Sashe 33
So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Abba ashe kana nan.”
Ya fad’a yana d’an murmushi.
A b’angaren Abba kuwa yanda yaga ya kafe mishi y’a da ido ne ya sanya yaji kamar yace su fasa fitar!
Ajiyar zuciya ya sauk’e yayi saurin kawar da tunanin daga zuciyarshi, sannan ya sake kallon Auwal d’in yace
“Kallo d’aya tak! Duk wani mai isheshen hankali zai yi maka ya fara yi maka zargin gudowa kayi daga gidan mahaukata!!Kalli wandon ka kamar wanda aka yi maka gorin kaya, kalla nan” Abban ya mik’e yana nuna mishi wandon da hannunsa kafin yace “har cinyarka ana iya hangowa!
Wannan d’an iskan askin shi kuma an hanaka amman naga abun naka gaba yake yi dan na yau ma yafi na kullum! Sai kace wani zakara.
Harda sark’a a hannu!!
Wai ni auwal mai kake son ka zama ne? Eh??”
Yayi mishi tambayar cikin b’acin rai, bai jira jin amsar shi ba yace
“Wallahi ka tabbar ka seseta wannan d’an iskan askin kafin ku dawo gidannan inba hakaba kowa sai ya ji kanmu!”
Yana gama fad’in haka yayi hanyar sama ranshi a b’ace…
Gaba d’aya In ka kalli Auwal ba zaka tab’a kiranshi da musulmi ba, ba abunda yafi b’ata mishi rai kamar sark’ar hannunshi ya lura harda wata sark’a a wuyanshi wadda ta b’uya a cikin rigar kawai shiru yayi masa dan in yaci gaba da kulashi zuciya zata jashi ya fella mishi mari!!
Anyi maganan anyi har an gaji amman saboda ya raina mutane sam bai fasa ba.
Auwal kuwa kamar ya had’iye zuciya…
Tunda Abba ya fara fad’a ya had’e rai! Ba abunda yafi b’ata mishi rai irin tijarar da Abban yayi mishi a gaban Yara, don haka ya ja hannun Sudais suka fice ba tare da yabi ta kan Hudan ba.
Ganin da tayi ranshine a b’ace yasa kawai ta bishi wajen, bata biye sa ba.
Sudais yasa a gaba, amman dake Yaron ya fishi hankali yana ganin Hudan ta taho ya bud’e mata motar shi yayi saurin tsallakawa baya.
Kamar zai yi magana sai kuma kawai yayi shiru.
Ko ida rufe murfin motar bata yi ba ya fige ta da azabar gudu..
Daman masu gadin tun da suka hangoshi ya tada mota suka wangale gate, gudun kar garin saurin bud’ewa idan ya taho yayi gaba da wani! In kuma kayi jinkiri a balbaleka da zage zage! Komin tsufan mutum.
Gudu yake shatatawa kamar zai tashi sama..
Hudan duk ta tsure, ta rik’e kujeran da take kai gam! Ta k’ame, yana lura da ita wanda hakan ne ma ya sa ya sake k’arfin gudun nashi.
Ikon Allah ne kawai ya kaisu inda za suje,
Ita ba sanin munjibur park d’in tayi ba, shiyasa bata gane inda suke ba!
“Fito”
Yace, yana k’ok’arin bud’e motar ya fita.
Sudais ma ya fito daga baya.
Tana fitowa tun kafin ta rufe motar gabanta yayi mugun fad’uwa ganin su a police station.
Juyowa tayi tana kallonshi wanda zagayowarshi kenan
kafin tayi magana yace
“Su Mom zan nuna miki, halinda suke ciki all because of you!”
Ganin ya tsareta da ido ne yasa ta wucewa jikinta sai karkarwa yake yi.
Direct wajen da suke ya nufa, bayan ya amsa gaisuwar police d’in da suka tarar a reception, sannan ya zaunar da Sudais a kan kujerun wajen yace mishi “kar ya kuskura ya tashi, ya jirasu a nan”
Da kyar ta iya k’arasawa wajen!
