← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 70

Sashe 28

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali yace “Hudan nima mahaifinkine kamar Maman ki, na san ba lalle ki fahimci komai ba, amman inaso ki san cewa ‘ban tab’a k’in ki ba’ Yadda Mahaifiyarki take sonki nima haka nake sonki, kina gani a gabanki na hukunta waenda sukayi nasarar raba ni dake!.
Ba zan tab’a yarda in barki ki koma gidan da kika taso ba, dan duk halin da kike ciki a gidan na sani.
Idan kin yarda kullum idan kina so to za kije ki dinga duba Mamaki, amman Hudan ba zan sake bari kiyi nesa dani ba..
I want to take care of you
Make it up to you
Make you forget all the sufferings that you go through.
Amman
hakan ba zai tab’a faruwa ba, sai da had’in kanki! Ba zan
b’oye miki ba har ga Allah banji dad’in yanda kike yi mini ba kwata kwata Huda, it’s like kamar ma bakya farin ciki da ganina, komai ke kawai Mamanki!
Ko maganan 10 minutes ban tab’a yi da ke ba!
Yanzu ma kalli yadda kike yi
min kukan in maidake wajen ta kamar irin na satoki d’innan?”
Ya k’arashe maganar a hankali.

Gaba d’aya Hudan sai taji jikinta yayi sanyi,
tabbas bata kyauta ba! Ya kamata ta nuna mishi shima Mahaifinta ne tunda gashi ata dalilinta har gidansu ya bari da shi da d’an uwansa don kawai ya zauna a tare da ita….
Tunaninta ne ya katse jin yana cewa
“I’m sorry Hudan dan unless you promise me ba zan tab’a barinki ki je ki ganta ba.”

Shiruu, d’akin ya d’auka kafin yaji tace
“Tam”.

Kallonta yake yi, kamar zai ce mata wani abun kuma kawai sai ya juya ya fita.

Kamar yadda ya fad’a haka aka kawo mata kayan da ya ambata..
Ita dai Hudan mamaki ta shiga yi dan bata ga kuma abun k’ari ba anan, komai akwai hatta inner wears sai dai kawai kamar ba za suyi mata ba, dan haka ta d’au tab d’in ta hau shopping…
Sai da ta hau d’in kuwa tukunna tayita gannin abubuwa dan haka ta zazzab’a, bayan ta gama ta rufe ta ajjiye.

Tana idar da sallar Magrib ta sauk’a k’asan kamar yadda Abban yace mata.

Bata samu kowa ba, amman dai ga uban abinci nan shak’e a kan dining d’in
wajen kala nawa..
Ga kuma wata maid cikin uniform sai kai komo take yi tsakanin kitchen da dining d’in tana jera su plates.
Bata yi minti uku a zaune ba, suka shigo daga masallaci…
Su Sudais ne suka fara shigowa, Sudais yana ta tsallen tsallenshi, Shuraim kuwa ya mazee, kallonsu take tana mamakin kamanninsu dan ita kam miskilancin Shuraim ne kawai yake sawa take iya gane su..
Tana murmushi tanata kallonsu tana jin tsananin k’aunarsu a ranta
su Abba ma suka shigo dukkansu, har a Auwal wanda Daddy ya matsawa akan dole sai yazo sun gaisa da cousin d’inshi! Sai kumbure kumbure yake yi, ba wanda yabi ta kanshi haka nan suka shigo abunsu ana d’an tab’a hira kowa yana fara’a banda shi.

Suna shigowa da Daddy suka fara had’a ido dan haka ya yafitota da hannu.

A hankali cikin nutsuwarta ta nufi dogon dining d’in mai kujeru kusan ashirin
inda taga sun nufa
kamar an tsamota a ruwa a haka ta k’arasa wajen,
Abba ne da kansa ya jaa mata kujera ta zauna, ita har kunya take ji yadda ake wani lallab’a ta ana janta a jiki musamman ma Abba yadda yi mata kamar ya goya ta yayita zagaye garin da ita.

