Sashe 25
So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Auwal kamar yayi hauka, gashi an gama kwashe kaya ya san
shi kawai Daddy yake jira ya kai Jalila sannan yazo su tafi, ga kuma batun ta na zata tona mishi asiri, kar fa Yarinyar nan ta jik’a mishi aiki!! A daa yana underestimating d’inta yanzu kam ta fara bashi tsoro gaskiya, he has to do something, duk da cewa Mom tace mishi ‘ya jira ta tana dawowa zata yi maganinta’ amman gaskiya he cant wait!! Yana tsoro kar kwab’arsa tayi ruwa, gara kawai ya k’are komai dan shi gani yake ma it’s like sun rabu da Arshaad d’in tunda ta sameshi dan haka tayaya zai iya breaking d’inshi!!!
Takaici ya taru ya yiwa Auwal yawa, ga Jalila sai maganganu take yab’a masa…
Da kyar ya iya controlling kanshi dan ji yake yi kamar yaje ya rufeta da duka ko ya samu sauk’i!
A hankali very calm ya k’arasa inda take ya kamo hannunta
Da sauri ta fisge hannun kafin tace
“Ai wallahi anyi an gama babu k’ari!! Mayaudari kawai, haka kurum ka cuceni!
Ga wasu zantukanka waenda har yau na kasa fahimtar alk’iblarka a kaina..”
Cikin tsananin fushin da ya kasa dannewa yace “na cuceki ko kin cuce ni?? Ke kin San ko waye ni kuwa? Wallahi ba dan abunda na shirya akan ki ba ko a y’ar aiki ba zan tab’a yarda ki zo mini ba!
Kina magana kamar irin dole d’innan nayi miki, Ina ce da yardarki kika bini har gidan?
Zaki wani rainawa mutane hankali, wallahi ki bini a hankali tun ban fito miki a asalin Auwal d’ina ba!!
Magana kad’an In anyi
kice wani ‘za kije ki tona min asiri’
To bari kiji, tsaf! Zan iya cewa Daddy na maidake gida! In
kulle ki anan yunwa ta kasheki daga baya in zo in fitar da gawar ki babu wanda zai ji labari, tunda itama uwarki kwad’ayi ya rufe mata ido ai bata cewa kowa kina nan ba! Stupid useless girl kawai! Banza wadda bata da daraja kwata kwata, Akuya ma ta fiki daraja tunda ita wani lokacin tana guduwa tana jan aji, ke kuwa ana ce miki kule za ki ce cass!.”
Takaici da tsoro ne suka sanya Jalila fashewa da kuka,
wani irin takaicin Umma take ji yana taso mata..
Shiyasa fa ita tayi ta dodging, har ga Allah irin rayuwar nan da yadda ta yarda dashi nan da nan ba hakan ta tsarawa kanta ba!
Ita dai ta san tanada burin son auren mai kud’i, amma
kalli yanzu yadda ta koma, duk ata dalilin biyewa son zuciyar Umma, gashi ta hanata zubar da cikin, kamar ba ita ta tsugunna ta haifeta ba!
Tunda take ba a tab’a yi mata zagin daya girgiza taji haushinshi ba kamar kalar zagin da Auwal yake yi mata especially na yau dan ko ranar daya maidata gida bata ji ciwon zagin kamar na yau ba,
kuma gaskiya ya fad’a!.
Gashi yanda taga ya birkice tabbas zai iya aikata abunda ya fad’a d’in…
Kuka take yi bil hakk’i da gaskiya.
A take ta gama tsarawa kanta zata ce a zubar da cikin kawai ta koma wajen Umma, kowa ya huta.
Ganin yadda tayi ladab
ne ya k’ara bawa
bawa Auwal kwarin guiwar aiwatar da abunda kwakwalwarshi ta shirya mishi yanzun nan, dan haka ya k’arasa inda take tsugunne shima ya tsugunna, fuskarshi ba alamun wasa yace
“Look Jalila, let’s just get this done over with…
Zan baki 5 million”
Da sauri ta d’ago manyan idanuwanta tana kallonshi.
D’aga kanshi yayi alamun ‘yes’ sannan yace
“Miliyan biyar!”
All I want you to do is
‘Kice cikinnan na Arshaad ne, kuma in sama da k’asa zasu had’e kar ki chanja maganan ki, ko a gaban waye, ke hatta uwar data haifeki inaso ki birkice mata kice na Arshaad ne kawai!’
Gaskiyar Maganar ya tsaya daga ni sai ke.
Kar ki damu In komai yazo gangara ni zan san yadda zan yi, komai zai fita normal, ba zaki samu wata matsala ba, understood???”.
Rarraba ido ta fara yi tana k’ok’arin yin magana, suka jiyo sallamar Arshaad.
D’agowa sukayi dukkansu suna kallon hanyar shigowa.
Cikin takunshi ya k’araso cikin parlour…
Wani killer smile Auwal yayi kafin ya mik’e tsaye yace
“D’an halak! Maganar ka muke yi”
Cikin nutsuwa Arshaad d’in ya k’araso inda suke, kallon Jalila yayi yaga yanda take kuka, a ranshi yana mamakin ina Auwal ya samota haka, gashi sai kuka take yi…
Ganin ba wannan ne ya kawo shi ba yasa ya d’auke idonshi a kanta ya maida kan Auwal d’in sannan yace
“Daddy is waiting, infact everyone, for you, kayi sauri dan yace karka bari yazo ya sameka a nan!”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fara k’ok’arin fita.
