← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 91

Sashe 40

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali Ummu tatura kofar ɗakin tashigo bakinta ɗauke da sallama,  ganin Zieyaderh nannaɗe acikin bargo yasanya Ummu ƙarasawa wajenta da sauri cike da kulawa tace.

"Zieyaderh lafiya kike kuwa?"

Zieyaderh da duk jikinta ke rawan sanyi, ta girgiza kanta cikin ciwo tace.
"Ummu zazzaɓine ke damuna!"

"Subahanallah shine kuma bakizo kin faɗamin ba? ba'a zama da ciwo ae, sam hakan ba kyau,  kin maci abinci kuwa?" Ummu ta tambaya.

Kai Zieyaderh ta girgiza alaman.       
  "A'a"

Juyawa Ummu tayi tafice daga cikin ɗakin. 

Mintuna kaɗan saiga  Ummu ta dawo hannunta ɗauke da plate da kuma cup ɗin tea, kan bedside drawer ta aje plate da cup ɗin, bargon da zieyaderh ke lulluɓe dashi Ummu taɗan yaye tare da miƙar da ita zaune, cup ɗin  tea ɗin Ummu ta bata, babu musu ta amsa,  ahankali takeshan tea ɗin,  sai da tasha kusan rabin cup ɗin, kafun Ummu ta amshi cup ɗin, plate ɗin soyayyen dankali da ƙwai wanda yaji sauce Ummu ta miƙo mata, nanma bata musaba ta amsa, ahankali takecin abincin duk batajin wani daɗin bakinta.   Pain reliever Ummu ta bata tasha,  sannan tace da ita ta kwanta tayi bacci,  luf tayi akan gado tana maida numfashi ahankali, cikin wasu mintuna ƙalilan bacci ɓarawo yayi gaba da'ita.  

Tunda Yafita sallan Magriba bashi yadawo gidanba sai 9 pm,  direct toilet ɗinsa ya wuce, wanka yayi yafito ɗaure da towel a weast ɗinshi, sama sama yashafa body lotion,  white trouser yasanya, tare da feshe jikinsa da turare me daɗin ƙamshi,  Luf yayi akan gadonsa tare da cusa kansa cikin pillow, sanyin AC ne ke ratsa naked skin ɗinsa, ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya, ƙoƙarin faɗa da tunaninsa yake, sam bayason wani abu yasake damunsa,  a ƴan kwanakinnan yana yawan jin zuciyarsa nayi masa zafi, sam bayason ciwonsa yayi ƙarfin da harsai kowa ya gane yana ɗauke da ciwon zuciya, akullum yanaji ajikinsa bashi da wani sauran farinciki daya ragemai,   numfashi ya fitar ta bakinsa tare da lumshe idanunsa,  duk yanda zuciyarsa taso da yayi tunani yaƙi bata daman hakan, yajima sosai kafun yasamu bacci ya ɗaukesa.

Washegari.

7:00 am daidai yagama shirya kansa cikin navy blue suit,  Sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake,   waya da key ɗin motarsa ne riƙe ahanunsa,  cikin nutsuwa yake takunsa har yakai bakin ƙofar da zai fitar dashi daga cikin falon. Muryar Ummu da yaji abayansa yasanyashi tsayawa, juyowa yayi cikin ɗan rusunawa yace.
"Good morning Maaa" 

Murmushin daya bayyana tsananin kamanninsu dashi Ummu tayi tare da cewa
     "Morning how are you?"

"Am fine!" ya amsa ataƙaice yana me gyara wrist watch ɗinsa. 

"Kasanar da Mas'oud Zieyaderh batajin daɗi, sannan yau bazata samu zuwa school ba ya kamata asanar" Ummu tayi maganar tana me ƙoƙarin zama akan kujera.
Kansa kawai ya jinjina alamar yaji kana yafice daga cikin falon.   

