← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 91

Sashe 15

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr. Haisam na fita daga cikin ɗakin tasoma jin ƙiran sallan Magriba, wanda yake fitowa daga cikin masallacin dake gefen asibitin.

Kallon ƙofar da Dr.Haisam yace mata nanne banɗaki tayi,  ahankali tatura ƙofar tashiga, banɗaki ne mai kyau da tsafta,  gaban sink taje ta ɗauro alwala sannan ta fito.

Tsayawa tayi tana nazarin yanda za'ayi tayi sallah babu sallaya, duk da cewa rayuwar rashin ƴanci da kuma ƙauyanci tayi, hakan baisa ta zamo mace mai wasa da sallah ba, duk da bawani ilimi take dashi akan addini ba, amma tana kyautata zaton wajen bazaiyi sallah ba idan har ba a shumfuɗa sallaya ba,   kallonsa tayi yananan dai a yanda yake, ahankali ta ƙarasa jikin gadon, aƙalla ta ɗauki sama da 7 minute tana kallonsa, jitayi duk ƙwalla suncika idanunta,   buɗe ƙofar ɗakin tayi ta fice.   Tana fita daga ɗakin taga wata nurse zata wuce, da sauri ta ƙarasa gareta haɗe da gaisheta. 

Amsa mata gaisuwar nurse ɗin tayi tana mai ƙare mata kallo.

"dama Sallah zanyi shine kuma banda sallaya ko zaki É—an aramin" Ziyada ta tambayi nurse É—in tana mai sanya mata fuskar tausayi.

"Biyoni muje ki amsa" nurse ɗin tafaɗi haka tana mai ci gaba da tafiyarta.   Sallaya hadda Hijab nurse ɗin ta bata, ta kumace ta riƙe a wajenta zuwa gobe,  godia Ziyada tayi mata sannan tadawo ɗaki, shumfuɗa sallayan tayi  haɗe da tada Sallah.   Sosai ta jima a sujjadanta na raka'an ƙarshe, addu'a tayi sosai akan Allah yabawa Mai taimakonta lafiya.   "Mai Taimako" shine sunan da Ziyada ta raɗawa Sooraj acikin zuciyarta.  Tananan zaune akan sallayan har aka ƙira sallan Isha..   Shima a sujjadan ƙarshe saida tajima tana addu'a kafun ta ɗago.  Shiru haka ta zauna akan sallayan haɗe da jingina bayanta ajikin bango.  Har ƙarfe 9 Ziyada na zaune agefen gadon,  sannu ahankali yunwa ke ƙwaƙulan cikinta,  gyan gyaɗi ta fara mintuna kaɗan bacci ya ɗauketa.  Cikin dare     Sanyin AC ya dameta, tashi tayi ta lulluɓe jikinta sannan ta koma bacci.

Washe Gari.

Tunda ta tashi da asuba tayi sallah, wani bacci yasake ɗaukanta, ba ita ta farka ba sai wajen ƙarfe 8 na safiya. Ban ɗaki ta wuce taje  ta wanko fuskarta, tana zama akan kujera Dr.Haisam ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, gaishesa tayi cike da girmamaw,   fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata.

Checking É—in Sooraj ya sakeyi, yaji daÉ—in ganin komai Normal kuma zai iya farfaÉ—owa ako wani lokaci.

Hannayenta ta ɗaura akan kumatun ta haɗe da kafesa da manyan manyan idanunta, kyakkyawar fuskarsa take kallo, babu wani abu dayafi saurin ɗaukar hankali akan fuskarsa kamar yalwataccen sajen sa, wanda yake baƙi siɗik, ga zara zaran eye lashes ɗinsa da suke a mimmiƙe, sosai suka ƙarawa fuskartasa kyau, hakan yasa bata taɓa gajiyawa da kallonsa...

Wasa Wasa har ƙarfe 5 na yamma Sooraj bai farfaɗo ba, haka Ziyada ke zaune awajensa, batare da ta ci wani abu wai sunansa abinci ba, ruwa kawai take ta zubawa cikinta.  Tun yunwar na damunta har tazo ta daina ji, yanzu bata da wani buri daya wuce taga Mai Taimakonta ya buɗe idanunsa.

9:30 pm  Babbar yatsan ƙafarsa ta dama ne ta soma motsawa  sai kuma yatsun hanunsa,   sannu sannu bugun zuciyarsa ta dai dai ta, yayinda cikin sakannin da basu wuce huɗu ba brain ɗinsa ta soma aikin.

