← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 70

Sashe 6

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da komai ya lafa sannan Gwaggo Asabe suka fito ita da Hudan daga d’akin….

Ita dai Huda gaba d’aya kanta ya kulle, hakan yasa ta kasa hak’uri ta hau tambayar Gwaggo “meke faruwa? Mai ya sameta take haka? Tun yaushe? An yi mata sauka?”

Dan ita Huda har ga Allah kawai ta fi jirkita akan lamarin na iska ne, tunda gashi dai ita da kanta ta tambayeshi but yana shigowa gaba d’aya ta firgice! Tayaya uwa zata dinga gudun d’anta haka?? Don ko ba a gaya mata ba ta gane itace Mahaifiyar Aslam ko dan yanayin kamar da suke yi da juna! But why him? Him alone?”

Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan tace “bani minti talatin, inje inyi wanka, Ina dawowa za kiji komai in shaa Allah.”

Kamar yadda Gwaggo Asabe tace
Sai da tayi wanka ta dawo ta zauna sannan ta fara bata labari…………
Asalin sunan Mommy, Aisha ana kiranta da Humaira, k’anwarta d’ayar duniya Khadijah wadda ake kira da Asabe.
Aisha da Asabe sun taso cikin yanayin k’unci na rayuwa ata dalilin babu..
Yahaya ya had’u da Aisha ne lokacin da ya kai ziyara Taraba, jalingo a wani d’an k’aramin k’auye.
Ata dalilin, masallaci da makarantun addinin daya d’auki nauyin ginawa.
A rafii yana zagaye ita kuma taje d’ebo ruwa suka had’u.
Tunda ya kyalla ido ya ganta ya rikice, a lokacin Mahaifiyarsu ta rasu Mahaifinta kawai ya rage musu.
Tun Aisha tana kauce mishi har itama ta fara kulashi sama sama.
Tashi d’aya ba kwana kwana ya nuna mata yana k’aunarta kuma yana son aurenta,
Bata bashi amsa ba tace “yaje ya samu Mahaifinta”.
Yahaya bai yi wani jinkiriba
yaje ya samu Mahaifinta da maganar
sannan yayi mishi alk’awarin ‘bayan auren zai barta tayi karatu har sai tace bataso’,
dan ya lura burin Mahaifin nasu kenan.

D’an guntun bincike akayi akan Yahaya, a lokacin, daga nan Mahaifinta ya bashi aurenta yace masa “duk lokacin daya shirya yazo da iyayenshi a d’aura”
To fa!! anan ake yinta, dan k’iri k’iri Granpa ya nuna k’iyayyar shi muraran akan Aisha da inda ta fito, acewarshi “sam ba a jin auren d’ansa bace ita d’in!!!”.
Buwayar Ubangiji, rabon Aslam, da soyayyar Granpa a matarshi ne
suka tabbatar da auren Yahaya da Aisha wanda aka d’aura a k’auyen Jalingo ba tare da halartar Granpa ba.
Tabbas anyi rigima ba k’arama ba, kafin, da kuma bayan auren!.
Zan iya cewa ban taba ganin macen da ta sha wahala a hannun suruki kamar Aisha ba!
Sauk’in ta d’aya Gramma tana mugun sonta ba kad’an ba, dan tun lokacin da Yahaya yaje mata da labarin Aisha farat d’aya taji Yarinyar ta kwanta mata, ita ta dinga lallab’a Granpa har aka yi auren.

To bayan auren ma haka tayi ta fama, in tak’aice miki labari
hankalin Granpa bai kwanta da Aisha ba har sai da ya aurawa Yahaya ajin nashi da yake ik’irari! Wanda ranar d’aurin auren ana d’aurawa Yahaya yana hawaye kamar k’aramin Yaro, dan zan iya cewa ban tab’a ganin Mijin da yake matuk’ar so da gudun b’acin ran matarshiba kamar Yahaya ba.

