← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 70

Sashe 66

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aaima ce tayi k’arfin halin k’arasawa tsakiyar parlourn inda Jalilan take
tana kallon ta da d’an mamaki dan kamar bata tab’a ganinta ba.

Fitowar Mom daga kitchen ne ya katse mata tunani har shi Auwal d’in
Uwa mai dad’i suna had’a ido yaji wani sanyi a ranshi…
Takawa yayi har inda take yana zuwa ya sa hannu yayi hugging d’inta.....
Tun a cell Mom take aiyyana kalar abubuwan da zata yiwa Auwal kala kala
In Allah ya maidota gida lafiya dukda kuwa tana shakkarshi,
babu yadda bata yi mishi shi da Arshaad akan su basu kud’i su samu su fito ba
amman suka hana su
saboda suna shakkar Granpa sannan basu san darajar su uba and sun rainasu!
Sannan ta dawo amman tun jiya take zuba ido but bataga k’eyarsa ba.
A hankali yace “welcome home“
Ta manta rabon da Auwal ya nuna wani affection a kanta irin haka, ba ta san lokacin da wata kwalla ta zubo mata ba,
a hankali tasa hannu ta share
tana jin duk wata wutar masifar da ta shirya juye mishi tana sauk’a daga k’irjinta.

Muryar Jalila ce ta katsesu jin da d’an k’arfi tace
“Adama ina shayin nawa??”
Da mamaki Aaiima take kallonta sai kuma ta juya tana kallon su Mom.

Da sauri Auwal ya cika Mom ya yunk’ura zai yi wajen
yaji ta rik’e mishi hannu
yana juyowa ta girgiza mishi kai daga nan ta koma kitchen ta d’auko tea d’in daman ta gama had’awa waya take so tayi shiyasa ta manta ta fito d’aukar wayar.
Zata nufi wajen Jalilan amma ga mamakinta sai taga Auwal ya tare, yace
“Ba zata kaiwa Jalilan ba wallahi!.
Idan tana son sha to tazo ta d’auka anan d’in!”
Ya fad’a hakan yana mai karb’ar tea d’in ya d’aura akan dining sannan yaja hannun Mom d’in za suyi sama.

Da kyar mamakin Auwal ya barta ta iya ce mishi
“Ban ci abinci ba,
Bara in na gama sai muyi saman dukkanmu ko?”

Ajiyar zuciya ya sauk’e ya watsawa Jalilan wata uwar hararar da sai da y’an hanjin cikinta suka kad’a!
Daga nan ya cika hannun Mom d’in ya wuce sama.

Tabbas Jalila ta d’an sha jinin jikinta kuma it’s like kamar akwai abunda yake damunshi
sannan tanada buk’atar kud’i daga hannunshi da kuma alfarmar ya barta ta je wajen Umma
dan she can’t afford to loose Arshaad, duk da kuwa Umman tace mata akwai nasara amman tana son zuwa yau ta bita ta je da k’afafuwanta, shiyasa ta barshi kuma bata sake yiwa Mom wani yunk’uri ba ta hak’ura kawai ta barshi akan idan ya d’an huce kamar nan da 20 minutes haka zata kirashi ta zayyane mishi buk’atun ta.

Hira sosai Mom da Aaima suke yi, Jalila kuwa tana gefe tanata hura hanci.
Chan Mom ta cewa Aaiman tazo suje suci abinci.
Haka suka mik’e suka isa dining d’in sukai lunch d’insu cikin kwanciyar hankali.
Sai a sannan Aaima take tambayar Mom wacece jalila?
Murmushi kawai Mom d’in tayi sannan tace mata
“no one”
kawai, daga nan tace
“Ta mik’e ta je ta jirata a parlourn sama.

Hakan kuwa akayi,
Mom na ganin wucewar Aaima ta mik’e itama tayi kitchen…..
Dama tun d’azu ta sallami cooks da masu goge gogen gidan! Tace musu “su tafi part d’insu In akwai wani abun zata neme su!”
Har ta shiga ta d’auko abunda zata d’auka ta fito
hankalin Jalila yana kan kallo.

A dai dai stairs na bakwai ta tsaya ta zuba abunda zata zuba tayi sama abunta da cup d’in cikin sand’a.

Kamar minti biyu ta dawo bayan ta ajjiye abun hannunta a d’an gefe kad’an a nan saman ta tsaya a saman bata sauk’o ba kafin ta d’an fara sauk’owa sai kuma ta tsaya tana lek’en parlourn k’asan kafin tace
“Jalila ga Ummanki tayi miki message, ungo wayarki, tunda na hau nake ta jin k’arar wayar shine na duba d’akin naga misscalls da messages
Za ki zo ki karb’a?
Ko kuma ma kawai bara in karanto miki kina daga zaune dan na san mik’ewa yanzu aiki ce a gareki saboda yanayin da kike ciki.”
Ba tare da b’ata lokaci ba Mom ta fara karantowa
“Aslm Jalila ya gidan, yau banjki....”

A zabure Jalila ta mik’e tayi hanyar stairs tana masifa
“Adama bana son rashin mutunci!
Yanzu ke inda ace uwarki ce
tayi miki message zaki yarda a karanto miki….?”
A fusace take maganar tana tahowa da d’an cikinta wanda ya d’an fara tasowa!
K’arfen stairs d’in ta kama cikin sassarfa ta fara taka stairs d’in har da d’an gudunta,
tana zuwa kan na bakwai kuwa ta zulme santsi ya d’ebeta a take ta hantsila ta gangara ta koma k’asa ta fad’a ruf da ciki a kan cikinta!
Wata azababbiyar k’ara ta saki daga nan ta saki jiki
bata sake motsi ba!.

