← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 70

Sashe 57

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K’amewa Sakina tayi ta kasa cire wayar daga kunnenta!
Sai da Hudan ta tab’ota tace
“Ya ake ciki Sakina?”
Tukunna tayi firgigit ta dawo daga tunanin tashin hankalin data fad’a na y’an sakanni....
….Dama da ita bata tab’a fadawa kowa ba ne amma
haka kurum idan ta tuna Mammy bata san dalili ba sai taji gabanta yana ta fad’uwa!
Dan bata san ya tsakaninta da Huda zai kasanceba. Kuma ta lura kamar Arshaad d’in yana ta saurin ayi ayi ai auren su samu su bar k’asar! Tabbas sai yanzu ta fahimci dalilinshi..
To amma mai yasa Ya Arshaad zai so ya had’a ta da surukar da ba zata amsheta ba?
Duk kuwa da tsananin k’aunar da suke yiwa juna ai da sun hak’ura!……
“Sakina, akwai matsala ne?”
Muryar Hudan cikin rauni, ta katse mata tunaninta….

Juyawa tayi suka had’a ido!
A take wani tsananin tausayinta ya rufeta
dan bata jin a cikin shekaru ukun nan akwai lokacin da take hango tsantsar k’aunar Arshaad a idanun Hudan kamar wannan lokacin.
Da kyar ta iya ce mata
“Aaiman bata gida,
bara in kira Auwal kawai.”
Ta fad’i haka tana me mik’ewa ta fice daga d’akin gaba d’aya.
Hudan kwata kwata bata gamsu da maganar tata ba
dan haka ta mik’e ta bi bayanta.

Suka bar Khadija wadda itama bata wani yarda da maganar Sakinar ba dan ta lura da yanayin da ta shiga tun fara wayarta da wadda suka kira da ‘Aaima’.

Tana fita ta samu damar zubar da kwallar da take ta k’ok’arin rik’ewa!
Yanzu Ina mafita?
Meye abunyi ?
Sune tambayoyin da suka toshe mata kwanya sannan ta kasa samun mai bata amsar su.
Daman y’an layi har sun fara k’ananan maganganu
suna cewa
....Allah dai yasa tarihi kar ya maimaita kanshi
Ita maryam bata daddara da family d’in Abba da abunda shi kanshi Abban yayi mata ba
shine zata aurawa Huda nephew d’inshi
dan kawai taga yana da masifar kud’i!
Ga dai Ummu ita da ta auri saffa saffa hankalinta a kwance rayuwarta gwanin ban shaawa
amman ita har yau bata samu kwanciyar hankali ba
a ta dalilin So da Buri! Ta mannewa mutumin da yafi k’arfin ta nesa ba kusa ba....

Jin k’arar bud’e k’ofar d’akin nasu ne ya sanya Sakina goge hawayenta da sauri, sannan
ta lalubo number Auwal
ba dan ranta yana so ba ta fara kiranshi….

Bacci bai dad’e da d’aukarsa ba dan bai dad’e da kwanciya
ba amman yana fara baccin ya hau mafarkinta.............

Yana cikin mafarkin nata
k’arar wayarshi ta katse mishi mafarkin….

Kamar ba zai juya ba bayan ya farkan sai kuma yayi tunanin ko Granpa ne dan haka yayi tsaki ya lalubo wayar akan bedside ya amsa ya kara a kunnnen shi ba tare daya duba mai kiran nasa ba.

Jin shiru yasa tace
“Ya Auwal”
A hankali.
Bude idanuwansa yayi da kyau kafin ya zaro wayar daga kunnenshi ya kalla sosai ya tabbatar itan ce tukunna
ya mayar da wayar kan kunnensa ya mik’e zaune
yana adduar ‘Allah yasa lafiya’
dan ya san ba k’aramin abu bane zai sanya Sakina ta kirashi kuma cikin daren nan ba.

Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“How far”
Dan lokaci d’aya ranshi ya b’aci bayan ya tuno ta Ita da Ashraff d’azu.

