← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 70

Sashe 51

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kukan jalilan ta hau yi mata bayani tiryan tiryan akan
yadda taji Gwaggo Asabe
suna maganar auren ita da wata mai aiki satin baya daya wuce
data tambayeta kuma ta gasgata mata hakan
sannan yanzu ma Arshaad d’in ya sake tabbatar mata.

Cikin b’acin rai Umman tace
“Kece ai Jalila
da shegen son abunki!
Nace miki ki kawo kud’i kin k’i ki bayar ya kikeso in yi?
Babanku ma yanzu haka baya nan ya gudu saboda ba zai iya rayuwa ba Maryam ba!
Ga Ja’afar ba lafiya!
Ga Junaidu ya b’ata!
Matsalalo gasu nan burjik sunyi mana yawa
ke kuma kin matse bakin aljihu ya kike so inyi???.

Ni kaina sai na mutu dan bak’in ciki in dai Huda ta auri Arshaad d’innan ba ke kad’ai ba!
Haba dan Allah mana sai kace
su kad’ai Allah yake so??
Baban ta mai kud’i sannan ta auri mai kud’i!
Inaa, ba zai yiu ba
gaskiya!”
Umman ta k’arashe maganar
cikin tsananin tashin hankali.

Cikin kuka Jalila tace
“Umma yanzu meye abun yi?
Dan Allah karta aure min shi
wallahi Umma ina son Ya Arshaad
sosai.”

Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace
“Ki bani kud’i!
Ki turo kud’i!
Ki zuba mini ido kawai,
shine abun yi.”

A hankali Jalila ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Tam shikenan,
Ta accnt d’inki ko?”.
“Eh”
Kawai Umman tace
saboda tsantsar tashin hankalin da take ciki
ba zai iya barinta tayi magana sosai ba.

“Tam” kawai Jalila tace
ta kashe wayar
daganan ta tura mata ragowar kud’in accnt d’inta
da ta ishi Auwal, ya tura mata da kyar..............

Bayan Arshaad ya tafi sun d’an tab’a hira tukunna Gwaggwo Asaben tace “itama bara taje ta bawa Mommy maganin nata ta sha ta shaafa dan yanzu ita take yi da kanta”
Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace
“Ka zo muje kaga jikin nata mana”.

Ahankali ya girgiza kai kafin yace “Gwaggo na san da sauk’i tunda gamu waje d’aya amman lafiya,
kuma kin ce tayi garau yanzu
to ai
Alhamdulillah!
Inaga ba sai na je ba, kar
muje a samu matsala.”

Shiruuu, Gwaggo tayi..
Ita har ga Allah so take Aslam d’in yaje ya ga Mommy watak’il In ya ga ta warke shima ya samu ya rage damuwar da ta hau kanshi.

Amman tunda taga baya so bara kawai ta kyaleshi.

Ganin dayayi kamar bata ji dad’in musun da yayi mata bane yasashi mik’ewa kafin yace
“muje to”

Murmushi ta saki tace
“Yauwa d’an albarka, muje.”

Itace a gaba shi a baya
Haka suka nufi saman ba don ranshi yana soba gashi k’irjinsa In banda dukan uku uku ba abunda yake yi.
Wutar parlourn a kashe suka tadda, suna k’ok’arin kunna flash d’in wayoyin su haske ya gauraye ko Ina!
Bata lura da shi ba tace
“Yanzun fa nake shirin kiranki na jiki yau duk shiru!
Sai kuma nace bara in yi wanka kafin ki zo, kin ga
banma ida shiga d’akin ba naji motsinki.”
Tana maganar tana tahowa garesu.

Aslam mutuwar tsaye yayi!
Dukda a cikin zuciyarsa hamdala yake yi na ganinta a hakan, amma kuma bayaso suyi ido biyu dan bai san ya zata kaya ba!
Hakan ne yasa shi fara ja da baya dan barin wajen
Ita kuma kamar ance ta d’ago karaf! Suka yi ido biyu da ita......

