← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 70

Sashe 13

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da farko da muka zo, mun tsara ne akan zamu rubuta mata ‘ta jiraka nan da 2 weeks in shaa Allah in ka gama settling da Granpa, zaka je ka sameta’
Kaga kafin nan tunda haihuwa zata yi already ta fita iddarka, ni kuma sai in san yadda zan yi in ja hankalinka mu koma, kuma mun tsara zamu tura wani yaje ya aure Maryam d’in kafin mu dawo tukunna mu saka ka fahimci kana da y’a ba tare da sunan mu ko laifin mu ya fito ba!

Amman karanta diary d’inka da muka yi ne ya sake hautsina komai!
Domin kuwa Abba kwata kwata baka da plan d’in yin rayuwa da ni, you promised maryam (a diary d’in) cewa nan da 1week zaka je ka maida ita, kuma ko parents d’inta sun yarda ko basu yarda ba zaka d’auketa ku sake barin k’asar!
Har sai lokacin da Allah yayi
Tou were willing to leave and risk everything for her, a plan na future Dinka kwata kwata babu ni a ciki!!
And you wrote it ‘a dalilina ne yasa ka tafi ka bar Nigeria, har iyayenta suka kasa hak’ura, suka biyoka, shi kuma Granpa ya yanke wannan hukunci, so I have to pay the price!’
Although ban san menene price d’inba tunda baka rubutaba, but na fahimci saki ne, tunda yadda kake tsarawa..y’ay’an da zaku haifa da sunayen da zaku saka musu, da irin tarin addu’o’in ka na burin samun babys daga gareta, na fahimci baka da tsarin zama da ni!
Kuma hankalina yayi matuk’ar tashi da naga kwad’ayi tare da kalar son da kake yiwa y’ay’an da zaku haifa( kai da ita), shiyasa kawai muka yanke hukuncin rubuta mata takardar da muka aika Daniel ya kaiwa k’anwarta!.
A baya tunani na son Maryam kakeyi, amman karanta diary Dinka da nayi tun daga farkon had’uwar ku har k’arshe bayan tafiyar Daniel, shi ya tabbatar min da cewa haukan somta kake yi
Dan haka with her in your life, Abba banida chance kwata kwata.”

Matsowa tayi kusa dashi ta kama hannunshi kafin tace
“Abba put yourself in my shoes, yadda kakeji akan Maryam wallahi nima haka nake ji a kanka!
Shiyasa da naji plans d’inka hankalina bai ida kwanciya ba har sai da muka had’u da mammy ta rakamu aka rufe maka baki akan batun mayar da ita d’in da kace zaka yi sannan aka cire ta a ranka gaba d’aya!

Sai dai kuma shekara d’aya kawai Allah ya bawa addu’o’i n namu ikon yin tasiri a kanka domin har yau zancenta kakeyi ba dare ba rana kuma na tabbatar ba dan ta yi aureba da tuni tana a gidan nan ni kuma na san karshenta zuciyata bugawa zata yi!”.

Cikin kuka tayi k’asa ta durk’usa a gaban shi still tana rik’e da hannuwanshi kafin tace
“Duk wani abunda kake buk’atar ji, gashi na fad’a maka, har wanda bai kamata kaji ba duk na fad’a maka Abba
Amman inaso ka cire son rai ka duba lamari na, wallahi duk kai ka janyo komai!
Komai kuma da nayi, na yishi ne saboda kai, saboda son da nake yi maka da kuma burin inga mun kasance tare har abada!.
Dan haka, dan Allah ka dube ni da idon rahama ka yafe min, ni kuma na yi maka alk’awarin ba zan sake wani attempt d’in tab’a rayuwar Maryam ko y’ar ta ba!
Tun farko ma da ace baka yi abinda kayi ba, da ba azo nan ba..
Inda ace ka bani time d’inka tun lokacin farkon aurenmu da ba zan yi attempting aika mata da sak’o ba wanda har yayi sanadiyyar da ya sanya ni karanta diary d’inka.

