← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 70

Sashe 64

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama da Ummu sun so hana mai video coverage da pics d’auka amman ganin yanda hankalin kowa yake a kansu
da kuma Mommy wadda tace ‘su bari kawai tunda ga wasu ma a gefe suna ta d’auka da waya’ ne ya sanya
kawai suka hak’ura.
K’awayen su Huda kuwa abun ba k’aramin d’aure musu kai yayi ba dan tabbas sun san wannan ba da shi akayi cocktail jiya ba, kuma ba shine a pre wedding ba!
A haka dai suka bar maganar akan in an tashi za suni komai a bakin Sakina....

Aslam kuwa so yake ya mik’e amman sam ya kasa!
Ya rasa dalili..tun da yake bai tab’a jin fargaba irin wadda yake ciki a halin yanzu ba!
Ana cewa k’afafuwa da gangar jikin mutun suna sagewa ya koma kamar gunki bai tab’a yarda da hakan ba sai yau da ya faru a kansa dan hatta kwayar idanunsa ya kasa juyawa, so yake ya runtse idanuwanshi ya samu ya dedeta zuciyar shi amman sam ya kasa!
Yana nan a haka yaji Ummu na rufa mishi wata jibgegiyar alkyabba akan jamfar jikinshi
Akan hular kanshi
Ummu ta d’aura mishi wani jan kyalle mai tambarin moon a gaba golden colour
(Allah yaso suna da extra)
Daga nan ta mik’a mishi wata sanda wadda ta ci ado! Tace masa “ungo, rik’e”
Mommy ce ta kama hannunshi ta sanya mishi
sandar sannan ta had’a da nata hannun ta maste!
Sai a lokacin ya samu nasarar lumshe idanuwanshi
sannan ya d’an bud’e su kad’an yana kallon k’asa....

Ba tare da b’ata lokaci ba aka fara gudanar da alada……..
Bayan uwar Amarya da uwar Ango sun yi, ragowar jama a suma suka zo suka sanya musu suka basu gift
daga nan aka fara serving abinci.

Sai a lokacin Anty Zainab da Umma suka samu suka iya zama…Umma so take yi ta sake mik’ewa tsaye tace
“To Ina y’an unwan Ango!?” ta sake creating scene amman sam ta kaasa dan in banda
dishi dishi babu abunda take gani! A ranta ta shiga aiyyana
…..Tabbas sai taci uwar malan ado! Wallahi sai ta saka an yi mishi yasin mai walk’iya!
Ba Malami ba ko uban waye shi. Kuma sai ya bata kud’inta.
Jiya jiyan nan fa ta sake komawa wajenshi dan ta sake nanata mishi, shi kuma ya
tabbatar mata da “babu aure tsakanin Hudan da Arshaad
ya riga ya gama aiki
kuma ya buga k’asa ya tabbatar ba Mijin ta bane ba
sannan
ya ingiza zuciyar iyayen shi (Arshaad) ya rura wutar k’iyayyar Hudan a cikinta
ta yanda ba zasu tab’a bari ayi auren ba musamman ma Mahaifiyarshi (Arshaad)…”
Amman kalli yadda Maman nasa taketa jan Hudan a jiki,
anyi musu hoto yafi kala nawa tare sai faman fara’a take yi tana washe baki kana ganinta ka san tana cikin tsantsar farin ciki….Inaaaaa!!!!!
Taya ma zata tsaya ta yarda Hudan ta auri wannan
No1 kyakkyawan da ita tunda take a rayuwarta ko a telebijin bata tab’a ganin mai kyawunsa ba! Ga uban kud’i ga kyau kamar aljani
Allah sarki Jalilan ta
dole ta mutu akan soyayyar Arshaad, ai kuwa idan zata yi yawo tsirara wallahi sai ta raba auren Huda da Arshaad ko sama da k’asa zasu had’e
Wallahi sai dai in rabo ya kasheta akan dai ta zauna ta nad’i wannan abun takaicin da ta san k’arshe in dai bata d’auki mataki ba to shine ajalinta!
Kuma ko yana so ko baya so sai ya auri Jalila!
Wannan alkawari ne ta d’aukarwa Jalila da ita kanta!
D’an halal ka fasa……..

