← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 70

Sashe 32

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin katseshi Daddy yace
“Ba interfering za muyi ba! Gramma za muyi wa magana, na san ya san yanda za tayi ta d’an shawo kanshi, at least a d’an sassauta musu, ya bari a dinga kai mu su abinci daga nan, sannan a ajjiye su a tsaftataccen waje,
dan gaskiya jikin Ummi ya bani tsoro jiya.”

Numfashi Abba ya fesar, sannan yace “ba komai zan kira Gramma d’in a waya zuwa anjima in shaa Allah.”

A hankali Aslam yayi k’asa da kanshi sannan yace.
“Zan yiwa Granpa magana, in sha Allah zai sauk’o, zan lallab’ashi.”
Shiruu, suka d’an yi, chan kuma Daddy yace “ok, hakan zai fi.”

Abba yana shirin mik’ewa, Daddy yace “akwai wata maganar still fa.
Jiya bayan mun rabu Arshaad ya kirani, wai yana son yin magana dani, i think kunyar ka yake ji shiyasa ya bari sai da na koma.”

Da mamaki Abba yace “Arshaad? Kunya ta kuma? Ikon Allah!”

Murmushi Daddy yayi, sannan yace “Bayan yace ‘yana son magana dani’ shine nace masa ‘ya zo tou muyi face to face’
Mun dad’e tare dan tare ma muka je station d’in da shi.”

D’an kallonshi Abban yayi sosai ya bashi dukkanin hankalinsa alamun yana buk’atar k’arin bayani…

Murmushi Daddy ya sake yi, kana ganinshi ka san yana cikin farin ciki da jin dad’in al’amarin, fuskarsa cike da annashuwa yace
“Good news ne,
Ashe wai ya san Huda, for the past 3 years, and suna dating ne, ita ce Yarinyar da muke da shirin zuwa nema masa aurenta!
So yanzu ya same ni ne akan ko za a fara maganar tasu tund........”

Kwarewar da Aslam yayi ne ya hanashi k’arasawa.
Da sauri Abba ya mik’a mishi ruwa dan haka ya karb’a ya d’an kurb’a yana tarin kad’an kad’an still, su kuma sunata jera mishi “sannu!”

D’aga kanshi kawai ya iya yi
Idanunsa sun yi jaaaa! Alamun ba kad’an ba yaji azabar kwarewar…

Sai da suka ga ya d’an nutsu
tukunna
Daddy ya kalli Abba yace “ya ake ciki?”

Shiruu, Abba yayi, kamar mai nazari, kafin yace “all those years kuma bai gane ta ba?”

“Abun mamaki ko? Suna tare amman basu gane junan su ba!”
Daddyn ya fad’a, kafin ya ci gaba da cewa
“Ya yiwa Dad ma maganar!
Wallahi baka ji yadda lamarinnan yayi mana dad’i ba!
Ni kam na riga ma na bashi ita.”
Ya k’arashe maganar yana murmushi mai kama da dariya wanda ke baiyyana tsantsar farin cikin da yake ciki.

A hankali Abba yayi k’arfin hali ya d’an k’ak’alo guntun murmushi kafin yace
“Tou Allah ya zab’a mana mafi alkhairi”
Ameen Daddy yace
sannan ya juyo ya kalli Aslam wanda ya runtse idanunsa ya kwantar da kansa da bayansa a jikin kujerar! Cikin zolaya Daddyn yace “wannan azumin da kaina zan buga maka wak’ar gauro!! Arshaad yayi maka wayo..”

D’an murmushi kawai yayi ba tare da ya bud’e idanunsa ba.

Abba baya son maganan shiyasa ya sako wata maganar daban dan haka suka hau tattaunawa……
Shi kam Aslam mik’ewa yayi yayi musu sallama ya kama gabanshi.

A b’angaren Hudan kuwa bayan sun gama dabdalar assignment d’insu dasu Sudais ta tafi d’akinta, tana kwanciya bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
Sai wajen 1:30 ta samu ta farka.
Alwalla tayi tayi sallah, sanin da tayi ba a gida za tayi sallar laasar ba ya sa ta karanta izu hud’u, tayi doguwar addua ta tofa, itama ta shafa.

