← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 91

Sashe 12

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka hau titi bata ɗago kanta ba,  wasa take da yatsun hanunta, yayinda ƙwalla suka cika idanunta, ita kanta batasan ƙwallan na menene ba.

Yana gama daidaita parking ɗin motar ya cire earpiece ɗin dake saƙale acikin kunnensa.

"Muje" ya faɗa yana maiƙoƙarin fita daga cikin motar.
Sai alokacin ta ɗago kanta ta kalli inda ya kawota,  batasan ina bane, saidai taga mutane nata shiga da fice a wajen,  haka ta fito daga cikin motar ta shiga bin bayansa, saida suka shiga cikin wajen sannan tafahimci cewa asibiti suka zo,  ji tayi gabanta ya faɗi, aranta tace  "Allah Yasa ba allura yakawoni ayi min ba."

Tafiya suka ɗanyi sosai itadai binsa kawai take kamar jela,  abakin wani ƙofa suka tsaya, knocking ƙofan yayi, daga ciki aka bashi izinin shigowa.

"Ki tsaya anan" yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin buɗe ƙofar, tana ganin shigewarsa taja ta tsaya haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.

Dr.Salees  Yana ganin Sooraj ya miƙe haɗe da soma haɗa kayan aikin dazai buƙata, atare suka fito daga cikin office ɗin.

Murmushi Dr. Salees Yayi haÉ—e da kallon Ziyada.

   "Ƴan mata yajikinnaki?" yatambayeta cike da kulawa.

"Da sauƙi!" tabasa amsa murya araunane, saboda tana ganinsa taji ƙirjinta ya tsananta bugawa.

Kansa yajinjina haÉ—e da cewa "Biyoni muje ko"

Da sauri takalli Sooraj saidai gani tayi idanunsa ba akansu yake ba, earpiece ne ma sanye akunnensa, ya wani haÉ—e fuska, hakan yasa cikin sanyin jiki tabi bayan Dr. Salees.

Akan wani ɗan gado ta zauna, yayinda Dr.Salees dakansa ya soma warware mata bandage ɗin dake nannaɗe akanta, yana gama cirewa ya ɗauki auduga haɗe da ɗan ɗiga wani farin ruwa mai ɗauke da sinadarai akai, hanunsa ya sanya ya kama goshinta  ahankali yasoma goge ciwon da audugan dake hanunsa, wani irin ƙara tasa haɗe da cije laɓɓanta,   sake riƙe kanta yayi cike da kulawa yace.   "Sorry da zafi ko? ki nutsu awanke miki hakan shine zai sa ciwon ya bushe"

Sake sakin wani ƙara tayi haɗe da soma ƙoƙarin ƙwace kanta daga hanunsa, sosai takejin zafin ruwan dayake sawa yana goge ciwon,    sake kama kannata yayi da ƙarfi, haka yashiga wankewa, ita kuwa banda kuka babu abun da takeyi, duk yanda taso ta ƙwace kanta ta kasa,  saida ya wanke ciwon tsab sannan ya sake naɗa mata wani sabon bandage ɗin.   kallon innocent face ɗinta Dr. Salees Yayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
"Sarkin raki, sai ki tsayar da kukan hakanan tunda angama" 

Harsuka fito daga cikin  ɗakin Ziyada bata daina zubar da hawaye ba,  gaba ɗaya idanunta sunyi ja, fuskarta kuwa duk yayi face face da ruwan hawaye.   Wasu magungunan Dr. Salees yabata sannan suka bar cikin asibitin.

Kamar yanda suka zo haka suka tafi babu wani wanda yace da ɗan uwansa ƙala,  gaba ɗaya hankalinsa nakan tuƙin dayake, ahankali yake ɗan kaɗa kansa, sosai yake enjoying cool music ɗin dake tashi acikin earpiece din dake saƙale acikin kunnensa.    Duk abun da takeyi yana lure da ita.  Sauƙa yayi daga kan titi haɗe da ɗan gangarawa gefen hanya, tsaida motar tasa yayi haɗe da ɗaukan goran ruwa ya kafa akan bakinsa,    sauƙe goran ƙasa yayi haɗe da fitar da wani dogon numfashi.

"Kukan me kikeyi?" yajefo mata tambayar da bata taɓa zato ba.