Anty Zainab ce ta tab’o ta
wanda hakan ne ya katse mata tunani.
Da kyar ta iya motsa wuyanta dan ji take kamar ba jini da rai a dukkannin ilahirin jikinta
Suna had’a ido taga itama Anty Zainab d’in idanuwanta sun kad’a sun yi jazir!
Kafin Umman tace wani abu
taji tace
“Sadiya taso mu tafi,
kai na ciwo yake yi min”

Suna shirin mik’ewa
suka fara jiyo gud’a daga parlourn Madu sai a sannan ma suka lura Shuwa da Baaba Talatu da wasu y’an tsirrun mutane basa wajen
A bakin matan wajen sukaji an fara k’us k’us d’in
“Ashe tun d’azu mazan gidan Ango suka zo sun kawo lefe yanzu suka wuce
da yake falon Madu yana da k’ofar shiga da fita ta waje, shiyasa har suka zo suka tafi ba wanda ya sani
Sai da suka tafi yanzu akace aje a fito da shi” Sunaji anata k’usk’us d’in “ai motocin da suka zo da su ma kansu abun kallo ne!
Gasu kana ganinsu kaga manyan mutanen da kud’i ya zaunamawa”

Da kyar Umma take iya jan numfashi, dan ji take yi gaba d’aya iskar wajen bata isarta!.
Ummu ce ta d’an matsosu kafin tace
“Umma kuzo muje a fito da lefen nan kowa ya gani ko?”

Anty Zainab ce ta iya ce mata “eh”
Itanma da kyar,
daga haka ta mik’e ta d’an dafa Umma kana tace
“Muje Sadiya”
Da kyar ta iya mik’ewa k’afafun ta suna rawa suka jera ita da Anty Zainab suka bi bayan Ummu suka yi parlourn b’aki.

Mutane kam wasu basu ma samu damar shiga ba
dan akwatunan sun cike parlourn tap!
Ganin kowa cirko cirko a tsaye iya y’an k’alilan kuma na a ciki suna mik’owa ana fitowa da shi ne yasa suma suka ja suka tsaya a gefe
kai kana ganinsu ka san basa cikin hayyacin su..

Ta gabansu aka fara wucewa da akwatuna
nan kuwa suka maida hankali suka hau k’irgawa!
Ana wucewa da goma
Umma ta nemi d’an dakalin slop ta zauna dan jiri ne taji yaana d’ibarta ba na wasaba!
A tunaninta su kenan
amman ga mamakinta sai taga ana ta sake fito da wasu!
Ganin ta k’irga ashirin da d’aya basu k’are ba ya sanya
ta janyo Anty Zainab wadda itama tayi mutuwar tsaye kafin tace
“Zainab zo mu bar wajen nan,
tabbas kwakwalwa ta ta d’an samu matsala sannan bana gani sosai!
Gani nake yi anata wucewa da akwatuna fa har yanzu basu k’are ba.”
Da sauri Anty Zainab d’in tad’an dafa ta
dan yanda take magana da sauri kuma da k’arfi kamar wata zararra ya sanya mutane har sun fara d’an juyowa ana kallonsu. A hankali tace mata
“Ba idonki bane!
Ashirin da hud’u ne cass! Gasu chan ragowar ukun
Sai kuma waenchan baskets d’in da ban san na menene ba”
Bata ida rufe bakinta ba aka fara fito da na Gwaggo da Kawu.
Ai kuwa
Umma bata san lokacin da ta mik’e tsaye ba tace
“Amman dai Maryam sayar da y’ar nan tata tayi ko!?
Haba mana wannan abu kuma ai ya zama hauka!
Meye hakan? Me sukeso su nuna?”

