← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 91

Sashe 34

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da safe Ummu da Ziyadah keta ƙoƙarin haɗa breakfast a kitchine kasancewar yau Abba zai koma KD, jirgin ƙarfe 9 zaibi shiasa Ummu keta ɗawainiya tanason yayi break kafun yatafi, don ita tace dawowarta ba yanzuba saboda Sooraj.   Ba abun da Abba yakeso kamar Tuwo hakan yasa yauma Ummu tuwo takeyi masa da moringa soup wanda yaji cow meat da biscuit bone,  ƙarfe takwas daidai suka kammala gaba ɗaya aikinsu, Ziyadah ce ta jere komai akan dinning table,   Koda Ummu tagama serving ɗin Abba kujera taja ta zauna, har Abba yafara cin abincin ya ɗago ya kalli Ziyada wacce tayi shiru kamar me tunani.  "Jeki ƙiramin yayanki" Abba yafaɗa yana me duban tsadadden  agogon dake ɗaure a hanunsa,   cike da ladabi tamiƙe tare da nufar inda zai sadata da ɗakinsa, duk da cewa ƙirjinta dukan uku uku yake, amma haka ta daure, tana tura kanta acikin corridor ɗin da direct zai kaika ɗakinsa ta shaƙi daddaɗan ƙamshinsa wanda yake matuƙar hautsina tunaninta, wani irin sanyi taji yana busata cikin sanyin jiki taƙarasa jikin ƙofar ɗakinnasa, hanunta na rawa tayi knocking amma shiru ba'a amsa taba, cike da tsoro tasakeyin wani knocking ɗin nanma shiru babu amsa,  ɗan jim tayi tare da juyawa zata koma, tunani tayi idan takoma me zata faɗawa Abba tace tayi knocking ba a buɗeba ko me? hakan yasa tayi karambani'n  murɗa handle ɗin ƙofar, kamar da wasa kuwa taji ƙofan ta buɗe, wani daddaɗan ƙamshi tare da sanyin AC ne suka daki fuskarta har saida ta lumshe idanunta.  Ahankali taɗan kutsa kanta cikin ɗakin,   kwance yake akan bed yayi irin kwanciyarnan ta ruf da ciki, dagashi sai dogon wando gaba ɗaya gadon a hargitse yake tamkar wanda akayi kokuwa akansa, kallonsa tayi tundaga ƙasa har sama, gaba ɗaya kwanciyanma baiyita a dai dai ba, domin kusan rabin ƙafafunsa suna lilo suba a sama ba suba a ƙasa ba, gangarjikinsa ne kawai ke kan gadon,   idanunta ne suka sauƙa akan bayansa inda fresh white skin ɗinsa ke shining  yana fidda ƙyallin zufa, mamakine yakamata ganin jikinsa na fidda gumi, domin kuwa sanyin ac ne keta tashi acikin ɗakin, hatta tiles ɗin dake malale aƙasan ɗakin yaɗauki sanyi sosai,   sam takasa sanin bacci yake ko kuwa idanunsa biu,  cikin yanayi naɗan tsoro ta ɗan tako zuwa tsakiyan ɗakin,   muryarta akarye tace   "Yaa..." kasa ƙarasawa tayi, ɗan cije laɓɓanta tayi tare da rumtse idanunta, gaba ɗaya jarumtarta ta tattaro tace "Ya--yah!"    Jin shiru bai amsa ba yasanya tace  "Dama Abbane yace naƙiraka!"   shima dai shiru babu amsa hakan yasa taɗan matsa kusa dashi, jin zuciarta take kamar zata fashe saboda fargaba, da ace zai juyo ya kalleta alokacin to tabbas abu me sauƙine ta sume masa awajen.    "Ya--Yah katashi!" Ta sake faɗa tana ɗan leƙa fuskarsa, domin yanzukam taga alamun cewa bacci yakeyi.    Ko motsi baiyiba balle tasaran zai bude idanunsa har yatashi kamar yanda take ɓuƙata,  cike da karanbani taɗan sanya hanu ta bugi katifan da yake  kai,  tun tana ɗan bugawa ahankali harta gaji taɗan buga da ƙarfi, still ko motsawa baiyi ba, hakan yasa tasa hanu tashiga jan bedsheet ɗin dayake kai cikin shagwaɓan da batasan ta iyaba tace.
"Please Ya--yah wake up!"   cikin bazata taga ya mirgino tare da juyowa hartana iya kallon fuskarsa saidai kuma bai buɗe idanunsa ba,  da sauri taɗauke idanunta daga kan faffaɗan chest ɗinshi,   cike da ƙosawa taɗan bubbuga ƙafafunta aƙasa murya agajiye tace "Nidai dan Allah katashi aikoni fa akayi!"   Bawai baitashi bane duk abubuwan da takeyi masa yana jinsune tamkar amafarki, sam ƙarfin maganin baccin da yasha baigama sakeshi ba, ko sallan asuba daƙyar ya iya tashi yayi nanma agida yayi baije masjid ba, ƙasa ƙasa yaɗan buɗe sexy eyes ɗinshi wanda sukayi masa matuƙar nauyi, dishi dishi haka yake ganinta hakan yasa ya maida idanunsa ya kulle, sam batama lura da cewar ya ɗan buɗe idanunsa ba, blanket ɗin dayake kai taja da ƙarfi waiko zai tashi amma sam ko sake motsawa baiyi ba,  hawayene suka cika idanunta sai kawai ta juya tabar masa ɗakin.  Tana shigowa cikin falon tasamu Abba da Ummu tsaye harsun kammala cin abincinsu.    "Ya haka naganki ke ɗaya ina Sooraj ɗin?" Ummu ta tambaya tana me ƙarewa Ziyada'n kallo, domin kuwa baƙaramin jimawa tayi aɗakin Sooraj ɗin ba. 

