← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 70

Sashe 54

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Sakina tayi
kafin tace
“Ango irin wannan kyau haka?”

Dariya ya d’anyi
sannan yace
“Ai ban kaiki ba.
K’anwar Amarya”
Yana mata magana idanunshi na kan Hudan!
Da kyar ma ya amsa gaisuwarta ita da k’awarta.
Lura da Sakina tayi hankalinshi baya kansu yasa ta saka mishi Hudan a motar ta rufe a ranta tace
“Gata nan ai sai ka cinyeta da kallo”
Tana d’an murmushi.

Ba dan hancinta ya jiyo mata k’amshin turaren Auwal ba da ba abunda zai hanata afkawa kanshi In ta tashi juyowa
domin barin wajen.
A hankali ta d’an juyo jin k’amshi da mutum a bayanta daff!
Suna had’a ido kuwa ta zabga masa wata uwar harara..
A wajen k’anwar Ashraff kawai ya samu gaisuwa, bai
damu ba ya amsa ta kafin ya juya ga Sakina yace
“Kin yi kyau over!”
Yad’an yi mata alamar perfect da hannunshi yana murmushi..
White suite ce shima a jikinshi da d’an ratsin black, yayi masifar yin kyau
sai dai askin sa da yayi yau d’in ne ya b’ata mata rai.

Hannu yasa ya bud’e gaban motar, kafin yace “Bismillah” yana kallonta still da murmushi akan kyakkyawar fuskarshi.

A hankali ta d’auke idanunta daga kanshi, daman tun d’azu da ta sunkuya suna magana da Arshaad ta ganshi zaune a mazaunin driver!
A tunaninshi zata yarda ta zauna kusa dashi kenan, tab!
Ai ko hauka take ba zata yarda ta zauna kusa da shi ba
ita da take k’ok’arin ganin ta kauce mishi ta kowacce hanya,
besides Ashraff ma yana jiranta tare za su tafi..’
Da wannan tunanin ta kamo hannun k’anwar Ashraff ta saka ta a cikin gaban motar ta rufe, ta yi gaba abunta.

Guiwa a sace Auwal ya bita da kallo har ta isa inda motar Ashraff d’in take a chan gefe bama a cikin convoy d’in nasu ba, ta shiga.
Da kyar ya iya dedeta kanshi ya juya yaje ya shiga ya kunna motar
dan har an fara yin gaba...

Suna isa inda za ayi event d’in
ya bud’e motar shi ya fito.
Sai hotuna ake d’auka amman shi bai damu ba, neman ta kawai yake yi..
Ganin ba ita ba dalilin ta yasa ya zaro waya ya hau kiranta!
Kowacce mota ta k’araso, har ta masu d’aukar hoto amman tasu bata iso ba..
Arshaad ne ya d’an kira sunan shi dan haka ya juya,
da hannu Arshaad d’in ya yafito shi, yana zuwa yace “Ana ta hoto babu kai, me kake nema?”
D’an murmushi kawai yayi ya tsaya aka yi musu, daga nan
aka fara k’ok’arin shiga hall d’in.
K’awayen Amarya, a baya Abokan Ango a gaba
Auwal da Jamil su ne daf da Ango da Amarya dan sune suka saka suit kamar Angon
ragowar mazan kowa kayan shi ya saka.

Shi dai Auwal har aka shiga bashi da nutsuwa dan haka Amarya tana zama ya juya ya fita yana mai
cewa Jamil yayi jawabin da da shine zai yi, yana da uzuri.

Arshaad bai yi mamakin rashin ganin Aaima da Aslam a wajen ba! Amman tabbas ranshi ya sosu, baya son b’ata wannan ranar ta musannan dan haka ya kawai sai ya basar ya ci
gaba da huld’ar gabanshi.

