← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 70

Sashe 52

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dare aka samu damar kaita wajen Granpa, dan Gramma ita tunda taji labari ta taho itama suna tare ranar har dare.
Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwarta ya yi mata ya jiki.
Ba abunda yake b’ata mishi rai irin yanda Gramma take ta faman yayatawa
cewa
“Ai Hudan ce ta bada shawarar yi mata sauk’ar Qur’ani kullum”.
Har sai da ya kwab’eta ta hanyar cewa
“Ta daina cewa ‘Huda’!
Kawai ta dinga cewa
Allah ne ya bata lafiya ya warkar da ita.”

Gramma ta so yi mishi bayani, amman ganin kamar ranshi a d’an b’ace yake kuma ta son ba ya son jayayya yasa kawai tace
“In sha Allah, Granpa.
Zan gyara.”

Tun daga kan Gramma har Aaima ba wanda bai bada zakka da sadaka ba na ban mamaki!
Sauk’a kuwa ba su daina ba
ana kan yi dan
Dad cewa yayi “zuwa k’arshen watan nan ma in Allah ya yarda aka kammala na Mommy
to ba dainawa za ayi ba
duk sati sai an yi sauk’a a cikin eatate d’in a tsakanin su, in shaa Allah”.

Yau kusan sati d’aya da warkewar Mommy, har su Hudan sai da suka zo suka yi mata sannu da barka a b’oye da daddare.
Mommy tayi matuk’ar murnar ganin Sudais da Shuraim
ita daman tana son twins, kuma tunda taji labarin suna da twins a family d’in taketa so ta gansu da su da Huda.

Tunda Mommy taga Huda Allah ya d’aura mata k’aunarta, especially ma da taji gudummawar data bayar akan rashin lafiyarta..
Tayi mata godiya yafi a k’irga!

Ita kam Hudan wani tsoron Allah da girman zatin shine ya sake shigarta, tana tunawa ko 2 month ba ai ba ta ganta a hargitse amman kalleta yanzu garau!
Tabbas a rayuwa, in dai mutum yana neman sauk’i! Waraka!
Taimako! To kuwa ya nema a wajen Ubangijin Talikai wanda bashi da kishiya.

Da kyar ranar ta barsu suka tafi, ita Huda mamakin ma yanda matar take mata take yi, kamar ta santa tun daa chan amman da ta tuna yanda Mommyn ta bata labarin shak’uwarsu ita da Mama sai tayi tunanin ko saboda Maman ne yasa take yi mata haka....
Sannan itama a lokaci d’aya taji girma da k’aunar matar ya shige ta.

A b’angaren Mommy kuwa, kawai tsintar kanta tayi da tsananin k’aunar Huda, dan koda bata kasance y’a ga Maryam ba tabbas Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar a ranta.
Ba abunda yafi sosa mata rai irin da taji cewa ‘an sa ranar ta da Arshaad!’ Saboda ita har ga Allah tun da ta d’aura idonta akan Yarinyar ta fara kwad’ayin ganinta da Aslam d’inta a matsayin maaurata!
Amman kuma da ta duba taga
abunda yayi Aslam shi yayi Arshaad sai ta hak’ura ta barwa Allah komai sannan ta bisu da fatan alkhairi.........................

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
50.

Yau saura sati biyu auren su Hudan, sai shirye shirye ake yi.
Yayinda jikin Mama yayi sauk’i sosai abun har mamaki yake bawa jamaa kamar ba wadda ta karye ba, follow up kawai take zuwa abunta.

Abba da kanshi yaje ya siyowa y’arsa kayan d’aki na gani na fad’a, hatta cokali bai bari ba sai da ya siyo mata komai bayab ya tambayeta taste d’inta, wasu kuma yana daga chan d’in yake turo mata Sakina ta tayata zab’a.
Sannan ya had’a mata gara nan ma na gani na fad’a.

Lokacin da bikin ya rage saura sati d’aya already
kayan gara da kayan d’akin amarya suna gidanta.
Duk da ba wai zama za suyi anan d’in ba, kai ta
kawai zaayi gidan daganan su wuce karatunsu amman hakan bai sanya an k’i yi mata kayan d’aki ba saboda
time to time za su ke zuwa hutu.

Shima Arshaad a nasa b’angaren hakan bai hana sa siyan gida ba!
Daa a cikin estate d’in zai zauna amman da yake Granpa ya san Hudan zai aura haka nan k’iri k’iri sai ya hana sa gida!
Da farko Granpa d’in cewa ma yayi ya bar mishi estate d’inshi,
tun kafin auren! Da kyar Aslam ya lallab’ashi
ya hak’ura amman dukda haka sai faman neman fad’a yake yi
kuma fa sai da Dad ya tambayeshi tun farko lokacin kafin ma a saka rana amma sai ya nuna irin shi ba ruwanshi d’innan su yi abunda sukeso..
Yanzu kuma da bikin ya taho sai neman rigima yake yi yana neman abokin fad’a!
Shiyasa kowa ya sha jinin jikinshi dan duk wanda yayi rashin sa’a ya yarda ya samu matsala da Granpa a wannan yanayin da yake, tou tabbas kashin shi ya bushe!
Wannan dalili yasa Arshaad ya sayi gidanshi da kanshi daman kuma shi har ga Allah ya ma fi son ya yi komai da kanshi, dan
da kyar ma ya yarda ya bari Daddy ya bawa Mommy mak’udan kud’ad’e take had’a mishi zazzafan lefe..
Gida kuwa da Abba yace zai siya mishi yi yayi kamar zai yi kuka, shi kuma Abban ya dage!
Sai da Mommy ta saka baki tukunna Abban ya hak’ura ya bar Arshaad d’in ya sayi gidanshi mai hawa biyu d’aki bakwai da parlour hud’u har da d’an k’aramin bq a gefe a nan cikin Nasarawa sai dai da d’an tafiya tsakaninsu da gida da estate....

