← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 91

Sashe 25

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

                *SOORAJ*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain and motivate he mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

#romance

           *Chapter 21*

Jini ne ke fitowa daga jikinsa yana malala akan white tiles ɗin da ya mamaye gaba ɗaya falon.   Wasu ƙattin maza guda biyune suka fito daga maboyarsu, wato bayan labule kenan inda suka ɓoye, ko wannensu fuskarsa sanye take da mask, dukansu suna sanye da baƙaƙen kaya, sannan kuma kowannensu ahanunsa ɗauke take da bindiga, ɗan ranƙwafowa  ɗayan yayi tare da ɗaura hannunsa adai dai saitin hancin Sooraj, jin baya numfashine yasa ya kalli ɗayan ɗan uwannasa.  Alama yayi masa da ido akan su tafi aiki ya kammala,  babu wani ɓata lokaci, aƙagauce suka fice daga gidan..   10 minute da tafiyarsu saiga ƴan sanda har mota biyu.  Alhaji Ilyass (maƙocin Sooraj)  dake laɓe jikin gate ɗin gidansa, yana ganin ƴan sanda ya ƙaraso garesu haryana jin tuntuɓe, aruɗe yace.   "Yauwa ranka ya daɗe kun ƙaraso? Ni ne nan naƙiraku, tabbas naji ƙaran harbin bindiga awannan gidan har sau biyu, saboda haka duk yanda akayi babu lafiya!" yafaɗi haka yana me sharce gumin dake yankowa ta gaban goshinsa, gaba ɗaya atsorace yake, ƙiran ƴan sandan ma da yayi baƙaramin Jahadi yake ganin yayi ba, saboda tsorone cike fal aransa. 

Cike da rashin tsoro haka ƴan sandannan suka rarrabu, kowanne daga cikinsu ya saita kunamar bindigarsa, ƙiris sukejira su saki harsasai,  haka sukayi cikin gidan Sooraj,  ahankali suka tura ƙofar falon suka shiga, ganin bakowa acikin falon yasa suka shiga ƴan dube dube, yayinda wasu daga cikinsu suka nufi bedrooms ɗin dake cikin falon, ɗaya bayan ɗaya haka suka shiga suna dubawa, ɗaya daga cikin ƴan sandan ne idanunsa suka sauƙa akan jinin dake kwance ya daskare akan tiles, jawo ogansu yayi ya nuna masa jinin,  aikuwa suna leƙa bayan kujera sukaga mutum yashe aƙasa, gaba ɗaya jini ya ɓata jikinsa, aɗan razane sukayi kanshi, daidai lokacin sauran ƴan sandan suka dawo cikin falon.   "Sir gaba ɗaya fa mungama duba gidannan bakowa acikinsa" suka faɗa suna mai kallon Sooraj dake yashe aƙasa.   Shiru ogannasu yayi tare da ciro wayarshi acikin aljihunsa ya danna ƙiran asibiti.  Kallon sauran ƴan sandan yayi yace subi hanya duk wanda suka gani sukamashi.  hakan kuwa akayi duk suka watse yazama saura mutane ƴan ƙalilan.  Ƙarar jiniyan ambulance ne yacika gidan.    Ɗaukan Sooraj akayi aka sanyashi acikin ambulance ɗin, suka wuce asibiti.
Babban asibitin dake cikin garin Lagos suka wuce dashi, direct ɗakin bada taimakon gaggawa aka nufa dashi, duk da cewa basu da tabbacin cewa yana da rai ko bayidashi.   Dr. Femus shine mutumin daya fara cire handglobes ɗin dake hanunshi, kallon sauran abokan aikinnasa yayi yace.  "He is dead!"   Jikinsune gaba ɗaya yayi sanyi, saboda haka suma suka soma ƙoƙarin cire handglobes ɗin dake hanunsu.

