← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 70

Sashe 49

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan k’uraa mata ido yayi, kafin yace
“Okay, banda shirme.”
Sannan ya juya har zai wuce sai kuma ya juyo yace
“Kina buk’atar cash ko?”
Yayi maganar yana mai zura hannunshi a aljihu.

Dasauri Auwal yace
“No. Abba I’ll take care of it.”

“Okay” kawai Abban yace, dan sauri yake yi, yayi gaba ya bar su a wajen.

Murmushi Auwal yayi kafin ya dawo dai dai setin Sakina inda ta kawar da kai ta mayar da fuskarta ta, yace
“For this surprises sake za a d’an kula ni ko?
Na wuni d’aya tak dai?”
Ya k’arashe maganar yana karyar da wuyanshi sannan ya maida fuskarshi kalar tausayi.

Kallonshi tayi, bakinta na d’an motsi, tana son yin magana amman yanda idanuwanshi ya sarke da nata ne, ya sanya ta kasa cewa komai.

A hankali ya lumshe idanunsa ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciyar da har sai da ta jiyo hucin numfashinsa mai d’umi wanda ya had’e da wani calm scent da kuma k’amshin turarenshi…
tana shirin d’auke idanunta daga kan kyakkyawar fuskarshi, ya bud’e idanunshi
cikin hikima ya sake yin nasarar sark’e kwayar idanuwan nasu waje d’aya, a hankali taji yace
“I love you!”.

Gabanta ne ya bada wani ‘Dumm!! Da masifar k’arfin da bata san dalili ba....

Da kyar ta aro jarumta ta yafa, da mugun k’ok’ari tayi nasarar zare kwayar idanunta a nashi k’irjinta na ci gaba da dukan uku uku.
Harara ta zabga masa, ba tare da ta yarda ta sake kallon cikin idanunshiba had’e da yin tsaki sannan ta juya da mugun sauri zata shiga ciki..a ranta tana aiyyana
‘Tabbas Auwal tantirin shed’an ne!’ Dan gashi yana k’ok’arin rusa mata tsari cikin mintunan da basu gaza ashirin ba…

Da kyar ya iya had’a kuzarin da ya bashi nasarar shan gabanta, ya tsaya a bakin k’ofar, dan ba k’adan ba jikinshi yayi mugun yin weak!
Da sauri ya had’a hannuwanshi biyu waje d’aya kafin yace
“I’m sorry? so sorry ba zan k’ara ba.
Please lets just..
Bari in kira wanda na san zai yi, a Kano yake yanzu nan zai zo, professional ne, okay?”
Ya k’arashe maganar da alamun serious a kan fuskanshi, yana mai d’aga mata gira duka biyu da d’an ware ido.

“Unhm”
Kawai tace sannan ta koma gefe tayi folding hannayenta tana kallon wani waje.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, ya fara k’ok’arin dialing number mai hoton….

A gabanta suka yi waya sukai fixing time @5:00 pm
Zai k’araso, nan da 2 hours kenan.

Suna gama wayar tace “thankyou” kawai sannan ta fara k’ok’arin wucewa.

A hankali yace
“Am, Sakina… i”.

Da sauri ta d’aga mishi hannu d’aya, alamar (stop)
Kafin tace
“Ya Auwal please..
Ka kyale ni!
Bana so!.
I’m in a very serious relationship, besides ko ma bana dating d’in kowa I will never ever choose you! After what you did to Jalila kuma still ka ke dodging..
Kullum ko sunan ka naji an kira abunda nake tunowa kenan!.
Ban shirya auren bazawari ba, ko da ace maza sun k’are ina rok’on Allah kar ya d’aura min k’addarar auren bazawari second hand.”

Auwal bai san san ya akai ba, amman tabbas kamar hawaye yake ji suna shirin zubo mishi.

Ita kanta Sakinar ta lura da yanda idanunshi suke kyallin hawaye. Jikinta ne ya d’anyi sanyi dan haka
ta yi k’ok’ari ta danne ragowar maganganun da take ji suna taso mata.

