Sashe 2
So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba bai san daliliba bai kuma san wacece a kwance a d’akin ba, amman yadda zuciyarshi take bugawa da kuma kalar karkarwa da jikinshi ya d’auka lokaci guda ne ya sake d’aure mishi kai!
Dan tabbas ya san in da ace za a auna jininshi a yanzu
To
da za aga yafi na mara lafiyar da ake cewa su taru sun kwantarwa da hankali hawa…
Muryar Aslam ce ta katse mishi tunani jin yana cewa
“Muje Abba. Bismillah.”
D’aga kai kawai yayi alamar ‘to’ sannan ya nufi inda yaga su Hudan da Arshaad sun shiga, Aslam ya mara mishi baya….
...Shekaru goma sha takwas rabon shi da ita, amman ba a yanayin rashin lafiya ba ko a garin makafi idan ya had’u da Maryam ya shafa yaji to sai ya gane ta!
Lokaci guda yayi baya luu!! Ba daban Aslam yayi saurin taro shi ba tabbas da sai ya zube a k’asa!
A b’angaren Mama kuwa!
Da farko da ya shigo ta ganshi ta d’auka gizo yake yi mata, sai da taga har Aslam ya taro shi yana cewa “Be careful” tukunna ta tabbatar da cewa shi d’in ne!
“Mai ya kawo shi?
Me yake nema?
Me zai ce mata?”
Sune tambayoyin da suka taru suka had’e da al’ajabi suka fara k’ok’arin tarwatsa mata zuciya!
Da kyar ta k’ok’arta ta tashi ta zauna sai kuma ta fara k’ok’arin tsayuwa.
Da kyar ya iya dedeta kanshi sannan ya sake sauk’e idanuwanshi a kanta…
Babu abunda ta k’ara ko ta rage, tananan kamar yadda ya santa 18 years ago! fatarta ce kawai ta d’anyi duhu amma
kyawunta da yanayin jikinta ba abunda ya ragu ko ya k’aru!
“Astaghfirullah!!”
Yayi saurin furta hakan, sakamokon tunawa da yayi ita d’in a yanzu mallakin wani ce!
Sai kuma lokaci guda ya fara ganin duhu duhu sakamokon kishin da ya turnuk’e sa!
Bai tashi dawowa dai dai ba sai da yaji Hudan da Arshaad suna tambayar ta “Ina zata je?”
Ba tare da ta kalle su ba tace
“Gida!!”
Sannan ta sa hannu d’ayan hannunta ta cisge cannular k’arin ruwan da aka d’aura mata a d’ayan hannu nata, tayi hanyar fita (inda su Abba suke tsaye!).
Da sauri ya tsaya a gabanta ya fara magana
“M mm Maryam Doc ya c ce jji kin kk ki ba kwari kark.......”
Mahaukacin Marin data d’auke sa da shi ne ya sanya hatta su Aslam sai da suka d’auke wuta na y’an sakanni!
Cikin b’acin rai tace
“That’s for Huda!!
Na duk wani kuka da bak’in cikin da ta fuskanta ata dalilin hukunci daka yanke tun kafin rayuwarta ta soma!”
Bana so ta san ka! Bana so taji komai!! Bana so ta san komai!!! Ba ma buk’atar ka!!!!
na rok’eka da girman Allah ka bar nan tun kafin raina ya k’arasa baci!”
Ta k’arashe maganar cikin b’acin rai da k’unar zuciya, wasu zafafan hawaye suna zubo mata.
Idan lissafinshi ya bashi dai dai to maganganun Maryam suna nuni ne da irin kalaman da ya kamata a yiwa uban da ya gudu ya bar y’arsa……
Bai damu ba sam! Dan bata k’umbiya k’umbiyar magana yake ba a halin yanzu…shi daman ko da ace ya tambaya ance mishi Yarinyar ba y’arsa bace ba to fa ba zai tab’a yarda ba!! Ballantana kuma yanzu da maganganun Maryam suka sake tabbatar mishi da ‘y’ar’ tasu ce!.
Hakan yasa ba tare da yabi takan Mama wadda Aslam yake ta rok’o ta koma a saka mata cannula tak’i ba! (Ta nace akan sai dai Abba ya fita ko kuma ita a tafi) Ya nufi inda y’arsa take tsaye!
Yana zuwa bai yi wata wata ba kawai ya rungume ta
sai kuma ya fashe da wani irin kuka kamar k’aramin Yaro.
Ita dai Hudan zuwa yanzu ta koma mutum mutumi!
Dan kwakwalwarta ta kasa aminta da amsar da kalaman Mama da kuma reaction d’in wannan bawan Allah suke bata.
Shigowar Likita ce ya juyo da hankalin su gaba d’aya, dan hayaniyar su ta fara damun ragowan patients d’in da suke gefen su…
Dukda inda suke an yankashi da girma sosai dan yayi biyun ragowar inda patients d’in suke amman dole in sunyi magana za a jisu
kasancewar labulaye ne kawai ake sakawa a tsakani.
Da mamaki yake kallon Mama a kan k’afafuwanta, sai kuma ya juya kan Aslam ya rufe shi da fad’a!
Da kyar ya lallab’a Mama bayan tace “ba zata koma ta kwanta ba sai Abba ya fita”
Shi kuma yace wa Abban “yayi excusing d’insu”
Bayan ya fita, aka samu ta tsaya ya maida mata cannularta.
Har zai fita yace musu “banda hayaniya!”
sannan ya juya ya fita.
Yana fita kuwa Abba ya dawo! Dan haka Mama ta sake mik’ewa..
