← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 91

Sashe 11

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bakiji bane?" yasake tambayarta cike da ƙosawa.

"A'a banci ba" tafaÉ—a masa haka a sanyaye.

Ledan dake aje agefensa ya jawo.  "Ɗauko min plate" yafaɗa still batare daya kalleta ba.

Inda take tunanin nanne kitchine ta nufa,  sum sum ta dawo riƙe da plate a hanunta. 

Durƙusawa tayi haɗe da miƙa masa plate ɗin.

Ledar ya buɗe ya ciro take away guda ɗaya, haɗe da tura mata gabanta,  ɗaukan ɗaya yayi ya juye abun dake ciki acikin plate ɗin da ta kawo masa. 

Spoon yasa acikin plate É—in yasoma tsakalan jalop rice É—in da yaji busashshen kifi.

Shiru  tayi ta kasa cin abincin, tsoron tashi take, sannan kuma bazata iya sakewa taci abinci a gabansa ba. 

Tunda yafara tsakalan abincin bai ko da ɗago kansa ya kalleta ba, abincinsa kawai ya ke cusawa,   fiye da rabi yaci sannan ya ture plate ɗin gefe, goran peach ɗin dake gefensa ya ɗauka, haɗe da tsiyayawa acikin wani ɗan ƙaramin glass cup, ahankali yake sipping peach drink ɗin,   yana kammalawa ya miƙe ya wuce ɗakinsa.

Tanajin rufe ƙofarsa ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, take away ɗin ta jawo gabanta, buɗewa tayi, amma amaimakon taga shinkafa kamar yanda taga nasa, sai taga ferfesun naman kaza ne aciki, wani yawu ta haɗiya haɗe da soma ci ahankali, bata wani ci sosai ba taji gaba ɗaya cikinta ya cushe, rufewa tayi tare da ɗaukan goran ruwan dake gefenta tasha.  Ɗauke plate da take away ɗin tayi tamayar kitchine, zama tayi afalon tana daɗa ƙarewa falon kallo, idanunta ta sauƙe akan makeken tv plasma'n dake cikin falon,  kasancewar ba akunne yakeba yasa ta ɗauke idanunta daga kansa, kanta ta jingina ahanun kujeran da take zaune aƙasanta,  shiru tayi haɗe da lumshe idanunta da suka kawo ƙwalla, tunanin babanta ne ya faɗo mata arai, take taji zuciyarta ta ƙara karaya,, tana cikin wannan tunanin bacci ya ɗauketa ahaka.

Tsab ya gama shirin kwanciyarsa,  bayan ya gama latsa laptop ɗinsa.   Kwanciya yayi flat akan gadon haɗe da lumshe idanunsa,  sosai yakejin daɗin sanyin Ac'n dake hurasa,   wani abune yazo ya toshe masa maƙoshi,  akowacce dare baya samun wata gamsashshiyar nutsuwa, yanaji ajikinsa akwai wani gibi a tattare dashi,  haƙoransa yasa ya datse laɓɓansa,  sakamakon tunowa da korar da Ummu tayi masa ɗazu da yayi,  sam baya ganin laifin iyayennasa, saboda kowa tunani yake cewa  ason ransa yake sakan matan da ake aura masa, tunowa da magungunansa da yasayo yau yayi, miƙewa yayi jiki a sanyaye ya ɗauko magungunan,  ruwa ya ɗauka ya sha.

Luf yayi akan tattausan katifarsa,  duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa ya kasa shikaɗai yaketa juyi akan gado,  saƙƙowa yayi daga kan gadon haɗe da zura slippers ɗinsa, falo ya nufa hanunsa riƙe da wayarsa.

Bai lura da itaba sam saida ya zauna akun kujeran dake facing É—in wanda ta É—aura kanta akai.

Shiru yayi haɗe da ƙura mata idanu,  kallon yanda tayi kwanciyar nata yasoma yi, duka jikinta na ƙasa yayinda kanta kuwa ke kan hanun kujera, dagani kasan baccinne ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba,  kallon ɗan ƙaramin bakinta dake ɗan buɗe yayi, tare da kawar da kansa gefe.  

Ɗan zamewa yayi ya jingina bayansa da jikin kujera, lumshe idanunsa yayi haɗe da soma sauƙe numfashi ahankali.

