wani ɗan ƙaramin towel ya goge jikakkiyar sumar kansa. yana gama tsane ruwan ya tako ahankali ya zauna abakin gadon, wani ɗan madaidaicin table yajawo gabansa, inda ya ɗaura laptop ɗinsa akai, cikin nutsuwa yashiga ajiye wasu bayanai cikin Email ɗinsa.

Ahankali taɗan sauƙo daga kan gadon, kanta aƙasa ta tako har zuwa inda yake, samun kanta tayi da durƙusawa agabansa tare dayin ƙasa da kanta, cikin rashin sanin madafa tasoma murza ƴan yatsun hannunta, bugun zuciyarsa data tsananta ne yasanyashi gane cewa tana kusa dashi, lumshe idanunsa yayi batare daya buɗe ba yace. "Menene?."
Kaman dama shitake jira, gyara zamanta tayi cikin nutsuwa haÉ—i da yarintar dake É—awainiya da ita tace...
"Dama...umm dama gobe hutun mu na school zai ƙare, shine Oummu tace na gaya maka."

Shiru yayi tare da ɗan juyowa ya sauƙe shanyayyun idanunsa akanta, jin yayi shiru ne yasanyata ɗan cije laɓɓanta, ahankali ta ɗago fararen idanunta aniyarta shine taɗan saci kallonsa, karab idanun ta suka sauƙa cikin nasa idanun, ganin yanda idanunsu suka sarƙe cikin najuna ne, yasanyata ɗan lumshe idanunta, kana takuma buɗesu alokaci guda, cikin wani irin yanayin da ƙwayan idanunnasa suka shigar da ita taɗan kwaɓe fuska kamar wacce ke sonyin kuka, ahankali take motsa bakinta kamar wacce takeson faɗan wani abu, karo na farko kenan arayuwarsa dayaji don kansa yana sha'awan yin kissing ɗin bakinta, sannu ahankali yakejin gargasan jikinsa na buɗewa, lumshe idanunsa yayi don bazai iya jurewa abun dayakeji ba, can ƙasan maƙoshi yace.
"Naji kije ki kwanta."
Jin maganarsa yasanya taji zuciyarta tayi mata sanyi, ahankali tatashi ta koma kan gadon, nannaɗewa tayi acikin lallausan blanket ɗin dake ta tashin ƙamshinsa, cikin wani irin shauƙi ta cusa kanta acikin pillow, ahankali take sauƙe ajiyar zuciya akai akai, ta rantse aduniya itakam bataga wani kyakkyawa mai kyawawan idanu tamkarshi ba, shi komai nasa na musammanne, magana ma yanayinta ne kawai alokacin dayaga dama, zuciyarta cunkushe da tunaninsa haka tayi bacci.

Shikuwa SOORAJ duk yanda yaso cigaba da aikin nasa kasawa yayi, don wani irin baƙon al'amarine ke ziyartar gaba ɗaya gangar jikinsa, akasalance ya rufe laptop ɗin tare da miƙewa tsaye, ahankali ya karasa gaban sif d'in kayansa, wani 3 guater jeans ya sanya, yayinda Kai tsaye ya nufi kan doguwar kujeran dake cikin dakin, kwanciya yayi tare da lumshe idanunsa, kasancewar adan gajiye yake yasanya baiwani jimaba bacci b'arawo ya d'aukesa.

Duk sammakon tashi da ta buga, Saida ta samu yarigayeta tashi, don ko da ta tashi daga baccin tsaraban k'amshinsa kawai ya barmata, cikin tsanaki tayi wanka, tana idar da sallah ta dauki sassanyan body lotion dinta Mai dadin kamshi tashiga shafawa ajikinta, sama sama ta shafa powder, wani dan pink lipstick ta goga akan labbanta, kamar yanda take ko yaushe bata cika kwalliya ba, hakama yanzun batayi wani kwalliya ba, dogon sket high waist, and long sleeve ta sanya, Wanda sune suke mazaunin kayan uniform dinta, tubke dogon gashin kanta tayi inda ta zura Dan madaidaicin hijab din makarantar tata, Wanda tsayinsa ya kawo harkan cikinta, katuwar school bag dinta ta rataya bisa kafadanta, agurguje haka tafita daga cikin dakin don kuwa lokacin har bakwai da rabi tayi, kamar da can baya yau dinma Kamalu driver ne ya kaita makarantar, sosai sukayi murnan ganin juna ita dasu Shukra, ba ita tasamu daman karyawa ba, Saida suka fita break, sosai yau din taji dadin makarantar saboda koba komai ya kore mata kadaici.