Tun daga lokacin jikinta ya mutu, yayi wani irin sanyi…
Da kyar ta iya bud’e baki ta gaishesu amman ba wadda ta amsa mata tsakanin Mammy da Mom, Ummi ce wadda take mugun jin jiki ta d’ago da ta kalle ta a hankali tace
“Lafiya Alhamdulillah.”
Sannan ta komar da kanta k’asa ta kwantar.
Wata jakar leda wadda ya shigo da ita yayi saurin mik’a musu, ganin wani police ya taho yasa Mammy tayi saurin b’oyewa a cikin mayafinta ,
sannan tace
“Ka cewa Arshaad inata jiranshi akan maganar mu naji shiru!!
Shekaran jiya dana samu waya nayi mishi more than 20 miss calls amman bai d’auka ba k’arshema kashe wayar yayi!
Kace nace Dan ubanshi shi nake jira in kuma ba zai iya ba to ya daina kashe mini waya kawai ya fito fili ya fad’a min!!”
Hudan kamar tace mata ‘ba kashe wayar yayi ba’ Don tana gani kamar wannan number da tayita kira ranar nan da wayar tana a hannunta ne Mammy take magana akai! Sanann sub’ucewa wayar tayi a hannunta ta fashe….
Amman kuma kawai sai tayi shiru ganin yanda ko inda take Mammyn bata kalla ba.
“Muje”
taji muryan Auwal.
A hankali tace musu
“Sai anjima’
Nan ma ba wanda ya kulata sau Ummi dake kwance taga ta d’an d’aga mata kai alamun ok.
Suna fita
Mom tacewa Mammy
“Nifa gaskiya ko Arshaad ya kawo kud’ad’en nan ba inda zan biki mu fita, maybe ma yaudararki police d’in nan yake shirin yi, dan ba miliyan uku ba gani nake ko miliyan arba’in zaki bashi ba lalle ya iya k’etare umarnin Granpa ba!
And in ma ya yarda, bakya tunanin irin mummunan hukuncin da shi Granpa d’in zai yanke mana muddin yaji labari?”
Murmushin takaici Mammy tayi kafin tace “Adama na gaji da halin mutanen nan! Na kawo wuya! Ke dai kawai kamar yadda na fad’a miki ‘ki zuba min ido’ wuyarta kawai mu fita daga nan, dakanshi shi Granpa d’in zai kira mu mu koma gidajenmu…
Shi kuma Yahaya wallahi kinji rantsuwar d’an musulmi ko? Sai na gasa mishi aya a hannu!
Wai ace mutumin nan ya dawo amman ban isa yazo ya ganni ba?
Hak’uri na ya k’are Adama!Maganar gaskiya na gaji da cin kashin da ake min na gaji!!!”
Ta k’arashe maganar tana share kwallar data zubo mata.
Matsowa daff da ita Mom tayi tana magana k’asa k’asa gudun kar Ummi taji, tana cewa
“To ki kira maman ki mana, ai kina nan ma ita d’in zata iya yi mana komai”
Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e kafin tace
“Tace babu ruwan ta, ranar dana ari wayar ai har ita na kira kin tafi fitsari lokacin, tace in yi hak’uri har lokacin daya yanke yayi, ita ba ruwan ta waye waye…..
Ni k’arshe ma kashe wayar nayi dan tsabar bak’in ciki.
Adama ba abunda yake d’aga min hankali irin maganar nan ta fita wasu suji, dukda shima Granpa d’in na san k’ok’arin b’oyewa yake tayi dan Inajin wanda yake sa mana ido yana gayawa wani Abokin shi wai ‘kar a had’a mu da kowa Granpa d’in yayi waya yace a ware mu.’
Inaga yana gudun kar wani ya gane mu ne.
Amman fa kin san zancen duniya ba ya b’uya, wacce irin kunya kike tunanin zamu kwasa idan k’awayenmu sukaji labari?”.
Ajiyar zuciya Mom ta sauk’e kafin tace
“Shikenan ba damuwa, amman kinada tabbacin ba zata kwab’e mana ba ko?”