Cikin ladabi ta shiga gaidasu suka amsa, su Aslam kuma tayi musu jimla tace “ina wuninku”
Aslam ne kawai ya amsa mata,
a hankali ta d’ago ta kalle setin da Arshaad yake taga ya wani had’e rai ya d’auke kai ko inda take bashi da niyyar kalla ma!
Nan kuwa ta k’ule, tana mamakin shi, a ranta tace “tabarmar kunya yake son nad’ewa da bori!”

A take ta d’auke kanta itama bata sake kallonshi ba, tana jin haushi da wani tuk’uk’in kishin dake sake taso mata.

Tana cikin wannan tunanin taji Daddy yace,
“Sorry dota mun barki ke kad’ai ko?
Za kini shiru kam, gashi Aaima na school, ya kamata a nema miki Abokiyar hira gaskiya!in ba haka ba bazaki ji dad’in zaman ba kwata kwata
tunda su Sudais suma islamiyyarsu da boko a had’ene sai pass 5 suke dawowa.”

Da sauri cikin tarar numfashinsa Auwal yace
“ai daman da ace Ummi tana nan ba a kaita cell ba to da zata ji dad’in zama sosai, gashi Gwoggwo Asaben ma da naga kamar sun d’an saba itama ta saka an baro inda take!
Dole ta sha zaman shiru kuwa ai!.”

Dakatawa Abba yayi da zuba mata abincin da yake yi ya rik’e serving spoon d’in kawai still yana kallon plate d’in!
Yana mamakin Auwal!!
Wato rashin kunyar tashi yau ta hauro kanshi kenan, a gabanshi haka yake zuba mishi magana…..
Yana shirin yin magana yaga Daddy ya taso ya nufi Auwal d’in a zuciye, da sauri Abba ya mik’e ya rik’e shi haka ma Aslam ya mik’e yana cewa
“Daddy dan Allah kayi hak’uri ka kyaleshi.”
Arshaad kuwa ko motsi bai yi ba dan shi kam tasa kad’ai
ma ta isheshi, ba k’aramin k’ok’ari yake ba wajen share Hudan da yake yi, gashi tunda ya zauna yake d’an satar kallonta amman yaga kamar ma ko inda yake bata son kalla!.

Cikin fushi Daddy yace
“Dan uban ka iskanci naka yau a kanmu zai k’are?
Auwal wallahi zan yi mugun sab’a maka fa!!”

Cikin katseshi Abba yace “ya isa haka Daddy ka kyaleshi kawai! Dan Allah”

Cikin rashin jin dad’i Aslam ya cewa Auwal d’in “you can leave, tunda ka ganta gashi har kun gaisa ma.”

A fusace Auwal ya kalleshi, yana shirin yin magana Daddy ya daka mishi tsawa yace
“Get out akace!! Stupid boy kawai!!!”

Fuu!! haka ya tashi ya fita kamar zai tashi sama.

Daddy da kyar ya koma wajen zaman shi ya zauna gaba d’aya guiwanshi a sace! Ya so ace a kusa da Auwal ya zauna yau da sai ya sauya mishi kamanni ya nuna mishi still da ragowar k’arfinsa shima har yanzun, dan yaga alamun Auwal d’in ya kawo k’arfin da yawa shiyasanya yakejin kanshi a sama kamar yafi kowa!.

To dai dinner d’in haka ta wakana babu dad’i,,kowa da abunda yake damun ranshi.

Sai wajen 9 Aslam da Arshaad suka yi musu sallama suka tafi, bayan an yanke yin wata sauk’ar gobe amman sai dare za a kammala,
kowa zai yi izu biyu bayan sallar farilla sai su tafi da ruwan addu’ar a shafa mata .