5 daidai aka tashesu atare suka jero tare da su Shukra, tafe suke suna hira harsuka iso babban compound din makarantar, tuni driver'n Nasmah yazo daukarta saboda haka tayi musu sallama tatafi, tana tafiya kuwa saiga driver'n gidan su Shukra shima yazo daukarta, haka suka watse sukabar Zieyaderh ita kadai, agogon dake daure atsintsiyar hannunta takalla 5:16 pm, fuska tadan kwabe tana me sake ware idanunta wai ko zata hango Kamalu, sannu ahankali hadaddiyar motar da takawo Kai cikin makarantar ta karaso gareta, agefe da ita kad'an motar wacce tasha tintect ta faka, bude murfin motar yayi tare da zuro da k'afafunsa k'asa, sannu ahankali ya fito gaba dayansa daga cikin motar, Sanye yake da k'ananan Kaya, yayinda ya manna sun glass akan idanunsa, Sam Bata kalli gefen da yake ba, cigaba tayi da duddubawa ko zata hango Kamalu driver, amma abun mamaki ko irin motarsu Bata hango ba.

Wani irin bak'on k'amshin da yaziyarci hancinta shiya Sanya tadan waiga bayanta, donjin daga Ina k'amshin ke fitowa, sauke idanunsa akanta yayi daidai da bugawar zuciyarta, lokaci guda kirjinta yayi wani irin tsalle kamar zai fad'o, cikin tsananin mamakin ganinsa tadan zaro idanunta waje,
wani irin kawataccen murmushi yayi mata, cikin takunsa ya karaso gab da ita, tsakanin su bai wuce saura taku daya ba ya tsaya tare da lumshe munafukan idanunsa, sun glass din ya zare daga kan idanunsa, inda ya waresu tas akanta, wani irin kallo, Mai dauke da tsananin shauki ya bita dashi, cikin kwantar da murya yace.

"I missed you so much babe, ganinki ya fiye min komai ayanzu, I Love you so so much!" Pharouk Yakare maganan Yana me byyana zallan shaukin dake ransa afili, kanta ta sunkuyar kasa, samun kanta tayi da kasa ce masa komai, batare da zato ko tsammani ba taji ya kamo hannuwanta, arazane ta d'ago kanta ta dubeshi, kansa ya langwabar gefe cikin salo irin nasa yace.
"Bazan iya jure rashinki ba, duk da nasan cewa anyi Miki Dole wajen aura masa ke, Inasonki Zieyaderh, burina shine kasancewa dake, please Kar kice Zaki rabu Dani, karkice zaki k'i aminta Dani, Inasonki!."
yakare maganar Yana me kokarin murza Yan yatsun hannunta, gaba daya ta rude tana kokarin zare hannunta, Amma rikon da yayi mata bana wasa bane.
Daidai lokacin wata hadaddiyar mota Kiran 4matic takawo Kai cikin makarantar, gaba daya fiye da Rabin daliban makarantar kowa ya kama gabansa, Yan tsirarune kawai suka rage, irinsu Zieyaderh da ba'azo daukarsu da wurine ba.
Ahankali yayi parking motar inda dagowan da zaiyi idanunsa suka Masa mummunan gani, ganin daya sanya kirjinsa wani irin dokawa, ganin daya sanyashi Jin wani irin d'aci amak'oshinsa, ganin daya sanyashi jin wani irin jiri yayinda wani irin tari ya taso masa, har takai numfashinsa na kokarin carkewa.

(Bani da bakin da zan baku hakuri bisa jinkirin yi muku update dana samu, wallahi wani babban uzurine ya rikeni, ina fatan zakumin uzuri, insha Allah gobe zan baku page 49 sannan zanyi kokarin Yi muku typing kullum insha Allah, saboda nikaina nakosa nayi ending labarin.... Son So nake muku my fans Dina...)

*Vote*
*and*
*comments*

fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ!!!*

  *Written By*
Phatymasardauna
Chapter 71 · 0% Book details