← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 70

Sashe 24

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Arshaad ne ya fara shigowa…
Tsayawa Hudan tayi tana kallonshi dan ta manta rabon da ta ganshi da k’ananan kaya, yafi ta’ammali da shaddodi da yadi, sab’anin yau da yake sanye da wata shirt army green dark an rubuta ‘KING’ a jikin gaban rigar da zanen crown d’in king d’in ata k’asa.
Rigar irin mai d’an kama jiki ce, hakan ya taimaka wajen fito da ainahin surar jikinshi dan kana iya hango packs d’inshi na sama sama ta cikin rigar da yadda dantsen hannunshi yake a mummurd’e!
Wandon nashi shima ba jeans bane yana yin rigar ne black in colour bai kamashi ba kwata kwata ta sama amman roba ne, kasancewar ya d’an matse daga guiwar wandon zuwa k’asa yasa ya zama kamar pencil trouser ta k’asan…
Kayan yayi matuk’ar fito da asalin surarshi ta giant!
Ga wani fitinannen k’amshi mai tsayawa a rai da yake zubawa
dan tunda ya shigo parlourn ya karad’e da k’amshin shi, tun bai iso inda suke ba….
Hudan bata gama k’are mishi kallo ba suka had’a ido da shi,
gira d’aya ya d’aga mata yana d’an murmushin gefen baki, da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kunya duk ta lullub’eta ganin ya kamata tana kallonshi .
Ganin yadda tayi ne ya sanyashi sakin wani lallausan murmushi, kafin ya k’arasa inda su Dad suke ya shiga gaidasu cikin girmamawa. Ya so ya k’arasa wajen Hudan dan shima ba k’aramin kyau tayi mishi cikin rigar abaya blueblack mai stones, d’aurin da ta yiwa kanta da d’ankwalin abayan ya yi matuk’ar burgeshi!
Amman sai Dad ya tsareshi ta hanyar fara yi mishi bayani abunda za suyi ba tare da b’ata lokaci ba, 100%ya amince da kuma jinjina ga wanda ya kawo shawarar dan abunda ya kamata ayi kenan, cikin jin dad’i Dad yace “ai Hudan ce”
da d’an murmushi ya juyo yana kallonta, yanzun ma sauri tayi tai k’asa da kanta, don still satar kallonshi take yi, harga Allah Ya Arshaad yayi kyau yau sosai……

Tana wannan tunanin hancinta ya fara jiyo mata wani k’amshi na daban, wanda a take ya cika mata hanci, kuma ta fahimci wanene
Kasancewar a kan kujerar dake gaban side d’inshi take ne yasanya ta fara jin k’amshin kafin kowa, bata san daliliba ba kuma tasan mai ya faru ba, amman ko lokacin idan anyi laifi a islamiyyarsu za a dakesu tabbas zuciyarta bata yin kalar bugun da take yi a yanzu….
A hankali ta runtse idanunta ta sake yin k’asa da kanta jin takunshi a daf bayanta!Sannan bugun zuciya da k’amshin da yake shak’a na k’ara yawa….
Kamar yadda Arshaad yayi shima hakan ya gaida su Dad waenda suke ata gefe kad’an kusan hanyar shigowa sai dai shi bai k’arasa inda suke ba, hasalima zagayowa yayi ya zo kan kujerar da Gwaggo Asabe take ya zauna..
Kasancewar Gwaggo Asabe a 3 seater take zaune Hudan kuma a 1, sai ya zamana kamar suna facing juna shi da Hudan!
A hankali ya d’ago idanuwanshi ya sauk’e su a kanta, da tayi k’asa da kai wanda ita kanta ta kasa tantance dalilinta na yin hakan

Magana Gwaggo Asabe take yi mishi amman kamar ma baya jin ta, ganin hakan yasa ta d’an tab’a shi kad’an..
Lumshe idanunsa kawai yayi kafin ya bud’e su ya sauk’e a kan Gwaggo Asabe, d’an murmushi kad’an yayi mata kafin yace “barka da gida”.
Cike da tausayawa Gwaggo Asaben take kallonshi, ko ba a fad’a mata ba ta san tun d’azu da ya fito daga d’akin Mommy yake cikin tashin hankali!! Dan gashi idanuwanshi sunyi jaaa sosai bakinshi yayi pink shima hatta kan hancinshi yayi jaaa
Amman kuma ko ba a fad’a mata ba ta san ba kuka yayi ba
wanda wani lokacin har addua take yi Allah ya bawa hawaye ikon fitowa daga idanun Aslam ko ya samu ya rage rad’ad’in da zuciyarshi take ciki.

Hannunta ta d’aura akan lallausan gashin kanshi ta d’an shafa…
Hakan ya sanya shi sake maida hankalinshi a kanta!
Tana shirin yin magana
Dad ya fara yiwa Aslam bayanin abunda ya tarasu anan bayan ya zagayo ya zauna,
Abba ma ya zauna.
Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e bayan ya gama sauraron Dad wanda ya k’arashe maganar shi da cewa
“Zamu fara yanzu saboda mu samu mu gama akan lokaci kafin a gama Parking su Abba su tafi”
A hankali ya juya ya kalli Abba kafin yace
“Abba ka bari I’ll speak with Granpa, dan Allah don’t leave.”
Murmushi Abba yayi ya mik’e daga kan kujerar da ya zauna ya k’araso inda yake kafin ya dafa kanshi tukun yace
“Karka damu Aslam, ai bamu da nisa anytime kakeso zaka iya visiting, ni kaina i need some time with my daughter, wanda in muna nan na san Granpa ba zai barni ba, and ya dinga k’untata mata kenan, ni kuma from this time forward inaso In bata cikakken kulawa da happiness d’in da ban bata ba a baya, so we need some space from him, Daddy kuma he wants to leave ne saboda yaci ace Granpa ya fara rage abubuwan da yake yi.
In bamu tashi mun tsaya munyi mishi haka ba, al amarin family d’innan ba zai tab’a daidaituwa ba!
I hope u understand”
Yayi maganan yana shafa kanshi, a hankali Aslam ya sauk’e ajiyar zuciya a karo na ba adadi sannan ya d’auke idanuwanshi daga kan Abba wanda tunda ya fara magana ya kafe shi dasu, a hankali
yace “shikenan” sannan ya mik’e ya wuce zuwa inda ya fito yana cewa “zan fara daga Fatiha zuwa Nisa’i ayat 147!
Someone should continue from were i stop.”
Yana gama fad’in haka ya shige ya jawo k’ofar shi ya zuge.