Sunkuyar dakai ƙasa tayi cikin muryarta me sanyi tace. "Bacci yakeyi, tun ɗazu nake tashinsa kuma baitashi ba!"

"Bacci?" Ummu ta tambaya cike da mamaki.

Kai Ziyada ta É—aga mata alamar "Eh"

"Badamuwa ku barshi idan yatashi zamuyi waya, yanzuma haka nakusa makara!" Abba yafaɗi haka yana me nufar hanyar barin falon, Ummu ce ta rufa masa baya, ita kuwa Ziyada  ɗakinta ta wuce domin kuwa lokacin da MBC Bollywood zasu fara haska series ɗin Ishqmeinmarjawan  *(حب خادع)*  ya kusa kuma bataso tayi missing saboda sosai series ɗin keyi  mata daɗi.

11:00 am daidai ya soma ware idanunsa ahankali har ya buɗesu  duka,  gani yayi kamar ɗakin na juya masa hakan yasa ya maida idanunsa ya rufe, mintuna uku tsakani yasake buɗewa, yanzu kam daidai yake ganin komai, jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi wani iri tamkar anyi masa duka, hannunsa yakai ya shafa tulin sumar dake kansa wanda yasha askin afro,   ƙafafunsa ya zuro ƙasa tare da miƙewa tsaye, hannu yasanya ya zuge zip ɗin wandon  dake jikinsa,  yana tafiya haka yacire wandon sannan ya buɗe wata ƴar glass drawer sabon white colour bathrobe na maza  ya ciro ya sanya ajikinsa, direct bathroom ya wuce,  wanka yayi sannan ya haɗa da brush,  yana fitowa ya jona handryer, dashi yayi amfani wajen busar da lallausan  gashin kansa,   sama sama yashafa mai ajikinsa,  wani oil and body perfume me daɗin ƙamshi ya shafa ajikinsa.    Kasancewar yau Jumma'a  yasanya shigar da zaiyi yauɗin ta da bance, duk da cewa shi baiwani damu da manyan kayaba amma time to time yana ɗan sanyawa,   wata haɗaɗɗiyar getziner blue colour wacce kuɗinta ya haurawa  40k ya zaro daga cikin tarin kayansa wanda yawansu basu faɗuwa,  wani haɗaɗɗen half cover shoe me kalan blue wanda akawa samansa ado da ɗan ratsi ratsin golding ash  ya zaro daga ma adanan takalmansa,  takalmine me kyaun gaske wanda aka sanya kuɗaɗe wajen sayansa, Hulan daya zaro ma ta musammance itama ajikinta akwai ratsi ratsin golding ash da blue,   Saida yagama kimtsa kansa cikin getziner'n wacce tasha ɗinkin half jumper, sosai yayi wani irin kyau me ɗaukar hankali, takalma ya zura aƙafafunsa sannan ya soma ƙoƙarin ɗaura agogon sa na companyn Gucci me tsadan gaske,  yana kammalawa ya sanya hula akansa,  baƙaramin kyau Sooraj yayiba acikin wannan shigan, wani irin ɗaukar hankali kwalliyartasa keyi, ga sajensa daya kwanta akan fuskarsa, juyawa yayi yaɗan kalli mirror, shikansa baƙaramin kyau yaga yayiwa kansa ba, musamman yanda kwarjininsa yasake bayyana afili, sosai ya fito a cikakken Namiji wanda ya amsa sunansa,  turarukansa ya ɗauka ya feshe jikinsa da su take ɗakin ya gauraye da sassayan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa,    wayarsa yaɗauka yasanya acikin aljihunsa tare da ɗaukan key ɗin Black Range rover car ɗinsa,   cikin takunsa me ɗauke hankali yake tafiya Iya kyau yayishi har ya gaji   (Team RajZiyada please kuyi imagine  yanda Sooraj ɗinku ya haɗe.lol)

