← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 70

Sashe 46

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da kyar suka lallasheta tayi shiru, tana tunanin rabonta da d’akin tun ranar da tabi Abba suka gudu!
Bayan nan
Ko tazo gidan, a tsakar gida ake tarar ta ko alwalla za tayi sai dai ta shiga band’akin tsakar gida, a hakan shima sai in ya zama dole ne kuma in Shuwa taga dama.

Ita da Sakina ne suka kamata suka d’aura akan gadon dukda tanata ce musu “zata iya fa”.

Favorite food d’inta Shuwa ta sa aka dafa, da mai aikin ta kawo tana bud’ewa suka saki murmushi a tare ita da Ummu.

Ummu kalmar “Alhamdulillah” kawai take ta maimaitawa a zuciyarta, ga dukkan alamu Shuwa ta sauk’o! Allah yasa ta yarda ta yafewa Maryam a samu komai ya dawo dai dai kamar daa.

Sai dare bayan Ummu ta tafi tukun Shuwa ta shigo.
Kwata kwata Maryam ta rasa dalilin da yasa Hajiya Shuwan bata iya had’a ido da ita
dan yanzun ma “ya jiki?” tayi mata ta kuma tambayeta “ko akwai abunda take buk’ata” ba tare da ta bari sun had’a ido
ba.
Da “a’a” ta amsa, dan haka tayi mata “Allah ya k’ara sauk’i” da “sai da safe” ta fice da sauri.
Da daddaren ma abincin da Shuwa ta san Maryam d’in tana so tasa aka yi a gidan.

A washegarin ranar da aka sallami Maryam aka sako ya Usman!
Tunda Baaba Talatu taji labarin za a sake shi yau ta tafi gidanshi ta chake.

Suna d’aki ita da Sadiya, suka ji k’arar bud’ewar d’akin shi
dan haka suka nufi chan.

Baaba Talatu tana ganinshi ta fara kuka haka ita ma Sadiya, sai da su Kaka suka daka musu tsawa tukun suka nutsu.

Abinci kawai Baaba Talatu ta bari ya ci, daga nan ta cewa Sadiya “ta d’an basu guri” ko gama fita bata bari Sadiyan ta yi ba ta hau kwararo mishi bayanin halin da ake ciki.

Tashin hankalin da ba a saka mishi rana!!!

Tsananin tashin hankalin da Baba ya shiga ba zai fad’u ba!
Gashi Kaka yace “wallahi ko a k’ofar gidan Madu ya ganshi sai ya tsine mishi!”
Madu zai yi magana, Kaka yace masa “Dan Allah yayi shiru, kar yace komai” daga nan ya jaa hannunshi suka fita, suka tafi.

Yadda Baba ya hargitse sai da Baaba Talatu ta yi dana sanin fad’a masa…
K’arshema kuka ya saka mata, ga tsananin rad’ad’in ciwukan jikinshi ga rad’ad’in zuciya ga tashin hankali!!
Kuka wiwi haka ya dinga yi kamar k’aramin Yaro.
Shi har ga Allah ya shirya ne akan
….Bayan ya saketa!
Ya san zata yi ta Allah Allah ta fita a idda dan ta auri Abba shima kuma Abban haka!
Shikuma ana i gobe ko jibi zata fita daga iddar sai ya zo yace ya maida ita!
A tunanin shi hakan zai sanya Maryam ta hak’ura gaba d’aya, dan ya san ta tun Yarinta bata son ayi ta ja mata rai akan abu........

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
48

Da kyar aka samu Baba ya d’an nutsu
Tukunna Baaba Talatu ta tafi
da alk’awarin gobe da sassafe zata dawo!

Washegari, tana zuwa ta tarar da Umma a d’akin tana kuka
bata kai ga tambayarta ba
Umman ta mik’a mata wata takarda, cikin kuka tace
“Yanzu saboda Maryam shine zai tattara kaff ya tafi wajen Ya Jamilu saboda Allah?
Ni kuma fa?
Ni da y’ay’ana ba damuwarshi bace kenan?.

Baaba Talatu rasa bakin magana tayi…..haka suka kasance Sadiya tana kuka ita kuma tayi zurfi a lissafi da tunane tunane ga damuwa kafin da kyar ta shiga bawa Sadiyan hak’uri har ta samu ta d’an nustu.

A Washegarin, da safe kafin Ummu ta wuce office
ta zo ta dubasu…
A d’akin ta tarar da Shuwa itama ta sauk’o duba Maman.
Sai da ta tabbatar komai yayi settlling
Maman tayi wanka ta ci abinci tukunna ta fara shirin fita dan client d’inta already tana office tana jiranta…
Tana mai cewa Huda “akwai bak’uwar da zata yi daga Maiduguri”.
Daga haka ta sa kai ta wuce bayan Hudan tace mata “to, Allah ya kaimu.” Tace “Ammen”.

K’arfe uku bak’uwar ta iso, mai gyaran jiki.

D’aki guda Shuwa tasa aka ware ake gyarata ciki da waje….tun tana nok’ewa har ta sake, Sakina ita ma ba a barta a baya ba, dan duk abinda aka gogama Huda a fatarta itama sai ta goga

Kafin sati biyu suka yi wani kyau na ban mamaki, in ka gansu kamar ka sacesu ka gudu.
A lokacin bikin Hudan da Arshaad bai kai saura sati uku ba. A lokacin kuma k’afar Mama ta warke ba laifi, kasancewar transverse fracture ta samu
shiyasa abun yazo da sauk’i, but still bata gama warkewa ba, so zata ke zuwa follow ups akai akai.

