← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 70

Sashe 60

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Mammy tace
“Matsalata da Dad, Aisha ce!
Na rigada na sani.
Ki bari kawai in fara kashe wannan boss d’in after that idan na tashi bi ta kan Aisha wallahi duk wanda ya ce zai shiga tsakani sai na had’a da shi”.
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice da sauri tana share hawayenta.
Ko bi ta kan y’an parlourn bata yi ba, ta wuce sama abunta tana huci.

Tana fita Maman nata ta sauk’e ajiyar zuciya!
A hankali ta kalli Hajiya Binta tace
“Allah ya rufa asiri..tunda tak’i jin maganata ni uwarta!
Ni zan tafi yanzu, idan ta yarda aje wajen event d’in su Amaryar to ku rakashi
Idan kuma ta hana sai ku zuba mata ido.
Sannan ki samu y’an uwanki ki jasu gefe kice nace ‘ko me zata yi kar wanda yayi yunk’urin hanata’
Ita ta sani.
Taje tayi yadda taga ya dace.”
Tana gama fad’in haka itama tayi hanyar waje cikin y’ar tafiyar su ta tsoffi...

Sallama ta yiwa matan dake babban parlourn daga nan ta wuce abunta.
Har k’ofar mota ragowar sister’s d’in Mammy guda biyu k’annenta suka rakata, suka
bud’e mata gidan baya
ta shiga suka rufe driver yaja suka tafi.
Su duk basu san wainar da ake toyawa ba Hajiya Binta wadda ta kasa fitowa parlourn tun tafiyar Mahaifiyar tasu ce kawai ta sani dan haka suna komawa aka shiga bidiri ana ciye ciye ana ta hotuna!
Fitowar Ango da Aaima ne ya k’arawa abun armashi, ba a dad’e ba Mom da Ummi wadda ta d’an ji sauk’i suka shigo, nan
suka had’u aka yi ta hotuna….

After kamar 30 minutes haka, aka fara shirye shiryen tafiya gidan su Amarya, anata had’a gifts..
Dai dai nan Mammy ta sauk’o.

Sai da gaban Arshaad ya yanke ya fad’i amman ya dake ya k’arasa inda take ya fara k’ok’arin jan hannunta yana cewa “ta zo su yi hoto”

Ko alamar zata motsa bata yi ba dan haka ya tsaya ya d’an kalleta yace
“Mammy dan Allah mana,
mutane suna kallo fa, ki zo
muje”
Ya fad’a yana sake k’ok’arin janta.
Suna a haka sisters d’inta da Aaima suka iso wajen.
Fisgewa tayi da mugun k’arfi, kafin tace masa
“Idan baka je ka cire wannan wata kalar shigar ba
wallahi Arshaad sai na ci ubanka!!
Sannan
ni za ka mayar y’ar iska mai magana biyu?
Mu gama magana da kai amma ka je ka wani shirya tsaf sannan dan tsabar raini kazo kana ce min wani muje muyi hoto?
Da kai da hoton kun ci kutumar ubanku!”

Runtse idanunsa yayi da mugun k’arfi!
Dai dai nan Mommy da Aslam waenda suka shigo yanzun
suka nufo su, suka k’araso!
Kusan duk sun ji furucinta.

Da mamaki suke kallonta,
a hankali Aslam yad’an dafa kafad’ar Arshaad d’in, dukda bai gama sanin wainar da ake toyawa ba amman yad’an fahimci wani abun, hakan
ya sanya shi jin mugun tausayinsa ya rufeshi....

Da mamaki Mommy take kallon Mammy
kafin tace
“Lafiya kuwa?
Me naji kamar kin ce?”

“Amin, wa alaiki Assalam Aisha!”
Mammy ta fad’a cikin tsareta da ido tana jin wani mugun tsanarta na taso mata…

Murmushi Mommy tayi
kafin tace “Assalam alaikom,
me yake faruwa ne Arshaad?”
Ta yi maganar tana me mayar da akalar tambayar tata kan Arshaad
saboda tsananin mamakin Mammy da ya rufeta..
Tunda suke tare ko da wasa Mammy bata tab’a yi mata kwatankwacin irin haka ba.

Arshaad Yana shirin yin magana Mom ta k’araso
tace
“Ya dai? Kukayi cirko cirko duk anan?”
Kafin ta kalli Mommy tace
“Ina ta yi miki magana Mommy, kika k’i kulani kika wuce.
Ina wuni.”
Dai dai nan Ummi itama ta k’araso wajen nasu.
Cikin kulawa Mommy tace
“Yi hak’uri Adama,
hankalina ya yo kansu ne dan naga kamar ba k’alau ba.”

Da sauri Mammy tace
“K’alau d’in....”

Cikin katseta da d’an k’arfi Mom tace
“Haba k’alau ne mana,
komai normal Ina?”
Ta fad’i hakan tana kallon Mammy da d’an sign d’in tayi calming down mana…

Tsaf Mammy ta fahimceta..
Itafa ta rasa gane dalilin da yasa su Adama da y’an uwanta suke tunanin zata iya yin wata kissa a wannan stage d’in!
Taya ma zata iya danne wannan duka dubu d’in da akai mata?
Ya an dake ta kuma suna so su hana ta kuka??…

Mom na shirin yin magana taji Ummi tace
“Arshaad akwai matsala ne?
Yi magana mana, kar
lokaci ya k’ure!
Kaga yanzu tafiya za mu yi.”

Da sauri Mommy tace
“Dankuwa har na cewa Maryam d’in ma mun kusan fitowa, na san mu suke jira yanzu haka.”

Ajiyar zuciya Mom ta sauk’e
tana ji kamar ta shak’e Mommy !
‘Wato irin ita har ta jone da Maryam d’innan’.