Da mamaki Auwal yake kallonshi da Jalilan wadda tunda Arshaad d’in ya fara magana take kallonshi,
Ganin arshaad d’in na shirin fita ba tare da ya ma sake kallon Jalilan ba yasa Auwal yin ta maza ya zagaya ya tsaya a gaban shi sannan yace
“Saurin me kake yi? I’m just trying to clean up your mess here fa, amman kayi kamar ma baka santa ba, ko In barta ta tafi wajen su Abba ne?”
D’an dakatawa Arshaad yayi sai kuma ya juya yana kallon Jalilan..
Da ido Auwal yayi mata signal d’in da ta kasa ganewa, ita dai kawai sai ta mik’e, kamar an tsoma ta a ruwa jikinta na d’an rawa.
Murmushi Auwal d’in yayi sannan ya zagayo yace
“Talk mana Jalila, ko tsoronshi kike ji yau kuma?”
Kame kame Jalila ta fara yi, ta rasa ta Ina zata fara dan Bata san me zata ce ba, gashi duk da halin da take ciki tunda taji Auwal ya ambaci miliyan biyar ta rikice, hali zanen dutse!.
Don haka tace
“Daman nazo ne akan maganar mu”
Tayi maganar jikina na d’an karkarwa dan har yanxu k’irjinta bugawa yake yi…
yau ce rana ta farko data tsaya ta k’arewa Arshaad kallo!!
Ita dai tun lokacin da yake zuwa wajen Hudan ta san yana burgeta kuma yanayin shi, maganarsa, tsayi da k’amshin turarenshi suna mugun k’ara kid’imata!
Kawai dai ita ta san tana so Arshaad har cikin zuciyarta, amman yau data tsaya ta k’are mishi kallo ta sake rikicewa kuma ta tabbatar idan har bata sameshiba to ko dai ta mutu ko kuma ta shiga hauka…
K’irjinta in banda bugawa babu abinda yake yi, gashi ya tsareta da dogayen shanyayyun idanuwanshi, cikin tsare gida yace
“Wacce magana kenan??
Do i know you?”
Wata dariya Auwal ya saka kafin ya k’araso yana cewa “Okayy!! Bari in yi maka dalla dalla..
Maganar cikinka wanda ke a jikinta! Shi ta biyo ka ku k’arasa.”
Arshaad zuwa yanzu yazo wuya! Don haka ya yanke shawarar cin uban Auwal dan ya lura bayan rainin hankalin da yake yi mishi, harda hauka ma ya fara damunshi kwana biyu, gara a yita ta k’are ko zai dawo hankalin shi, in hauka ya za ayi ya d’auko Yarinyar da bai tab’a ganiba a rayuwarshi ya hau yi mishi wani maganan banza da wofi??!
A fusace ya juyo yana shirin yin kan Auwal, sukaji k’arar fad’uwar abu, da sauri duk suka juya suna kallon k’ofa..
Arshaad, ya san yana da gaskiya amman kalar kallon tuhumar da Hudan take yi mishi da kuma yanayin fuskantar, ne
ya sanya gabanshi yayi mugun fad’uwa sannan wata zazzafar zufa ta hau keto mishi, tabbas ya san taji shirmen da Auwal ya gama fad’a yanzu.
Auwal kam tsayawa yayi yana kallonta yana mamakin tsananin kamanninta da Abba da Aslam!
“Who’s she!?”
Ya fad’a a hankali ba tare da kowa ya jishi ba.
Chan kuma sai ya tuno da case din y’ar gidan Abba da har ta kaiga kulle su Mom d’inshi a cell!
Antake kwakwalwarshi ta d’au chaji, don haka a zafafe ya nufeta, daman neman ta yake yi ya kora mata warning!!
Jalila kuwa tsorone ya rufeta ganin Huda, a tunanin ta Umma ce ta fad’i inda take, su kuma suka zo har da su Kaka tafiya da ita, dan haka karkarwar jikinta ya tsananta ba abunda take tunawa irin auren ta da Mati mai wanki ta san yanzu kam babu fashi!.
Cikin zafin nama Auwal yana karasawa inda Huda take tsaye yace
“Hey! Couz…
You must be Huda right?
Inaso kije ki samu uban ki kice mishi......”
Cikin katseshi Arshaad wanda shima ya k’araso inda take yanzun yace
“Huda lets go don’t mind him, he’s crazy!!
Muje kawai za mu yi magana a waje.”
Ya k’arashe maganar yana durk’usawa don k’ok’arin d’aukar wayarshi data jifar a k’asa.
Hudan ita kanta bata san tana da kishi irin haka ba, sai yau. Wato ba zai ma iya fuskantanta a gaban Jalilan ba?!
Gashi yadda duk ya rikice jikinshi yana d’an karkarwa yasa ta d’aura ayar tambaya akanshi…
Ita Arshaad zai yiwa haka? Why? Of all people kuma yayarta!!!
Bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba!.
Ai kuwa a rikice, Arshaad yace
“Oh nooo, Huda dan Allah kar muyi haka dake mana, na rantse miki da girman Allah ban san wacece waccar ba!
Ban tab’a ganinta ba a rayuwata, wallahi!
Muje waje we ‘ll talk outside.”
Yai maganan yana k’ok’arin kama hannunta..
Da sauri ta fisge cikin kuka tace
“Don’t touch me! Ai dole kace baka santa ba mana, Ya Jalilan ce baka sani ba?
Daman Mama tace min rannan kaje kana nemanta, kuma nima naji Umma ma rannan suna wani magana da Anty Zainab dana kasa fahimta a kanka kaida Ya Jalila.
And if baka santa ba mai take yi a nan ya akayi ta san gidanku da ni kaina ban saniba?
Ana tunanin tana gidan Anty d’inta a gida ashe tana wajen ka!
I trusted you,I tot.....”