Ba tare da b’ata lokaciba tace mishi
“Ya Arshaad ne suke tunanin bashi da lafiya dan yanzu ma kamar suma yayi suna cikin waya da Hudan.”
Ta san maybe Hudan ce ta fito d’azun kuma maybe tana tsaye a bayantata dan haka sai ta tak’aita maganar tata
sannan tace
“Dan Allah yaje ya dubo shi”

“Okay”
Kawai yace
daga nan ya kashe wayar ya mik’e ya fad’a toilet yad’an d’auraye fuskarshi ya chanja zuwa jallabiya tukunna ya fita..........

Sai da ya daddannawa gate man d’in zagi, tukunna ya barshi ya fita
A cewar shi (gateman d’in) Daddy ya hana a na barinshi yana fita cikin dare.

Sai mita yake yi shi kad’ai a mota haka ya isa gate na estate d’in MT
..a ranshi yana aiyyanawa
‘Da mutane sun san halin da yake ciki to da ko kallonshi ba zasu dinga yi ba!
Komai b’ata mishi rai yake yi
tun d’azu...’
Allah ya so shi bai samu matsala da mai gadin main estate d’in ba, sai dai ya rok’esa akan ‘ya bi a hankali kar ya bari Granpa ya ganshi dan zai iya cewa a bakin aikin shi’

Jinjina kai kawai yayi ya wuce ciki.
Ya dad’e yana knocking jin shiru yasa ya yanke shawarar kiran Aaima yace mata
‘ta kira layin wata a cikin masu aikin gidan tazo ta bud’e mishi k’ofa.......’

Tunda Sakina ta kira ta bacci ya k’aura daga idanunta,
tana cikin chatting kiranshi ya shigo wayar tata.
Ta dad’e tana kallon number, kasancewar ta dad’e da goge numbershi amman ta na nan a kwakwalwarta
bata gogu ba!
A take jikinta ya mutu..
Sai da wayar ta kusan tsinkewa tukun ta samu damar amsawa, cikin sanyin jiki ta kara a kunnenta tace
“Hello”
Ba tare da ya amsa ba
yace
“Aaima Arshaad is sick, na zo duba halin da yake ciki kuma k’ofan ank’i bud’ewa..
Can you do me a favor ki kira wani wanda kika sani a cikin gidan yazo ya bud’e min?
It’s an emergency”

Tunda ya fara magana ta lumshe idonta har ya kai aya
a hankali tace “to”
kawai, ta tsinke kiran.

Kamar 5 minutes yaji ana k’ok’arin bud’e k’ofar, ana bud’ewa ya kutsa kai ciki ba tare da ya kalli
bayan k’ofar ba inda take,
yayi hanyar side d’in Arshaad direct kawai.

“Ina wuni”
Yaji muryar ta.

D’an juyowa yayi ya kalleta
a ranshi yace
“Ashe ta dawo.”
Ba yabo ba fallasa yace
“Lafiya”
Kawai ya juya ya nufi hanyar part d’in Arshaad.

“Ya k’ara haske, sai dai yad’an rame kad’an!
Ya k’ara kyau.”
Ta fad’a a k’asan ranta!
Bata san dalili ba amman taji zafin yanda yayi mata,
taso ta koma sama kawai abunta amman sai ta tsinci kanta da kwad’ayin bin bayanshi, dan haka ta rufe k’ofar ta nufi side d’in Arshaad.

Direct main bedroom d’in dake side d’in Auwal ya nufa.
Yana shiga ya ganshi yashe a k’asa da jikakkun kaya.
Da sauri ya k’arasa wajen ya durk’usa ya hau jijjigashi yana kiran sunanshi….

Dai dai nan Aaima ta shigo,
duk da fushin da take yi dashi hakan bai hanata fashewa da kuka ba da ganin halin da yayan nata ke ciki.
Da sauri Auwal ya juya gareta yace
“Yi maza Aaima d’ebo ruwa a toilet yi sauri plss..”
Ya fad’a cikin gigita da kid’ima.

Da gudu ta nufi toilet d’in ta d’ebo ruwan ta fito ta na zuwa Auwal ya amsa ya hau yayyafa mishi….

