← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 70

Sashe 34

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sosai yayi this time around kafin ya matso da fuskarshi dede tata tukun yace
“If she’s cousin and more would I do dis in front of her?”
Ya k’arashe maganan da kissing lips d’inta lightly…..

Da sauri Hudan ta bar wajen tana had’a hanya.

Kujerun data gani a gefe chan taje ta zauna tana haki tana istighfari.

A chaan wajen su Auwal kuwa murmushin jin dad’i budurwar tayi sannan suka shiga sabgogin gabansu..........

A tap d’in wajen tayi alwala, wasu mata manya ta gani da darduma sun shinfida k’atuwa suna zazzaune ga kuloli alamun picnic suka fito, dan haka ta k’arasa tayi musu sallama tace
“Dan Allah tanaso za tayi sallah”
Da fara’a suka tarbeta suka matsa mata d’ayar ta fiddo hijabi a jakanta ta bata..
Bayan ta idar suka yi mata tayin abinci, gorar ruwa kawai ta d’auka ta sha tayi musu godiya a wajen ta ci gaba da zamanta a wajen, tana hango Sudais yanata wasanshi, chan gefe kuma Auwal da budurwarshi an cika musu gaba da kayan kwalama kala kala amman ita ko ruwan sha ya kasa bata…
Ganin bata da abunyi yasa ta bud’e wayarta ta hau karatunta ragowar ruwan da ta sha d’an mitsitsi ta rage ta tofa a ciki..

Sai da aka fara kiraye kirayen sallar Magrib tukunna taga ya taso…
Yana tasowa ta mik’e ta hau sallarta dan ta lura In suka kama hanya yanzu sai sun kusan 40min suna tafiya.

Takaici, kamar ya kifa mata mari haka yaji, ba yadda ya iya shima yaje yayi alwalla yayi iya magribar d’in daya tarar maza sunyi jam’i suna yi.

Tare suka jero da budurwar da Sudais da yaje ya d’auko, suka nufota.

Sallama da godiya ta yiwa matan da suma suketa shirin tashi, ta rik’e hannun Sudais wanda ya iso gareta da sauri suka nufi inda suka yi parking.

Sai da ya k’araso ya bud’e motar tukunna suka shiga
Ita da Sudais suka zauna a baya shi da budurwar suka zauna a gaba.
Sai da suka biya wani gida a lamido crescent flat mai kyau suka ajjiyeta tukunna suka wuce…Abunda ya d’aurewa Hudan kai shine shi Auwal d’inne ya bawa budurwar makullan gidan!

Ita dai batayi magana ba, ta yi shiru kawai tana mamakin shi..
Ko da yace wani ya koma gaba, Sudais ta matsawa ya tsallaka.

A gajiye suka isa gida yana ajjiye su yayi reverse ya sake fita.

A parlourn ta tarar da Arshaad
wanda suna dawowa daga kai Amarya ya had’u da Aslam cikin hira yake gaya mishi ‘Hudan sun fita munjibir da Auwal!’
Ko wanka kasa yi yayi ya taho gidan…
Yana tunanin bin bayan su kenan suka shigo.

Ajiyar zuciyar daya sauk’e lokacin da suka shigo sai da taji, sarai ta lura dashi amman ta d’auke kai tayi wucewarta….ganin yadda ta bawa iska ajiyarshi kuwa hakan yayi mugun bak’anta mishi rai!
At least in tana jin haushinshi ai ko darajar kallo yaci ace ya samu.

Sai da ta raka Sudais d’akin shi tukunna ta nufi side d’inta.

Tana shiga parlourn ta saki jakarta ta tafi da gudu tana ihun murna.
Rungume juna sukayi suna dariya kafin tace “tun yaushe kika zo?”
Dariya itama Sakina tayi tace
“D’azu Abbas yaje da kanshi ya d’auko ni hala ke kikayi mishi kwatance ko?”
“Eh” tace
tana sake hugging d’inta, sannan ta jata suka nufi bedroom.

“Ma shaa Allah,
Ubangiji mai zamani”
Sakina tace.