Sosai tasha bacci sai 10 tafarka, Alhamdulillah ta ɗanji sauƙin jikinta, saidai kuma duk da haka bakinta babu daɗi,   fitowarta daga wanka kenan, wani riga da sket ƴan kanti tasanya, sket ɗin irin rubber pencil ɗinnan ne yayinda rigan takasance me buɗaɗɗen kafaɗa, sosai kayan sukayi mata kyau ajiki,  rubber hijab tasanya ajikinta, sannan tanufi ƙasa,   ahankali take saƙƙowa daga kan steps ɗin, Ummu ce zaune afalon tasha ado cikin wani tsadadden lace maroon colour wanda yayi matuƙar amsar jikinta, gefe da ita wata matace wacce bazata wuce shekarun Ummun ba itama zaune ta caɓa ado, dagani basai anfaɗa ba kasan naira yazauna musu su dukansu.   Cikin ladabi taƙaraso tare da durƙusawa ta gaidasu, fuska ɗauke da murmushi Ummu ta shafa kan Zieyaderh'n tare da cewa

"Kintashi? har baccin ya isa kenan, to ga can break fast akan dinning"
Murmushi Zieyaderh tayi tare da miƙewa tsaye tanufi dinning area. Hajiya Munah dake zaune tabi Zieyaderh da kallo, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da duban Ummu cikin yanayi naɗan mamaki tace.
"Hajiya Sulaimiyya ina kikasamo wannan kyakkyawar yarinyar kodai daga ƙasarku take ne?"

Murmushi Ummu tayi tare da cewa. "Ƙanwar Mas'oud ne abokin Sooraj, ai kindai san Mas'oud?" 

Murmushi Hajiya Munah tayi tare da cewa "Ayya gaskiya balaifi yarinyar akwai hankali, uwa uba gata da kyau masha Allah!"

"Wannan halayyan nata shiyasa nakeson haɗata aure da Almustapha, nasan bazaiyi takaicin samunta amatsayin mata ba"  Cewar Ummu wacce ke sipping pineapple juice ahankali.

Murmushi Hajiya Munah tayi tare dacewa "Gaskiya kinyi tunani me kyau, amma ae zai fi kyau ki haɗata da Sooraj, don aganina yafi Almustapha buƙatar mace akusa dashi"

Aje glass cup É—in hanunta Ummu tayi tare da duban Hajiya Munah, wani murmushi me ciwo Ummu tayi cikin wani irin yanayi tace "Saikace bakisan waye Sooraj ba Hajiya Munah? hmmm Sooraj É—in da baibzauna da matan da suka amsa sunansu mata ba ma, mene zaiyi da Æ´ar wannan ta tsitsiyar yarinyar da duka duka shekarunta basu wuce 18 to 19 ba"

Ajiyar zuciya Hajiya Munah ta sauƙe tare da cewa "Allah ya kyauta"

Da  "Ameen" Ummu ta amsa daganan suka ci gaba da hiransu.

Zieyaderh kuwa zama tayi akan dinning tare da zubawa kanta pepper chicken soup, and chips, ahankali take tsakalan abincin don gaba ɗaya bawani daɗinsa takeji ba.   Koda ta kammala ɗakinta takoma magungunanta tasha kana ta kwanta, tashar Mbc  Action take kalla da haka har bacci ya ɗauketa.

Dayake magungunan da tasha suna da ƙarfi sosai hakan yasa ba ita ta tashiba sai wajen 5 na yamma, wanka tayi tare da sanya wata blue gown marar nauyi,  yunwa takeji sosai hakan yasa tashiga ƙoƙarin zura hijab ɗinta don sauƙa ƙasa, jin anturo ƙofar ɗakinne yasanyata waigawa da sauri, ido biyu sukayi da Ummu wacce fuskarta ke ɗauke da murmushi.

"Barka da yammaci Ummu" tafaÉ—a murya asanyaye.

"Yauwa, dama wai me gadine yanzun yashigo yace wai wani yana sallama dake awaje, shine nace ko kunyi da wani zaizo wajenki ne?"

Idanu Zieyaderh ta zaro, lokaci guda ƙirjinta yashiga wani irin bugu, bakinta narawa tace "Ni....ni...kuma?"

"Eh haka dai yace, yanaga kin tsorata? Maza kije kiga ko wayene bakyau kabar mutum yana jira!" Ummu nagama faÉ—an haka ta juya ta fice daga cikin É—akin.

Tsorone ya kama Zieyaderh adaburce ta sanya hijab dinta,kana ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice.   Bataga Ummu afaloba kai tsaye saita nufi hanyar waje. 

Koda tafito compound É—in gidan idanunta tashiga warewa ko zata hango wanda akace na nemanta.