Su Ummu da Mommy ne suka je suka yi mata jerenta tsaf!
Wanda yanzu kawanchen Mama da Mommy ya dawo sabo fil! Dan har gida Mommy taje ta dubota, duk da Dad ba wani son yawan fitar tata yake yi ba amman indai abu ya shafi Maryam to ya kan bari saboda Mommyn tana yi musu campaign a lamarin Abba,
sai ita kuwa Mama duk maganganu da Mommy take mata akan Abban amsa
d’aya zuwa biyu take bata kullum
‘Allah ya zab’a mafi alkhairi’ ko kuma tace ‘ita fa ta riga ta hak’ura da Abba har abada! Ba akan dalili d’aya ba sai akan dalilai barkatai’.
Amman duk hakan bai sanya Mommy ta hak’ura ba, haka nan suke fama kullum.........

Yau sauran kwana uku d’aurin auren!
Su Hudam basu samu komawa wajen Mama ba sai a yau d’in.
Kafin su wuce Abba ya nemi ganinta..
Kamar ko wanne uba haka nan ya zaunar da ita yayi mata nasiha mai ratsa jiki!
Yana hawaye tana kuka
haka su Sudais suma da suka zo yi mata sallama…
A haka dai ba dan suna so ba suka yi sallama Abba ya sanya mata albarka.

Mommy da kanta ta kaita har gidan Shuwa gaban Mama
Hudan tayi mamakin ganin baki y’an Maiduguri da suka zo dan gidan a cike tap! Suka tarar anata hada hada.
A yau d’in zasu fara event!
Dan haka suna isa suka tarar har mai kwalliya ta k’araso
tana jiransu, waensu a cikin friends d’in su ma duk sun zo,
da yake mai kwalliyar da tayi mata ita ce za tayi musu saboda Arshaad Maiduguri style yayi..duk shi ya biyawa friends d’inta kud’in makeup da anko.

M T
Tunda Mommy ta warke
kullum itake ce take yiwa Aslam girki…
Wani special kulawa take bashi amman ta rasa dalilin damuwarshi dan ko jiya ma sai da Doc ya zo ya dubashi kuma ya tabbatar musu jininshi ya k’i sauk’a instead ma k’ara hawa yayi!
Sannan ga zazzab’insa shima ya dawo.

Gaba d’aya hankalinsu duk a tashe yake, dan sun rasa gane kan Aslam kwata kwata.

Arshaad tun yana kulashi, yana tambayarshi meke damunshi yana lallab’ashi,
har ya zo ya hak’ura kawai ya watsa shi a kwandon shara
Dan Arshaad d’in gani yayi kamar ma Aslam d’in haushinshi yake ji!
Idan ma yana waje Arshaad d’in ya shigo kawai sai dai ya tashi ya fice ya bar mishi wajen, ko magana baya so ta had’asa da shi!
Kamar ma wanda yake k’ok’arin yin gaba da shi ta k’arfi da yaji! Shiyasa Arshaad d’in kawai ya rabu da shi
amman a chan k’asan zuciyarshi mamakin abubuwan da Aslam d’in yake mishi a wannan lokacin da ya kamata yafi kowa tayashi murna, yake yi.
Hatta Dad Abba da Daddy sun lura da hakan, basa son shiga tsakaninsu tunda sun fi kusa shiyasa kawai suka zuba musu ido a ransu suna mamakin mai ya had’a best friends haka??…….

Da yamma, Mommy na d’aki tana jera kaya a wardrobe
Dad ya shigo..
A bayanta ya tsaya yayi hugging d’inta.
A hankali tayi murmushi kafin ta juyo still yana rik’e da ita tace
“ina wuni Dad”
Murmushi shima yayi mata yana jin tsananin k’aunarta tana nunkuwa a cikin zuciyarshi, a hankali yace
“Bayan waennan akwai wasu kuma da kike buk’ata??”
A hankali ta girgiza mishi kai alamun ‘a’a’.

Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya jawo hannunta suka nufi gadon dake d’akin.
Sai da ya zaunar da ita shima ya zauna a daff da ita tukunna yace
“Aisha, magana nake so muyi dake ta gaskiya da gaskiya”
Da sauri ta mik’e tana k’ok’arin kawar da kanta daga gareshi kafin tace
“Not again Dad, na gaya maka ban tuna komai ba, please Dad ka bar maganar nan.”
Mik’ewa shima yayi ya sake rik’o hannunta kafin yace
“Look at me kice mini ‘wallahi Dad ban tuna komai ba‘.”
Hannunta ta fara k’ok’arin kwacewa a cikin nashi ta had rai sosai cikin fushi tace
“Tunda baka yarda da ni ba, shikenan!”

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
“Jiya da yamma kin manta wayarki a d’akina kin tafi kitchen, naje kai miki wayar saboda a nata kira..
I didn’t mean to eavesdrop but i have no choice!
Naji komai maganan ku da kuka yi ke da Asabe!..
Mai yasa kika b’oye min?”.

Gabanta ne ya yanke ya fad’i!
A hankali ta tsaya tayi tsit ta nutsu ba tare da tace komai ba, sannan ta kasa d’agowa ta kalleshi…

Hannu yasa ya kamo hab’arta ya juyo da fuskarta ya d’ago fuskar, da sauri ta runtse idanuwanta.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin a hankali yace
“Maimaita min abinda ya faru that very day da kika fad’o, waye ya turoki?! Ina so inji daga bakinki, don’t lie, kin san naji komai..
Kawai i want you to tell me.”
Chapter 52 · 0% Book details