← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 91

Sashe 65

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannu ahankali ƙiran sallan assalatu da akeyi ya ratsa cikin kunnuwansa,  ahankali ya ware manyan idanunsa, ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe,  tare da ɗan cije laɓɓansa sakamakon yanda yaji ƙafafaunsa sun ƙage waje guda, hakan ya faru ne kuma saboda jimawa da sukayi anannaɗe,   ƙasa ya ɗanyi da idanunsa tare da duban fuskarta, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali da natsuwa, yayinda take ta faman sauƙe ajiyar zuciya akai akai,  saurin ɗauke idanunsa wanda suka sauƙa akan breast ɗinta yayi,  tare da ɗan yunƙurawa ya tashi da ita ajikinsa.
Ahankali ya shumfuɗeta akan gado,  tare da juyawa ya nufi hanyar bathroom.
Zip ɗin wandon jeans ɗin dake jikinsa ya zuge, tare da zame wandon nasa yayi ƙasa,
daidaita tsayuwarsa yayi agaban shower, tare da ɗan murɗa makunnin shower'n,  sassanyar  ruwan dake fitowa acikin shower'n ne ke dukan jikinsa, sannu ahankali yakejin wani irin sanyi na ratsa gaba ɗaya jikinsa, cikin nutsuwa yayi wanka tare da ɗauro alwala,  farar bathrobe ya sanya ajikinsa kana yafito daga cikin toilet ɗin.
Kaitsaye gaban sif ɗin kayansa ya nufa,  wani black jeans tare da white long sleeve shirt yasanya, kana ya fesa turarensa mai daɗin ƙamshi, wani ƙaton darduma ya shumfuɗa aƙasa, inda ya gabatar da sallah  raka' biyu, yana idarwa yaji ana ƙiran sallan Asuba a masallaci, shafa addu'an da yakeyi yayi tare miƙewa tsaye,  har yakai bakin ƙofar fita daga cikin ɗakin, sai kuma yaɗan tsaya tare da juyowa ya kalli inda take, haryanzu baccinta take sha cikin kwanciyar hankali, handle ɗin ƙofar ya murɗa kana ya fice daga cikin ɗakin.  

7:30 am.
Ahankali take buɗe idanunta wanda sukai nauyi kana kuma sukai ja, sake ɗan lumshe idanun nata tayi sakamakon sihirtaccen ƙamshinsa daya samu daman kawowa hancinta ziyara, ahankali tatashi zaune daga kan gadon, ɗakin tasoma bi da kallo, kana ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya, ahankali ta zuro da ƙafafunta ƙasa, wanda suka sha jan lalle gwanin ban sha'awa, direct inda trolly ɗinta yake ta nufa, zuge zip ɗin jakar tayi tare da fito da wata maroon ɗin abaya gown mai kyau wanda aka ƙawata jikinta da adon ƙyalƙyali, cikin sauri ta shige toilet.
Tsayawa tayi tana me ƙarewa haɗaɗɗen toilet ɗin kallo, komai dake cikinsa nead, sosai aka ƙawata toilet ɗin, gaba ɗaya toilet ɗin ƙamshi yake, ahankali ta ƙarasa jikin wani glass wanda aka jere kyawawan bathrobe da kuma towels acikinsu,  rigar dake hannunta ta ajiye tare da zage zip ɗin rigar,  ɗaya daga cikin towel ɗin ta ɗauko  ƙoƙarin ɗaurawa ajikinta take, daddaɗan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa ne ya daki hancinta, jingina bayanta tayi da jikin bango tare da lumshe idanunta, sosai ƙamshin nasa ke kashe mata jiki, ɗaura towel ɗin tayi ajikinta tare da ƙarasawa gaban bathtube ta haɗawa kanta ruwan wanka, cikin nutsuwa tayi wanka inda ta zura abaya gown ajikinta,  sosai rigar tayi mata kyau ta kuma amshi jikinta, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar bathroom ɗin tafito,  kaitsaye dressing mirror ta nufa, tsadaddun kayan shafansa ne suka cika gaban mirror'n, gwanin ban sha'awa,  hannunta takai ta ɗauki wani kyakkyawan kwalban turarensa dake kan mirror'n,  jujjuya kwalban turaren tayi ahannunta tare da sauƙe ajiyar zuciya,  nannaɗe dogon gashinta tayi tare da sanya ribbom tayi parking gashin atsakiyar kanta, nan tashiga kimtsa kan gadon, duk dama nead yake bai wani ɓaci sosai ba,  saida ta gyara komai dake cikin ɗakin, kana ta wuce toilet ta wankesa  tsab,  zama tayi akan gado haɗe da jingina bayanta da jikin gadon, lumshe kyawawan idanunta tayi sannu ahankali wasu daga cikin abubuwan da suka faru atsakaninsu jiya da dare suka soma dawo mata,  tabbas Ƙaddara tayi mata sauyi, Ƙaddara ta canza duk wani tunaninta, wasu irin sanyayyun hawayene suka samu damar gangarowa daga cikin idanunta, kwanciya tayi akan gadon tare da cusa kanta cikin pillow ta saki wani irin marayan kuka,
tayaya zata fara koyawa kanta zama dashi? wani abu takeji na daban acikin rai da zuciyarta dangane dashi.