*** *** ***

4:50 am  dai dai ya shiga buɗe idanunsa ahankali, azabure ya tashi zaune yana bin inda ya gansa akwance da kallo,  yana jingine akan kujera bacci ya ɗaukesa batare daya sani ba, hanu yasa ya dafe goshinsa haɗe da furzar da wani iska mai zafi daga bakinsa.  Kallon gefensa yayi tananan kamar ɗazu saidai yanzu tadawo da kanta ƙasa, yayinda ta takure jikinta waje ɗaya da alama sanyin AC ne ke damunta.

Miƙewa yayi ya wuce ɗakinsa yana me mamakin kansa, tunda yake bai taɓa kwana afalo ba sai yau, sam baisan yaushe bacci ya ɗaukesa ba.

Toilet yashiga haɗe da sakarwa kansa ruwa.  Yana fitowa ya zura maroon jallabiya tare da ɗaukar sallayansa ya fice daga cikin ɗakin.

Haka ya wuceta afalon tana ta bacci ko kallon inda take baiyi ba ya fice.

Ahankali ta ware idanunta akan haɗaɗɗen zanen POP'n dake mamaye saman falon, fuskarta ta ɗan yatsuna haɗe da sanya hanunta akan wuyanta, jitayi wuyannata ya ƙage waje ɗaya sosai yakeyi mata ciwo,  ahankali ta miƙe tsaye, kallon falon tayi sannan ta wuce ɗaki, banɗaki tashiga ta ɗauro alwala,  tana idar da sallan ta zauna akan sallayan haɗe da sake lumshe idanunta, ciwo wuyanta keyi mata sosai hakan yasa ko motsa kanta batason yi.

Tunda yafita daga gidan baidawo ba sai Ƙarfe 9 na safiya, yana shiga bedroom direct toilet ya nufa,  kwanciya yayi luf acikin jakuzzien daya ji ruwan wanka wanda aka cakuɗasa da daddaɗan turaren wanka mai ƙamshin gaske, lumshe idanunsa yayi, kansa ne ke ɗanyi masa ciwo kaɗan kaɗan, ajiyar zuciya yayi, sakamakon tunawa da yayi cewa gobe zai wuce Abuja,  sai dai kuma baisan ina zai saka wannan kayan daya ɗaukowa kansa ba.

***

Acan Ƙauye kuwa, Inna Ma'u sun wayi gari anata shirye shiryen ɗaurin aure, basu farga da cewa Ziyada bata gidan ba saida jama'a suka hallara don ɗaurin auren, tashin hankali kam Inna Ma'u ta shigesa, babu inda ba su bazama ba wajen nemanta amma babu ko wani wanda yace ya ganta.  Sosai hankalin Mahaifinta ya tashi, har baisan sanda wasu ƙwalla suka gangaro daga cikin idanunsa ba,   Inna Ma'u kuwa bala'i tashigayi haɗe da tsinewa Ziyada tana cewa wai ta cucesu ta kunyatasu,  shikuwa Tsoho Ɗan Dashe ai masifa yadingayi kamar zai tashi sama, take rashin mutumcinsa ya tashi, nan yakafe kaida fata lallai sai Inna Ma'u ta biyasa kuɗaɗen daya dinga narka mata, idanu Inna Ma'u tashiga zarewa kamar munafuka.....
***

Riga da wandone ajikinsa wanda suka matuƙar yi masa kyau, cike da ƙosawa ya ture laptop ɗin dake gabansa, kusan awansa biyu yana aiki da ita, gaba ɗaya jinsa yake agajiye,  kitchine ya wuce ya haɗa tea ɗinsa, dawowa cikin falon yayi ya zauna, kallon ƙofar ɗakin da take ciki yayi, kana ya dawo da kallonsa ga agogon dake saƙale ajikin bangon ɗakin 2:00pm dai dai yagani,  sake kallon ƙofar ɗakin yayi, sai alokacin ya tuno da cewa ko break bai bata ba,   kallon tea ɗinsa yayi haɗe da sake kallon ƙofar nata, yakan manta da cikinsa ma balle na wani, shi dama sam abinci bai dameshi ba, sannan ba ɗawainiyar kowane akansa ba,  shiyasa baiwani damu da wani yaci ko karyaci ba, baisan ya ake kula da wani ba, saboda shikaɗai yake rayuwarsa bawani a ƙasansa,  Saida yagama shanye tea ɗinsa kafun ya tashi daga zaunen da yake.  Wayarsa ya ɗauka ya turawa wata number text message, yanaganin alamar saƙon yatafi ya ajiye wayartasa.  Kwanciya yayi akan kujera haɗe da lumshe idanunsa.