Tsarin wajen ba k’aramin had’uwa yayi ba
Tebur da kujeru uku a zagaye wajen guda ashirin!
Sai chan wajen sit d’in Amarya da Ango gefen dama da hagun su kuma akwai kujeru goma goma da dogon tebur
a lamun nan ne wajen zaman best friends dan har ma sunje sun zazzauna matan masu anko mazan kuma waenda suka zo tare.
Kwata kwata friends d’insu da suka tarar a wajen ba sufi ashirin ba!
Cool music ke tashi ba wani hayaniya..
Cocktail ne da cake da sweet da hot chocolate da kuma menu mai d’auke da abubuwa daban daban akan tebur d’in, sai waiters a gefen tebles d’in a tsattsaye su wajen 30 da uniform, duk
abinda kake buk’ata sai ka kira ka gaya musu a menu d’in aje a kawo maka
In ka gama su d’auke.

After kamar 20 minutes da fitar Auwal, motar su Sakina ta shigo wajen..
Ranshi a mugun b’ace ya k’arasa inda motar take!
Bai yi wata wata ba yasa hannu ya bud’e side d’inta ya kamo hannunta ya fito da ita.
Da kyar ta iya tsayawa ta gyara mayafinta wanda yake k’ok’arin zamewa…
Ko lura da guy d’in da ya fito shima ya zagayo inda suke Auwal d’in bai yi ba ya fara magana
“Ina kuka tsaya??
Kin san mintunku nawa kuwa?
Almost 30 minutes kowa ya k’araso banda ku, Ina kuka biya haka?”
Ya k’arashe maganar cikin tsananin b’acin rai, kamar wani ubanta…

Kallon shi take yi kawai.
Sai da ta barshi ya kai aya tukun ta fara k’ok’arin wuceshi ba tare da tace uffan ba!.
Tafarfasar da zuciyarshi keyi ba kad’an bane dan
haka cikin zafin nama ya sake sa hannu ya fincikota ya dawo da ita unintentionally ta bugu da jikin motar.

Da sauri Ashraff ya k’araso inda suke ya juyo da shi ya cukumi wuyan rigar shi!
Cikin tsananin b’acin rai yace
“Meye ne matsalar ka?
Who the hell are you?
A iya sani na bata da yaya!
Ka fito kawai ka fara yiwa mutane hauka..
Ka godewa Allah ni ba mahaukaci bane Irin ka dan wallahi da sai na gyara maka zama a wajen nan!”
Ya k’arashe maganar yana sakin mishi kwala da k’arfi.
Auwal ya taso kenan yana shirin yin magana a zafafe
Idanuwansa suka sauk’a kan Sakina wadda ta fara hawaye.

A take yaji duk jikinshi yayi sanyi…
Tun lokacin da ya tura ta jikin mota har yanzu bata motsa ba tana a yanda take sai dai
hawayen da ita kanta ta rasa na menene waenda suke zuba
akan k’uncinta.

Kamar an tsoma shi a ruwan sanyi haka yaji, ya kasa motsawa zuciyarsa na dukan uku uku, gashi tak’i yarda ta kalli inda yake.

A hankali Ashraff ya k’arasa inda take ya fara yi mata maganar da Auwal d’in baya jin me yake cewa.

Goge hawayenta tayi ta gyara tsayuwarta.
Sannan Ashraff d’in ya bud’e bayan motar ya d’auko k’aton cake d’in da suka tsaya karb’a.
Daganan suka zo suka wuce shi ba tare da sun ce mishi komai ba!.

Sam ya kasa motsi ya kasa yin komai.
Kawai iya hawayen da ya gani daga idonta ne ya kashe mishi guiwa ya sanyaya mishi jiki.
Yafi 10 minutes a wajen
kafin da kyar ya samu ya wuce ciki, yana zuwa ya nemi waje ya zauna..
Ba abunda ya iya ci a wajen yana nan zaune a wajen shi kad’ai amman dukkannin hankalinshi na a kan Sakina wadda itama ya lura bata da sukuni ga Ashraff a gefenta wanda yake ji kamar yaje ya rufe da duka, sai wani shishshige mata yake yi.