Abba baya samun zuwa gidan ganin Mama, sai dai yakan zo
ya karb’i ruwan karatu a wajen su Hudan time to time!
Wani lokacin kuma yace kawai suyi addu’a daga gidan
Arshaad ma daga inda yake , yake yi.

Idan Abban yazo Hudan ce
ke kai mishi a mota inda yayi parking, yana so ya shiga ya gaida Shuwa yaga jikin Maman amman bai san ta ina zai fara ba! Har yau yana tuno b’acin ran da ya gani a idanun Shuwa ranar daya kawo Maryam
Madu kam suna had’uwa su gaisa da shi da Kaka
wasu lokutan ma tare suke yin sallar Isha..
Haka nan yanaji yana gani in ya karb’a sak’on zai tafi, ga dai
Maryam a kusa amman ba daman ganinta.
Yana yawan kiran waya yace Hudan ta bata amma k’iri k’iri zata k’i karb’a, ayi ayi tak’i, k’arshe dai In ya kira sai Sakina ta karb’a ta sa wayar a speaker ta ajjiye akan gado, su fita da sauri…
Tun Maman tana yi musu fad’a har ta daina.

In suka dawo a inda suka ajjiyar wayar anan suke tarar da ita, Mama tayi ta mata fad’a amman gobe ma sai ta k’ara, in
ta cika magana tace
“Ai lada take nema, dan ita aure take shirin k’ullawa!”
Dan haka kawai Mama sai ta daina fad’an ta daina biyeta, dan ta ga alamun kakarta ma take son mayar da ita,
ita kuma bata shirya biyeta akan zancen Abba ba.

A Satinsu na biyu ne
Abban ya nemi su koma haka, Mama taso yin musu
amman Shuwa tasa baki..

Sakina kam ta nace ba zata bi Hudan ba tace “ai yanzu ta saba da kowa”
Sai da taga Huda na shirin yi mata kuka tana had’awa da magiya tukunna ta yarda zata bita a ranta tana tuno irin nacin Auwal da bataso! Dan wallahi ita saboda shi ne ma daa d’in tace ba zata bi Hudan ba!
Bata san a ina ya samu nunbertaba amman kullum sai ya kirata bata gajiya da rejecting shi kuma baya gajiya da kira!

Sai dare Abba ya zo d’aukar su, tun safe daman da ta san zasu tafi taketa nuk’u nuk’u
Da suka zo tafiya kuwa sai da tayi kwalla!
Ummu ce ta rakasu har mota
(Sakina Hudan da mai gyaran jikinsu ) ta dawo.
Tana shigowa d’akin ta tarar da shuwa tana lallab’a Mama
Abun yayi matuk’ar burgeta dan haka ta zauna a gefe tana jin Shuwan tana cewa
“Duk abunda hak’uri bai bada ba fushi da zuciya ba zasu kawo ba!
kwanaki da kika d’aga hankalinki akan sai Hudan ta dawo hannunki, waye waye aka yi ta rikice dai kina kukan ya rabaki da y’arki
hankalin kowa a tashe!.
Yanzu ki gaya min a cikin wata d’aya da sati d’ayan nan da wa Hudan tafi zama tsakanin ke da shi?
Ai ita y’a mace da Mahaifiyarta aka santa, ki ci gaba da bin komai a hankali wata rana sai labari!
Kuma in dai za kiyi wa Abba adalci shima ya kamata ace ya d’an zauna da y’arsa kafin aurenta, kuma kinaji da kansa yace ‘In bikin ya rage saura kwana biyar nan zai dawo da ita a hannunki za a d’auketa!’ Wanne kalar adalci kuma kike buk’atar yayi miki sama da wannan??”…..
Shuwa bata barta ba sai da ta tabbatar ta gwada mata gaskiya sannan ta d’an sauk’o tukunna tayi musu sallama ta tafi d’akinta.

Ummu da Sumayya su suka ci gaba da zama da ita saboda Baban Sakina yayi tafiya tun wanchan satin.

Arshaad ma yayi tafiya zuwa Uk da kuma garin da za suyi honeymoon d’insu…
Yaje domin ya d’an yi settling accomodation da sauran harkar karatun su shi da Amaryarsa kafin su tarkata su yi chan gaba d’aya.

Satinshi biyu, sai yau ya dawo shima (Washegarin ranar da su Huda suka koma GRA).

Aslam ne yaje ya d’auko shi.
Ba yadda Arshaad bai yi da Aslam ba akan ya kaishi ya fara ganin Hudan amman furr!! Aslam d’in ya k’i! Yace “ai shi ce mishi yayi yazo ya d’auko shi ya kaishi gida ba golden G Avenue ba.”
B’ata rai Arshaad yayi, yana ji yana gani Aslam ya kaishi MT estate.
Ko thankyou bai che mishi ba ya bud’e k’ofar fito ya bud’e baya ya d’au kayanshi
yana ta b’ata fuska..
Yana shirin rufe murfin motar Aslam yace masa “Amm, by the way you are welcome”
Yana d’an dariya k’asa k’asa.
Rufe murfin motar Arshaad yayi ya juya shima yana d’an murmushi sama sama har ya isa gida.
Chapter 46 · 0% Book details