← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 91

Sashe 9

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanye yake da riga da wando na suit masu mugun tsada da kyau, navy blue colour,  takalmin ƙafarsa kuwa toms ne mai kyau shima navy blue colour,  sosai yayi kyau acikin kayan, nikaina bansan haɗuwarsa takai hakaba, sai yau dana gansa acikin shigar suit. Lol.
Agogon Rolex yake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turarensa mai sauƙar da nutsuwa, gashin kansa kuwa sai ƙyalli yake fitarwa, sosai yasha gyara da mayuka kala kala,    wayarsa mai tambarin Apple abaya ya ɗauka, tare da key ɗin motarsa, kana yafice daga cikin ɗakin.. 

Haɗaɗɗiyar sabuwar motarsa BMW ya hau,  mai gadi na buɗe masa ƙofa ya cillata kan titi ahankali yake murza steering motar cike da nutsuwa..

Tun ƙarfe 7 tatashi zama tayi jigum acikin ɗakin,  kallon kayan jikinta tashigayi gaba ɗaya sunɓaci da jini, gashi sunyi bala'in yin dotti, banda ɓarkewan da saman rigarta yayi.

Tun tana zaune tana nazari harta kwanta, juyi kawai take tayi, amma gaba ɗaya bata da nutsuwa,  jin ana knocking ƙofar ɗakinnata  yasa taji ƴaƴan cikinta sun sake hautsinawa saboda tsoro,  cigaba akayi da knocking ƙofar, yayinda itakuma ta matse jikinta waje ɗaya,  mugun tsoronsa takeji.  

"Good Morning Madam" taji muryan mai knocking ƙofar na faɗan haka.

Tsorone yasake kamata,  raba idanu tashiga yi tana neman wajen ɓuya don batasan meyake cewa ba, tasan dai wani yare kawai yake yi.

Peter dake tsaye jikin ƙofa hanunsa riƙe da leda ɗin abinci, yaji yasoma gajiya saboda haka, yaciro wayarsa yaƙira ogansa,    bansan mai SOORAJ yafaɗa masa ba, sai gani nayi ya aje ledan  abakin ƙofa yajuya yayi tafiyarsa.

Jin shiru andaina ƙwanƙwasa ƙofarne bakuma alamar motsin mutum, yasata sauƙo daga kan gadon ahankali.  Saɗaf saɗaf take tafiya harta buɗe ƙofar ɗakin, bugewa tayi da ledan da Peter ya ajiye.  ko kallon ledan batayi ba tashiga takawa harzuwa tsakiyan katafaren falon.   Gaba ɗaya bata cikin nutsuwarta sai waige waige take, ƙirjintane keta bugawa da sauri sauri fatanta ɗaya Allah yasa kada wani yakamata.   Wata ƙofa dake cikin falon tanufa, tana buɗe ƙofar kuwa ta buɗu,  wani irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya tasauƙe sakamakon ganinta a waje da tayi.   Da sauri sauri ta nufi  inda ta hango wani ƙaton gate, burinta ɗaya shine ta ganta awaje, sam batajin zata iya zama agidan ƙattin maza, wataƙilama da wata manufa suka ajiyeta.      Taci sa'a kuwa babu kowa abakin gate ɗin saboda haka gadan gadan tanufi ƴar ƙaramar ƙofan dake jikin gate ɗin ɗaura hanunta tayi ajikin ƙofan tare da buɗewa....

*(Niba cikakkiyar bahaushiya bace dole sai kunyi haƙuri da hausana, nasan wasunku bakomai suke ganewa acikin rubutuna ba😥)*

            *21/March/2020*

*✅OTE ME ON WATTPAD*
         @fatymasardauna

#hearttouching
#truelove

  
[4/7, 12:02 PM] fatymasardauna: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

          
             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

*🎂HBD Yaya Hayat wishing you long life and more money in to your bank account*

             *Chapter 8*

Tana buɗe ƙofan idanunsu ya sarƙe acikin na juna, wani irin tsorone taji ya kamata, take jikinta ya ɗauki rawa.  

Kallo É—aya yayi mata ya watsar agadarance yace.