Ɗago kanta tayi ta kallesa, daidai lokacinne kuma wani guntun hawaye dake maƙale acikin idanunta, yasamu daman gangarowa.

A fakaice ya kalleta ta gefen idanunsa...  "Inaganin lokaci yayi daya kamata ki koma ga iyayenki, saboda haka zan ajiyeki anan peter zaizo saiki nuna masa garinku zai kaiki gida" yafaɗi haka cikin halin ko inkula yana mai latsa iphone 11 pro ɗin dake riƙe a hanunsa.

Hawayene suka shiga gangarowa daga cikin idanunta kamar an buÉ—e famfo, murya araunane tace.

"Bansan kowa ba, bani da kowa sai mahaifina wanda kwata kwata bai ɗaukeni a matsayin ƴarsa ba, tun farko na fara rayuwata ne acikin ƙunci, bansan wani abu waishi ɗan ɗanon farinciki ba,  kataimakeni banaso rayuwata ta salwanta!" tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.

Tunda tafara maganan bai ɗago ya kalleta ba baikuma daina abun dayakeyiba, sai ayanzune ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake...   "Wani irin duhu ne acikin rayuwarki da har kika zaɓi salwantar da kanki? wacece ke?"  yatambayeta batare daya ɗaura idanunsa akan ta ba.

Hawayen da kebin kan kumatunta ta sanya hanu ta share.

"Nima bansan koni wacece ba, saidai kawai nasan tsananin duhu ne ke bibiyar rayuwata" tafaÉ—i haka tana mai sharce hawayen dake kan fuskarta.

Sai alokacin ya ɗago idanunsa ya kalleta, gaba ɗaya idanunta sunyi jajur dasu,  bai sake ce da ita wani abuba ya tada motar suka bar wajen.    Harsuka isa gida bata daina sheshsheƙan kuka ba.

Yana shiga cikin ɗakinsa ya zauna akan gado haɗe da sanya hannayensa ya dafe kansa,  baisan meyasa yakejin son taimakon yarinyar acikin ransa ba, sai dai tawani ɓangare na zuciyarsa bata aminta da abun dayake ƙoƙarin aikatawa ba,  sam bayaso wata ko wani su shigo cikin rayuwarsa, amma kawai yana ganin zaiyi abun daya dace.

** ** **

Ajiyar zuciya yasauƙe akaro na barkatai haɗe da jawo trolly ɗin dake gefensa, tun adaren jiya ya gama shirya kayansa, ƙarfe 6 na yamma jirgin da zai hau zuwa Abuja zai tashi, kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa yayi ƙarfe 5:20 na yammaci dai dai, ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da fitar da numfashi daga bakinsa.   Jan ɗan ƙaramin trollyn nasa ya yi haɗe da ficewa daga cikin ɗakin.

Tsayawa yayi abakin ƙofar haɗe dayin knocking.  Kamar dama jira ake yayi knocking ɗin aka buɗe ƙofar.

Ganin ta buɗe ƙofar ne yasashi juyawa yasoma tafiya, batare da yace da ita wani abuba. Ganin haka yasa ta fito jikinta asanyaye tashiga bin bayansa.

Ganin yana ƙoƙarin shiga cikin motar yasanya itama tashiga ta zauna haɗe da takurewa waje ɗaya. 

Ga mamakinta sai gani tayi yashiga gidan baya ya zauna yayinda Peter ya zo yashiga mazaunin driver. 
Tafiya sukayi mai ɗan nisa kafun suka isa inda zasu,  baki hanci da ido duk ta buɗe tana ƙarewa wajen data tsinci kanta aciki kallo.  A hankali tafara bin mutanen dake ta hada hada a wajen da idanu ɗaya bayan ɗaya,  yawancin jama'ar dake wajen ɗauke suke da ƴan akwatunansu, yayinda wasu kuwa ke tsai tsaye.

"fito muje" Sooraj yace da ita yana maiƙoƙarin cire sit belt ɗin dake jikinsa. 
Tana biye dashi abaya sai wurga idanunta takeyi takota ina,  daga bayanta kuwa peter ne ke riƙe da ƴar jakan Sooraj,  tunda suka shigo cikin wajen, idanun yawancin mutane musamman ƴan mata ya dawo kan Sooraj,  suna ƙarasowa wajen ana sanar da cewa matafiya Abuja su shirya jirginsu yakusa tashi.   Tsayawa daga tafiyar da yakeyi yayi haɗe da juyawa ya kalli peter.    "Kawuce gida kawai peter sai munyi waya"  yafaɗa yana duban lokaci a gogon dake hanunsa.

