← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 70

Sashe 15

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai tashi fahimtar babu Mom a gidan ba sai da safe da ya fito zai tafi office!!
Cikin nutsuwa yake break fast d’inshi, tun sauk’owarshi Jalila dake kitchen ta had’a uban milo da mdara tana sha ta jiyoshi, tana lek’awa kuwa ta ganshi..
Don haka da sauri ta koma ta hau danna kwab’etar a bakinta har tana kwarewa, cikin minti kad’an ta shanye sannan ta goge bakinta ta nufi k’ofa dan bata so ya fita ba tare data karbi uban kud’ad’en data k’udira a ranta zata amsa ba!
Dan bazata iya jira sati biyu ya cika ba kamar yadda Umma ta fad’a ba..
Sannan inta karb’i kud’in ma ba bata zata ke yi ba
Dan ita ba sakarya bace ba
tana gani sati hudu da suka wuce
Kaff kud’in hannunsu sai da suka Kare aka dinga cewa ‘Auwal zai dawo gareta a rikice kuma da maganar auren ganga ganga!’
Ga shi har ita tazo gidan shi bai je ba
k’arshentama da tazo d’in da mari yayi mata sannu da zuwa…
Sannan bataga alamar rabuwa tsakanin Huda da Arshaad ba dan haka
kud’inta kawai zata amsa taje ta yi fafa na kwana biyu ta sayi kayan kwalliya da turarurruka tazo ta yak’i Arshaad tunda gasu a gida d’aya!…..
Da wannan tunanin ta fice daga kitchen d’in

Ya gama breakfast ya mik’e kenan ita kuma tana fitowa.
Sarai ya ganta amman sai ya basar kawai, ya juya ya d’auka jakar shi kafin ya fara k’ok’arin barin wajen, dasauri ta shiga gabanshi ta tsaya sannan tasa hannu ta rik’e jakar, bata damu ta gaisheshi ko ta tambayi ya yake ba tace
“Muna biki, inaso zan je, kuma ni wannan mai girkin gaskiya bana iya cin abincin ta tayar min da zuciya yake yi, tun jiya da Adama ta tafi nake fama da yunwa, so anjima ka taho da wata sabuwar mai abincin ta gwada inga ko zan iya ci!”

Yayi mamaki da yaji tace ‘Mom bata nan’, a ransa yace “to Ina ta tafi kenan??” Sai kuma ya raya “anyways zai kira ta yana fita yaji mai ya faru!
Dan kwata kwata he can’t stand Jalila, shiyasa cikin k’aguwa da son ta rabu da shi yace mata “tou” kawai, sannan ya fara k’ok’arin barin wajen.
Da mamaki yake kallon ta ganin tak’i sakin mishi jaka, da d’an fad’a yace “dalla Malama cikani kar In yin latti!”

Itama cikin tsantsar rashin kunya tace “sai aikin zuwa office kullum amman kwakwalwa kamar ta kifi, simple abu idan an fad’a maka ba zaka d’auka ba ni ina mamakin ma ta yadda kake yin aikin wallahi!!
Da kaji nace maka za muyi biki Ina so zan je kenan! sannan
ina nufin yau nake son zuwa maybe kuma kwana zan yi maybe ko kwana biyu
dan an riga an fara bikin!
Dan haka ka saka driver ya kaini idan na gama kuma yaje ya d’auko ni, in kuma ka bari na dawo da kaina to ka san mai zai faru ba sai na tsaya yi maka bayani ba!.
Sannan kuma inaso a cika min jaka ta!”
Ta k’arashe maganar tana hard’e hannayenta a kan k’irji, sannan ta fara jijjiga irin ina sauraronka d’innan.

