← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 91

Sashe 54

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani iri taji yayinda wani irin nauyi da kunyarsa suka lulluɓeta alokaci guda, jikinta asanyaye ta miƙe tsaye tare da kaɗa kanta alaman "Babu komai"  cikin nutsuwa haka tajuya tanufi cikin gida, ita kanta bazata iya tantance awani hali take ciki ba awannan lokacin. Kamar wanda ƙwai ya fashewa haka ta haura sama ko lura da Oummu dake tsaye a bakin kitchine batayi ba, Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da duban hanyar da Zieyaderh'n tabi, wani irin fargabane taji ya kamata, sai yanzu takejin tsoron haɗin da tayi, musamman ma da taga yanayin da Zieyaderh'n tashiga ayanzu, shiru tayi tare da faɗawa wani sabon duniyar tunani.
Ita kuwa Zieyaderh tana  shiga ɗaki ta rufo ƙofarta, samun kanta tayi da sulalewa ta zauna daɓas aƙasa, batare da ta ankara ba taji wasu hawaye masu ɗumi suna sauƙa akan ƙuncinta, tabbas wannan sabuwar ƙaddaran da ta tsinci kanta aciki tayi mata girma, ƘADDARA tana neman haɗa aurenta da Almustapha, sannan kuma agefe guda ga Pharouk da yake neman ta amsa masa soyayyarsa, ƘADDARA mafi girma awajenta kuwa itace soyayyar Mr.Helper, hannayenta tasanya ta share hawayenta,  wata zuciya ce me bata ƙwarin guiwa akan ta yarda da duk wata ƙaddara da tazo mata me kyau ko akasin haka, samun kanta tayi da kwanciya luf akan gado, mintuna ƙalilan bacci ɓarawo ya saceta.

Pharouk. Gudu sosai yake sharawa akan babban titin gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya jikinsa, maganganun da Almustapha ya faɗa masa suketa yi masa yawo acikin ƙwaƙwalwarsa, da ƙarfi ya daki steering motar ransa amatuƙar ɓace yace
"Bazan taɓa zama looser akaro na biyu ba SOORAJ, awannan karon tabbas bazan bari kasake nasara akaina kamar lokutan baya ba,  bazan taɓa bari ka auri Zieyaderh ba SOORAJ!!"  wani irin murmushi yayi tare da cije laɓɓansa, ahankali yashiga rage gudun da yakeyi tare da ƙoƙarin samarwa kansa nutsuwa tahanyar aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa.
***
Oummu ce ta shigo cikin haɗaɗɗen ɗakin wanda yake mallakin Mijinta ne, Abba dake tsaye yana sanya garen kayansa ya ɗan juyo tare da kallonta murmushi yayi mata tare da cewa "Saboda kawai ɗanki zaiyi aure shiyasa kika kasa zaune kika kasa tsaye ko Sulaimiyya!" yaƙare maganar cikin yanayi na ɗan tsokana.

Murmushine ya faÉ—aÉ—a akan fuskarta tare da cewa "Yanzuma ai nashigo ne nasanar dakai abokan tafiyanka sun iso"

Murmushi ya kumayi tare da cewa "Bake kaɗai kikejin farinciki aranki ba Sulaimiyya nima inaji, saidai kuma ata wani ɓangare na zuciyata ina ɗauke da fargaban abun da zaije ya zo"

"Insha Allah Alhajina babu wani abu da zaizo sai alkhairin Allah!" Tafaɗa cikin son ƙarfafa masa guiwa.
Yaji daɗin maganan nata sosai hakan yasa yayi murmushi, har wajen motarsa Oummu ta rakasa inda ya haɗu da manyan aminansa su Uku suka kama hanyar airport, kai tsaye suka wuce Kaduna, daga nan kuma zasu shige cikin motocinsu su wuce ƙauyen saminaka.

Itakuwa Zieyaderh gaba ɗaya wunin yau batajin daɗin jikinta, hakanan takejin kanta cikin ƙunci, wani irin kewa me taɓa zuciya takeji yana ratsa duk ilahirin jikinta, gaba ɗaya su Shukra sun lura da rashin walwalan da takeyi kwana biyu, yanzuma zaune suke su duka ukun akan wani ɗan dakali suna me shan iskan dake kaɗawa asararin samaniya.  Cikin yanayi naɗan zolaya  Nasmah tace "Amarya badai wai cin amarcin aka fara tun yanzu ba? naga gaba ɗaya duk kin rame, sometimes kuma kina cikin damuwa"
Hararanta Zieyaderh tayi tare daɗan murguɗa mata baki cikin yanayin ɓata fuska tace
"Ni ba amarya bace"
Dariya Nasma da Shukra suka sanya, wanda hakan yaƙara ƙular da ita. "Uhumm kigama zille zillenki yarinya wallahi sai mun fidda ankon bikin ki ehe, sannan kuma sai mun sha rawa koya kikace Besty" Shukra tafaɗa tana kallon Nasmah. "Ƙwarai kuwa" Nasmah tafaɗa tana me gimtse dariyanta. Cikin turo baki gaba Zieyaderh ta miƙe daga zaunen da take tare da nufar hanyar da zai sadata da class ɗinsu.  Kallo su Nasmah suka bita dashi harta ɓacewa ganinsu, sannan suka sa dariya, har acikin ransu su mamakinta suke na yanda gaba ɗaya tabi ta takura kanta.