"Wuce mukoma ciki"

Samun kanta tayi da kasa musa masa, tana gaba yana biye da ita abaya, suna shiga cikin falon ya murzawa ƙofar key, direct ya wuce ɗakinsa ko kallonta baiyiba,  tana ganin wucewarsa cikin ɗaki ta saki wani irin marayan kuka.    Yana shiga cikin ɗakin yasoma rage kayan jikinsa.  Toilet yashiga yayi wanka, fitowa yayi dagashi sai towel dake ɗaure a ƙugunsa.     Sama sama yashafa mai, farin riga da blue ɗin wando yasanya,   ba abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshi, buɗe ƙofar ɗakinnasa yayi yafita zuwa falo, ko kallon inda take durƙushe tana kuka baiyi ba, kitchine ya nufa, mintuna ƙalilan yadawo hanunsa ɗauke da wani faranti wanda samansa ke ɗauke da kayan fruit.

Zama yayi akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon, haɗe da ɗaura ƙafansa akan rug,  apple ya ɗauka yana gutsura ahankali, jingina bayansa yayi da jikin kujera haɗe da lumshe idanunsa, ahankali yake  tauna apple ɗin dake cikin bakinsa, a rayuwarsa idan yaji kukan mace sosai hankalinsa ke tashi, amma a yau ko ajikinsa, daɗima kukannata keyi masa,  gani yake ita damuwarta ma  mai sauƙice tunda hartana iyayin kuka, shi kuwa shi kaɗai yasan abun da ya keji,  idan da zai samu daman yin kuka to tabbas da yayi, idan da za'ace dashi idan yayi kuka matsalarsa zata yaye to tabbas da shikam yayi kuka irin kukan da ya amsa sunanshi kuka, ba irin nata kukan na shagwaɓa da sakalci ba.  Ahankali sautin kukanta ke tashi acikin falon, ware idanunsa da suka somayin ja yayi haɗe da watsa mata su.     "Keee!!"   yafaɗa murya akausashe.

Ɗago fuskarta da yayi caɓa caɓa da hawaye tayi ta kallesa.  Yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur ne yasa taji gabanta ya faɗi, miƙewa tsaye yayi, haɗe da takowa harzuwa inda take, hanunsa yasanya ya finciko nata hanun, yana janta haka suka fita daga cikin falon, yana zuwa bakin motarsa ya buɗe murfin motar haɗe da cillata ciki da ƙarfi, har saida ta buge goshinta, shiga cikin motar yayi haɗe da kunnata, baijira mai gadi yagama wangale masa gate ɗin bama, ya figi motar da wani irin gudu haɗe da cillata kan titi.  Gudu yaketa shararawa akan titi, bai tsayaba harsai da ya kusan fita daga cikin Kaduna, parking yayi agefen titi.

"Fita!"
yace da ita cikin wata irin murya.

Tsaida kukanta tayi cak, haɗe da ƙura masa ido.

"Kifitarmin amota nace!!" yanzu kam atsawace yayi maganar.

Jikinta na rawa tasoma kiciniyar buɗe murfin motar.  Yanajin fitanta yayi reverse haɗe da cilla motarsa kan titi, bayan ya buleta da ƙura yabar wajen.

Tana ganin ɓacewar motarsa ta saki wani irin kuka haɗe da durƙushewa a wajen,  kuka take mai cike da tsananin tausayin kanta,  kuka take nakasancewarta marar gata, kuka take nakasancewarta ƴa mace marar galihu... Sama da mintuna 14 ta kwashe tana durƙushe a wajen,  jifa jifa motoci ke wuceta.

Wata haɗaɗɗiyar motace ta tsaya adai dai gabanta,   da sauri taɗago atunaninta shine yakuma dawowa,    wani saurayi tagani ya sauƙe glass ɗin motar sa, haɗe da sakar mata murmushi.  

"Ƴan mata mai yasameki haka kike kuka?" yatambayeta yana mai ƙarewa ƙirjinta kallo.

Sunkuyar dakanta ƙasa tayi batare da ta tanka masa ba.

Ganin bata kulasa bane yasashi fitowa daga cikin motar, batasan cewa yafito daga motarba sai ganinshi kawai tayi agabanta, har numfashinsu na dukan na juna. Da sauri ta matsa baya tana mai rau rau da idanunta.  Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake matsota, kallonta yake kamar tsohon maye.
  