A yadda nake sonka inda zaka dinga kula da ni, sannan ka min alk’awarin adalci da zama dani har abada, wallahi Abba da zan rufe idona In danne duk wani kishi, in barka da Maryam
Amman yadda ka nuna gaba d’aya baka da plan na rayuwa dani shi......”

Hannun shi da ya warce a cikin nata ne ya sa ta had’iye ragowar maganganun data d’ebo!

Cikin b’acin rai yace
“Ummi! ban tab’a ganin selfish being irin ki ba!.
And FYI ba saboda son da kike yi mini bane ya sa kika aikata waennan abubuwan wake up!! Saboda tsananin son da kike yiwa kanki ne ya saki aikata hakan!

Kinga dai Ina son Maryam fiye da raina ko??
Amman wallahi inda ace tun farko ta nunamin bata sona kuma akwai wanda take tsananin so, kamar yadda na nuna miki, tou da tabbas zan iya hak’ura da ita, saboda farincikin ta!!

That is love, ba wannan shirmen naki ba.”
Yana gama fad’in haka ya warce k’asan rigarshi da ta kamo ya wuce ya bud’e k’ofar ya fice a d’akin ya barta nan durk’ushe tana kuka tana kiran sunanshi…..

Mom tana zaune a falon da k’unshinta, taga sauk’k’owar Abba…
Da k’arfi k’irjinta ya buga!
Yadda taga ya sauk’o ya wuce fuuu ranshi a mugun b’ace ko adawo lafiyanta bai amsa ba.

Gaba d’aya sai ta kasa nutsuwa…
kusan minti biyar ta bayar amman shiru ba Ummi ba labarin ta, dan haka ta yanke shawarar cire lallen!
Ko bi takan mai k’unshi da take ta ce mata “bai kamaba” Bata yi ba ta bata kud’inta ta kira mai aiki tace “ta tattare wajen”dan gaba d’aya k’irjinta bugawa yake yi ta rasa dalili.

Kaf falon sama da d’akunan ta duba bata nan, har d’ayan side d’in ta sauko ta hau ta sake dubawa nan ma bata nan.
Tunawa da tayi Abba yace ta kai mishi abinci bedroom d’inshi ne, yasa da sauri ta nufi stairs d’in da zai kaita side d’in nasa.

Tun kafin ta k’arasa d’akin ta fara jiyo sheshshek’ar kuka..dan haka ko sallama bata yi ba ta k’arasa ciki da mugun sauri.

A yadda Abba ya fita ya barta a haka ta tarar da ita, da sauri ta k’arasa ta d’ago ta kafin a rikice ta hau tambayarta “mai ya faru?”

Kukanta ne ya k’aru, wanda hakan ya sake rikita Mom! Ta d’ago hannu kenan zata tab’ata taga shatin yatsu kwance akan farar fuskarta..
Cikin gigita ta cigaba ta tambayarta tana faman jijjigata
Da kyar Ummi wada tun shigowar Mom kukanta ya tsananta ta iya sassauta kukan nata da kyar
ta hau gayawa Mom dukkanin abunda ya faru, tana sheshshek’a….

Tunda ta fara magana Mom tayi mutuwar tsaye! Har ta kai aya ta d’ago tana kallonta amma ko gezau bata yi ba.
Sai da Ummin ta d’an tab’ata tukunna ta juyo da hankalinta gareta kafin cikin b’acin rai ta fara magana
“Ban tab’a ganin dak’ik’iya Irin ki ba! A tunanina rashin wayon ki bai kai haka ba!
Amman yau kam na gasgata ya kai har ma ya wuce zatona.
In banda rashin hankali, ba duka ba ko kanki Abba zai saka a gabas da wak’a a hannunshi, ya kamata ki fad’a mishi wannan maganganun da muka yi alk’awarin rufawa juna asiri akai har abada???
Barazana ce fa yayi miki!! Tayay ma za kiyi tunanin Abba zai iya yi miki illa?? Na tabbatar ko suman k’arya kika yi tuni zai dawo dai dai hankalinshi kuma ya tashi!!

