← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 70

Sashe 23

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shawara d’aya Granpa ya yanke shine na ‘kai Aslam boarding school’
don samun sauk’in kowa and ya kamata yaci gaba da karatu kuma ya maida hankali saboda an barshi a baya sosai…
A lokacin shekarunshi sun haura 14.

Da kyar Aslam d’in ya yarda, ya tafi bayan Granpa yayi mishi alkawarin ‘duk inda magani yake a duniyar nan in dai akwaishi to zai nemawa Mommy d’insa, ko nawa ne kud’in ba zai gaji da biya ba, koda kuwa zai k’arar da duk abunda ya tara ne!!!’.

Haka nan aka tarkata Aslam aka kaishi boarding cikin tsananin k’unci, yana kuka
muna kuka ba dan munso ba.

Wani abun takaicin ko hutu Aslam bai isa ya zo ba, sai dai In kana buk’atar ganinshi kai kaje ka ganshi a inda yake, k’iri k’iri zaman estate d’innan ya gagareshi…
Ganin abun na Aisha bana k’are bane yasa suka kira wani babban Likita daga k’asar waje har gida Nigeria ya dinga kula da ita, shi ne ya bada shawarar a kulle su ita da Aslam a d’aki d’aya su kad’ai, for 24 hours, to kuma abun bai yi dad’iba don shi yayi sanadiyyar da Aslam ya bar k’asar nan wanda sai yanzu ne Allah ya dawo mana da shi!

Da farko an tsara akan zai d’an dinga lek’owa Hutu sai yake sauk’a gidan Abba, yadda ba zasu had’u da ita ba, har zuwa lokacin da Allah zai kawo sauk’i
Amman abunda ya faru a wannan rana ya sanya Aslam yin yaji mai mugun tsayi ya tarkata komai nashi ya tafi
sai dai waya, shima wani lokacin sai yake gudun d’auka!.

Arshaad da su Abba suna yawan zuwa duboshi, Auwal ne ma yaje sau d’aya, amman Arshaad a shekara ma yakan je sau biyu shi da Abba..saboda shi Aslam
ko hutu idan anyi na makaranta baya iya dawowa sai dai yayi achan Oxford Uni inda yayi karatunshi.

Aslam a Oxford yayi karatu,
Arshaad kuma Dubai aka kaishi Auwal kuma Cairo.
Da yake Granpa ne duk ya kaisu..duk da halin da Aslam yake ciki sai da aka fara k’ananan maganganu, Adama da Ummi, wai ‘har yanzu Granpa bai daina nuna bambanci ba’
Sosai Granpa da maganar ta koma mishi yayi musu tataas!!!Kuma ya taso da maganar mallakawa Aslam MT gaba d’aya inyaso sai yaga me za suyi!.

Da kyar da sid’in goshi Gramma ta tausheshi, sannan ta lallabashi, sannan tai k’ok’arin fahimtar dashi abubuwan da hakan ka iya janyowa….
Awannan lokacin kuwa anci sa’a ya fahimceta sosai, don da kanshi kuma ya dawo yace ‘a tsakanin Auwal Arshaad da Aslam, duk wanda yaga he’s capable to shi zai mallakawa MT’.
Dad yayi mugun mugun yin farin ciki daga jin wannan decision na Granpa, bawai yana zargin wani ba, kawai dai yaji releaf, kuma shima baya son bambancin da Granpa d’in ya dad’e yana nunawa especially tsakanin Arshaad da Aslam, don duk abun nan da ake yi ko sau d’aya Arshaad bai tab’a nuna b’acin ranshi ba, dukda kuwa uba d’aya ne ya haifesu shi da Aslam d’in,
Idan akwai fitinanne tou Auwal ne!
Amman Arshaad shi ba ruwanshi yana da kauda kai
kunyarshi ce ma ta sanya Dad yake yiwa Mahaifiyarshi wani abun dan kar yaga ga kamar bai damu da ita sosai ba.
Kowa idan zaki tambaya a estate d’innan ya baki sheda akan Arshaad to zai ce miki ‘yanada hak’uri da kauda kai da kuma saurin yafiya’.

Aslam yana kammala degree na farko aka d’aura shi a matsayin MD na MT branch d’in dake achan k’asar da yake, wanda ada Abba ne a wajen.

Ayyuka Aslam yake yi bashi da lokacin kanshima,
kuma daman hakan yake so dan hakan ya tsarawa kanshi tun farkon komawarshi UK d’in,
yana k’ok’arin kullum yaga ya zama busy dan kar ma ya bawa kanshi daman yin tunani..
Aikin kuwa ya taimakeshi ta b’angarori da dama
dan
Yana da nashi campny d’in a chan, na sarrafa takalma wanda k’wazonshi guminshi da kuma taimakon Granpa wanda yake aika mishi kud’i kamar hauka suka taimaka
masa ya had’a ya bud’e
wanda yanzu naji suna cewa yanaso ya bud’e wani branch d’in anan ko kuma ya dawo nan ma, gaba d’aya. Kuma akwai wani daban da zasu bud’e na zanen gidaje shi da Abba!
Ga mt ga kuma karatu wanda a yanzu ya kammala PHD d’inshi…
A b’angaren nasarori Aslam ya samu kam ba a magana sai dai kuma shi duk basa gabanshi, inda za ace ya tatttara ya bada abashi lafiyan Mahaifiyarshi na tabbatar kafin k’iftawar ido zai iya sallama komai!
Ba shi kad’ai ba hatta mu duk tsawon wannan lokacin buri daya muke da shi shine ‘Aisha ta warke hankalin kowa ya kwanta’
Dan shi kanshi Aslam d’in abun a jiye mishi ne, saboda gaba d’aya rayuwarshi ya yita ne cikin fargaba, k’unci da damuwa. Yanzu haka ko Abokanai baya iya tarawa shi kad’ai d’insa yake komai
sai dai a d’an dinga zumunci sama sama, Abokin shi na k’ut da k’ut guda d’aya tak a duniya wato Arshaad, da Arshaad ne kawai za kiji suna waya suna d’an raha amma ko mu y’an gida wani lokacin idan ka kirashi sai yak’i d’auka.
Tsoronma shiga mutane yake yi balle yayi huld’a dasu..
Naji su Abba suna cewa
‘Kana ganinshi in dai ka fahimci yanayin shi tou tashi d’aya zaka fahimci he’s depressed! Kuma hakan ba a so a mutum especially mai k’arancin shekaru kamar nashi, zai hanashi yin farin ciki a rayuwa ne kwata kwata, har abada!.”

