← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 70

Sashe 44

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun suna ganin abun kamar wasa har bayan sallar Isha shiru dan haka Ummu ta yanke shawarar zuwa domin taga ko lafiya saboda Mama ko 2 misscalls bata bari ayi mata take amsa waya........

A hankali take bud’e idanuwanta….dishi dishi ta fara gani kafin ta samu ta d’an fara gani.

Gefen fuskar Hudan wadda ke zaune a gefenta ta fara gani ta sharkaf da hawaye, sai kuma cikin fad’a sosai taji Kaka yana cewa “Wallahi tallahi Talatu zan yi mugun b’ata miki rai! Wannan wanne irin rashin tunani ne da son kai? Mutumin da yayi wannan b’arnar shi kike cewa a saka? Reputation d’in yaci k’aniyar sa! Ai babu wani maganar image da reputation shi da kansa
ya riga ya lalata kayanshi…”

Tana k’ok’arin yin magana ta fara ganin dishi dishi still..
Har ta koma ta sake sumewa babu wanda ma ya san ta farka!

Bata farfad’o ba sai washegari da safe, d’akin daga Ummu sai Hudan, Arshaad da Sakina.

Sakina ce ta fara lura da ta farka dan haka ta k’arasa da sauri tana cewa “Ummu kinga ta bud’e ido yanzun nan kuma ta sake rufewa”.
“Alhamdulillah” Ummun tace sannan ta fita dan zuwa ta kira Likita saboda yace tana farkawa a kirasa.

Bayan y’an dube dube ya k’ara mata wasu allurai ta drip sannan yace “su yi k’ok’ari su bata abinci mai kyau, ta ci.”

Yana fita Hudan ta k’araso, duk yadda taso ta rik’e hawayenta kasawa tayi dan haka ta fashe da kuka Sakina ma haka,
haka itama Ummu wadda ke tsaye a gefe.

Arshaad ne yayi k’arfin halin lallashinsu da kyar suka samu suka yi shiru, sannan suka shiga tambayar ta “ya jiki”

Fahimtar da Arshaad d’in yayi suna buk’atar space ne ya sa shi yi musu sallama sannan yace “zuwa anjima zai dawo ya tafi dasu, akwai abunda ake buk’ata?”

Da “Babu” suka amsa sannan Ummu ta sake yi mishi godiya, ya fita.

Yana fita Ummu ta juyo tana kallonta kafin tace “shi ya kawomu nan shekaran jiya.”

Da mamaki Mama tace “Shekaran jiya?” Da kyar.

Shiruu, Ummu tayi kafin tace
“eh! Kwanan ki biyu a nan.
A yanayin dana ganki na yi tunanin na rasa ki ne Mama”
Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka sannan cikin kukan tace
“Ban yi tunanin kina da ragowar rayuwa a gaba ba,
sannan na san muddin Abba ko Hajiya wani ya ganki a yadda na ganki to ba lalle su iya jura ba tsaf za su iya yanke jiki su fad’i dan ni kaina sai da na zube a wajen, da na ganki.
Gashi Baban Sakina baya gari,
shiyasa na kira Arshaad wanda shi kuma ashe a lokacin ma su Hudan sun d’agawa Abbansu hankali akan suna so su zo su ganki dan sunyi ta kira bakya d’auka, gashi kuma nima a lokacin sunata sake kirana amma ban d’auka ba!
Dan haka suka taho.
Banyi 20 minutes da kiransu ba, suka k’araso duk su ukun a hargitse dan a yanda sukaji muryata (lokacin da na kira Arshaad) sun san ba lafiya ba.
Shigowar da suka yi ya sanya maimakon a d’auki mara lafiya d’aya sai kuka zama ku biyu! Dan itama Hudan suma tayi,
Arshaad ya d’auketa a hanyar fitar da ita suka had’u da Baba!
Yana ganin fitarshi ya datsa sakata wai Namiji ba zai sake shigar mishi gida ba!
Kuma muka ce masa ya taimaka mu fitar dake ya k’i!.
Ba yadda na iya sai su Abba Madun muka kira, abunda muke gudun kuwa sai da ya faru don yanzu haka shima yana kwance tunda ya ganki jininshi ya hau sosai! Don shima yayi tunanin mutuwa kika yi.
Amman abu d’aya wanda aka yi yayi mini mugun dad’i shine ‘bayan an kawoki an tabbatar da kina da rai da Kaka da Abba Madu suka je dakansu suka yi arresting Baba! Kuma sun ce basu ga ranar fito da shi ba’.”

Cikin kuka Mama tace “ki kira min su Kaka, ina da buk’atar magana da su, Bilkisu na gama auren Ya Usman, wallahi.”

Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin ta zaro wata takarda a cikin jakarta, ta mik’a mata......

Wani sanyi ne ya lullub’e Mama, atake taji kamar an yi mata bushara da gidan aljannah!
Saki d’aya tak! taga yayi mata
“Alhamdulillah” ta hau jerowa wasu hawaye suna gangaro mata…..

A hankali Ummu ta dawo ta zauna kusa da ita kafin tace
“A ta sanadiyyar dukan da yayi miki! Cikin da ke kanki na san baki san kina d’auke da shi ba ya zube jiya, har an yi miki wankan ciki!”.

Mama bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.............

Ta d’an ci abincin kuwa ba laifi.
Zazzab’i da zafin ciwukan jikinta especially karayar k’afarta ne suka sanya aka yi mata allurar bacci dan ta samu sa’ida.