D’aga mata kai kawai tayi alamar ‘eh’
Shikenan nima zan gwada yiwa Auwal magana, inaga maybe ya taimaka, dan
naga kamar abun ya dameshi.
In kuma yak’i, to ko sark’ata ce zance ya duba ya d’auki d’aya ya saida sai ya kawo kud’in”
Cewar Mom.
“Allah ya shige mana gaba”Mammy tace
Daganan suka ci gaba da maganganunsu, ita kam Ummi tun d’azu bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, ata dalilin allurar da akayi mata.....
Tabbas su Ummi basu kyautaba amman a nata tunanin bai kamata ayi musu haka ba! Hukuncin yayi yawa kuma abunda akai musu d’in tabbas zai jawo mata bak’in jini a wajen y’ay’ansu ne, besides ita tama yafe musu har k’asan zuciyarta……
Tana waennan tunanin suka isa munjibir park, sun sha doguwar tafiya ba kad’an ba, ita Huda jikinta ma duk ya fara ciwo.
Parking yayi duk suka fito, sai da ya gama komai ya siyaawa Sudais ice cream d’inshi, ya d’aura shi a lilo tukunna ya dawo inda take tsaye.
Kallonta yayi kafin yace “Ko kema lilon kike son hawa k’atuwa dake??”
Kauda kai tayi ta girgiza kai, kawai.
Murmushi yayi kafin yace
“Ta kwancen, itace wacce aka saki Mamanki a dalilinta! Matar Abbanki har a yanzu.”
Taji zafin maganar amman ta shareshi kawai…
“Wadda ta bani sak’o kuma, na san daga maganar da tayi mini kin fahimci Mahaifiyar Arshaad da Aaima ce!
D’ayar kuma Mom d’ita ce!
Ummi, ko dan su Sudais da kike pretending kina so, ya kamata ki tausaya mata.
Mammy kuwa ko Arshaad ya kauda kai saboda son da yake yi miki, to ina tausaya miki In Aaima ta dawo dan sam ba za kiji dad’i ba at all.
Mom d’ina kuwa, to be sincere ba ma wani shiri da ita, but blood is thick!
And you should know me by now
I’m capable of anything..
Huda! All you need to do
Is talk to your stubborn father
ya san abun yi…
Idan ba haka ba kuma
Wallahi!
Ni kaina ina jin tsoron abunda zan yi miki!…
A matsayin ki na so called cousin d’ina yasanya nayi
deciding in baki warning first akan in aiwatar da abunda nayi niyya akanki kai tsaye.
Idan kika yi min abunda nakeso to kin tsira
In kuma kika yi taurin kai!
To fa gaskiya i can’t save you from me.
Lastly, kar ki kuskura kiyi mentioning cell d’in da kika je yau, to anyone.”
Ya k’arashe maganar yana kallon cikin idonta.
Da sauri tayi k’asa da kanta…
Tabbas ta hango b’acin rai a cikin idanuwanshi, gashi har colour d’insu ya soma chanza wa.
Bud’e baki yayi zai yi magana yaji an dafa shi ta baya.
Kafin ya juya ita ta zxagayo gabanshi ta tsaya tsakaninshi da Huda.
Murmushi yayi kafin yace
“Har kin iso?”
Yayi maganan yana mai rik’o waist d’inta ya d’an jawota jikinshi.
Yadda Huda ta zabura zaka d’auka ita aka janyo..
D’an jaa da baya budurwar tayi ta d’an juyo tana kallon Hudan kafin tace
“Who’s she??”
Tayi masa tambayar ba tare
data kalleshi ba, da d’an alamun b’acin rai a fuskarta.
Murmushi yayi kafin yace
“Relax! She’s just a cousin, daga k’auye tazo shine Daddy yace In kawota ta ga gari.”
Ture hannunshi da yake rik’e da waist d’inta tayi, har yanzu idonta nakan Hudan wadda ita ma ta kasa d’auke idanunta akan su tana kallon ikon Allah, budurwar tace
“Cousin and more, ha?”