Tun fitowarta daga cikin falon yake kallonta, sosai tayi masa kyau acikin hijab ɗin dake jikinta, ashe sosai uniform ke ɓoye kyawunta.     Kamar wanda akace tawaiga bayanta, hangosa tayi tsaye ajikin black car ɗinsa mercedes benz, sanye yake da riga da wando na bugaggiyar shadda Blue colour wanda tayi matuƙar yi masa kyau, mamakin ganinsane kwance acikin ranta amma saita sunkuyar da kanta ƙasa tare da nufar inda yake,  murmushine kwance akan fuskarsa yana me kallonta harta ƙaraso. Cikin siririyar muryarta tayi masa sallama.  Bai amsa sallamannata ba saima tsayawa kallonta da yayi, jin shiru bai amsa mata ba yasanya ta ɗago  kanta ta dubeshi, idanunsune suka sarƙe cikin na juna, yanayin kallon daya mata yasanya ta sauƙar da idanunta ƙasa da sauri tana murmushi.   Kansa yaɗan sunkuyo yana leƙa fuskarta, ganin haka yasa tasanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta da sauri.  

"Jiya nakasa bacci saboda bansan wani hali kike ciki ba,  amma ganinki danayi yanzu yasa naji sanyi araina, basai ma kin faɗa ba nagane kinji sauƙi" Yafaɗi haka cike da tsantsar nuna kulawarsa gareta.

Har acikin ranta taji daɗin maganganunsa, domin tanada buƙatar kulawa sosae.

Ɗan matsowa kusa da ita yayi hartana iya jiyo sassanyan ƙamshin dake fita ajikinsa.  Hannayensa yakai ya zame hannunta dake kan fuskarta. 

Cikin wata irin sweetness voice yace "Kullum ƙara kyau kike, komai naki me kyaune, zanso kasancewa dake akoda yaushe sannan akowacce rana, please faɗamin kina sona?"  yaƙare maganar yana me juya idanunsa akan kyakkyawar fuskarta.

Lumshe kyawawan idanunta tayi sosae zuciyarta ke bugawa, batasan me zatace masa ba, sannan kalamansa sunyi mata nauyi sosai, shikaɗai ya lura da mota ƙiran black range rover  dake shigowa cikin gidan, kasancewar ita tabawa ƙofar gate baya, sannan gaba ɗaya tunaninta yatafi izuwa wani wajen daban.    Ahankali taɗan buɗe idanunta tasaci kallonsa, abun da bata saniba shima kallonta yake sai kawai idanunsu ya sauƙa acikin na juna. Da sauri ta kawar da kanka gefe tare da sanya hijab ɗinta ta kare gefen fuskarta, idanunta ne suka sauƙa akan motar da ta shigo cikin gidan, wani irin masifaffen tsorone ya kamata take jikinta ya soma ɓari, lokaci guda jikinta yashiga fidda gumi,   yana gama daidaita parking ɗin motar yafito,  sanye yake da white t-shirt and  combat army jeans,  baƙaramin kyau yayi ba sosai kayan suka fitar da kwarjininsa.  Cikin isa yake takunsa yana me dosowa cikin gida, saidai abun mamaki bai ɗago kai ya kallesu ba, bawai kuma don baigansuba tun shigowansa idanunsa sukayi masa tozali dasu,    baya baya Zieyaderh keyi tana me ƙoƙarin ɓoyewa abayan Pharouk,  tuni hawayen tsoronsa sun cika idanunta. Yayinda shikuma yake daɗa kusanto inda suke, fuskarsa sam babu alaman wasa ko murmushi akanta.

*Vote*
*Comment and share......*

9/June/2020

      

            Fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

        *WATTPAD*
  @fatymasardauna

#romance

        *Chapter 32*

Cikin nutsuwa yake takunsa, tuni Zieyaderh ta koma bayan Pharouk ta ɓoye, rumtse idanunta tayi ƙam cike da fargaba.  Ƙamshin turarensa da yacika hancinta ne  yasanya jikinta ya soma  rawa, saboda tasan zuwa yanzu yana gab dasu.    Sam bai kallesuba balle yasa aransa cewa  da gaske mutanene awajen, kansa tsaye ya wuce.

Aƙalla taɗauki kusan 5 minute ahaka, idanunta a rufe suke, jin shiru bataji motsin kowa ba   yasanya tasoma buɗe idanunta ahankali,  da beuty face ɗinsa tasomayin arba yayinda ya kafeta da sexy eyes ɗinsa,  waro idanunta waje tayi tare da ɗanja da baya tashiga waige waige.

Murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi, tare da  ɗan kashe mata idanunsa ɗaya.              
"Tsoron me kikeyi haka? ba Brother É—inki bane?"
Chapter 40 · 0% Book details