Ta k’uraa mishi idanu ko kiftawa bata yi
tana kallonshi kamar da mamaki akan fuskarta…

Lura da hakan da Gwaggo Asabe tayi ne wadda itama ba k’aramin firgice ta shiga ba ya sanya ta daure taje ta fara jan hannunta tana
“Muje ga tofin naki kisha In kin fito wankan sai ki shafa ko?”

A hankali suka ji Mommy tace
“Aslam!”
Aslam wanda already ya juya da niyyar tafiya har ya d’aga k’afar shi jin ta kira sunanshi ya sanyashi dakatawa ba tare da ya sauk’e k’afar shi ko ya juyo ba!
Sai da ta sake cewa
“Aslam”
Tukunna ya ajjiye k’afar ya juyo yana kallonta da idanuwanshi da suka rine lokaci guda!.

Dafe kanta tayi da k’arfi, ta runtse idanuwanta kamar mai son tuno wani abun…

Ganin haka yasa Gwaggo Asabe ta sake kamo ta kafin ta ce mata
“Muje ki huta dan Allah”
Sannnan ta baya ta yiwa Aslam d’in alamar ya tafi da hannunta.

A hankali Mommy ta bud’e idanunta tana sake kallonshi
kafin tace
“Asabe me ya faru da ni?
Kin ce nayi rashin lafiya
meye ne ya sameni?
Na shekara nawa?.
Kinga fa Aslam
kina ganin abunda nake gani kuwa?
Shekara ta nawa a kwance?
Dan Allah kimi.....”
Gigitacciyar rungumar da Aslam wanda ba suba tahowarshiba
yayi mata ne ya sanya ta kasa k’arasawa…
Tana shirin yin magana taji Gwaggwo Asabe ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi cikin kukan banda kalmar
“Alhamdulillah!”
Ba abunda take ta nanatawa.

Da kyar Mommy ta iya b’amb’aro Aslam daga jikinta,
a hankali da hawaye sharkaf akan fuskarta ta shafa fuskarshi wadda ta koma jajir kafin tace
“Loosing memory nayi ko?”
Ta fad’i hakan
tana mai fashewa da kuka.

Rasa wanda zai rarrashi wani akayi tsakanin ita da Gwaggo Asabe..
Aslam kam banda ajiyar zuciya ba abunda yake sauk’ewa!
Shi kanshi yau
so yake hawaye ya zubo ta idanunsa amman abun ya gagara!
A hankali ya cika mata hannunta dake cikin nashi
ya dan jaa da baya kafin ya seseta gabas ya durk’usa yayi sujjada!
Da sauri itama Gwaggwo Asabe tayi sujjjadar, ita kam
Mommy tsayawa tayi tana kallonsu tana hawaye da mamakin abunda ya sameta haka…
….Wani abun mamakin still shine yanda ta kasa tambayar inda Aslam d’in yake har sai da ya baiyyana a gabanta!
Wanne irin loosin memory tayi haka ita kam? Aslam wanda ta san shekarunshi basu wuce 12 ba shine yanzu haka wanda ta tabbatar yafi 30!
Daman tun kwanaki 7 da suka wuce tayi noticing yanda Gwaggo Asabe tayi aging da kuma ita ma kanta!
Mai ya faru?
Wanne irin ciwo tayi haka?
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Allahumma ajirni fi musibati…
Take ta maimaitawa
cike da rud’ani da alajabi
gaba d’aya kwanyarta ta cunkushe............

A hankali Aslam ya mik’e ya kama hannunta suka shiga d’akinta ya zaunar da ita kafin yace
“Ina yake miki ciwo, yanzun?”
Murmushi tayi ta shafa fuskarshi a hankali tace
“Ba ko ina”
Sai kuma ta sake fashewa da kuka.
Hugging d’inta kawai yayi yana tapping bayanta.
A hankali ya d’auko wayarshi, ya hau kiran Dad video call, bai damu da time ba.

