← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 70

Sashe 43

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai bayan sallar azahar, Ummu tayi musu waya tace “su fito, suna waje.”
Sai da suka gayawa Abbas tukunna suka fita….
Babu yadda basu yi da su ba akan su shigo ciki amman suka k’i shiga gidan.
Sun d’an jima a wajen, dan ma unguwar ba mai mutane da yawa bace ba dan babu k’afa a layin, shima titin shiruuuu.
Daga baya Mama ta bawa Hudan ledar su tsami gayen da tace ta taho mata dasu.

Aikuwa taji dad’i sosai, ta dinga murna, nan Mama ta cewa Sakina “kar su durfafi mand’on suyi ta sha fa dan in suka sha da yawa zai kunche musu ciki.”

Mama, tunda sukazo dama taga wata adaidaita sahu tayi parking, sai yanzu taga mai mashin d’in yana juyowa, kamar ance ta kalli cikin napep d’in suka had’a ido da Baba!
A take gabanta ya yanke yayi wani irin fad’uwa! Sannan zufa ta hau keto mata ta ko wacce b’ular gashin dake jikinta…
Daman tun da safe da tace masa “za su fita ita da Ummu” taga kamar rashin yarda a fuskarshi. Laifinta d’aya da tak’i fad’a masa gaskiya wanda ita kuma dalilinta shine
‘Ta san ba barinta zai yi ba’ ita kuma har ga Allah tana so tazo taga Huda.

Dafa ta d’in da Ummu tayi ne yasa ta d’anyi firgigit ta dawo cikin haiyyacinta, tana mai k’ak’alo murmushi.

Cikin d’an k’arfin hali ta cewa
su Huda “su koma gida, kar a ga sun dad’e.”

Sai da suka d’anyi y’ar kwallar su, tukunna suka rabu bayan ta sake tambayar Hudan akan “tana son Arshaad d’in?” Hudan kuma ta amsa mata da ‘eh’ sannan suka wuce…
…Tunda Ummu da Madu suka zaunar da ita( Mama) suka fahimtar da ita sosai ta d’an dawo saita, tana k’ok’ari taga ta jaa y’arta itama a jiki su zauna lafiya wata rana sai labari…fushi da turjiya ba inda yake kai mutum sai garin dana sani,
In Allah yayi auren yanzu shine mafi alkhairi kuma sai anyi a yanzun to fa idan ta dage tace zata hana tsaf rabo zai iya kasheta!
Shiyasa tun ranar farko a waya bayan su Hudan sun dawo da ta tambayeta ita kuma Hudan tace mata ‘eh,
tana sonshi’ shikenan Mama ta shafe komai, ta rungumi abunda Allah ya k’addaro da hannu bibbiyu…….

Da kyar suka samu adaidaita sahu, Ummu dai ta lura akwai abunda ya firgita Mama amman ganin tayi tanbayar har ta gaji bata bata amsar komai ba ya sanya kawai ta kyaleta, a tunaninta maybe ko Abba ta gani.

Mama aka fara ajjiyewa,
sannan Ummu suka wuce ita da mai napep d’in ko shiga bata yi ba dan yau week end so tana son yin kwalema, saboda tun da Sakina ta tafi aiyuka duk sun yi mata yawa sun ch’ab’e mata.

Tun a soro taga machine d’in Baba kamar yanda ta fita ta bari, amman k’ofar d’akin shi a rufe da kwad’o!
Tunani ta fara a ranta tace “kenan bai dawo ya d’auka ba ko dai aiki ya wuce a napep d’in?
Mai yasa ma ya bisu a napep in the first place?….”
Da wannan tunanin ta k’arasa k’ofar d’akinta ta zaro makulli a y’ar purse d’inta.

Gidan shiruuu, ba kowa.

Tana d’aura makullin a ramin shi taji k’ofar tayi motsi!
A take gabanta ya yanke ya fad’i.
A hankali ta d’an tura k’ofar, ga mamakinta sai ta ga ta bud’u!
Cikin rawar murya tayi sallama tare da kutsa kai ta shiga ciki.