Ahankali ya soma buɗe idanunsa,  da kaɗan kaɗan yake ware idanun nasa hakan yasa ya soma ganin komai dishi dishi. Sannu ahankali idanun nasa suka washe, kallon saman ɗakin daya gansa aciki ya soma yi.  Sake ɗan lumshe idanunsa yayi, komai daya faru ya dawo cikin kansa,  ɗan yunƙurawa yayi ya tashi zaune haɗe da jingina bayansa da pillow,    juyo da kansa yayi zuwa gefen damansa,  idanunsa suka sauƙa akanta, tana zaune akan sallaya ta jingina bayanta da kanta a  jikin gadon da yake, bacci takeyi cikin yanayi na takura, da dukkan alamu bata shiryawa baccin ba ya ɗauketa, domin kuwa hadda goran ruwa riƙe ahanunta, ƙurawa fuskarta idanu yayi,  hango wasu  zanen busassun  hawaye  yayi  kwance akan fuskarta,   kallon yanda ɗan ƙaramin bakinta ke ɗan buɗe yayi.  Janye idanunsa yayi daga kanta, haɗe da ɗan tattaro ragowan ƙarfin daya rage masa ya sauƙo daga kan gadon.

Ƙofar da yake tunanin nanne toilet ya nufa, yana shiga ya soma rage kayan jikinsa.  Kunna shower yayi ya tsaya ruwa ya dake shi sosai.   Dogon wandonsa kawai ya maida batare da ya sanya rigar shi ba ya fito daga cikin toilet ɗin.

Zama yayi abakin gadon haɗe da sanya hanu ya dafe kanshi dake yi masa ciwo sosai, hakanan yakejin shi  wani iri,  gaba ɗaya babu wani isashshen kuzari ajikinsa, yasan hakan kuma duk yana daga cikin sharrin Alluran da yayiwa kan shi ne.

Kallon shi  ya kuma maidawa zuwa gareta, har yanzu tananan tana wahalallen baccin daya ɗauketa,  gaba ɗaya jikinta a tukuikuye yake da Hijab,  tashi yayi ya ƙarasa jikin window'n ɗakin, hanu yasa yaɗan buɗe labulen window'n kaɗan, gani yayi gaba ɗaya duhu ya mamaye sararin samaniya,  hanu yakai yashafi aljihun wandon dake jikin shi,  atunanin shi wayar shi na tare da shi.  sai dai kuma saɓanin haka yaji shi  wayam, ɗan kalle kalle yasomayi acikin ɗakin ko zai hangota amma baiganta ba,  komawa yayi ya zauna akan gadon yana mai lumshe idanunsa, saboda wani juwa da yaji yana neman ka da shi.   Aƙalla yakusan mintuna goma idanunshi suna  lumshe, jin da yayi juwan yasoma lafawa ne yasanya ya tashi tsaye, inda take zaune ya nufa, tsayawa yayi akanta ya kasa ta ɓuka komai.  Ɗan ranƙwafowa yayi ya ɗagota caɗak,  kan gadon da aka ajiye musamman don taya majinyaci kwana ya ɗaurata,   a hankali ya zare hijab ɗin dake jikinta ya ajiye mata shi agefe.  Ziyada da baccinta yayi nisa sam batasan meke faruwa ba, saima ƙara gyara kwanciarta  da tayi, sakamakon jin ta samu sauyin makwanci.     Komawa kan nashi gadon yayi ya kwanta,  lumshe idanunsa yayi bawai kuma don yanajin bacci ba saidan kawai babu wadataccen ƙarfi ajikinshi..

Yatsun ƙafanta ya ƙurawa ido, azahirin gaskiya yatsunnata yake kallo, amma kuma hankali da tunaninsa ba agareta suke ba, yayi nisa acikin wani tunanin daban, baiso ace ya biyewa zuciyarsa ba, baiso ace ya kasa haƙurin ɗaukar ƙaddaransa ba,  duk da cewa shiɗin mai raunine amma yana fatan dacewa anan gaba, saidai aduk sanda yayi wannan tunanin sai wata zuciyar ta gargaɗesa da kada ya yaudari kansa, dolensa haka yake haƙura  ya watsar da tunnin acikin ransa.