D’auka Dad yayi suka gaisa yana tambayarshi “ya shirye shirye na bikin su Arshaad?”
A hankali Aslam
yace “Alhamdulillah”
Sai kuma ya gyara zamanshi ya matsa kusa da Mommy ya kamo hannunta cikin nashi
ya d’an kalleta yayi murmushi yana ganin yanda ta k’urawa Dad d’in ido, kafin ya juyo ya kalli Dad shima yace
“Alhamdulillah Dad..”
Bai ida rufe bakinshi ba, yaji Dad d’in ya saka kuka, cikin kukan shima yace
“Alhamdulillah!
Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!!”
Sannan yace “Aslam ganinan zuwa yanzun nan, in shaa Allah”
Da sauri Aslam d’in yace
“No dad, kabari sai gobe yanzu dar....”
Kit! Dad ya kashe wayar ba tare da ta tsaya jin maganar Aslam d’in ba.

Anan aslam ya zauna, ya rik’e mata hannu gam kamar ance za a kwace mishi ita!
Sai kallonta yake yana murmushi yana sauk’e ajiyar zuciya in yaji hakan bai mishi ba yasa hannu yai hugging d’inta.

Ita ma Gwaggo Asabe a daren ta kira Yaranta duk biyun ta fad’a musu halinda ake ciki,
murna a wajensu ba a magana, suka ce “in shaa Allah, za su tambaya.
Za su taho suma in shaa Allah.”

A haka Mommy ta sha addu’o’i ta shafa da hannu d’aya dan Aslam yak’i cikata, Gwaggo Asabe tana musu dariya tana kuka at the same time.

Ko cikakkiyar awa biyu Dad bai yi ba, sukaji tsayawar mota.

Aslam ne yace “Oh Dad, dana sani da ban fad’a mishi ba.
Waye ma ya d’auko shi a airport d’in sai Allah
tunda gashi bai kira ni ba.”

Murmushi Gwaggo w tayi kafin tace “ai ko kaine a matsayin shi na tabbatar sai ka zo”
Murmushi shima yayi kafin yace “Kuma fa hakane”

Cikin minti goma ya iso cikin d’akin!
Yadda ya gansu a zaune ne yasa hawayen da yake ta koma run yaga ya danne
suka samu nasarar zubowa.
A hankali ya k’araso ya had’asu waje guda ya rungume ..
Shi kuka Mommy da kanta ya d’aure da komai kuka Gwaggo Asabe ma kuka
Da kyar Aslam wanda duk ya fi su son yin kukan ma
ya samu ya lallashesu,
daga nan aka hau murna
k’arshe dai ba wanda ya runtsa a cikinsu har asuba.

Kafin gari ya gama wayewa kuwa, labari yaje kunnuwan kowa a estate d’in, har su Abba.

Daga masallaci Arshaad ya biyo Aslam suka zo tare dan ya ganewa idanuwanshi, ai kuwa shima har da kukan shi na tsananinfarin ciki.

Haka shima Auwal yazo da daddare tare da Daddy da Abba duk a b’oye kar e ya gansu.
Sun ji dad’in ganinta kuwa, sukayi barka suka tafi .

Mommy kuwa tunda aka bata labari sannan taga su Arshaad da Aaima yadda
suka girma da shi kanshi Aslam d’in, ta shiga alhinin
‘shikenan tayi missing teen age d’insu, da yanda suka taso kenan har abada?’
Gaba d’aya tausayin kanta da Aslam d’in sai ya lullub’eta..
Da kyar ta iya cin abinci, in banda kuka ba abunda take yi,
tun ba ma da Dad ya gaya mata irin abubuwan data dinga yiwa Aslam d’inba, da irin rayuwar da yayi, gaba daya sai ta sake birkice musu, tana kuka tana cewa Aslam do yayi hak’uri ya yafe mata.
K’arshe dai barin gidan ma yayi dan ba zai iya tsayawa tana kuka haka tana neman gafarar sa ba bayan ya san ba laifinta bane ba.

Dad kanshi kasa zama yayi sai gidan su Abba yaje, ya d’an zauna yana dana sanin fad’a mata d’in da yayi.
Chapter 51 · 0% Book details