Tunda yafita sallan asuba bashi yadawo gidan ba sai 8:30.

Ahankali ya tura ƙofar ɗakin yashiga,   Zieyaderh wacce take fidda sheshsheƙan kuka tana jin motsinsa tayi shiru tare da sake ɓoye fuskarta acikin pillow, hakanan wani ɗan banzan tsoronsa ya shiga zuciyarta, ko ƙaunar haɗa idanu dashi batasonyi ayanzu.

Sam baidamu da cewar waidon tana ɗakin bazaiyi abun da yakeso ba, hasalima ko inda take baikalla ba, tundaga bakin ƙofar ɗakin yashiga ɓalle maɓallan rigarsa, zuge zip ɗin wandonsa yayi tare da cire rigar jikinsa, cikin takunsa dake amsa amo yanufi gaban sif ɗin kayansa,   tamkar ƙirjinta zai fito waje haka takeji saboda tsoro, sake duƙunƙune jikinta tayi tare da ɗauke numfashinta tayi luf akan gadon kamar wacce ke bacci, ƙasa yayi da wandon jeans ɗinnasa, tare da cire wandon gaba ɗaya daga jikinsa, wani white towel ya ɗaura akan waist ɗinsa, kai tsaye ya wuce bathroom, tanajin motsin rufe ƙofarsa, tasaki wata kyakkyawar ajiyar zuciya. 

Ruwan wanka ya haɗawa kansa acikin bathtube inda ya cika turaren wanka aciki,  kwanciya yayi luf acikin bathtube ɗin yana me sauƙe ajiyar zuciya, sosai yakejin wani irin bacci na fusgarsa, wanka yayi kana yafito daga cikin toilet din, ƙamshin sabulunsa ne gaba ɗaya ya cika ɗakin,  wanda hakan ya narkar da zuciyar Zieyaderh dake kwance, cikin nutsuwa ya gama shafa body lotion ɗinsa, men crazy t-shirt black colour tare da pencil crazy jeans shima black colour yasanya, sosai kayan suka fito da natural white skin ɗinsa, suka kuma yi masa kyau matuƙa,   Duk abunda yakeyi tanajin motsinsa, amma saboda tsoro takasa koda kyakkyawan motsine.
 Yana gama kimtsa kansa ya nufi kan lallausan doguwar kujeran da ayanzu ta zame masa gado,  kwanciya yayi akanta yana me fitar da wani irin numfashi,  idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗesu ya sauƙesu akanta, ahankali yake bin jikinta da kallo, harya kawo idanunsa kan fararen ƙafafunta wanda aka ƙawatasu da zanen jan lalle, cikin nutsuwa yake kallon zanen lallen dake ƙafafunnata tamkar mai nazartar wani abu, azahirin gaskiya kuwa idanunsa ne kawai kekallon zanen, dan sam ƙwaƙwalwarsa ba zanen take kallo ba,  ayanzu damuwarsa tafi ta da yawa, yakanji kamar zuciyarsa zata tarwatse, sannan yakanji kamar ana buga masa guduma atsakar kansa, musamman aduk sanda ya tuno da cewa ita din matsayin mata take agaresa, yazaiyi da haƙƙin ta dake rataye a wuyansa? tayaya zai zama cikakken namijin da zai iya maidata cikakkiyar mace?  kwarai ya sani bazata iya ɗaukar rauni da damuwarsa ba.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da lumshe idanunsa, inama da ace Kaddara bata zamo silar haɗuwarsu ba, ya tabbata da duk haka bata faru ba, inama da ace wani namijin daban kaddara ta zaɓa mata ba shiba, tayaya zai fara fuskantarta da matsalarsa? lumshe idanunsa wanda suka soma sanja launi daga fari zuwa ja yayi tare da sakin zazzafar ajiyar zuciya, mintuna goma kacal da kwanciyarsa bacci ɓarawo ya saceshi.