Sannan tace “gaskiya wajen nan ya burgeni Huda, over!!
Ina tunanin had’uwar parlourn ashe bedroom d’in har ya fishi? “
Murmushi Hudan tayi tace
“Ni kuma duk toilet d’in yafi burgeni” da sauri Sakina tace “muje In gani” ta fad’a tana cire hijab d’in jikinta dake nan har k’asa.
Suna shiga nan itama tace “gaskiya kam toilet d’in duk yafi had’uwa”
Haka nan suka taru suka dinga hauka, daga su kunna wannan sai su kashe wannan, wani abun ma ba iyawa suka yi ba da karambani suka koya. Babu abunda yafi burge Sakina irin closet dan haka ta fito wajen tana kuma setawa Hudan zaman kayanta kafin ta fito a wanka.

Bata wani dad’e ba ta fito a wankan
tana fitowa tace “itama ta shiga tayi wanka sai ta chanja kayan jikinta, lace d’in zai yi mata nauyi dan garin ana zafi sosai”
Murmushi Sakina tayi kafin tace “Ni fa daga ni sai hand bag d’ina nazo, Ummu daa hanani zuwa tayi fa, sai da Baba ya bud’e mata wuta!Amman tace wai gobe da safe in dawo, har na d’auko kaya set uku tace wai In na tafi da kaya ba zan dawo da wuri ba!
Shi kuma Baba yace tunda Abba ne da kansa ya rok’esa to sai lokacin da kika saba da nan d’in tukunna zan koma!.

Wallahi tun d’azu jikina a sanyaye yake, Mama ma bata san na taho ba, dan Ummu tace bata san da wanne ido zata kalle ta ta fad’a mata ba!
Shinema dalilinta na hanani zuwa tun farko daman.”

Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin tace
“Ranar dana tafi ya aka yi? Ina ta kiran Ummu bata d’auka.”

“Hmm..
Mama ce ta rikita kowa wai Abba ya aiko an sace ki!
Amman har yanzu a haka su Ummu suka barta basu gaya mata ke kika tafi da kannki ba saboda kar taji haushinmu, kawai dai ance mata kina nan d’in so ta kwantar da hankalinta tunda kina wajen Mahaifinki ne ba wani mugun hannu ba.”

Hawaye Hudan ta goge kafin tace “Sakina wallahi ni ban san ya zan yi ba” ta fad’a tana fashewa da kuka, rungumeta Sakina tayi kafin tace “wallahi Huda ni kaina abun nan yana daure min kai, sai ka rasa ina zaka tsaya, gaba d’aya ni kaina i’m confused, ballantana kuma ke.
Muyi ta addua kawai ki kwantar da hankalinki, kinji?Please”.

Hawayenta ta goge jikinta duk yayi sanyi, sannan ta d’an d’aga kanta
a hankali kafin ta cewa Sakinan “kije kiyi wanka sai ki sa kayana
Inner wears kuma ina da sababbi suma, muyi
sauri dan na san yanzu Abba zai fara kira, lokacin dinner yayi.”

Hijab d’inta wanda ta ajjiye a bedroom Hudan ta fita ta d’auko ta wuce ta sa a washing machine ta fito ta bata towel,
Ita ta tayata wankin dan sai da ta tayata ma shanya kayan data cire suka wanke d’in tukun ta fito ta barta dan tayi wankan.

Sallah ta tarar Hudan tanayi lokacin da ta fito dan haka itama ta nemi hijab ta tayar da sallar.
Sauranta izu d’aya a izu goman daya kamata tayi, dan haka ta hau karatu bayan ta idar….
Tana idarwa tayi addua ta tofa ta had’e ruwan d’azu data shigo dashi dana d’akin waje d’aya!.
Da mamaki Sakina ta kalle ta kafin ta tambayeta
Bayani ta hau yi mata a kan ‘na maman Aslam ne wanda ta basu labarinta….’
“Allah sarki Allah ya bata lafiya, abun tausayi wallahi”
Sakinan tace.

