← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 91

Sashe 26

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗago kanta tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, ita kanta batasan awani yanayi take ciki ba, batasan meke damunta ba, hakan kawai tasamu kanta da cewa "Yayana ne, yau kusan kwana 10 banganshiba, kuma sannan inayawan jin faɗuwar gaba, inaso naganshi, bansan ina zanganshi ba!" wasu sabbin hawayene suka sake gangarowa daga cikin idanunta.

Ɗan kafeta da idanunsa yayi tare da ɗan yin murmushi,  hakanan yanayin yanda tayi maganar ya burgeshi, yanason mace mai shagwaɓa sosai.   "Kiyi haƙuri kinji Baby na, very soon yayanki zai dawo gareki"

Ɗago idanunta dake cike da ƙwalla tayi ta kalleshi, shima kallon nata yake, cikin wani irin yanayi dayake matuƙar kashe jikin mace, janye idanunta tayi daga kansa, tare da sunkuyar da kanta ƙasa, wasa ta shigayi da yatsun hanunta, aranta tunanin mai taimako ne kawai ke yawo,  duk bayan kowani bugun zuciarta ɗaya da tunaninsa take tafiya.     "Ziyadah!!!" yaƙira sunanta cikin wata cool voice.  Da sauri ta kalleshi cike da mamaki haɗi da yarinta tace.
"A ina kasan sunana?"

Murmushi yayi tare da cewa "Kamar yanda shaƙan numfashi da fitarsa keda matuƙar mahimmanci haka sanin sunanki yake da mahimmanci a wajena, saidai kuma ke ko sau ɗaya baki taɓa tambayar nawa sunan ba why?"

Wani murmushi tayi tare da cewa "To meye sunanka?"

Dariya yayi harsaida fararen haƙwaransa suka bayyana, sosai tambayar tata ta basa daria.  "Sunana FAROUK YUNUS HAMMA ni haifaffen ɗan garin Kano ne, domin har yanzu iyayena acan suke, aiki ne ya kawoni Abuja,  ina zaune a unguwar Wuse zone 2,  ke kuma sunanki Ziyadah kina zaune a unguwar Asokoro,  iya abunda nasani akanki kenan"

Dariya Ziyada tayi tare da kallonsa.  Shima kallonnata yayi, miƙewa tayi ta soma tafiya batare da tace dashi komai ba, da kallo ya bita harta ɓacewa ganinsa, ajiyar zucia ya sauƙe tare da lumshe idanunsa, yanason komai nata, musamman ƴan saffa saffan cute lips ɗinta masu kyau,  ya ɗan jima awajen kafun ya tashi ya shiga motarsa ya tafi......
***
Mas'oud ne keta kai kawo atangamemen falon Alhaji Mai Nasara, gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa, baisan ta ina zai fara ba, baisan taya Alhaji Mai Nasara zai ɗauki maganarsa ba.   
"Mas'oud yana ganka a atsaye? Bismillah kazauna mana" Inji cewar Alh. Mainasara, da fitowarsa kenan daga cikin ɗaki.  Jikin Mas'oud na rawa haka ya zauna akan kujeran tare da sanya hanu ya dafe kanshi.

⚠️NOT EDITED

(Kuyi manage banda enough charge)

*VOTE AND COMMENT*
[4/23, 12:04 PM] +234 814 541 1152: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

#romance

          *Chapter 22*

Jikin Mas'oud na rawa haka ya zauna akan kujeran, tare da sanya hanu ya dafe kanshi. 
Kallonsa Alhaji Mansur Mai Nasara yayi tare da cewa.  "Yanayin ka kaɗai ya tabbatarmin da cewa ba lafiya ba Mas'oud, meke faruwa? wani abu yasamu SOORAJ ne?" Alhaji Mansur Mai Nasara ya tambayi Mas'oud, fuskarsa cike da  damuwa.

Shiru Mas'oud yayi ya kasa cewa komai.   "Tabbas akwai matsala kenan" Inji cewar Alhaji Mansur.

Kai Mas'oud ya kaÉ—a alamar "Eh"

"Sooraj ne?" ya kuma tambaya.