Ahankali tace
“To amman ya za ayi? Magani in dai sunanshi magani tou ba kalar wanda ba ayi ba amman har yanzu shiru............”
Ta k’arshe maganar tana share d’an hawayen daya biyo idanunta a karo na ba adadi.

Hudan, itama hawayenta ta goge, a ranta tace “Allah sarki bawan Allah, ashe shiyasa kullum yake cikin fushi, da har nake jin haushinshi..
In shaa Allah daga yau na daina jin haushinshi, Allah ya bawa Mahaifiyarta lafiya.”
Maganar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa
“Kema dan Allah idan kin yi sallah ki dinga sakamu a addua Allah ya kawo k’arshen wannan abu.”

A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“In shaa Allah”
Sai kuma ta gyara zamanta ta ci gaba “Amman Gwaggo a duk cikin bayaninki banji inda aka yi mata Sauk’ar Alqur’ani ba!”
Cikin katseta Gwaggo Asabe tace “anyi sauk’a Huda, Granpa da Dad da kansu suka je suka raba kud’i lokacin da suka dawo farko farko a islamiyoyi da tsangayar almajurai aka yi ta sauk’a!.”

Murmushi Hudan tayi sannan tace “Gwaggo Asabe, idan zan bada shawara a d’auka inaga daa mu da kanmu ya kamata muyi mata sauk’ar bayan an raba a islamiyoyin, kuma in na fahimceki kamar sau d’aya aka tab’a yin sauk’ar ko?”
Bata jira jin mai Gwaggo Asaben zata ce ba ta ci gaba
“Ni a lokutan baya, idan bamu da lafiya ko wani alamari mara dad’i ya afku
Tou bayan Mama ta bamu magani sai ta kammala mana sauk’a, ko lokacin da nake k’arama akwai Yayanmu da yake shaye shaye sai da Mama tayi mishi sauk’ar AlQur’ani sau bakwai!!
Ta fara tayi sau hud’u ya warke ya daina amman dake tayi niyyar bakwai d’in zata yi sai da ta k’arasa.
Da kuma muka yi wayo haka zata rarraba mana muna tayata da ni dasu Ya Jalila koda izu d’ai d’ai ne mu kan taimaka.
Ko yanzu haka In wani abun ya faru rabawa muke yi ni da ita da Sakina wani lokacin da Sumayya, bama wata d’aya muke k’arasawa, in kuma mun kwallafa to a sati muke idawa.
Balle nan gidan munada d’an yawa..
Yanzu for example ace mutum shidda kowa ya d’auki izu goma, duk bayan sallar Farilla kayi izu d’aya a kwana biyu fa za mu dinga kammalawa, In kuma izu biyu za ana yi a cikin kwana 1 mun kammala, inda hali kowa in ya kammala sai yayi mata addua dafatan waraka bayan an tofa aruwa a bata tana sha,
Daganan ayita yi, kuma akai akai.
In Allah ya yarda sai kiga an dace.
Dan dai gaskiya kamar yadda kika fad’a abun sam kamar bana asibiti bane ba!
Koda ace ma na asibitin ne Sauk’ar Alqur’ani fa shine k’arshen waraka
Especially idan mune muka yi da kanmu, saboda waennan na islamiyya ba mu da tabbas, yanzu duniya ta chanja ba lalle In sun karb’i kud’in suna sakawa anayi ba…..”
Maganarta ce ta katse jin mutum a tsaye a bayanta ya dafa kanta, tana juyowa sukai ido hud’u da Dad
da Abba a bayanshi suna murmushi, waenda shigowarsu kenan suna d’an tatauna wata magani suka ji bayanin Hudan.

Dad ne yace “y’ar albarka, naji dad’in wannan shawarar taki sosai.
Kuma daga yanzu in shaa Allah zata fara aiki.
Kafin masu kwashe kaya su gama na san mun kammala in shaa Allah, na yau.”
Yana gama fad’in haka ya d’au waya ya kira Arshaad da Aslam yace “su sameshi.”

Sai da ya gama wayar, Hudan ta d’an zame daga kan kujera inda take ta shiga gaida Abba. Shima Dad d’in ta sake gaidashi.
Cikin kulawa suka amsa mata sannan suka cigaba ta tattaunawarsu da alamun magana mai muhummanci suke yi.

Hudan sai d’ar d’ar takeyi a tunaninta kar Abba yai mata fad’an abunda tayi mishi jiya, shima ya lura da yanayin ta shiyasama ya fasa zuwa inda take, amman da yayi niyyar jin yadda ta kwana da kuma jin ko akwai abunda takeso dan harga Allah shikam yana so ya zama tare da y’arsa ya jaa ta a jiki ko sa samu su saba da juna sosai.
Chapter 23 · 0% Book details