Amman da yake ke d’in dabba ce!! Shine kika tonawa kanki asiri da mu da muka taimakeki, gaba d’aya!! Yanzu ya kike so muy.....”.

Cikin katseta Ummi, tace
“Adama wallahi ke kike ganin kamar barazana ce amman ba haka baneba, da gaske na hango tashin hankalin da ban tab’a gani ba a cikin kwayar idanunsa, kuma na tabbatar zai iya aikata dukkanin abunda ya fad’a din.
Ba abinda yafi d’aga mini hankali irin kalmar ‘saki’ da ya ambata!
Shiyasa kika ga nayi haka, kin sanni zan iya yin komai domin inga na kare aurena!
Kuma baya ga haka a tunanina idan na fad’a mishi gaskiya to zai yarda da ni kuma ya fara trusting d’ina daganan ya so ni!
Shi da bakinshi yace ‘In na fad’a mishi gaskiya komai zai wuce, in kuma ban fad’a ba har saki sai ya had’a mini dashi km....”
Marin da Mom ta d’auketa da shi ne ya katse mata ragowan maganartata…
Cike da mamaki ta d’ago tana kallon Mom….za ta yi magana Mom d’in tayi saurin d’aga mata hannu sannan tace
“Lalle Ummi, wato kin yi komai saboda kare aurenki da jawo hankalin mijinki gareki ko?
Mu kuma fa? Da kika zubar mana da k’ima, kika sakamu a matsala? Ke a ganinki kin yi mana adalci kenan?.
Ko dan kinga ke baki da wani ishashshen laifi a cikin lamarin shiyasa?
To bari kiji in gaya miki
kinga wannan abunda kika yi?”
Bata jira jin amsartaba tace “ba zai jawo yarda tsakaninki ke da Abba ba ballantana a tafi kan maganar so, in banda bak’in jini da tsana ba abunda rashin tunaninki ya jawo miki!!!.
Kuma inaso ki sani, ni da sake shiga harkarki har gaban abada!! Saboda na lura kowa kanshi ya sani dan haka kowa yayi ta kansa.”
Tana gama fad’an haka ta juya tayi hanyar fita, sai kuma ta sake juyowa kana tace mata
“In zan baki shawara ki d’auka, gara ki hak’ura, saboda inda ace Abba zai so ki to da tuni an wuce wajen!! Amman har yanzu shiru..
Ga kuma sababbin obstacles a gabanki
Kin tonawa kanki asiri
kuma ga Maryam ta dawo rayuwar shi
sannan ga y’arsa da mukeda tabbacin ita zata had’a su!!
So kawai gara….”
K’arar jiniyar y’an sandan da ta jiyo ne ya sakata yin shiru!!
Take gabanta ya yanke ya fad’i, kallon Ummi take yi wadda itama jin jiniyar y’an sanda ya sakata sake rud’ewa!
Cikin karkarwar jiki tace
“Kamar jiniyar y’an sanda nake ji.”
Tun kafin ta rufe bakinta, Mom tace “Ba ‘kamar’ baneba tabbas jini y’ar y’an sanda ne.

Tuni ilahirin jikin Ummi ya sake rikicewa da karkarwa, ga uban gumi sai sake keto mata yake yi ta ko wacce k’ofar gashin jikinta, kana ganin ta ka san bata da gaskiya, fuskarta tayi jajir.

Da sauri ta k’araso kusa da Mom kafin tace
“Adama me kenan hakan yake nufi?
Kina tunanin Abb....”

“Tabbas Zainab mijinki ya cika tantirin d’an iska kuma mara mutunci!
Da y’an sanda zai had’a mu kenan ko me??”
Cewar Mom.
Chapter 13 · 0% Book details