Turus! Haka ta ja ta tsaya sakamokon ido hud’u da suka yi da Baba wand yake a kwance a kan gadon nata
yayi pillow da hannuwanshi akan pillows d’in da ya d’aura kanshi, ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya yana d’an jijjigawa….

Ba abunda yafi d’agawa Mama hankali sai yanda taga idanun Baba sun sauya kala! Idan aka ce mata tunda ya dawo yake kuka tabbas ba zata musa ba
domin kuwa idanunsa sun yi jaaaaa!! Sun k’ank’ance hatta fuskarshi sai da ta d’an kumbura.

Bata gama fahimtar yanayin da yake ciki ba taji yace
“Ai nayi tunanin ba zaki dawo nan ba!”
Yayi maganar yana mik’ewa ya isa k’ofar d’akin, kawai taga ya sa key ya juyo yana kallon ta.

A take wani mugun tsoro ya dirar mata, for the first time da taji tsananin tsoron Baba tunda take a rayuwarta
dan hatta yanayin maganar shi yau ta sauya, kamar wani wanda yayi shaye shaye.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e, yana kallonta kafin ya sake cewa
“Tun yaushe kuka fara had’uwa?”
Yayi mata tambayar yana kallon kwayar idanunta waenda suka rine da b’acin rai da takaici, ga tsoro
sannan ga ruwan hawaye da ya cika su taf!!

Itan ma shi take kallon, tsaf ta fahimci wa yake nufi amman kawai sai tace mishi
“Da wa kenan??”

Murmushi yayi, kafin yace
“Abba”
Kanshi tsaye.

Hawayen da take k’ok’arin rik’ewa ne suka yi nasarar zubo mata, cikin karyewar zuciya tace
“Zargina kake yi?”
Bata jira jin amsarshiba taci gaba da magana
“Ka yarda ko kar ka yarda
Rabo na da in ga Abba a idona wallahi tun ranar da ya d’auke Huda daga wajena a asibiti!
Wanda a ranar kuma rabona da shi shekara goma sha takwas!..”

Cikin katseta yace
“Mai ya kai ki gidanshi yau?”

“Y’ata naje gani, kuma ko gidan ban shiga baduk da na san ka sani kuma ka gani….Indai bibiyar da kayi mini ta biya to ya kamata ace ka fahimci ba wajen Abba naje ba!
Tun da muka je ko gate d’in gidan ban tab’a ba, kuma inda wajenshi zan je to da ba zan d’auki Ummu muje tare ba da ni kad’ai zan je.”

Ajiyar zuciya ya sauk’e, ransa na k’arasa baci yace
“Kinga kin kama kanki!! Abunda nake so inji kenan! Kalmar ki ta k’arshe da kika fad’a yanzun ta bada ma’ana kwarai Maryam!
Amman karki damu dan a yau d’innan ba zan barki ba sai na tabbatar da cewa ko a hanya In Abban ya ganki ba lalle ya iya gane ki ba!”

Cikin b’acin rai Mama tace
“Ko a musulunci ba a aure da zargi! Na gaji da halinka na gaji da abunda kake yi min na gaji da komai na gidan nan!
Kuma wallahi tunda zargina kake yi to ba zan sake zaman second d’aya da kai ba!.”
Ta k’arashe maganar tana kuka ta zagayeshi…
Tana k’ok’arin fita yayi mata wata mahaukaciyar fincika, ya janyo ta da k’arfin tsiya kafin ya cillata ta tafi ta fad’a kan dressing mirrow, ta bugu sosai dan hatta madubin sai da ya fashe, sannan ta buga cikinta a jikin tudun katakon da ake jeran kayan kwalliya….