A hankali yace
“Sakina na rantse miki da Allah a yanda nake jin ki a cikin zuciyata, ba abunda ba zan iya sacrificing akan ki ba, kuma babu abunda ba zan iya yi a kanki ba, zan iya chanja kaina in koma yadda kike so na zama, muddin zaki yarda da ni.
I don’t know how why but ni kaina ina jin tsoron kalar k’aunar da nake yi miki! I just knew you but i have fallen head over heels…
Na tabbatar ba wanda ya tab’a yiwa wata kalar pure love d’in da nake yi miki..
Ba wai wani abu daban ba
kawai k’aunarki, yardarki, soul d’inki shi nake muradi.”
Ya k’arashe maganar cikin karyewar zuciya.

Shiruu, tayi kawai tayi k’asa da kanta, bata k’aunar abunda zai sa ta sake had’a ido da shi.
A hankali tace
“Ka rabu da ni!
Dan Allah.”

Yana shirin yin magana Arshaad ya bud’e k’ofa
Hudan na a bayan sa.

Juyawa Auwal d’in yayi
aka hau kallon kallo..,,

Arshaad ne ya katse shirun ta hanyar mik’awa Auwal hannu suka yi musabaha, a hankali Hudan ita kuma ta gaidashi.
Yana amsawa ya wuce ya nufi part d’insu yana ji kamar zuciyarshi zata fashe! Tabbas ya san ba komai ke binshi ba sai hakki..Hakkin y’an matan da ya yaudara, da waenda ya wulak’anta, da waenda yayi mocking soyayyar da suke yi mishi! Duk hakkin su ne yake binshi. Yayi mocking soyayya, ya yaudari dayawa ta hanyar kalmar soyayya, ya wulak’anta dayawa dan sun nuna mishi zallar soyayya, shiyasa shi kuma yanzu Allah ya d’aura mishi tsantsar so mai mugun zafi da azabtar da zuciya
wanda ya san wadda yake yi wa ba lalle ta soshi ba,
gashi yanzu ma direct ta fad’a mishi ‘she’s in a very serious relationship’ wanda hakan sai da ya kusan kasheshi ba tare da ta lura ba.
Daman haka so yake?
Dama haka mutum yake ji?
Tabbas shi kam ya san ajalinshi..dan muddin Sakina bata yarda dashi ba akwai matsala! Ranar kuwa da akace ta auri wanda take ik’irarin suna tare d’in ya san a ranar zai bar duniya……
Yana wannan lissafin da tunanin ya k’arasa b’angarensu, direct side nasa ya nufa, yana zuwa ya rufe ko Ina ya k’ara k’arfin ac ya zxube a kan kujera, ko d’aki kasa k’arasawa yayi..........

Hudan ta bud’e baki kenan zata yi magana Sakina tayi sauri ta wucesu ta shige ciki.
Direct sama d’akin Hudan ta nufa, ta dad’e ta kusan awa d’aya tana juyi a kan gado ita kad’ai, daga baya ta hak’ura ta sauk’o.
Suna zaune suna hira su Sudais suna gefe suna chess,
tun da suka dawo daga karb’o gown d’in ta (Hudan) wadda delivery man ya kawo suke zuba idon ganinta amman bata sauk’o ba, Hudan taso zuwa amman Arshaad ya hanata…
.....Sakina bata dace da Auwal ba at all, amman in haka Allah ya tsara basu da damar shiga tsakani, besides yayi mamakin changes d’in da yake gani a Auwal those days, maybe in ya samu wadda yake so ya aura a samu ya nutsu!
Ko a office yanzu ya daina biye biyen matan da a daa yake yi kamar bunsuru....
Arshaad, yana wannan tunanin yaji sauk’owarta dan haka ya juyo yana kallon yanda take tafiya a hankali kamar ba Sakina ba.

Cikin kulawa yace
“Sai yanzu?”