Acan Ƙauyen Saminaka kuwa Tuni Abba sun gana da Malam Garba baban Zieyaderh, inda yayi musu karɓa ta mutumci, babu laifi kuma sun yaba da halin karamcin daya nuna musu, nan suka zauna suna me sake fahimtan juna, sam su Abba bada wasa suka ɗauko maganan auren ba hakan yasa lokaci guda suka gama magana inda Malam Garba ya shaida musu cewa ya basu auren ƴarsa Zieyaderh, Alhaji Maham ɗaya daga cikin aminan Abba shi ya ciro wasu kuɗi dake cikin aljihunsa inda ya miƙa amatsayin sadakin auren Zieyaderh, naira dubu ɗari ne cas, cewar da sukayi basason bikin ya ɗauki lokaci ne yasanya Malam Garba cewa suyi haƙuri suɗan bashi lokaci zuwa nan da kwana huɗu zai sanar dasu kowani lokaci ya yanke, shikuwa yayi hakanne don yanason tattaunawa da Zieyaderh akan batun auren, domin tun da aka fara batun auren baiji ta bakinta ba kuma itama tana da haƙƙi, cikin mutumta juna su Abba sukaiwa Malam Garba sallama inda suka kama hanyar dawowa cikin garin Kaduna.
..........

15 minute da tashinsu a school kenan amma har zuwa yanzu Kamalu driver baizo ɗaukarta ba kamar yanda ya saba, waige waige taɗan somayi wai kozata hangosa amma babu ko me kama dashi, gashi gaba ɗaya ƴan makarantar sun soma watsewa don tuni su Shukra ma sun tafi,   ahankali take takawa harta isa bakin gate ɗin fita daga makarantar,   tsayawa tayi daga ɗan gefe kaɗan tana me ƙarewa motocin da keta hada hada awajen kallo,   wata haɗaɗɗiyar blue car wanda taji black tinteck ne ta tsaya adaidai gabanta,  kallon motar Zieyaderh tayi amma ganin bata iya ganin wanda ke cikin motar ya sanya ta ɗauke kanta gefe,tare da cigaba da kallon hanya, ahankali ya shiga zuge glass ɗin motar, fuskarsa ɗauke da murmushi yace "My ƴar kyakkyawan budurwata!"  jin muryarsa acikin kunnuwanta yasanya tayi saurin ɗagowa ta kalleshi, hakanan taji gabanta ya faɗi amma sai tasaki murmushi,  da hannu yayi mata alaman da ta taho, samun kanta tayi da kasa musa masa sai kawai taɗan ƙarasa jikin motar, daga ciki yasanya hannu ya buɗe mata murfin motar,  duk da cewa ƙirjinta na dukan uku uku haka ta daure tashiga cikin motar saidai bata rufe murfin motar ba,  kanta ta sunkuyar ƙasa tare da kama ƴan yatsunta tana wasa dasu, shikuwa Pharouk ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ƙiran sunanta murya asanyaye. Jin yanda yaƙira sunannata yasanyata ɗago da kanta ta kalleshi, gani tayi gaba ɗaya murmushin dake kan fuskarsa ya kau, zuwa yanzu damuwane shumfuɗe akan fuskarta sa,  kasa ɗauke idanunta daga kansa tayi saidai kuma ba cikin idanunsa take kallo ba, tunowa da tayi cewa jiya tabarsu da Almustpha batare da tasan me Almustaphan ya faɗa masa ba yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, jitayi idanunta naneman kawo ruwa, ahankali yasanya hannunsa ya ɗago haɓarta, hakan yasa suka jefa idanunsu cikin na juna, cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa yace "Kinason aure'n?"  gabantane ya faɗi dajin tambayar tasa amma kuma saita samu kanta da kasa amsa masa,  fuskarsa yasake mareraicewa tare da cewa "Da gaske kenan aure za'a miki? me yasa kika amince da hakan? kinyarda arabani dake kenan ko?" yaƙare maganar yana me matuƙar nuna rauninsa akan fuskarsa.
Hawayen dake kwance acikin idanunta ne suka samu daman gangarowa batare da ta shiryawa hakan ba.     Ganin hawaye akan fuskarta ya sanyashi lumshe idanunsa tare da matso da fuskarsa gaf da tata har suna iya jiyo hucin numfashin juna, jin sauƙan numfashinsa akan fuskarta yasanya azabure tayi saurin buɗe idanunta , shima buɗe nasa idanun yayi wanda suka kaɗa sukai ja, wani irin kallo daya mata ne yasanya tayi saurin jan jikinta baya tare da ture hannunsa dake kan haɓan ta,  kuka ne yake neman cin ƙarfinta hakan yasa ta juya da sauri ta fita daga cikin motar, dai dai lokacin kuma motar da aka saba zuwa ɗaukanta dashi wanda kamalu driver ke ciki ya tsaya adai dai ƙofar shiga gate ɗin makarantar, da ɗan sassarfa taje ta buɗe murfin motar tare da faɗawa ciki kana ta jawo murfin ta rufe, kanta ta cusa acikin cinyoyinta tare da sakin kuka me sauti, Ko bi takan Kamalu driver dake bata haƙurin rashin zuwansa da wuri da yayi bata biba, kuka take sosai tana me kakkame jikinta, wani irin zafi zuciyarta ke mata, Me yasa har izuwa yau baice komai ba? me yasa ya hanata ganinsa har na tsawon kwana uku? tanajin zafi acikin rai da zuciyarta, safe, rana, dare, duk shine acikin rayuwarta me yasa takejin hakan? Kukanta taci gaba dayi wanda babu me rarrashi, zuwa yanzu harta soma jin haushin kanta, musamman yanda tamaida kanta wata wawiya akansa.

Ganin tashin motarsu yasanya Pharouk sakin wani murmushi wanda shikaɗai yasan ma'anarsa, key ɗin dake jikin motar yaɗan murza, tare da cilla motar tasa kan titi, yayiwa kansa alƙawarin matuƙar shine Pharouk to SOORAJ bazai taɓa samun Zieyaderh amatsayin mata ba.
Chapter 54 · 0% Book details