Shiru Auwal yayi, ji yake kamar ya shak’eta ta mutu kowa ma ya huta!
Cike da gajiya da ita yace
“Nawa kike buk’ata??”
Ba tare da b’ata lokaci ba tace
“Dubu d’ari shidda!!”.
kallon tsana ya fara jifanta da shi, chaan! Kuma sai ya d’an yi murmushi kana ya matso kusa da ita
ya mik’o mata hannunshi kamar wanda zai karb’i wani abun, cikin yin k’asa da murya ahankali yace
“Ban gishiri in baki manda!”
Yana murmushi tare da d’age mata girarshi d’aya.

Tsaki Jalila taja, Dan sarai ta fahimci me yake nufi hakan yasa ta fara k’ok’arin barin wajen….

Zagayeshi tayi da sauri ganin yana shirin ruk’ota, amman bata tsira ba dan tana wuce shi shima ya juyo kafin ta ankara taji ya ruk’o hannunta sannan cikin sanyin jiki yace
“Ko har kin hak’ura da kud’in yanzu kuma bakya so? Na San fa kema kinyi missin….”
Maganarshi ce ta mak’ale sakamokon idanuwanshi da suka sauk’a a kan Daddy wanda ya hard’e hannuwanshi kawai ya zuba musu ido, kana ganin fuskarshi ka san yana cikin tsananin b’acin rai!.

Da sauri Auwal ya cika hannun Jalila sannan yayi saurin yin k’asa da kanshi..
Daddy yana k’arasowa ya jaa hannunshi kawai ba tare da ya ce mishi k’ala ba suka fice.
Mukullin mota ya bashi sannan ya fad’a mishi inda zai kai su.

Auwal yana son tambayarshi ‘me zai kai su police station’ amman sai kawai yaja bakinshi yayi shiru sakamokon ganin yadda Daddyn ya had’e fuskarsa tamau!!

Suna shiga ciki Auwal ya fara yatsina yana toshe hanci sannan a hankali ya cewa Daddyn “pls, zan jira ka a waje.”

Banza Daddy yayi da shi bai ce mishi komai ba..
Suna a haka dpo d’in ya fito, yana ganin Daddy ya ganeshi
dan haka ya shiga gaidashi cikin girmamawa..
Amsawa Daddy yayi sannan yace mishi “yana son ganin su Mom”
Sai a lokacin Auwal ya d’ago a razane yana kallonshi fuskarsa na nuna buk’atar son jin k’arin bayani.

Babu wanda yace mishi komai, dpo d’inne yace “To dan Allah yaje office d’inshi zai kawo mishi su”
Daddy bai so hakan ba amman yadda dpo d’in ya nace ne yasa kawai suka nufi office d’in nashi shi da Auwal.

Ko minti biyar ba a yi ba aka shigo da su!
Dakyar Auwal da Daddy suka iya gane Ummi, Mom itama ta wujigatu ba k’arya!
Duk cikin su Mammy ce mai d’an kyan gani.

Mom tanaganinsu ta fashe da kuka, da sauri Daddy yaje ya rumgume yayi ta lallashinta tukunna ta zauna.
Ummi ma kukan take yi, Mammy kuwa suna gaisawa ta nemi waje ta zauna, dama tsaftataccen wuri take ta adduar samu don ta samu damar baje hanci ta shak’i tsaftatacciyar iska.

Auwal gaba d’aya kanshi ya d’aure, dan haka yaje wajen Mammy ya hau tambayarta ba’asi, dan ya lura ita kad’ai ce ke a cikin hankalinta.
Tiryan tiryan haka Mamyn ta zaiyyano mishi komai, tana gamawa ta fashe da kuka kafin tace
“Na san mun yi laifi, amman wallahi hukuncin nan yayi mana tsauri! Ka ga inda aka ajjiye mu kuwa!
Wallahi ko wajen tumaki ya fishi daraja,tsafta da kyan gani
A wajen fa ake kashi ake fitsari, gashi ka san Adama da Zainab suna da allergy..kalli jikinsu kaga gaba d’aya borin jini ne,jiya ba wanda ya runtsa a cikinmu!!
Ban san tayaya za muyi wata biyu a irin wajen nan ba, dan wallahi Auwal na tabbatar muna yin sati a nan to sai dai a kwashi gawarwakinmu.......”
Tana gama fad’an haka ta sake rushewa da wani irin kuka mai cin rai.