Buɗe gajiyayyun idanunta tayi, ganin haske tarwal acikin ɗakin yasa ta tashi aɗan zabure, kallonta takai wajen window gani tayi har hasken rana yasoma bayyana ta jikin window'n.  Da sauri ta zuro ƙafafunta daga kan gadon,   dai dai lokacinne kuma idanunta suka sauƙa akansa, yana kwance ya bata baya.

Sake waro idanunta tayi haɗe da mutsutstsukasu  atunaninta ko gigin bacci takeyi ganinsa da tayi babu riga, bayan koda zata kwanta tabarshine sanye da riga ajikinsa.        "Kodai likita ne yazo ya cire masa riga'n tana bacci bata sani ba?" tambayar da tayiwa kanta kenan.

Ahankali ta sauƙo daga kan gadon, cikin sanɗa tataka harzuwa inda yake kwance.

Kanta ta É—aura ajin gadonnasa, lokaci guda idanunta suka kawo hawaye murya araunane tace.

"Mai Taimakona Allah yabaka lafiya, tausayinka nakeji sosai, banso wani abu ya sameka!" taƙare maganar daidai lokacin da hawayen dake cikin idanunta suka samu daman gangaro zuwa kan fuskarta,  daidai lokacinne kuma shima da tun tashinta zuwa yanzu yanajin abun da takeyi ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan....

     *Vote Me On Wattpad*
        @fatymasardauna 

#love
#fantasy
[4/7, 12:02 PM] fatymasardauna: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

             *WATTPAD*
      @fatymasardauna

#romance

            *Chapter 13*

Wani numfashi mai ɗumi ya fesar daga bakinsa, haɗe da maida idanunsa ya rufe,  kalamanta ne suka shiga yi masa yawo acikin kunnuwansa, ji yayi tsikar jikinsa na tashi, hakanne ma yasa ya kasa yin koda kyakkyawan motsi ne.

Ban ɗaki ta wuce ta je ta ɗauro alwala, sam bata san ya akayi bacci ya ɗauketa ba, taso ace bata makara ba, kasancewar yanzu har hasken rana ya bayyana.   Tana idar da sallan ta gyara zamanta akan sallayan,  sai alokacinne ta tuno da cewa aƙasa ta kwanta ba akan gado ba, "To kenan ya akayi ta koma kan gado?" tambayar da tayiwa kanta kenan, ƙaran buɗe ƙofar ɗakin da akayi ne ya katse mata tunaninta.   Dr.Haisam ne yashigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa tayi haɗe da gaidashi.  Fuska asake shima ya amsa mata gaisuwar. Ƙarasawa gaban gadon da Sooraj ɗin ke kwance yayi.    "Ya jikinna ka dai?" Dr.Haisam ya tambayi Sooraj wanda har yanzu bai sauya kwancia daga juya bayan da yayi ba.

Ziyada nashirin ce da Dr.Haisam bai farfaÉ—o ba, taji muryarsa ta doki dodon kunnenta.

"Da sauƙi!" Sooraj ya bashi amsa ataƙaice, sai alokacin ya juyo ya fuskanci Dr.Haisam ɗin.

"Masha Allah dama kullum haka mukeso, yanzu babu wani inda yake maka ciwo?" Dr.Haisam yatambayeshi cike da kulawa.

"Babu" ya bashi amsa ataƙaice.

"Masha Allah zamu baka sallama zuwa anjima, amma yana da kyau ka riƙa kulawa da lafiyarka, kasan fa lafiya itace komai arayuwa, sai da itane mutum yake sanin daɗin rayuwa, saboda haka kakiyaye abun da zai cutar dakai!"

Kai kawai Sooraj ya jinjina alamar yaji, sam baison magana mai tsawo.

Kallon Ziyada dake zaune tana kallonsu Dr.Haisam yayi. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace. "Congrat ƴar ƙaramar ƙanwa, da alama brother ɗinki ya samu lafiya" 

Murmushin daya bayyana kyawun fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, hakanan taji wani irin sanyi acikin ƙirjinta.   Dr.Haisam na fita ta ɗago da kanta takai dubanta ga Sooraj wanda yake ta murza fatan hanunsa,  kallon yanda jijiyoyin jikinsa suka fito sukayi raɗa raɗa tayi, gani tayi ya sanya haƙoransa ya danne lip ɗinsa na ƙasa,  tamkar wani wanda yakejin wata azaba ta daban,  tashi tayi daga kan sallayan cikin sanɗa tashiga takowa zuwa inda yake.
Chapter 15 · 0% Book details