Sauk’i d’aya da Aisha ta samu a gurin Granpa shine haihuwar Aslam da tayi, zan iya ce miki ko y’ay’an da Granpa ya haifa a cikinshi bayayi musu kalar son da yake yiwa Aslam, ko dan ya kasance jikansa na farko ne? Allah kad’ai ya sani.
Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi aka tabbatar da hakan, domin kuwa kalar farin cikin da yayi kowa sai da ya gani ya tabbatar da ‘Granpa na cikin farin ciki’!.
Zakkah da sadakar da ya bayar kuwa bana jin har yau a tarihin kaf garin Kano an tab’a bada irinta.

Aslam ya taso cikin gata, duk wani abu da kika sani Granpa ne yake yi mishi…
A tunanin kowa, Granpa zai kasance irin kakannin nan masu shagwab’a jikokinsa ne, sai dai kuma shekarar Aslam biyar a duniya aka haifi Arshaad amman kwata kwata Granpa bai yi wani murna sosai ba ma balle aje ga maganar shagali da jan shi a jiki kamar yadda kowa ya d’auka…
Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi bai k’ara d’aukar sa ba, Aslam kuwa kullum suna tare, hatta abinci tare suke ci, takanas ya nemo wani bature yake yi mishi lesson a gida, da yamma kuma wani balarabe ne yake koyar da shi addini!
Sai da Granpa ya fahimci loneliness da rashin wasa da Yara agemate d’in Aslam d’in kan iya jawo mishi wani ci baya a rayuwarshi tukunna ya nemi makarantar da tafi ko wacce tsada a kaf Nigeria ya turashi a Abuja wajen mahaifinshi, tare da kwakkwaran warning a me makarantar na “kar a tab’a mishi jika ko me kuwa zaiyi! Kuma kar a bari aci zalinshi.” Duk da yana da wayo sosai dan, a lokacin shekararshi tara
Arshaad hud’u Auwal kuma uku wanda shima Granpa bai wani nuna farinciki ko tunanin janshi a jiki ba tun sanda aka haifeshi.

A lokacin ne kuma Yahaya ya sake tadawa Granpa maganar yana so ya tafi da Aisha Abuja , daman ya tab’a nunawa Granpa son yin hakan amman fur k’iri k’iri Granpa ya nuna mishi sai dai ya tafi da Mammy saboda itace tayi karatu bayan k’iri k’iri babu irin artabun da baayi da shi ba amman fur haka ya hana Aishan yin karatu acewarsa ‘irin su In suka yi karatu gagarar mutum suke yi!’.
A lokacin ya nace akan sai dai ya tafi da Mammy ita zata iya zaman Abuja wata k’ilan ma ta d’an dinga taimaka mishi ta fannin aiki, shi kuma Yahaya yace ‘ba zai tafi da ita ba!
Ko da ace Aisha bata kasance uwargidanshi ba tou tabbas da ita zai tafi’…..
Mistake d’aya wanda Yahaya yayi kuma yake kan yi har yanzu shine ‘k’iri k’iri yake nuna fifici a tsakanin matanshi’ (k’iri k’iri yake nunawa kowa ba tare da shakkar wani abu ba ‘ya fi son Aisha a kan Mammy’.

Da kyar a wannan lokacin dan sai dai Gramma ta shiga tsakani tukunna case ya mutu, dan daa Granpa cewa yayi sai ya tafi da Mammy dole! Shi kuma yak’i.

Tou kuma da Aslam ya koma chan ma da ya sake yin maganar Aisha ta bishi, still magana d’aya irinta farko shima Granpa ya maimaita mishi ‘sai dai ya tafi da Mammy’ shi kuma yak’i,
Shiyasa har yau shi kad’ai yake zaune a Abuja, yanzu haka shi da Aaima ne kawai a gidan.