Suna fita Abba ma yace mata “ta d’auko hijabinta ya kaita ta duba Mama”
Murna a wajen Hudan ba a magana dan da gudu ta haye benayen, bata yi minti uku a saman ba ta sauk’o sanye da hijab har k’asa wanda ta gani a cikin kayan da aka bata.

Ya lura da yadda jikinta har karkarwa yake yi, shiyasa bai b’ata mata lokaci ba yace “suje”.
Da sassarfa ta shige motar.
Shi dai Abba kallonta kawai yake yi, tabbas Hudan da shi take kama komai da komai amma idan tana wani abun sai ya dinga ganinta kamar Maryam!!!
Wani d’an murmushi ne ya sub’uce mishi, a hankali cikin sanyin jiki ya murza key ya tada motar ya nufi gate.

Masu gadin gidanjensu na chan estate su suka d’auko suka taho dasu..
Suna Isa gate d’ayan ya ajjiye rediyonshi a kan dogon bencin da suke zaune su wajen biyar harda driver da mai wankinsu da gyaran fulawar, yaje ya bud’e musu makeken gate d’in, suka fice.

Tunda suka fita Huda ta kasa sukuni, tsabar zumud’i, gani takeyi kamar Abba baya gudu, har d’an tasowa take yi ta d’an lek’a gaban titin ta gaban glass d’in motar..
Dariya ta bashi sosai dan haka yace “Gani kike kamar bana gudu ko?”
Ya fad’a yana dariya sannan ya k’arawa motar wuta…
Itama murmurshin tayi ta koma ta zauna da kyau a mazaunin ta.

Tafiyar minti ashirin ce ta kaisu AKTH emergency, dan ma sun d’an tarar da go slow a hanya.

Tana shirin fita taji yace
“You promised Hudan, right?”

A hankali ta d’aga mishi kai, sannan tace
“Na gode sosai Abba”
sannan ta fita.

Da kyar security suka barta ta shiga bayan tayi ta nacin ce mishi Mamanta ne a kwance, Allah ya taimaketa, wanda yake gadi ne a wajen ranar da suka kawota ita da Aslam, kuma d’azu tabbas yaga Maman nata an fito da ita tana d’an zagaye, shiyasa ma ya barta ta shiga, don ya tunata tun ranar da suka zo ita tana kuka shi kuma yanata mamakin had’uwar Yarinyar, hakanan yaketa ganin hoton fuskarta a zuciyarshi amman ya san ko hauka yake ba zai ma yi tunanin tunkarar ta ba.

Dube dube ta hau yi bayan ta shiga, da kyar da sid’in goshi ta hango su…
Mama da Ummu a kan gadon a zaune suna magana da alamun mai matuk’ar mahimmanci ce sai Sakina ita kuma a gefe kan kujerar mai jinya da waya a hannunta.

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
41

Basu ga tahowarta ba, kawai suka ga an afka kan Mama da gudu an rungumeta!
Kukan da ta fashe dashi ne yasa suka gane itance, da sauri Sakina ta d’ago ta, ai
kuwa tana ganinta tayi hugging d’inta tana dariya.

Ummu itama murna kamar tayi me, Mama kuwa ba a magana.

Ummu ce ta zare Hudan daga jikin Sakina sannan ta d’an muskuta ta ajjiyeta a tsakiyar su ita da Mama.
A hankali Mama tasa hannu ta shafa fuskarta tana hawaye, da sauri itama Hudan ta goge mata hawayen tace “ki bar kuka Mama, i missed you so much, kwana biyun nan ji nayi kamar shekara wallahi”
Ta fad’a tana sakin wani kukan, sannan ta kwanta jikin Mama.

Sakina ce ta d’aka mata duka a cinya kafin tace “dalla Malama d’agata, kin wani zo sai kuka kike yiwa mutane salon ki karya mana zuciya muma mu biye ki! To Mama dai ance a daina sakata a damuwa dan haka sai kiyi k’ok’arin tashi ki ware garau ki bar wannan tab’arar.”
Chapter 28 · 0% Book details