Sai dare Arshaad yazo, ga mamakin Sakina har da Auwal… Tana d’an murmushi suka shigo amman tunda suka yi ido biyu da Auwal ta had’e rai ta turb’une fuska!
Dariya ta bawa Arshaad dan haka suna had’a ido ya hau yi mata dariyar tsokana ai
kuwa ta chuno baki gaba ta sake kumbura jira kawai take a tab’ata ta fashe.
Ba abunda yafi bawa Arshaad mamaki irin yanda Auwal ya durk’usa har k’asa ya gaida su Mama, shima (Arshaad) d’in d’an rissinawa yayi ya gaidasu, daga nan suka d’an zauna. Kafin daga baya suka mik’e
suka ajjiye musu jibga jibgan ledojin da suka shigo musu da su, suka yi musu sai da safe…

Ummu ce ta cewa su Sakina “su tashi kar ayi ta jiran su” da kyar suka fita tare da su Arshaad da alk’awarin gobe da sassafe za su dawo!.

Sai da suka fita tukun suka ga ashe har da Abba aka zo.
Ita da Sakina ne suka shiga motar Abba, Arshaad kuma suka wuce shi da Auwal.

Suna yin parking Sakina ta bud’e ta fara fita bayan ta yiwa Abban sai anjima, Hudan na shirin fita Abban yace mata
“Ya jikin Maman naki?”
A hankali tace “da sauk’i”.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Arshaad yace har da karaya ko?”
“Eh”
Ta bashi amsa.
Cikin d’acin zuciya yace “na yiwa Mamanki laifi! Na saka polisawan wajen da akai kai Mijinta sun yi mishi duka bana wasa ba! Wanda shima hakan da nayi na san maybe idan taji labari zata iya jin haushina!
But maza irin Usman irin haka ya kamata a dinga yi musu.
Inaso in cire hannuna akan case d’in amman sam na kasa Hudan ban san mai yasa ba.
Wallahi da ace ina da hali ko inda Maryam tabi Usman bai isa ya taka ba! Amman k’addara ta riga fata,
kuma ance ba a shiga tsakanin Miji da mata, sam.”

Shiruuu, Hudan ta d’anyi, tana son gaya mishi amman kuma sai taji ta kasa.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace mata
“Good night, kije ki huta kun sha jigilar asibiti.”

A hankali tace “good night Abba” ta fice.

Sun dan tab’a hira kad’an a parlour da Arshaad sannan ta sallameshi ta bashi sak’on Mommy, ta nufi d’aki a ranta tana mamakin yajin da Aslam yayi musu, lokaci d’aya kawai ya d’auke k’afa!.

Har ta haye bata ga shigowar Abba ba kuma ta san ba fita yayi ba.

Ya dad’e a mota, kafin da kyar ya samu ya fito ya shiga ciki yana ganin dishi dishi tsabar tashin hankalin da b’acin ran da yake a ciki, ya rasa me zai yiwa Usman ya huce takaici da bak’in cikin da yake ji…..

Sai da su Hudan suka zo kwanciya tukun take gaya mata yanda suka yi da Abba d’azun sannan a hankali ta d’aura da cewa “bana son had’awa Mama case biyu shiyasa na k’i ce masa komai”

Murmushi Sakina tayi kafin ta kamo hannuwanta duka biyu tace “Ki yi tunani, duk abinda kika ga ya dace, kiyi musu.”

Da sassafe ta tashi ta shirya, tana shirin zuwa side d’in Abba taga call d’in Arshaad, sai da ta d’anyi jimm!! Tukunna ta amsa ta gaidashi. Cikin kulawa da so ya amsata kafin yace “ta sameshi a k’asa”

Tare suka sauk’a ita da su Shuraim waenda za su school.
A parlourn ta tsaya tayi musu a dawo lafiya, sannan ta k’arasa inda Arshaad d’in yake zaune.

“Za ki fita ne?
Naga kin shirya da sassafe”
Yace yana kallon ta.

A hankali tace
“eh, amman sai wajen 9 yanzun ina son yin magana da Abba ne”

Cikin bata dukkannin attention d’inshi yace “Exactly abunda ya kawo ni kenan.
Did you tell him? I’m sorry na san bai kamata in yi miki wannan maganan ba but naga kamar Abban is disturbed, na dad’e ban ganshi a wannan yanayin ba.
Me kikayi deciding? Za ki fad’a masa ne?”
Ya jero mata tambayoyin yana mai tsareta da ido.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “jiya dai ban gaya mishi ba, but yau na yi deciding in fad’a mishi d’in, duk da ban san ya zai yi handling abunba, and I’m not even sure they still want each other back.”

Murmushi Arshaad yayi kafin yace
“Believe me they do!
Amma kin tabbatar this is the right time?
After all that has happened especially ma a ita Maman”

A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“I’m sure.
Na riga na gama deciding”

Murmushi Arshaad d’in yayi sannan yace
“Ok dear.
Allah ya taimaka, ya sa a dace.”
“Ameen” tace.
Yana d’an murmushi ya mik’e yace “Anjima idan na koma gida na d’an shirya zan zo asibitin in shaa Allah.”

“Allah ya kai mu” tace.
Kafin daga nan suyi sallama ya wuce office ita kuma ta nufi side d’in Abba.....

A bakin k’ofar parlournshi ta tsaya ta d’anyi knocking jin shiru yasa ta tura ta shiga.

Ba kowa, dan haka ta nufi bedroom.
Ta jima tana knocking tukun chaan, taji ance “come in”

A hankali ta tura ta shiga, da alamun tun d’azun a balcony yake dan yanzun taga yake shigowa cikin d’akin.

Yayi mamakin ganinta da sassafe, dan haka suka fito parlourn suka zauna kafin ya kalle ta yace
“Ya aka yi dota?”
Chapter 44 · 0% Book details