Dr. Fawwaz da bai yarda da abunda Dr.Femus yace ba, yaɗan matso gaf da Sooraj ɗin tare da kama hanunsa ya riƙe, sannan ya ɗaura kansa adai dai saitin ƙirjinsa inda zuciarsa ta ke.  Da sauri ya ɗago da kansa tare da cewa "Bai mutu ba, zuciyarsa na bugawa, muyi sauri mucire masa bullet ɗin dake jikinsa!"   nan suka duƙufa aikin cire bullet ɗin dake jikinsa.    Sunyi masa gwaje gwaje sosai,  inda suka tabbatar da cewa bai mutu ba, amma kuma su kansu basu san awani condition yake ba, abu ɗaya suka sani shine, zai iya wucewa tacan zai kuma iya tashi, duk wannan na Allah Ne.  Duk abun daya kamata suyi mishi sun masa, sannan suka killaceshi awani ɗaki na musamman. 
***
Gaba ɗaya ta hargitsa gadon, sai juye juye take, ta ya mutsa ko ina, gashin kanta gaba ɗaya ya watse akan gadon, yayinda ta sanya hanunta ta damƙi zanin gadon da iya ka ƙarfinta,   duk da cewa sanyin ac na tashi acikin ɗakin, amma ita wani irin gumine ke fitowa daga jikinta.  Arazane ta ware manya manyan idanunta da sukayi jajur dasu, tashi tayi ta zauna tare da dafe ƙirjinta dake bugawa da sauri.   "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!" tafaɗa cikin wata murya me rauni, kawai saita  samu kanta da fashewa da kuka, kuka tayi sosai wanda itakanta batasan na menene ba, aƙalla taɗauki kusan 40 minute tana kuka harsaida muryarta ta dashe, idanunta ne suka sakeyin jajur dasu,  jin ana ƙiran sallan asuba ne yasata miƙewa ta nufi toilet,  doguwar rigan dake jikinta ta cire tare da tsayawa agaban shower ruwa yashiga dukan ta,   bazata iya tuna mafarkin me tayi ba, amma tabbas tasan taga wani abu wanda yake shirin taɓa rayuwarta,  wani irin bacci tayi wanda adunia bata taɓa bacci marar ɗaɗinsa ba,  MR. HANDSOME shine wanda tunaninsa ya kutso cikin rai da zuciarta,  aƙalla ta ɗauki kusan sama da 15 minute tana tsaye ruwa na dukanta,  da ƙyar ta iya ɗauro alwala tafito, domin gaba ɗaya bata jin ƙarfin jikinta.

Tsayawa tayi agaban madubi tare da kallon kanta, hanu tasanya ta shafi jajayen idanunta wanda suke cike tab da ƙwalla,  ai kuwa take hawayen suka gangaro kan ƙuncinta, ita kanta batasan kukan metakeyi ba, kawai dai tasan tanajin ƙunci acikin zuciyarta, tanajin wani irin babu daɗi acikin ranta, tanajin wani ƙaton rauni ya rataya awuyanta,  gaba ɗaya tuna nin mai taimakone ga cika ranta,  gefe guda kuwa sosai takejin faɗuwar gaba, tana fatan kada wata mummunar ƙaddara tasake
samunta.     Sosai ta jima a raka'an ƙarshe tana kai kukanta ga mai duka, addu'a take kome zai sameta Allah Ya kawo mata shi da sauƙi.  Haka ta zauna akan sallaya har gari yayi haske, ko samun daman sake duba takardan jarabawanta ma batayi ba, gaba ɗaya jin kanta take acikin ƙunci.    Akullum cikin kuzari da ƙarfin jiki ta ke shirya kanta zuwa makaranta, amma yau hakanan take sanya uniform tunani fal ranta.  Jakarta ta saɓa akafaɗa tare da fitowa cikin falon, akullum ta saba haɗawa kanta break fast amma yau batajin zata iyacin komai.     Ba irin tambayan dasu Shukrah basuyi mata ba,  akan tasanar dasu abun dake damunta, amma  tace dasu sam batasan meke damunta ba.    Suna fitowa a exam ta tsaya ajikin wata bishiya,  tare da tsaida idanunta akan hanyar shigowa makarantar, hakanan tasamu kanta da son ganinsa, duk da cewa bawai ta wani damu dashi bane, amma yau da takejin kanta wani iri sai taji tanason ganinsa, tasan ko ma yaya zai iya cireta acikin ƙuncin da take ciki.  Har Kamalu driver yazo tana tsaye ajikin wannan bishian, Saidai kuma har zuwa lokacin  bata ganshiba kamar yanda taso, haka ta koma gida zuciarta ba daɗi.   Indomie ta dafa amma haka ta kasa ci, dole ta zauna jigum tana kallon TV....

LAGOS NIGERIA....  