Ahankali taɗan buɗe idanunta, sam babu wani ƙwaƙƙwaran motsi dake tashi acikin ɗakin, sai sautin ƙaran ac da kuma sautin numfashinsa dake fita ahankali, ɗan juyo da fuskarta tayi ta fuskanci inda yake kwance, ajiyar zuciya ta sauƙe ganin cewa yayi bacci, zuro da ƙafafunta ƙasa tayi tare da miƙewa tsaye, cikin takun sanɗa tanufi hanyar fita daga cikin ɗakin, murɗa handle ɗin ƙofar tayi ahankali kana ta fice.

Tana samun kanta acikin ƙawataccen falon nasa, tasaki wata irin narkakkiyar ajiyar zuciya, daidaita nutsuwarta tayi tare da zame ɗan kwalin dake kanta ta yafa bisa jikinta, duk da cewa tana matuƙar jin kunyan Ummi ayanzu, amma tanaga zama da Ummi'n zaifiyi mata daɗi akan tazauna shiru cikin miskilancinsa.  
Bakinta É—auke da sallama haka ta kutsa kanta cikin falon Oummu'n, zaune Oummu take akan kujera, yayinda Aunty Muhibbat kuwa ke kan dinning area tana haÉ—a abinci acikin basket.
Ganin Zieyaderh yasa Oummu faÉ—aÉ—a fari'arta.
Cikin ladabi haɗi da girmamawa Zieyaderh tayi ƙasa da kanta tare da durƙusawa har ƙasa tagaida Oummu'n,  fuska ɗauke da murmushi haɗe daso da kuma ƙauna Oummu ta jawota, tare da zaunar da ita akan kujeran da take.
Cikin kulawa Oummu ta tambayeta jikinta.
"Dasauƙi."
Tabawa Oummu'n amsa murya asanyaye,  ƙarasowar Aunty Muhibbat wajen yasanyata sauƙowa daga kan kujeran cikin girmamawa tagaida Aunty Muhibbat ɗin.
Fuska asake Aunty Muhibbat ta amsa mata tare da cewa.
"Yanzu nake shirin kai muko break fast, sai kuma gaki kin fito, wa yace miki amarya tana zuwa gaisuwa? ae saidai azo agaisheta." 

Mumushi Zieyaderh tayi cike dajin kunya tayi kasa da kanta, basket din abincin Aunty Muhibbata tamiƙo mata tare da cewa.
"Idan kina buƙatar wani abu waya kawai zakinayi amma kizauna aɓangarenki kinji, nan ɓangaren Oummu ne saboda haka sai angayyaceku kafun kuzo!." Cikin sigar wasa Aunty Muhibbat taƙarishe maganan.
Wani irin kunyane yasake rufe Zieyaderh, Oummu kuwa murmushi kawai tayi, karɓan basket ɗin tayi inda tamiƙe asanyaye ta nufi ƙofar dazai sadata da ɓangaren nasu,
da kallo Aunty Muhibbat ta rakata, aranta tana me ƙissima abubuwa da yawa, hakanan jikinta yafara bata wani abu dangane da SOORAJ, duk da cewa tunanin nata yayi gaggawa, amma dai tabbas zuciyarta nayi mata wani zargin na daban, lumshe idanunta tayi aranta tana cewa.
"Ya Allah Kasa kada tunanina ya zama gaskiya."

Hira suka shiga ɗan taɓawa kaɗan kaɗan ita da Oummu.
Chapter 65 · 0% Book details