Ahankali take saƙƙowa daga kan step ɗin dake cikin falon, Plate ɗin da taci abincine riƙe ahanunta tafito daniyar zata kaisa kitchine,   ƙamshin dayake kashe mata jiki yake kuma sanyata acikin wani irin yanayi shine yafara dukan hancinta lokaci guda ya gauraya da numfashinta, saboda tsabar daɗin ƙamshin batasan sanda ta lumshe kyawawan idanunta ba, tana buɗesu kuwa idanunta suka sauƙa akan zallan kyawu da kwarjinin dake dosowa cikin falon, wani irin dokawa taji ƙirjinta yayi, take jikinta yasoma karkarwa kamar maijin sanyi batare data kulaba tayi missing step ɗaya take tatafi zata faɗi da sauri tariƙe ƙarfen dake gefen matattakalan plate ɗin hanunta kuwa faɗuwa yayi dayake plate ɗin  irin na cikin gift set ɗinnan ne tassss haka ƙaran fashewarsa ya cika falon,  jin ƙaran fashewan abu abayansa yasanya shi juyowa, ido huɗu sukayi shida ida,  kallon yanda plate ɗin ya tarwatse awajen yayi, baiko sake kallon gefen da take ba yasakai yafice daga cikin falon yana gyara zaman agogonshi, ita kuwa Ziyada tamkar wacce aka dasa haka ta kasa motsa koda ɗan yatsan ƙafanta ne,  wani irin ƙarya idanunta ke mata don har yanzu gani take tamkar yana wajen.

"Zieyadah!"

Ƙiran sunanta da Ummu tayi shiyayi sanadiyar sauƙar da idanunta ƙasa murya asanyaye tace "Na'am"

Kallon plate ɗin daya tarwatse aƙasa Ummu tayi cikin ɗan mamaki tace.
"Ya akayi haka ta faru?"  

"Umm dama bankula bane shine yafaɗi!" Ziyada tafaɗa tana me ƙoƙarin maida ƙwallan dake cikin idanunta.

"Inadai baijimiki ciwo ba?" Ummu ta tambayeta cike da kulawa. 

"Eh!" tasake faɗa murya araunane.  

"Shikenan to kidai kula kada yamiki illa, ni zan fita bazan jimaba zan dawo ki kula sosai" Ummu tafaÉ—a tana me gyara zaman gyalen dake jikinta.

"Adawo lafiya" cewar Ziyadah tana me ɗan satan kallon Ummu wacce tasha ado da gwala gwalai masu tsadan gaske, itakam da badon ɗan zaman da tayi acikinsu ba to tabbas da zatace ba Ummu bace ta haifi Sooraj domin sam jikin Ummu bainuna hakan ba zallan kudi da jindaɗi haɗi da wayewa kawai jikin Ummu ya nuna.  

Haka Zieyada ta gyara wajen amma gaba ɗaya tunaninta yana wani waje daban, daga wani ɓangare na zuciyarta kuwa daɗi takeji ranan monday zasu koma makaranta.

Sooraj kuwa yana fita haɗaɗɗiyar car ɗinsa ya shiga tare da bata wuta,   kai tsaye Central Mosque ya nufa domin samun sallan jumma'a, koda aka idar da sallan daga masallacin direct JABI LAKE yanufa don sunyi da Mas'oud zasu haɗu acan.

Vote
   &
Comment

1/june/2020

          fatymasardauna

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SOORAJ !!!*

    *Written By*
phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

            *Wattpad*
    @fatymasardauna

#romance

           *Chapter 28*
Chapter 34 · 0% Book details