Tana idarwa Shuraim yazo ya kirata yace “taje inji Abba, yana parlour”
Jikinta ba kwari ta fito, dan still ta sake gwada number Ummu tana shiga amman tak’i d’auka!
Gashi har yanzu Sakina itama bata kunna wayarta ba, ba kuma ta k’araso ba, Allah yasa ba hanata aka yi ba!.
Tana wannan tunanin tana tafiya domin amsa kiran Abban nata.

A parlourn saman inda sides d’insu yake ta sameshi.

Tun daga yanayin ta ya fahimci tana cikin damuwa..
Ajiyar zuciya ya sauk’e bayan ya amsa gaisuwar ta kafin yace
“Zauna, i want to talk to you”

Zama tayi, a one seater d’in parlour da yayi mata nuni da.

Ba tare da b’ata lokaci ba , ya fara magana
“D’azu Daddy yake cewa wai Arshaad ya sameshi akan maganar ku!”

Da sauri ta d’ago ta kalleshi, a zuciyarta ta hau mamakin Arshaad da kalar nerve d’inshi! Despite abunda yayi da kuma fushin da suke yi da juna amman shine yaje ya samesu da maganan! Me kenan yake so? Auren yakeso ayi ko tanaso ko bataso kenan ko me!?….

A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa, jin Abban ya sake cewa
“Yace wai you two knew each other for a while ko?”

Sai da ta taushi zuciyarta, tukunna ta iya d’agawa Abba kai alamar ‘eh’ sannan ta bashi labarin yadda Arshaad d’in ya kaisu makaranta…
Hatta wayoyin daya siya musu sai da ta fad’a mishi bata b’oye komai ba a labari da tarin alkahairan da yayi musu tun daga had’uwar su har kawo yanzu. Dan ita bata kasance mai manta alkhairi ba kwata kwata.
Tanaso ta fad’a mishi issue d’inshi da Jalila amman sai ta kasa.

Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e bayan ya gama jin bayaninta
ya na k’ok’arin fassara lamarin Arshaad amman ya kasa!
Tabbas akwai abinda Arshaad ya sani tun farko kuma yayi shiru wanda shi kad’ai ya san dalilin yin shirun da yayi! Dan a cikin labarin da Huda ta bashi yanzun yaji inda Arshaad ya had’u da Mama ba so d’aya ba, and in dai Arshaad ne ya tattare mishi d’akinsa kwanakin baya da za suyi parking ya kai personal kayayyakinshi gidanshi na kwandila, tou tabbas ya san wacece Huda!

Ahankali yaji tace
“Amman Abba yanzu bama tare mun yi fad’a sosai..”
Ta k’arashe maganar ta na kuma yin k’asa da kanta.

Murmushi Abban yayi kafin
yace
“Ai kuwa ke kad’ai kike fad’anki! Don shi gashi yazo yana binmu one by one
yana expressing how much he loves you.”

Da sauri tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta…
Tashi d’aya Maryam ce ta fad’o mishi arai, yanayin kunyarsu iri d’aya ce, kalli fa fad’a tace sunayi amman kuma anyi magana ta hau jin kunya….
Murmushi yayi
kafin yace
“Kije ki shirya dan na san yanzu Auwal zai zo, Shuraim yace min “zai bada hadda yau a islamiyyarsu da suke zuwa duk asabar da lahadi so nan zai je shi ba zai samu daman binku ba.
Sai kuje da ke da Sudais kawai.”

“To” tace, sannan ta mik’e,
har tayi gaba sai kuma ta juyo
Tace
“Abba Allah da gaske nake yi munyi fad’a dashi, fad’an gaske!”

Dariya ta bashi ganin yanda ta dage akan ita fa sun yi fad’a, amman ko a cikin bayaninta, yadda take yabon Arshaad d’in, ya sanya ya fahimci still tana son abunta.

Murmushi kawai ya sake yi yace
“Tam na yarda kun yi fad’a, shikenan.”
Ahankali ta juya ta wuce don taje ta shirya.