Sai da suka fidda ran ma zai farfad’o tukunna yayi wata wawiyar ajiyar zuciya wadda ta taho mishi tare da tari!
Auwal ne ya d’an d’ago shi kad’an yahau bubbuga mishi baya yana jera mishi sannu.
Da kyar ya samu tarin ya tsaya
ya shiga jejjera ajiyar zuciya....

Sai da Auwal ya kamashi ya kaishi kan gadonshi, tukun ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran family doctor d’insu….
Kamar Arshaad d’in ya san me yake shirin yi, yace nasa
“Kar ka kira kowa Auwal,
i’m fine.
Please.”
Kallonshi Auwal d’in yayi kafin shima yace
“Dan Allah kar ka gwada yin wannan taurin kan!
Ka bari a kirashi ya duba ka kawai.”
Cikin d’an fushi Arshaad yace
“Auwal zamewa nayi na fad’i na buga kaina!
Yanzu kuma na farfad’o…
Ka gaya min in akwai abinda Doc zai yimin idan ya zo d’in
bayan wanda kukai min.”

D’an k’uraa mishi ido Auwal d’in yayi kawai ya tsaya yana kallonshi.

A hankali Arshaad d’in ya koma ya jinjina a jikin gadon
sannan yace
“sorry”

Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e
kafin yace
“Are you sure that’s all?”

Jinjina kai kawai Arshaad d’in yayi.

Auwal bai wani gamsu da maganan shi ba
but yaga kamar he wants to be alone shiyasa yace
“Shikenan,
Allah ya kare gaba, ka kira su Hudan hankalinsu ya tashi sosai.
And dan Allah ka sauya kayan jikin nan naka, sai da safe.”

“Ok”
shine abunda Arshaad yace sannan ya k’ara da cewa
“Thanks a lot”

Murmushi yayi kawai yace mishi
“Good night”
Daganan ya nufi hanyar fita.

Kallonshi (Arshaad) itama Aaima tayi tace
“Ka kira wayana if you need anything”

Jinjina mata kai kawai yayi sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa dan chanja kayan jikinshi.

Ganin haka yasa Aaiman yi mishi sai da safe itama ta juya tabi bayan Auwal wanda
har ya kusan ficewa…
Sai da ya kusan isa k’ofar fita ta main parlour tukun ta samu ta cin mishi ta wuce ta isa bakin k’ofar ta sa hannu ta bud’e.
Ba tare da ya kalletaba dan shi har ga Allah ta fara k’ular dashi
Ya sa kai zai fice.

Daurewa tayi tace
“Mun gode sai da safe”

“Allah ya kaimu” yace
daga nan ya fice.

Ta jima a parlourn bayan ya fita..
Daga k’arshe ta nufi side d’in Arshaad har bedroom ta lek’a ganin yayi bacci yasa ta fito ta nufi sama ta koma d’aki.
Da kyar ta samu bacci ya d’auketa.

Shi kuwa Arshaad yanda yaga rana haka ya ga dare!
Yana jinta lokacin da ta shigo,
baya san ganin kowa shiyasa yayi baccin k’arya, ko
Hudan text kawai ya iya tura mata cewar ‘he’s okay’.

Kafin safiya ya gama deciding yanda zai yi da abunda zai cewa Mammy amman still yana d’an d’arr! Ga fargaba
ga tunani barkatai
shiyasa zazzab’i yace salama alaikom...........

Zazzab’in da ya rufar masa ne yaasa da kyar ya iya mik’ewa yayi sallah a daddafe!
Kafin 7 kuwa zazzab’in yayi masa rufdugu….

Ganin yana shirin mutuwa ya sanya shi kiran family Doctor d’in da baya so, dole! Ya kira fad’amshi yana zazzab’i mai k’arfi.

Ba a rufe 30 minutes ba Doctor d’in ya iso..

Allurai yayi mishi bayan ya duddubashi dan ya san Arshaad ya tsani magani,
daga nan ya jona mishi drip yayi mishi sallama…
Chapter 57 · 0% Book details