(Readers anya Sooraj bazai kashe Ziyada da yunwa ba kuwa? My Wattpadians karku taɓa mantawa saboda ku kawai wallahi nayi typing, saboda haka kuma ku ɗaga darajata tahanyar bani comment da Vote, sannan kuma ba kullum zakuna samun Update ba.)

*Vote me on Wattpad*
     @fatymasardauna

#romance
#heartouching

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

          
            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

        *Chapter 10*

Baijima da kwanciya ba aka soma knocking ƙofar falon, yana daga kwance yabawa maiyin knocking ɗin izinin shigowa.

Peter ne yashigo cikin falon hanunsa riƙe da wasu ledodi, cike da girmamawa ya rusuna ya gaida ogan nasa.

Amsan ledodin Sooraj yayi haɗe da ciro wallet ɗinsa ya zaro fararen ƴan dubu dubu har guda uku ya bawa peter,  karɓa peter yayi yana godiya ya fice daga falon.

Ɗaukan duka ledodin yayi haɗe da nufar ɗakin da take,  amemakon yayi knocking kamar yanda ya sabayi kullum, sai kawai ya tura ƙofar  ya shiga ciki, a zuciyarsa kuwa yana maijin haushin bautar da yakeyi mata.

Tana kwance akan gado tayi kwanciyar ruf da ciki, bacci takeyi hankalinta a kwance,  harara yaɗan wurga mata haɗe da aje ledodin, har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya, kallonta yashigayi tundaga ƙafanta har zuwa kanta,   ahankali yataka zuwa inda take kwance, ƙafansa yasa ya ɗan zunguri nata ƙafan, azabure tatashi ta zauna tana mai murje manya manyan idanunta da sukayi ja.      Sake kallonta yayi, sai alokacin ya lura tun rigar jiya itace har yanzu ajikinta. "Ƙazama" yafaɗi haka acikin zuciarsa.

"Ki tashi kije kiyi wanka, ke wace irin ƙazamace zaki wuni da kaya ki kuma kwana dashi?" yatambayeta yana mai kawar da kansa daga kallonta.

ÆŠago idanunta tayi ta kallesa, gani tayi kamar bashine yayi maganan ba, saboda yanda ya fusge yawani kawar da kansa gefe guda.

Kallon kanta tashigayi, sam rigar jikinta bata da wani alaman abu wai shi datti,  ita lokacin da take ƙauye ai sai kaya suyi sati ajikinta ma bata cireba, to inama taga yawan suturun balle ta dinga sanjawa akai akai.

"Idan kin gama ki sameni a falo"  yanagama faɗan haka yafice daga cikin ɗakin.

Kamar yanda yace haka tayi, kayan jikinta ta cire taje tayi wanka, tana fitowa awanka still wata doguwar riga ta ɗauka ta sanya, sai dai wannan ba kalan waccar da ta cire bane.   Ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, yau madai robobin take away ne acikin ledan har guda uku,  ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, sosai taci sannan tasha ruwa.    Mayafin rigar tayafa asaman kanta sannan tafito zuwa falo.

Yana tsaye agaban fridge yabawa cikin falon baya,  jin motsinta afalon yasa batare da ya juyoba yace.   "Muje"  nufar hanyar fita daga cikin falon yayi.

Yana gaba tana biye dashi abaya har suka ƙaraso inda motarsa ke fake.   Buɗe murfin motar yayi ya shiga, key yasanya zai ta da motar,  gefen da take tsaye ya kalla cike da takaici. 
"Sainace ki shigo sannan zaki shigo?"  yatambayeta cikin yanayi naɗan jin haushi. Buɗe murfin motar tayi ta shiga ta zauna, ƙirjinta kuwa bugawa yake kamar zai fito waje.
Chapter 11 · 0% Book details