Kayan bacci dukkansu suka sanya, sai suka d’aura hijabai a sama, sannan suka sauk’a dan Abba har ya kirata kamar yanda tayi tsammani.

Sai da ta lek’a d’akin su Sudais, ganin basa nan yasa suka nufi k’asan.

Har Aslam suka tarar a dining d’in da Arshaad amman yanzu ya chanja kaya wanda hakan ke nuni da wanka yaje yayo.

Yaji tahowa amman bai d’ago ba, dan babu abunda yake sosa mishi zuciya irin yadda ko kallon inda yake bata yi.

Sai da suka k’araso tukun Abba yace “a’a inyee! Yau ga annuri a fuskar princess, duk a dalilin Sakina, irin wannan murmushi haka?!”
Ya fad’a yana murmushi
kafin yace “bismillah ku zauna mana”

A hankali suka fara k’ok’arin jan kujera…
Yana shirin d’agowa ya ga da gaske Sakinan ce jin abunda Abba yace, yaji tace “Ya Arshaad Ina wuni.”
Da sauri ya d’ago, ya d’an zaro ido alamun mamaki, sai
kuma ya fara murmushi yace
“Lafiya, Alhamdulillah.
Ashe kece da kanki!
Welcome, ya gida?”

“Alhamdulillah” tace kafin ta d’an turo baki tace
“Ai gani nayi da farko ka wani had’e rai ko kallon inda muke ma bakayi ba”
Dariya yayi kafin yace
“Hankalina baya wajen ne,
sorry”
Itama murmushi tayi ta sake gaida Abba da Aslam wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba!
Tunda suka sauk’o ma ta lura bai ko kallesu ba…
Tana ganinshi tashi d’aya ta fahimci shine Aslam.
Lokacin da Hudan take zuzuta mata kyawun Aslam d’in bata yarda ba, dan har ta fara tunanin wani abun a tare da Hudan na daban,
but yanzu kam tagani itama!
“Tubarakallah!”
Ta fad’a a k’asan ranta.

Cikin nutsuwa taji Hudan suna gaisawa da Abba wanda yake zaune a opposite d’insu shi da Aslam. Da kulawa yake tambayanta hope taji dad’in ganin Sakina? Is she happy now? Taji dad’in zuwa munjibir park d’in? Ba wata damuwa ko?……
Murmushi Hudan tayi duk tana ta binshi da “Alhamdulillah komai Alhamdulillah..”

Abun yayi matuk’ar burge Sakina a ranta tace “yau ina Baba da Umma suzo suga gatan da akewa Huda, suga yanda Abbanta yake janta a jiki yana lallab’a ta”
Wani farin ciki ne taji ya lullub’eta, tabbas tana yiwa Hudan murna da baiyyanar Mahaifinta!
Itafa sometimes ji take a ranta kamar ma tafi Hudan farin ciki.

A hankali taji sun gaisa da Aslam, taga ita Hudan ta d’an samu darajar kallo a wajenshi tukunna yace “lafiya” da d’an mitsitsin bakinshi.

Har an fara serving ta mintsili Huda da k’arfi ta k’asa k’asa inda ba za a gani ba.
“Ouch” tace, a hankali sannan ta juyo tana kallon ta, harara Sakina ta zabga mata k’asa k’asa tace “shi ba zaki gaidashi ba???”
Itama Hudan hararar ta maida mata ta cigaba da zuba abincinta!
Mintsilinta Sakina ta sake yi, kafin tace
“Wallahi ko ki gaisheshi ko kiyi ta karb’ar ruwan mintsili kala kala!”
Dai dai nan wayar Abba tayi k’ara …
Excusing kanshi yayi ya mik’e ya d’an koma gefe yana amsa wayar dan it’s a very important call ba zai yiu yayi ignoring ba.

Kamar jira Sakina take, nan ta sake sakar mata wani sabon mintsinin da sai da tayi k’ara mai sauti sosai this time around har su Aslam sai da sukaji suka juyo suna kallonsu…
Sudais kuma ya fara kyalkyala dariya dan shine a kusa da Sakina yana kallonta tun d’azu!
Chapter 34 · 0% Book details