Farfashewar da gilashin yayi ne ya sanya wasu suka ji mata ciwo a goshi da hannu, take jini ya b’alle ya fara zuba.
Bai damu ba! Ya sake juyo da ita ya kifa mata wani marin da sai da ta kai k’asa, tana shirin tashi ya hau dukanta ba ji ba gani yana ball da ita! Cikin tsananin b’acin rai yana cewa “Yanzu kin shirya da su Hajiya ko? Wato kina da wajen zuwa kuma y’arki ta samu matsugunni
shine har kike da bakin ce mini za ki bar gidana saboda rashin halacci ko?
Ai daman na san using d’ina kawai kike yi tun ba yau ba, burinki a yanzu bai wucce in barki ki je ki auri Abba ba ko?
To wallahi bari kiji ko mutuwa
zan yi sai dai mu tafi tare ba dai in barki ki koma masa ba!!…”
Yana hawaye yana maganganu kamar zararre yana jibgarta….. .

Idan ana maganar dakuwa to Mama ta daku a hannunshi,
tun tana salati tana neman d’ouki har k’arfinta ya k’are ta kasa furta komai.

Ya fad’i gaskiya kam Tabbas!
Dan ko ita da kanta a yanzu da ace zata kalli madubi to ba lallai ta iya gane kanta ba, ballantana kuma Abba.
Karshema da Baba yaga abun bai yi mishi ba, katakon da take rataye jakankunan ta ya raruma ya maka mata a k’afa!
Tun daga nan da tayi wata razananniyar k’ara bata sake motsawa ba!

Fahimtar da yayi ta sume ne ya sanya shi sarara mata
ya juya nufi gefen gadon yana layi ya zauna dab’ass!!! Ya dafe kanshi sai kuma ya fashe da wani irin kuka..
Ba abunda idanunsa suke hararo masa sai irin yanda yaga Mama tana ta k’arewa gidan Abban kallo! Tayaya? How? A haka shi zatayi appreciating d’inshi!?
He has been trying his best ya goge Abba a ranta, amman abun yak’i yuwuwa sam ya
kasa cireshi a ranta, in dai abu da Abba a ciki to ba zata iya hak’ura ba
Duba fa yanda ta shirya mishi k’arya yau ta tafi gidanshi……
Yana wannan tunanin shed’an kuma yana sake rura mishi wutar zarginsu d’in da yake yi ita da Abban
A ranshi yake aiyyana “to in ba hakaba in dai ba suna tare ne ba tayaya za su dinga bawa juna mahimmanci haka?” Ya lura da yanda ran Abba ya b’aci matuk’a ranar da yaje gidanshi da y’an sanda a lokacin da ya aibanta Maryam d’in a gaban kowa, aiban ta tan da yayi ne ma Ummul abaisin dalilin da yasanya Abban ya kulle shi……

Ya jima ya na kuka kamar k’aramin Yaro, zuciyar shi ce ta bashi shawarar gwara ya karyar mata zuciya ta hanyar
nuna mata Abba fa yayi mata nisa ba zai tab’a dawowa ba!
Amman ta yanda zuciyartata za tafi karyewa ta hak’ura shine idan ta saka rai sannan ta samu full hope akan zata samu Abban for the second time sai hakan yak’i yiwuwa ta sake rasa shi!
In ta samu wannan disappointment d’in ya san zata ji zafi zuciyarta zata karye
kuma tabbas zata cire rai ta hak’ura da Abba
ta rungume shi (Baba) a matsayin Masoyi.

Da wannan tunanin ya mik’e ya fara dube dube..
Da kyar ya samo takarda, ya yi rubutu ya d’aura mata akan k’irjinta, ya juya ya bud’e k’ofar ya fice ya barta kwance cikin jini cikin mawuyacin hali.

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
47

Tun bayan sallar la’asar su Hudan suka fara neman layukan su Mama domin su ji ya suka isa gida.
Ummu dai ta d’auka amma Mama har bayan Maghrib bata d’aga ba.
Chapter 43 · 0% Book details