Mammy na shirin yin magana

Arshaad wanda ya ga b’oye b’oye shi ba inda zai kaisa dan kwata kwata ya kasa shawo kan Mammy kuma yana ganin in dai ya gayawa Mommy maybe a samu sauk’i ta hanyar Dad da Gramma
ne, yace
“Mommy cewa tayi ko a fasa auren ko ta tsine min”

Da sauri Mommy tace
“Whatt!!”
Cikin firgici kafin ta juya kan Mammy tace
“Rukayya wanne aure kike so a fasa?”

Ba tare da b’ata lokaci ba
cikin b’acin rai da tarar numfashin ta tace
“Auren Huda da Arshaad, Aisha!
Shi nake so a fasa
Idan kuma kina da ja to sai in ji...”

Sai a sannan Aslam ya d’ago ya kalleta, bata san mai ya faru ba amman sai Yaron yayi mata kwarjini ta kasa ci gaba da magana.

Mommy ta yunk’uro za tayi magana kenan taji Aslam d’in ya rik’e hannunta, ba tare
da yace mata uffan ba kawai ya juya da ita suka fara tafiya.

Har suka fice a parlourn bai ce uffan ba ita kuma bata yi mishi tirjiya ba, sai da suka isa tsakiyar compound d’in tukunna ya zaro waya
ya danna kiran Dad!
Ba tare da b’ata lokaci na ya gaya mishi halin da ake ciki…

Suna gama wayar, ya ga
tana k’ok’arin komawa
A hankali yace
“Mommy please kar ki koma ciki, kina jin fa yanda take yi miki magana ba respect.
Please dan Allah kar ki je.”

Za tayi magana yace
“Please Mommy, i can’t take it”

Ajiyar zuciya ta sauk’e
kafin a hankali tace
“To kaini gidansu Huda.
I have to be there,
suna ta expecting d’inmu.”

Da k’arfi yaji zuciyarshi ta buga !
Sai kuma yaji zafi kamar
an soka mishi wuk’a…

Sai da ta sake maimaita maganar tata tukun yace
“Tam”
Daga nan suka fara tafiya suka wuce inda motarsa take a chan wajen gidan, suka shiga suka wuce.

A chan parlourn kuwa
Zuwa wannan lokacin gaba d’aya hankalin matan parlourn ya koma kan su Mammy.
Su Mommy suna fita Ummi ta hau lallab’a Mammy
tana bata baki, basu kulata ba sam daga ita har Mom dan
tun a cell daman sun fita harkarta saboda ta zama
wata salaha doluwa wawiya! kamar ba ita ba.

Arshaad kuwa ji yake kamar ya chaka wa kanshi wuk’a!
Babu abunda yafi d’aga mishi hankali kamar kalmar ‘sai ta tsine mishi’ da taketa faman ambata, hakan yasa kawai ya juya zai bar wajen
suka yi karo da Dad! Fuskarshi sam babu alamun annuri dan hatta Arshaad d’in sai da ya d’an tsorata da yanayin shi.

Ganin yana shirin fara zuba musu tujara a gaban jama’a ne
ya sanya Mom tace
“Dad da mun d’an shiga daga ciki ko mu hau sama
Kalla kowa ya zubo ido mu yake kallo”
Juyowa yayi yana kallonta
wanda hakan yasanya ta sha jinin jikinta.
Da kakkausar murya yace
“Granpa ya san kina nan?”

A hankali jikin a mace ta girgiza kai,
Snapping fingers d’inshi yayi
kafin ya nuna mata hanyar main door straight!

Ba k’aramin sanyi jikin Mom yayi ba! Kunya da takaici kuwa kamar su kashe ta,
a hankali tace
“Sai anjiman ku”
daga nan ta fara k’ok’arin wucewa taji Ummi tace
“Adama d’an jirani in je in d’auko wayata a side d’in Granpa In zo mu wuce.
Ya sallameni tun jiya.”

Ba tare da Dad ya kalleta ba yace
“Ki jirani zan maidake anjima, ina son ganinku tare, ke da Abba.”

“Ok” kawai tace
Mom kuma ta wuce ta fita.

Sai a sannan Dad ya kalli Mammy yace
“Magana d’aya zuwa biyu nake son gaya miki…
Na farko shawarace
Na biyu kuma zan iya kiranshi as treat..
Ki kwantar da hankalinki ayi auren Hudan da Arshaad cikin lafiya da kwanciyar hankali
Ko kuma wallahi idan kika yi wani abun da ya b’ata auren nan tou ki tabbatar sai na sauk’e igiyoyin aure na da suka yi saura a kanki.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce.

A rikice Aaima da sisters d’in Mammy suka hau cewa
“Kawai ta hak’ura dan Allah
kar ta b’ata aurenta”

Bata bi ta kansu ba,
cikin b’acin rai ta kalli Arshaad tace
“Arshaad kaje ka cire waennan kayan na gaya maka babu inda zaka je!
Wallahi idan ka fita a gidannan yau ni da kai ne.”
Daga haka ta juya ta wuce sama.

Sai a sannan Hajiya Binta ta k’araso
tanajin abinda tayi tace
“Suje kawai a sallami y’an wuni suma su zo su wuce gida tunda ba za a je kaulun ba!”
Nan take gayamusu ma sak’on Mahaifiyarsu da tace a fad’a musu…
Jiki a mace haka duk suka bar gurin aka je aka rarraba souvenirs d’in k’atuwar jaka
an rubutu sunan Amarya da Ango a jiki
a cikin jakar an zuzzuba turaruka da atamfofi guda biyu da vail da jaka da takalmi,
a each bag..........
Chapter 60 · 0% Book details