Ƴan sanda da kansu suka koma gidan Sooraj sukayi bincike, inda suka gano cewa shiɗin cikakken  ma'aikacin CBN ne, don haka direct branch ɗinsu dake Lagos suka nufa, BM ɗin  wajen wanda yakasance tamkar aboki ga Sooraj,  shi suka samu suka sanar dashi gaba ɗaya abundake faruwa,  aikuwa baƙaramin tashi hankalinsa yayi ba,  koda yaje yaga halin da Sooraj yake ciki tamkar gawa, saida ya zubda ƙwalla, nan yaƙira wayan Mas'oud yasanar masa komai da komai, ai Mas'oud tamkar wani zararre haka yazama, wani irin mugun tashin hankali yasamu kanshi aciki, batare daya sanar dasu Abban Sooraj ba ya hawo jirgi yataho Lagos.

Kallon Mas'oud Babban likitan asibitin yayi tare daɗan gyara zamansa yace.  "Inaga basai anfita dashi waje ba ae, amma tunda ka matsa zaku iya fitar dashi, saidai kuma dole muna buƙatar ku ƙara mana sati ɗaya, idan baidawo cikin hayyacinsa ba shikenan sai ku fita dashi"

Shiru Mas'oud yayi tare da sanya hanu ya kama kanshi, adunia ayanzu babu wani mutum dayake tausayi sama da SOORAJ.  Cikin cushashshiyar muryarsa yace.  "Shikenan Dr. Babu damuwa Allah dai ya bashi lafiya!"     da "Ameen" doctor ɗin ya amsa nan sukayi musabaha, Mas'oud ya nufi ɗakin da Sooraj yake kwance, duk da ba abarin kowa ya shiga, amma zaka iya hangoshi ta glass ɗin window'n ɗakin.  Tsayawa yayi ajikin window tare da sauƙe idanunsa akan Sooraj wanda yake kwance flat, bazaka taɓa cewa akwai rai ajikinsaba, saidai na urar dake jikinsa  kawai dake aiki,  wani irin hawayene suka cika idanun Mas'oud, har baisan sanda suka silalo kan ƙuncinsa ba.  "Wani irin ƙaddarori masu girma ne haka suke ɗawainiya da RAJ? yaushe RAJ zai huta? yaushe RAJ zaiyi dariya yayi farinciki kamar kowa? yaushe damuwar RAJ zata yaye?" abun da Mas'oud yake ta tambayar kansa kenan, tausayin SOORAJ yakeji mai tsanani, ayanzu baisan da wani baki zai iya furtawa iyayen Sooraj wannan mummunar labarinba, yace musu ɗansu yana cikin halin rayuwa ko mutuwa, ko kuwa yace musu ɗansu yazama marar amfani, ya zamanto tamkar gawa.   Hanu yasanya ya share hawayen dake kan fuskarsa, aransa yaci alwashin nemo duk wani wanda yake da hanu akan harbin SOORAJ, wayarsa dake ƙara ya ciro ya duba, ganin commisioner'n ƴan sanda ne ke ƙiranshi, yasanyashi fita daga cikin asibitin baki ɗaya bayan ya ɗaga wayar ya kara akan kunnensa.
***
Zaune take akan wani ɗan dakali, yayinda shi kuma yake tsaye abayanta, ɗan ranƙwafo da kansa yayi  daidai saitin kunnenta ahankali yace. 
"Sau ba adadi na faɗa miki banaso ina ganin damuwa akan fuskarki" yaƙare maganar yana mai zagayowa ya zauna aɗan kusa da ita.

Raunannun idanunta ta ɗago ta kalleshi, ga mamakinsa sai kawai yaga hawaye sun gangaro daga cikin idanunta.  Jiyayi wani abu ya soki zuciarsa, lumshe sexy eyes ɗinsa yayi tare da buɗesu alokaci guda. 
"Menene?" yatambayeta cike da kulawa.   Samun kanta tayi da cusa kanta acikin cinyoyinta ta fashe da kuka. Hankalinsa ne yaji ya tashi, cikin yanayi na rashin jin daɗin kukannata yace. "Meke damunkine Baby? wani abu ya samekine? ko wanine ya taɓaki? ko kuma anɓata ranki ne? please dear na faɗamin meke damunki!!" yayi maganar cike da tsantsar nuna kulawarsa gareta.
Chapter 25 · 0% Book details