"Wai tsorona kikeji ne? haba karki bani kunya mana, zo muje nakaiki masauƙina kiyi wanka kinji!" yanayin yanda yayi maganar saida yasa tsikar jikinta ya zuba.   Da sauri tashiga girgiza masa kai tana mai sake ja da baya, shikuwa sai ƙara matsota yake,  hanunta ya cafke haɗe da yunƙurin  jawota jikinsa,   tureshi tasomayi yayinda ruwan hawaye keta ambaliya akan fuskarta. 

"Ka...ƙyale..ni" tafaɗi haka cikin rarrabewar murya cike kuma da tsoro.    Idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da sanya harshensa ya lashi laɓɓansa, cike da iskanci yace.
"Haba Babe karkimin haka mana, nafa kamu, please ko 30 minute ne kiban, muje mota please!"  yanzukam kuka mai sauti tasanya haɗe da soma turjewa,  hanunsa yakai zai taɓa kafaɗanta,  yaji anyiwa hanunnasa wani irin riƙo, da sauri yajuya don ganin wanda yayi masa katsalandan.    Ido huɗu sukayi, take saurayinnan yaji gabansa yayi wani irin faɗuwa, bakomai ya tsoratashi ba kamar  ganin ƙwayar idanun SOORAJ.    da gudu Ziyada tayi bayan SOORAJ ta ɓuya haɗe da sakin wani marayan kuka.    Irin kallon da SOORAJ keyiwa matashin saurayinne  yasashi sulalewa yashige motarsa da gudun gaske yabar wajen.

Aƙalla sun kusan mintuna 9 ahaka yana tsaye ya rumtse jajayen idanuwansa, yayinda ita kuma ke tsaye abayansa ta saƙala hannayenta akan cikinsa, fuskarta ta ɗaura akan bayansa tana kuka.

Hanunsa yasa ya zare hanunta daga kan cikinsa,  baice ƙalaba, yakama hanunta suka nufi wajen da motarsa ke fake.  gidan baya ya buɗe ya sanyata aciki, kana yaja motar suka ɗauki hanyar komawa cikin gari.

Tunda suka shiga cikin motar ta kifa kanta acikin cinyoyinta taketa faman rera kukan maraici.  Shikuwa ko ƙala baice mata ba har ya iso gaban wani tafkeken mall.  Fita yayi daga cikin motar yashiga cikin mall ɗin.  Aƙalla ya ɗauki kusan sama da 20 minute acikin mall ɗin, fitowa yayi, yayinda wani yaro ke binsa abaya hannayensa riƙe da ledodi, inda Ziyada ke zaune SOORAJ ya buɗe masa yaron ya zuba ledodin aciki.     Shiga motar yayi suka sake ɗaukan hanya.

Horn biyu kacal yayi maigadi ya wangale masa gate, a parking space yayi parking motar.

   "Biyoni"
yace da ita ataƙaice batare da ko kallonta yayi ba,  babu musu tafito daga cikin motar, dai dai lokacin Tanimu maigadi ya iso wajen. 
 "A kwai kaya acikin mota kashigomin dasu ciki!"  SOORAJ yafaɗi haka ga maigadi, kana yasa kai ya wuce ɓangarensa Ziyada na biye dashi.

Harsuka ɓace Tanimu maigadi baidaina kallonsuba, tsantsar gulmane ke cinsa,  a iya tsawon rayuwar da sukayi da SOORAJ baitaɓa ganin SOORAJ yashigo da wata mace cikin gidanba, ko auren da yakeyi ma kawo masa matan ake, amma yau abun mamaki gashi da wata ƴar ƙaramar yarinya,  ganin cewar gulma bazata kai mishi bane yasashi kwashe kayan ya bi bayansu SOORAJ ɗin.

Suna shiga cikin falon SOORAJ ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa, ɓalle murfin goran yayi, haɗe da kai bakin goran kan nasa bakin,  baicire bakin goran daga kan nasa bakinba  har sai da yashanye ruwan cikin goran tas,  a durstbin  ya jefa roban ruwan haɗe da dawowa tsakiyar falon ya zauna akan kujera.  Dai dai lokacin Tanimu maigadi yashigo, aje ledodin dake hanunsa yayi kana yafice daga cikin falon sumu sumu.
Chapter 9 · 0% Book details