Kai Mas'oud yasake kaÉ—awa alamar "Eh"

Hanu Alh.Mansur Mai Nasara yasanya ya dafe daidai saitin zuciyarsa, da ke ɗanyi masa zafi, gaba ɗaya acikin kwanakinnan haka yakejin faɗuwar gaba na ruskarsa, sannan gefe ga Ummu (Hajiya Sulaimiya) ta sameshi da zancen cewa tana yawan mugayen mafarkai akan ɗanta Sooraj.  Lallai tun da yaga Mas'oud a birkice haka, yasan matsalan babbace.   Hular kansa ya cire tare da ajeta agefe, har fargaban tambayar Mas'oud ɗin yake wani hali Sooraj din ke ciki, Sooraj shi kaɗaine ɗansa, sannan kuma yana matuƙar sonsa, sam bayason wani abu ya samu Sooraj, baisan yazaiyi ba, shi ya haifi Sooraj amma baisan Sooraj wani irin mutum bane, komai nasa aɓoye yake,baya bayyana duk wani sirrinsa. kullum cikin ƙunci da damuwa zaka ganshi, ada suna tunanin rashin zama da mace shine  matsalarsa, amma da sukayi masa aure, sai suka ga ashe wannan bashine matsalarsa ba. 

"Abba akwai matsala, Sooraj yana asibitin Lagos baida lafiya,  hari aka kai masa a gidansa dake Lagos!" Mas'oud ya faɗi haka idanunsa suna mai cikowa da ƙwalla. 

Arazane Abba yatashi daga zaunen dayake, tare da rumtse idanunsa. Muryarsa amatuƙar raunane yace.  "Kada kacemin wasu sun cutarmin da Sooraj, Mas'oud, zan iya jure komai, amma banda labari mummuna akan Sooraj, sun kashemin shi ko? " idanun Alhaji Mansur tuni sun ciko da ƙwalla. 

"Ka kwantar da hankalinka Abba, Sooraj bai mutu ba kawai dai yana da buƙatar kulawarku ne ayanzu" Mas'oud yafaɗi haka yana mai ɗan share ƙwallan daya zubo daga cikin idanunsa.

"Kayi mana booking flight Mas'oud, amma banaso Ummu ta sani, yau zamu tafi Lagos" Alh. Mansur yafaɗi haka cike da damuwa. 

Gaba ɗaya Alh. Mansur baya cikin nutsuwarsa, hankalinsa atashe yake sosai, baisan awani hali zaije ya taradda tilon ɗansa ba.  Babban damuwarsa ma itace Ummu, tabbas yasan idan Ummu taji to dole sai ciwonta ya tashi.
***
Yau aɗan acikin nishaɗi ta dawo gida, domin kuwa kwana biyunnan sosai Farouk ke ɗan ɗebe mata kewa, babban abun dayasanya ta shaƙu dashi, shine irin yanda yake kawar mata da damuwarta,  yana sakewa da ita sosai, sannan kuma yana bata dukkan kulawansa, ako da yaushe yakan kashe ayyukansa yazo gareta, hakan yasa tayi sabo dashi.
Gobe zasu kammala jarabawansu, sannan kuma agoben za'a basu hutu.   Fitowarta awanka kenan ta sanya wata doguwar riga ja, kitchine ta wuce, tsaye tayi agaban gas tare dayin shiru, damuwarta ne ta dawo sabuwa fil.  Motsinsa takeson ji acikin gidan, rashin jinsa da kuma rashin ganinsa yana damunta sosai, tanason koda ƙamshinsa ne taji, hakanan takeji ajikinta cewa baya lafiya.  Cikin rashin daɗin rai haka ta soya indomie taci sama sama. Tunda tayi sallah take aikin duba littafin Physics da zasuyi gobe.   Kamar kullum idan ta kwanta mafarkinsa kawai take, yauma hakance ta kasance domin kuwa gaba ɗaya shitake ta gani acikin mafarkinta, yanayin halin da take ganinsa acikin mafarkin sam baya mata daɗi.  

Ƙarfe goma daidai suka fito a exams, direct wajen assembly suka nufa.   Hutun 3 weeks kawai aka basu, duk da haka ɗaliban sunji daɗi sosai. 