Dad ne yace “Abba ko zaku tafi tare, kasan yadda kuka saba da shi, and ga incidence d’in daya faru d’azu kar abun yai mishi yawa”

“Ba zai yarda ba but let me try”
Inji Abba, ya mik’e yana k’ok’arin shiga side d’in Aslam d’in.

Dad ne yace mishi ya tsaya tukunna…
Sai da suka tsara yadda za suyi, su mazan za suyi arba’in d’in sama, Huda kuma da Gwaggo Asabe za suyi ashirin d’in k’asa, kowa ya d’auka izu goma goma…
Tukunna Abba ya nufi side d’in Aslam.
Kamar yadda yace d’in kuwa sam Aslam k’in yarda yayi ya bishi hakan yasa ya hak’ura, ya zauna a d’akin yana d’an kwantar mishi da hankali, daga nan suka hau karatu a tare suka kammala nasu, dede ana kiran sallar azahar…

A chan parlour ma Huda da Gwoggwo Asabe kusan tare suka kammala, Dad ne ma da Arshaad suka d’anyi delay don suna hawa sama Mommy taci gaba da kuka da kyar suka lallab’ata tukunna suka samu suka yi nasu.

Sunyi addua sosai, kafin su samu ruwan zamzam aka tofa mata aka bata tasha aka shafa mata….

K’arfe hud’u dai dai komai ya kammala, duk sun shirya kaya kuma an gama jidesu, sai y’an tsirrai da za suna kwasa a hankali a hankali, waenda ba wani important bane!.
Abba Dad da Daddy ne suka nufi wajen Granpa don yi mishi sallama..

Har sun kama hanya Daddy ya juyo ya cewa Arshaad “yaje ya samu Auwal yace masa ya kawo wannan Yarinyar nan sannan ya tabbatar komai d’inshi ya zama ready dan suna fitowa za a tafi”
Da to ya amsa har ya juya ya nufi k’ofa ya jiyo wadda ta biyo shi da d’an sauri tana ki ranshi
a hankali ya juyo yana kallonta
Sai da ta k’araso ta d’anyi k’asa da kanta tana wasa da y’an yatsun ta tukun tace
“Ina wuni..
Dan Allah ka ara mini wayarka zan kira Mama”.

B’ata rai yayi kafin yace
“Nima ba zan kulaki yanzu ba”
Yana d’an turo baki kamar wani k’aramin Yaro.

Dariya ma ya bata dan haka ta d’ab yi y’ar dariya mai k’aramin sauti kafin tace
“To kayi hak’uri naga su Abba ne shiyasa kuma ka d’an yi nisa ne, da kana kusa da sai mu gaisa”
Murmushi kawai yayi ya mik’a mata wayar sannan yace “bara yaje ya duba Auwal kar suyi ta jiranshi…”

Huda ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba dajin Mama na asibiti an sake admitting d’inta har yanzu, Sakina sai k’ok’arin kwantar mata da hankali take amman taki hak’ura, barema da taji wai an mata har eco, gashi ance Maman tana bacci ba zai yiu suyi waya ba!!
Kwata kwata sai ta gaza kwantar da hankalinta, dan haka kawai tabi Ummu da ‘to’ bayan tace mata tayi hak’uri ta d’an Kara jira
Amman tasa a ranta yanzu zata samu ya Arshaad ya kaita emergency d’in…

Tana cikin wannan tunanin bayan sun gama wayar, wayar Arshaad ta hau k’ara!

Kiranshi akeyi akai akai, gashi ya fita.
Ganin an jera mishi sama da 20 misscalls ne ya sanya ta yanke shawarar kai mishi wayar.

A bakin gate d’in gidan ta tambayi mai gadin ko “Ina Arshaad d’in yayi?”
Opposite
gidan da yake kallo wanda take ya nuna mata, dan haka ta nufi gidan.......

Tun lokacin da Auwal ya dawo daga wajen Mom ake kai ruwa rana da Jalila har yau da suke shirin barin gidan!
Dan tace “wallahi ba zata je wajen wata Gwaggo Asabe ba, kuma ba zata koma gidansu ba!
Ta gano wayo yake so yayi mata ya yakiceta,
ai tunda babanshi yace baya sonta ta san in dai ta yarda suka bar gidan babu ita tou shikenan magana ta k’are”
Bikin ma cewa tayi “ta fasa zuwa” gashi ta amshe kud’i, tace “sai anje sabon gida an nuna mata d’akinta ta zuba kayanta tayi settling tukunna maybe taje”
Tace kuma “In ya tilasta mata a yau sai ta tona mishi asiri, wallahi.”
Chapter 24 · 0% Book details