Murmushi tayi tace
“Bacci ne ya kwashe ni”

Shima murmushin kawai yayi
Hudan kuwa bata ce mata uffan ba…
So take sai sun keb’e tukunna
dan tabbas In tunanin ta ya bata dai dai to Sakina tana k’ok’arin rufta kanta inda dai dace ba.

Suna zaune Auwal ya shigo,
kujerar da Sakina ke kai 2 seater yaje ya zauna ya fara yi mata magana k’asa k’asa..
Ga mamakin Hudan sai taga Sakinar ta biyeshi, suna ta
k’us k’us daga baya kuma ta mik’e ta cewa Hudan “ta zo taji”, shi kuma ya mik’e ya juya ya nufi hanyar fita.

Binta Hudan tayi, suna kaiwa hanyar bene ta rik’o hannun Sakinar wadda ta fara taka stairs.. Juyowa tayi tana kallon ta, k’asa k’asa Huda tace
“Sakina kar fa ki biyewa Ya Auwal!
Naga kamar ya fara cin galaba a kanki. Kin san Allah kuwa dan iska ne!
Ranar da muka je Munjibir park baki ga y.....”

Da sauri Sakina ta matsa kusa da ita ta sa hannuta ta toshe mata baki!
Tun lokacin da Hudan ta fara magana taga tahowarshi, tana so ta hanata taga ya sa hannu ya d’aura akan lips d’inshi alamun tayi shiru yana d’an murmushi
Bama jin Hudan take yi sosai ba saboda gaba d’aya hankalinta ya tafi wajenshi sai da taji tana neman b’aro musu aiki tukunna...

Kallonta Hudan take,
tana “hum um hum um”
Alamun ta saki mata baki.
Ganin tak’i barinta
ya sa ta sa hannu ta janye hannun Sakinar akan bakinta
kafin tace
“Dan na fad’a miki gaskiya shine kike k’ok’arin kasheni? Har da hancina fa kika toshe.
Kin san Allah, tou su Ummu zan gayawa dan ba zai yiu inaji ina gani ki kula d’a is....”
Da sauri Sakina tace
“Shhh, behind u.”

Tsit! Hudan tayi kamar ruwa ya cinye ta, a hankali kuma ta juya…
Karaff! Suka had’a ido da Auwal, yana d’an murmushi yana kallonsu.

Hudan ta san gaskiya ta fad’a, amman sai ta tsinci kanta da jin mugun kunyar shi…
Juyawa kawai tayi ta haye sama, Sakina kuma ta tsaya, ta fad’a mishi amsar abinda ya manta bai tambayeta ba, har ta kaishi ga dawowa.

Bata dad’e da shiga ba Sakina itama ta shigo.
A parlournta ta sameta, dan haka ta zauna akan hannun kujerar da take kai kafin tace
“Hudan, dan Allah ki daina had’a ni da wannan mutumin, na fad’a miki ba zan tab’a sauraron sa ba, infact kin san ina da wanda zan aura ko?.
Kinaso ki san maganar me muke yi?”

Sai da ta d’an k’uraa mata ido, tukun tace
“Eh”

Murmushi Sakina tayi kafin tace “Zo muje d’aki to ki shirya, in yaso muna sauk’a k’asa zaki gani.
Kamar tayi mata musu, sai kuma ta mik’e ta bita.

Suna shiga taga Sakina tanata fito da kayan kwalliya, aikuwa tace bata san zance ba!
Dan in akwai abinda Hudan ta tsana to a shafa mata foundation da concealer, ji takeyi kamar anyi mata suminti a fuska, sometimes har numfashin ta take ji yana d’an yin sama sama, bata tab’a jin iskar gari sai ta wanke.”

Ba kalar rok’on da Sakina bata yi mata ba, amman furr tace “wallahi ba da itaba, ko me za ai sai dai ayi a haka” ita a tunanin ta ma ko wani get together su Sakinar suka had’a, dan tace mata surprise ne suka had’a musu ita da Auwal.
Chapter 49 · 0% Book details