K’in tafiya da Mammy da Yahaya yayi ata dalilin Aisha yasa Granpa ya rufe ido ya dinga keta mata ruwan rashin mutunci kala kala, ga Adama da Ummi suma basu barta ba, Mammyn ce ma ita bata shiri da ita kuma bata fad’a da ita.
A lokacin ne kuma Mahaifinta ya rasu, Allah yaso ni nayi aure don da ban san ya zan yi ba saboda shi kanshi Mahaifin namu su uku aka haifa biyun duk sun rasu, Mahaifiyar mu kuma daga gidan marayu ma aka aurota, balle inyi tunanin zuwa gidan y’an uwa!
Dan a lokacin halin da Aisha take ciki a gidannan, ko mage bata isa ta d’auko tace zata rik’e ba.

Aslam shekara biyu kawai ya iya yi a Abuja ya d’agawa kowa hankali Akan shi fa ‘Mahaifiyarshi yake buk’ata’ Dan ba kad’an ba suna mugun k’aunar juna, kuma yana da k’ulafucin uwa ba kad’an ba, itama kuma haka, komai Aslam, shima komai Mommy.

Saboda tsabar tsananin shak’uwar dake a tsakaninsu yasa har kusan zarewa tayi lokacin da aka kaishi Abuja,
Idan nace zan tsaya fasalta miki kalar soyayyar da sukewa junansu sai mu kai jibi anan..........

Ba yadda Granpa ya iya haka ya tarkatoshi ya dawo dashi kano gurin Mahaifiyarshi, akan dai ya bari a tafi da ita d’in.

Sai dai kuma daya dawo d’in
abun bai yi dad’i ba sam!
Dan k’iri k’iri Granpa ya dinga nuna banbanci k’arara ba tare da shakkar komai ba!
Abun mamaki hatta driver d’in da zai kai Aslam makaranta daban ne da nasu Arshaad.

Tun abun baya damun mutane har aka fara k’us k’us, su kansu Yaran suma suka fara fahimtar waensu abubuwan….dan shi Arshaad ma a tunaninshi Aslam d’in d’an Granpa ne shiyasa a lokacin yake kiranshi da ‘Uncle Aslam’ a lokacin.

Ranar 12th birthday d’in Aslam ne Granpa yayi wani abun da ya girgiza mutane!
Gida guda ya d’auka ya bawa Aslam as birthday gift, a Dubai!
Wanda su kansu y’ay’ansa basu ma san yana da shi ba, kar ki ce k’aramin gida fa mansion ne mai zaman kanshi! Dan ko a jikin takardar wajen d’akuna ashirin ne suka fito a cikin gidan, iya d’akuna kawai!.

Mutane basu dawo daga shock ba ya cewa Yahaya “ya yiwa lawyer d’inshi magana a fara had’a takardun MT! yana so zai mallakawa Aslam su tun yanzu, in yaso shi (Yahayan)sai ya rik’e mishi idan ya kai 18 years ya bashi abunshi.”

Cikin nuna k’in amincewa Dad ya d’an fara k’ok’arin fahimtar da shi akan shekarun Aslam d’in da kuma gudun abunda hakan ka iya janyowa
K’asa k’asa ba tare da ya bari kowa yaji ba.

Amman Granpa maimakon ya fahimceshi sai ya birkice mishi, ya fara magana yana fad’a kowa yana ji!
Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba!
Fad’a a ranar ba kalar wanda bai yi mishi ba a gaban taron y’an birthday…
Sai da Aslam d’in yayi kamar zai yi kuka yana bashi hak’uri tukunna aka samu ya hak’ura.
Jiki a mace haka Dad ya fita ya kira lawyer ya hau kora mishi bayani……

Kusan minti talatin tukunna ya dawo ya sanar mishi lawyer d’in yace zuwa nan da jibi in shaa Allah komai zai kammala.
Kaf a wajen!
Y’an tsirarrun mutane da Granpa ne kawai suke farin ciki
amman kowa a family d’in in ka kalli fuskarshi ba zaka iya tantance me ke wakana a cikin zuciyarshi ba, sai dai tabbas tashi d’aya zaka hango damuwa binne a k’ark’ashin komai.

Ana i gobe takardun zasu iso, wato washegarin birthday!
Wani mummunan al’amari ya afku.”
Chapter 6 · 0% Book details