Da sauri Mom wadda daman da tsummanta har biyu
ta ajjiye
a gefe farkon stairs d’in
dan haka ta d’an juya ta d’auka ta sauk’o, dai dai wajen na bakwai d’in ta saka wet one d’in da ta jik’a a ruwan omo ta goge wajen tass kafin
ta saka dry one d’in ta goge wajen sosai shima.
Dai dai nan Auwal da Aaima waenda k’arar Jalilan ya janyowa hankali suka taho a tare…

Da sauri Mom ta d’ago ta kalleshi a rikice kafin tace
“Yauwa Auwal zo ka duba inaga jiri ne ya kwasheta kaga ta fad’i kamar ma ta suma bara in d’ebo ruwa.”
Ta fad’i hakan tana mai sake duk’unk’une tsummokaran a hannunta Yayinda su kuma gaba d’aya hankalinsu ke a kan Jalila…
Idan idanuwansu ba gizo suke musu ba kamar jini ne yake fitowa ta k’asan ta!
Shiyasa ma kwata kwata basu lura da Mom d’in ba
suka fara sauk’owa har suna y’ar rige rige, ita kuma ta wuce wuff!! Tayi kitchen tana mai cewa “bara in kawo ruwan”

Hankalin Aaima ba k’aramin tashi yayi ba ganin kamar ma ta mutu ne! Ga kuma jinin da taga yanata kara b’ulb’ulowa,
shi kanshi Auwal duk da cewa babban burinshi a halin yanzu yayi getting rid of Jalilan ne
amman sai da ya firgita ba kad’an ba.

Suna a haka Mom ta fito,
ruwan da ta zo da shi a jug gaba d’aya sai da ta juye mata shi amman ko gezau Jalilan bata yi ba!

Ganin haka yasa Auwal yin sama da gudu ya je ya d’auko makullin motarshi ya dawo ya zo ya kinkimeta yayi waje su Mom suna binshi a baya….
Yana gama sakata a bayan mota motocin su Dad na shigowa
ganinshi a d’an firgice yasa suka tsaidashi suka hau tambayarshi..
Da kyar ya iya ce musu Jalila ce ta fad’o a bene ta suma
ya shige ya tada motar ya fice a 70 ya bar su Mom suna sake yi musu bayani
“Allah ya sauwwak’e” suka ce.
Shi kam Dad bai ma san wacece suke magana akai ba
daga haka suka nufi side d’in Abba
dan Dad yad’an yiwa Daddy bayani a mota
So ya kamata su sameshi ya maida Ummi first kafin granpa ya tsine mishi, sannan kuma ayi maganar ta yanda za a b’ullo wa haukar Mammy
dan sun yi alk’awarin in dai sune mazan mt masu fad’a aji
to tabbas gobe sai an d’aura aure bi izinillahi!
Babu fashi…..

GANDUN ALBASA
“Ku bata iska mana ya duk kuka lullub’eta haka ne??!!”
Cewar Baaba Talatu wadda take k’arasowa wajen da kyar.
Da sauri duk aka fara matsawa gefe.
Hansai da Anty Zainab da wasu mata
Baaba Talatu ta umarta da su d’auketa a kaita parlourn
da ga nan ta cewa Maryam “ta kirawo Likitan da take zuwa tana dubasu.”

Hakan kuwa aka yi
Nan tace mata “gata nan zuwa tana ma kusa dama, su bata nan da minti goma.”
Ko da Likitan ta zo da kyar ta samu Umma ta farfad’o
amman ta bada shawarar a kaita emergency a take dan jininta ba k’aramin hawa yayi ba!
A motar Abba k’arami wanda suka iso yanzun nan shi da iyalinshi da Mahaifiyarsa da Baban sa aka kaita asibitin.
Duk da halin da take ciki da suka had’u da Ya Jamilu a waje bakin motar sai da ta tambayeshi “ina Baba?”
“Yana nan”
kawai ya iya ce mata daga nan ta shige ita da Anty Zainab wadda ta zauna a gaba suka wuce asibitin.

Da kyar Mama ta iya tsayawa aka gama kallon lefen da ita
daga nan ta wuce ta shige tayi sama…

Tun a corridor d’in d’akin Shuwa ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa. Da sauri ta tura k’ofar ta shige tana wani matsanancin kuka a tunaninta ba kowa amman tana shiga suka yi ido biyu da Sakina. K’ok’ari take yi ta danne kukan ta wayance amman ta kasa dan haka kawai sai ta durk’usa ta sake sakin shi a wajen da dukkan k’arfinta tanayi kamar ranta zai fita.........

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
54

Da sauri Sakina ta k’arasa wajenta ta hau tambayarta “mai ya faru?”

Bata iya bata amsa ba, sai da ta d’an dedeta kanta da kyar
tukunna ta d’ago jajayen idanunta tana kallon Sakina tace
“Kina da number Abba?
Baban Huda.”

A hankali Sakina ta hau girgiza mata kai..kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai
ta mik’e ta isa gado inda ta ajjiye purse d’inta,
tana cewa
“Amman ga wayar Hudan, bara in kira miki shi ta nan”

Da sauri Mama ta mik’e ta isa inda take dai dai
Sakina ta fara dialing number Abban, Mama ta sa hannu ta karb’a wayar ta kara a kunnenta.

Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna ya d’auka! A hankali taji yace
“Princess, how was your day?”

Sai da Mama ta lumshe idanunta na sakanni wasu zafafan hawaye suna zubo mata tukunna tace
“Horrible, Abba!
Her day was horrible!”.

Da sauri ya gyara zamanshi
kafin yace
“Maryam”
Cikin son sake tabbatarwa.
Chapter 66 · 0% Book details