Su y’an matan wajen a tunanin su tsabar kyau da had’uwar sa ne yasa yake shan k’amshi yak’i shiga mutane
basu san shi kuwa zuciyarshi ce take shirin tarwatsewa ba!
Gashi ank’i a tashi daga wajen.......

Sai after kamar 2 hours tukunna aka ce Amarya da Ango su yanka cake!
Bayan sun yanka Huda na k’ok’arin durk’usawa ta bashi yayi saurin tarota ya karb’a shi ya durk’usa ya bata!
Ai kuwa aka hau tafi ana ta videos da pictures.
Daga nan masu bada gifts suka bada aka yi addua aka tashi a lokacin already Auwal ya dad’e da komawa cikin mota su kawai yake jira.
Suna fitowa kowa ya fara kama gabanshi….

Bai yi tunanin Sakina zata shigo motar ba!
Dan haka ya fara k’ok’arin tada motar bayan su Hudan sun shigo
Arshaad ne yace
“Wait Auwal, bara mu d’an jira Sakina”
Yana juyawa yaga sun yi sallama da k’awarta da wanda ya gansu tare sun tafi..

Sai da taga wucewarsu, tukunna ta zo ta shiga a lokacin ita kad’ai ce ma ta rage a harabar wajen.

Har suka isa gidan su Mama bai ko kalli inda take ba
Motar shiruuu sai hirar su Arshaad da suke yi k’asa k’asa ba wanda yake jin me suke cewa..

Sallama Sakina tayi da Arshaad
Hudan kuma ta cewa Auwal sun gode, daga nan
Arshaad ya dawo gaba su kuma suka wuce cikin gida.......

Dad, Mommy, Gramma, Aslam Arshaad sai Aaima
kawai Granpa ya buk’aci gani tunda a ganinshi ya riga ya cire Dad da Abba da su Hudan acikin zuriarshi…..

Mammy da Mom kawai suka tarar a parlourn dan Ummi kusan a sume ma aka kawota, shiyasa Granpa ya kira Doc akai d’akin Gramma ma da ita domin bata taimakon gaggawa.

Aaima tana shigowa da suka had’a ido da Mammy sai tayi
kanta ta gudu ta rungume kawai tasa kuka.
A hankali Aslam yaje ya gaida Granpa tukunna ya dawo wajensu ya gaidasu yana mai shafa kan Aaima alamun lallashi, haka itama Mommy bayan ta je ta gaida Granpa d’in ta dawo wajensu….
Gaba d’aya hankalinsu yana ga Aaima, wani abun mamaki kwata kwata basu lura da
Mommy ba har sai da muryarta ta yiwa dodon kunnuwansu dirar mikiya!
A firgice duk su biyun suka d’ago suna kallon ta!
Itanma su d’in take kallo da murmushi akan fuskarta
especially ma Mammy wadda
bakinta yake rawa ta kasa furta uffan!
Mom na shirin yin magana Granpa yayi gyaran murya.

Duk nutsuwa suka yi suka maida hankalin su a kanshi bayan sun d’an gyaygyara zama..
Kallonsu yayi d’aya bayan d’aya, kafin yace
“Ina Muhammad?”
A hankali cikin girmamawa Aslam yace
“Yana wajen event d’insu an fara yau”

Da mamaki Mom da Mammy suka kalleshi, suna shirin yin magana suka ji Aslam d’in ya sake cewa
“Ni da Aaima ma da yanzu zamu wuce
to kuma sai kiranka ya riskemu”.

“Call him! Kace ya bar duk abunda yake ya zo yanzun nan!”
Cewar Granpa.

A hankali Aslam yace
“Granpa plss..”

Cikin d’an fad’a fad’a abunda bai tab’a yi mishi ba yace
“Call him now!!”
Chapter 54 · 0% Book details