A fusace Auwal ya mik’e a wajen yayi hanyar fita, Daddy yana ganin yanayin mik’ewar tashi shima yayi saurin mik’ewa ya sha gabanshi yana cewa “ina zaka je?”

Cikin d’acin zuciya yace “ba ruwan ka Daddy, this is between me and Abba!!”
Yana gama fad’an haka ya sake yunk’urin fita, da sauri Mom wadda itama ta k’araso wajen tayi hanzarin rik’o hannunshi, yana juyowa yace
“Mom dan Allah ki barni kawai, i need to teach him a lesson!! In banda tsabar rainin wayo a kan y’arsa zai yi muku haka? Y’ar gwal ce ita?”

Cikin fad’a Daddy yace
“Tou sannu sarkin marasa kunya!! Uncle d’in naka zaka koyawa hankali? Haukan naka ya tashi daga tsakaninku yana shirin haurawa kan y’an uwana kenan?? To wallahi a kul d’inka Auwal!!
Raina a b’ace yake da kai tun d’azu shiru kawai nayi maka, kar ka yarda ka kaini mak’ura!!”
Yana gama fad’an hakan ya koma wajen dpo ranshi a mugun b’ace…

Da sauri Mom ta sake rik’o hannunshi duka biyun ta matse gagam sannan ta fara magana
“Kayi hak’uri ka sauk’a daga kan wannan dokin zuciyar Auwal, dan babu inda zai kaimu, idan ma za a hukuntasu to bata haka za a yi ba, kaji??
Yanzu na tabbatar kana yin wani abun laifin ka za a gani, kuma nima kaga dai gani da nawa issue d’in, sannan ga matsalar ka da Granpa abun zai yi mana yawa.”
Cikin yin k’asa da murya tace
“Kana gani ai Arshaad da ya fika wayo tun jiya bai zo ba, kuma na tabbatar yana cikin gidan, shi kuma Aslam dayake babu uwar shi a ciki ta sama ya mak’ale yanata kallonmu bai ce ko yayi komaiba, bai san ba ganshiba.
Don haka inaso kayi hak’uri ka danne zuciyar ka, tukunna sai mu san abun yi, kaji ko?”.

Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya yana bin hannun Mahaifiyar tashi da yayi jajur ya kumbura ga borin jini kala kala, da ido. A haka har gara ita nata da d’an sauk’i akan Ummi, dan ita nata har fuska…

“Kaji ko?”
d’in da tace mishi ne ya sanya yayi mata nodding kai kawai sannan ya koma ya zauna, itama ta dawo ta zauna.

A Chan teburin dpo kuwa
Babu yadda Daddy bai yi da shi ba akan “zai biya ko nawa ne a ware musu office d’in wani d’an sandan a gyara musu toilet su dinga amfani da shi su uku kawai zuwa nan da 2 months d’in”!
Amman furr!! Dpo d’in yak’i, yace
“Jiya bayan na dawo sojoji Mahaifinta ya aiko suka kaini har gabanshi da daddare
ya ja mini warning akan in tabbatar na basu horo mai tsanani, kuma ya shaidamin yana da cid’s da yawa, muddin na k’etare umarnin shi to a bakin aikina.
Tsabar yanaso ya tabbatar min idanunsa suna kaina, yau da safe ya kirani, duk wani abinda ya faru a nan daga dawowata zuwa tafiya ta gida da zuwana nan yau da safen kaff! Babu abinda bai gayamin ba, har na cikin dare wanda bananan a bakin shi na ji.
Hatta abinci yace sau biyu kawai za a dinga basu…

So, dan haka dan Allah ka rufamin asiri ina son taimakonku tabbas amman ina jin tsoron rasa aiki na. Da kuma hukunci da yayi alk’awarin yanke min, wanda ban san meneneba.”
Chapter 15 · 0% Book details