Cikin sanyin jiki ta ɗago idanunta ta kalli Farouk wanda shima kallonta yake, gaba ɗaya idanunsa sunyi wasu narai narai dasu,  harshensa yasanya ya ɗan lashi kan lips ɗinsa.
 "Banason wannan hutun, kwata kwata  banason duk wani abu da zai nesantani da ganinki pretty na, da gaske nake inasonki har acikin zuciyata!!"       jin sauƙar kalaman nasa acikin kunnuwanta, ya sata jin tamkar aradu ce ta sauƙa,  idanunta dake kan fuskarsa ne suka kawo ƙwalla,  "So......na!!" tafaɗa murya asarƙe..

Kallonta shima yayi cikin wani irin yanayi,  ɗan matsowa kusa da ita yayi, tare da kai hanunsa ya kama nata hanun.      "Nasan ke ƙaramar yarinyace, sannan kuma bakisan menene so ba, dan inasonki bawai yana nufin zan cutar dake bane, ban taɓa jin soyayyar wata mace  azuciyata kamar yanda nakejin taki soyayyarba, Inasonki Ziyadah, dan Allah Kada ki ƙini, tun ran da naganki nakamu da Sonki, har abada kuma zan ci gaba da sonki, namiki alƙawari  bazan taɓa rabuwa dake ba!!" Yaƙare maganar cikin wata murya mai sanyi, yayinda gaba ɗaya yanayin   idanunsa suka sauya.    Hawayene suka gangaro daga idanun Ziyada, karo na farko arayuwarta da wani yafurta mata kalmar SO, karo na farko arayuwarta da wani namiji ya tsaya yayi mata magana cikin kulawa har haka,  saidai kuma sam bata fahimci kalamansa ba.  Ganin yanda hawaye yake fita daga idanunta ne ya sanyashi, kai hanunsa fuskarta da niyyar share mata hawayen, da sauri taja da baya, tare da ƙwace hanunta dake cikin nasa.   Juyawa tayi cikin yanayi na gudu gudu sauri sauri tabar wajen, ƙiran sunanta Farouk yake amma ko waiwayosa batayi ba, balle yasa ran tsayuwarta,   ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, tare da lumshe idanunsa da suka soma sauya kala, har acikin jininsa yana jin son yarinyar, komai nata me kyau ne, kallonta, tafiyarta, nutsuwarta,  sau babu adadi yakan samun kansa cikin wani irin yanayi idan yana tare da ita, da ƙyar ya iya shiga motarsa yabar cikin makarantar.

Ziyada kuwa direct inda su Nasmah ke zaune ta nufa, tana zuwa ta faÉ—a kan cinyar Shukrah, tare da rumtse idanunta.

Kallon kallo Nasmah da Shukra suka shiga yiwa juna, cike da tsantsar kulawa suka haɗa baki wajen tambaryarta.  "Lafiya Ziyada? meke damunki?"  duk waƴannan tambayoyin sunyi mata shine alokaci guda.

Ɗago kanta dake kan cinyar Shukrah tayi, gaba ɗaya hawaye ya ɓata mata fuska.     Ganin haka yasa suka ƙara ruɗewa.

"Kuka Ziyada, meke faruwane?" Inji cewar Shukra dake ƙoƙarin share mata hawaye.

Kanta taɗan girgiza cikin muryarta mai ɗauke da rauni tace.  "Bansan me yake nufi ba Shukra, bansan menene So ba, bansan ya akeyinsa ba, gaba ɗaya ya juyarmin da tunanina, dan Allah Shukra ki faɗamin menene SO?" taƙare maganar tana mai sakin ɗan guntun hawayen dake maƙale cikin idanunta.

Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da ɗanyin murmushi.   "Dama nasan haka zata faru Ziyada, saboda tun randa yasake dawowa nasan ya kamu da sonki ne,  So ba ƙarya bane ba Ziyada, akwaita azuciyar kowa, kuma sannan Allah Ne ke halittarta aduk inda yaso akuma lokacin da ya so, zaki gane kin kamu da son mutum ne kaɗai,  ta hanyar yawan tunaninsa,  yawan damuwa dashi, zai dinga faɗo miki arai aduk wani halin da kike ciki, ƙunci, ko daɗi, amma ni aganina Farouk baida aibu, domin irin Farouk ko wacce mace zataso yin soyayya dashi, gayen yayi tako ina" Shukra taƙare maganar tana sakin murmushi.
Chapter 26 · 0% Book details