Kai Peter ya jinjina alaman gamsuwa haÉ—e dayi masa Allah Ya Kiyaye hanya.

Pass yaciro daga cikin aljihunsa guda biyu ya miƙa mata ɗaya, amsa tayi tana mai kafesa da ɗara ɗaran idanunta.

Suna zuwa bakin ƙofar shiga yanuna pass ɗinsa, ganin abun da yayi yasa itama ta nuna ƴar takardan daya bata, dan batasanma takardan ko ta mecece ba, sannan aka barsu suka wuce.

Idanu ta ware tana bin jiragen dake wajen da ido, tunda take aduniarta bata taɓa ganin jirgi ido da ido ba sai ayau, hakanne yasa take ganin abun kamar almara,   direct inda jirginsu yake ya nufa,  har yaje kusa da matattakalar jirgin ya juyo donyi mata magana, amma abun mamaki bai ganta abayansa ba,  ɗan kalle kalle ya somayi, can ya hangota tsaye tana ta kallon jirage. (Like ƙawata hauwa lokacin da ta fara zuwa airport.Lol)   takaicine ya turnuƙeshi,  nufar inda take yayi, yana zuwa ya kamo hanunta, haɗe da turata gabansa, suka soma tafiya,   saida suka kawo ƙofar shiga jirgin, ta tsaya tana kallonsa lokaci guda idanunta sukayi raurau dasu, zuciyarta ta karye, wani tunanine yashiga yawo acikin ranta.   Da Kyawawan idanunsa ya kalleta, aƙufule yace. "Wuce muje!"   

Kasa koda motsa ƙafafunta tayi, tsanin tsoro takeji, bazata iya taka matattakalan ba.

Kamar yasan abun datake tunani kenan, ganin tana masa wasting time yasa ya kama hanunta suka soma haura matattakalan.

Direct  ɓangaren Business class suka nufa,  suna shiga ya nufi  inda kujeransa yake ya zauna wacce take kusa da window,  tsaye tayi takasa zama sai raba idanunta take, abun kamar amafarki wai yau itace acikin jirgi.   Ganin ta tsaya mai aka yasa shi ɗago da kansa ya harareta,  aibatasan lokacin da ta zauna akan kujeran dake kusa danasa ba.   Sit belt ya ɗaura ajikinsa, haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujera, kana ya lumshe idanunsa.   Gaba ɗaya Ziyada amatuƙar tsorace take, jitake kamar tazama tsuntsuwa ta fire.  Lokacin da aka soma announcement  cewa kowa ya ɗaura sit belt ɗinsa,   ɗan ranƙwafowa kusa da ita yayi, har suna iya jiyo hucin numfashin juna, sit belt ɗinta ya ɗaura mata, kana yakoma ya kwanta ajikin kujeransa, sannu ahankali jirginsu ya ɗaga sararin samaniya.

Tsananin sanyin AC'n dake ratsa cikin jirgin, shine dalilin da ya sanya tatakure jikinta waje É—aya, sam bata saba da sanyiba ko kaÉ—an.

   *Vote Me On Wattpad*
      @fatymasardauna

 
#arrogant
#fantasy

[4/7, 12:02 PM] fatymasardauna: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

                *Wattpad*
          @fatymasardauna

     *Chapter 11*

Tunda jirgin su ya ɗaga bai buɗe idanunsa ba har jirgin nasu ya sauƙa a NNAMDI AZIKWE Internation airport. Buɗe idanunsa yayi a hankali tare da  zare sit belt ɗin dake jikinsa, dubansa ya kai zuwa gareta, wani babban abun mamaki ganinta yayi tana bacci, fuskarta  ɗauke da wani bushashshen hawaye,  takaicinta ne ya sake kamashi, shi sam baisan ita wace irin bagidajiya bace ba, yanzu aɗan tafiyan da bai wuce 30 minute ba har ace tayi bacci ?

Hanunsa yasa ya zunguri kanta, da yake baccin nata baiyi nisa ba, hakan yasa ta buɗe idanunta, ta sauƙe ƙwayar idanunta a kansa.
Chapter 12 · 0% Book details