This time around Aslam ne ya k’arasa inda take ya rik’e mayafin da take k’ok’arin yafawa ya fara magana
“Mama dan Allah ki tsaya ki sauraremu, bafa ke kad’ai ya kamata ace ranki ya b’aci a lamarin nan ba, shi kanshi Abba yana da ikon yin fushi kawai dai daurewa yake yi dan yaga an zauna lafiya!! Amman na tabbatar ko kotu aka je to kinada laifin b’oye masa y’arsa da kika yi tsawon shekaru ba tare da ya ma san Akwai ta a duniyar ba!
So i think its about time da ta kamata ki nutsu!
Whatever it is that happen between you and Abba destiny d’inku ne, so don’t mix it up da issue na laifin ‘b’oye mishi y’a da kika yi’ kiyi putting blame d’in ankanshi, wannan laifin ki ne ba nashi ba!
And if kika ci gaba da acting stubborn muma zamu biyo miki ta hanyar da baki tab’a tunani ba!”
Da sauri Arshaad yace “haba Aslam wanne irin magana ne kake yi haka?? At least ai she is an elder watch your tongue mana!!!”
Tabbas daman ko Arshaad bai fad’a ba Mama ta gane wannan Aslam ne, dan kamanninshi basu chanja ba kwata kwata, kenan Arshaad d’in shima realative d’insu ne maybe ma brother d’inshi ne dan gashi suna kama sosai!!
Ta yiu Abba ne ya turo shi ko kuma me kenan hakan yake nufi? idonshi yana kansu all this time amman sai yanzu yaga ya dace ya nuna kanshi ko ya ne abun yake????
Gaba daya kan Mama ya d’aure tamau!!!.........
Maganar da Aslam ya fara yi a fusace ne ya dawo da hankalinta wajen
“Elders! elders!! elders!!!
Shin duk meye ne farkon issue d’in nasu?”
Bai jira jin amsar da Arshaad zai bashi ba yace
“Biyewa son zuciyan elders d’in da akayi ne ai duk ya jawo haka!! Itanma kuma I’m pretty sure idan aka yi musu laga laga problems d’in da zata kawo ba kad’an baneba!
Tun ranar da Granpa ya nunawa Abba video d’in d’aurin aurenta Abba yake fama da ciwon zuciya har yau d’innan!! Kuma all those years bai samu sauk’i a wajen kowa ba! Fama yake yi da rashin lafiyanshi ba wanda ya damu!!
Sannan yanzu kuma itama zata b’ullo da nata issue d’in? Da wanne akeso Abban yaji da?”
Ya yiwa Arshaad tambayar yana kallonshi..
Bai damu da jin amsa daga gareshiba dan daman ya san ba lalle ya samu ba, ya juya ya kalli Mama sannan yace
“Ba zan d’agawa kowa k’afa ba! daga yau, ke ko Ummi, hatta Granpa!!
Therefore I’m advising you to drop this attitude and stubbornness da kuma haushin Abba da kike ji, ki tsaya ku dedeta akan issue d’in Huda
If not, wallahi kinji na rantse miki da kaina zan kaiki kotu!! Kuma sai inda k’arfina ya k’are!!!
Dani za kiyi ba da Abba ba...”
“Huda mik’o mini purse d’ina”
Shine kawai abinda Mama tace ba tare da ta zare kwayar idanunta a cikin na Aslam wanda tunda ya fara magana suke kallon juna ba!.
A hankali Hudan ta zare hannunta daga cikin na Abba sannan ta d’auko jakarta ta zaro y’ar k’aramar purse d’in Maman a ciki ta mik’a mata
tace
“Gashi”
Hannu Mama wadda har yanzu take kallon Aslam ta mik’a ta amsa sannan ta d’auke idanunta daga kanshi ta sauk’e akan purse d’in ta zuge ta!
Bayan wayarta ba komai a ciki sai chanjin naira talatin ashirin da biyar biyu.
Zip d’in dake a gefe acikin purse d’in ta zuge sannan ta zira y’an yatsunta ta fara lalubawa..
Wasu takardu an ninkesu ninkin k’anana guda biyu ta zaro ba tare da ta rufe ba ta mik’awa Hudan purse d’in..
Ta farkon ta fara bud’ewa ganin ba ita take nema ba yasa ta mik’awa Hudan tace “ta ninke ta mayar mata ciki”
Sannan ta fara k’ok’arin bud’e ta biyun…
Hawayen da suka zubo mata ta sa hannu ta share bayan ta gama karantawa sannan ta cillawa Aslam a dede setin fuskar shi.
Da sauri jin takardar tana shirin sauk’a k’asa yasa hannu ya cafe ta sannan ya d’ago ta ya fara karantawa…
Mama bata jira ya k’arasa karantawan ba ta fara magana
“Aslam za ka iya kaini kotu! amman ka sani ni ba zan biyeka inyi shariah da kai ba, nasan kun fi k’arfi na ta ko wacce siga, sai dai kuma ni kotun Allah zan kaiku! Nan ce k’arshe kuma shine zai bi mini hakkina!
Dan ba zan yarda ku dake ni kuma ku hanani kuka ba!”
Tana gama fad’in haka kuka ya kufce mata ba tare da ta shirya ba.
Da mamaki Abba wanda ya k’araso ya karb’i takardar ya hau karantawa yake sake maimaitawa….
Shiruuuu, ya d’an yi sai kuma kawai ya ninke takardar ya sa a aljihun gaban rigarshi!
Dan tabbas yau za a yita ta k’are a estate d’insu!! Ba zai yiu ace yana rubuta takardun da bai san lokacin da ya rubuta su ba!
A daa yana kokwanto yanzu kam ya samu clue.
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya k’araso gaban Mama yace
“Maryam! na rantse da girman Allah ba nine na rubuta wannan takardar ba! Ban san da zamanta ba kuma ban san dalilinta da ranar data iso gareki ba!”