Cikin takaici Anty Zainab tace
“Wallahi Sadiya za kiyi hanyarki nima inyi tawa har a tashi daga bikin nan gaskiya!
Maganar Allah kenan, haba mana! So kika mu zama abun kwatance?
Sai wasu abubuwa kike yi kamar tab’abb’iya?
Kiyi controlling kanki mana
Haba?”
Ta fad’i hakan tana mai wucewa ta barta a tsaye nan dan a yanda take jin zuciyarta yanzu, tsaf zata iya sauk’e ruwan bala’i da fushinta akan matan dake k’ok’arin maidasu telebijin….

Sai da Umma taga an gama fito da kayan an watse daga wajen sannan ta samu da kyar taja y’an k’afafuwanta ta isa harabar tsakar gidan.

Banda gud’a da hayaniyar mata ba abunda yake tashi
A lokacin har an bud’e akwatunan farko an fara dubawa….

Sai a sannan ne Aslam ya samu ya tatttaro nutsuwar shi da d’an ragowar kuzarinsa ya mik’e tsaye!
Yana mik’ewa Ummu da Mommy suka k’arasa wajensu..
D’an b’ata rai yayi kafin yace “Mommy zan wuce
wannan bidi’ar bada ni ba gaskiya”
Murmushi Mommy tayi ta shafa kanshi kafin
ta juyo ta cewa Ummu
“Zai iya tafiya?”

Murmushi Ummun tayi kafin tace “eh, zai iya ai an gama komai”
A hankali yace mata
“Sai anjima”
Cikin kulawa tace
“Mun gode kwarai Aslam,
mun gode.”

Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e
daga nan ya ajjiye sandar hannunshi a gefe ya juya
dai dai nan su Sudais suma suka mik’e
Shuraim yana ta b’ata rai shi ala dole ya gaji..

Ummu da Mommy ne suka yi musu rakiya har waje, shi da Sudais da Shuraim bayan ya kira drivern da zai maida Mommy gida yace masa ya taho yanzun…
Mutane in banda kallonsu ba abunda suke yi sunata yaba kyawun Angon
Gashi bai wani zak’e ba irin yanda Angwayen yanzu suke yi! Instead shi ya kama kanshi matuk’a, hakan kuwa ba k’aramin burge jamaar wajen yayi ba.

Su Mommy suna komawa
suka tarar anata ware lefe an yi filla filla ana gani…

Tun daga kan atamfofi Umma ta raina kanta…
Zata iya cewa tunda Laraba ta kawota duniya bata taba shiga tashin hankali irin na wannan lokacin ba!
Hankalinta bai gama tashi ba sai da aka zo kan akwatunan jewelry’s
kit kit
waenda aka ware guda biyu aka shak’e taff da sark’a da y’an kunne
Na farkon fashion ne
Na biyun kuwa gold ne zalla!
Matar dake gefen ta ce taji tana cewa
“Ai dama su family d’in MT haka suke lefe duk matan gidan da aka tashi aurar su ko wacce sai da aka yi mata kit d’in gold!
Yanzu kuma wannan kinga shine jika na farko da yayi aure.
Kaii ammanfa wannan Yarinyar ta tako, gaskiya tayi goshi
Allah yasa y’ay’anmu a danshinta. Zata sha gata ba kad’an ba!
Naji ma kamar ance wai k’asar zai bari ma da ita gaba d’aya!”.

Tabbas zuwa wannan lokacin Umma ta daina ganin komai in banda duhu! Maganar ma sama sama ta dawo ji
daga nan kuma jinta da ganinta suka d’auke d’iff!!

Mutanen wajen kowa hankalinshi yana kan kallon lefe mai abun mamaki da alaajabi
Saboda kaff cikin su babu wadda zata ce ta tab’a ganin lefe kwatan kwacin wannan....

Dimmm!!!
K’arar fad’uwar Umma ta sa jamar dake kurkusa da ita zabura suka jujjuyo…..

“Subahanallah!
Mai ya sameta!!
D’in da aketa maimaitawa ne
ya janyo hankalin mutanen gurin kaff kowa akayi kanta akai mata rumfa......

A zaune Auwal ya tadda shi,
a d’akinsa. Ya jinginar da kanshi a jikin gadon ya lumshe idanuwanshi fuskar shi tayi jajawur! Kana ganinshi ka san yana cikin tashin hankali.
Chapter 64 · 0% Book details