Lumshe idanunsa yayi ya kwantar da bayanshi da kanshi jikin kujerar...
.....Zai fara yin magana da Arshaad first! He just hope yanada kwakkwaran reason ba munafuntar su yayi ba all this time..
Saboda in dai hakane tou gaskiya zai murzawa idanunsa toka, ya hanashi Huda! Dan ba zai bari y’arsa ta rayu da Namiji mai b’oye b’oye ba.

Ya lura da tana sonshi, so yana adduar Allah yasa Arshaad d’in ya zamana yanada reason d’in da zai kare kanshi kwakkwara!
Zai yi farin ciki da hakan
domin kuwa ya san that’s wat she wants..
Dukda kuwa yana da wani buri da ya d’aura akanta tun lokacin da ya fahimci yanada y’a mace mai shekarunta
amman tunda he’s late ta riga ta zab’i Arshaad, shikenan ba komai, yana yi mata fatan alkhairi…..

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
43.

Cikin nutsuwa ta shirya ta d’auki y’ar k’aramar jaka da wayarta ta fito.
Bata samu Abba a wanann parlourn ba! Dan
haka ta sauk’a chan k’asa cikin nutsuwarta…
Tun kafin ta k’arasa ta hangoshi shi da Sudais wanda
shima har ya shirya da alamun ita yake jira.

Har ta sauk’o Abba bai lura ba, yana nan ya dulmiya duniyar tunani….surutun Sudais ne ya d’an dawo da hankalinshi parlourn, dai dai nan kamar had’in baki Auwal ya shigo..
Riga da wando ne a jikinshi, rigar maroon mai dogon hannu
da black jeans asalin crazy!
Ga wani had’add’en takalmi sau ciki mai mugun kyau black!
D’azu uban gashi ne a kanshi amman yanzu yayi sabon aski an aske gefe da gefe da k’eyar an bar tsakiyan (saman kan) lallausar sumar ta taru a kanannad’e iya tsakiya sai shek’i take yi, gefe wajen kunnenshi na dama ta sama inda aka aske an sake bi anyi wani style kamar zigzag, asalin farar fatar kan nashi ta baiyyana ta fito da design d’in radau!!
Ga wani bracelet kamar sark’a a hannun daman shi, sannan ya maka wani arnen bak’in glass mai shek’i wanda kana gani kasan mai mugun tsada ne……

Yana shigowa k’amshin turarenshi ya gauraye ko ina.
Tafe yake yana danna waya, har ya k’araso cikin parlourn bai ma lura da su Abban ba.

Da Hudan ya fara lura kasancewar ta a tsaye
sai kuma sudais wanda ya k’arasa wajenshi da sauri yace “Ya Auwal har da wannan wajen nan zaka kaimu ko? Wanda ake sa glass ayi game..”
Dariya yayi ya d’an sa hannunshi akanshi ya hautsina y’ar sumar data d’an tarar mishi ba sosai ba sannan yace
“Ashe yau za asha ihu kenan”
Dariya dukkansu suka yi, sannan ya dago ya kalli Huda..
Three quarter riga mai fad’i ce a jikinta wadda ta wuce mata har gaba da guiwowinta peach colour, sai pencil trouser white, ta yi mopling da white vail, sai y’ar k’aramar white bag d’inta.
Kwalli kad’ai ne a idonta sai d’an pink d’in jam baki data shafa amman tayi masifar kyau!
A ranshi yace “Yarinyar akwai kyau kamar aljana” sai dai shi ko sau d’aya bata tab’a burgeshi ba, asalima shi haushin ta yake ji! Ko dan ita tayi sanadiyyar zuwan su Mom da Mammy cell ne, oho!
Duk da ba wani shiri yake yi da Mom d’in tashi ba amman yayi mugun jin zafin abunda aka yi musu ata dalilin y’ar k’aramar Yarinya.

Gyaran muryar da Abba yayi ne ya katse mishi tunani..
Bai ma lura da shi ba, sai yanzun.
Chapter 32 · 0% Book details