← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 70

Sashe 56

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya d’ago yana kallon setin inda yaji muryar tata ta fito, “ai kuwa ita d’in ce”
ya fad’i hakan a ranshi.
Da murna ya k’arasa inda take zaune ita da aiima…
Ita kam ko wankan ma bata samu tayi ba! Tana nan a yanda ta fito a cell! Yo
ina zata iya wanka, ko sama bata samu ta hau ba tun da Aaima ta fad’a mata mummunaan labari take zaune take jiran dawowar Arshaad.

Huggin d’inta yayi
kafin ya d’ago yayi kissing forehead d’inta tukun yace
“Welcome home Mammy,
we miss you.”

Murmushin takaici tayi kafin ta mike tsaye, cikin tsananin b’acin rai tace
“Ba kayi missing d’ina ba Arshaad, da kayi missing d’ina to da ba zaka yi min yaji ka daina zuwa inda nake ba”

Kamar zai yi kuka yace
“Mammy bana son ganin b’acin ranki, abunda kike so inyi ne ba zai yi ba, kiyi hak’uri please.”

Cikin katseshi tace
“Ka san cewa Aslam baya yin kwana uku bai lek’o mu ba?
Haka Auwal shima!
Daddy kuwa kullum sai ya kira waya an had’ashi da Adama
Ummi kam daman kowa ya san Mijinta ba zuwa zai yi ba tunda shi ne ya kulle mu!
Kai fa? Arshaad
da kai da uban ka laifin
me nayi muku, a rayuwa?

Anya ni na haifeka kuwa Arshaad?”

Da sauri ya matsa sosai inda take idanuwanshi har sun cicciko kamar zai yi kuka ya d’aura hannunsa ya rufe mata baki kafin yace
“Mammy pleas...”
Bai k’arasa ba ta buge hannun
cikin tsananin b’acin rai tace
“Kar ka yi mini ‘please’ bana son ji!
Kun riga kun nuna min matsayi na da kai da ubanka!
Naji nagani kuma na fahimta,
akwai lokacin da na ware muku kai da shi zan waiwayeku amman ba yanzu ba dan wallahi sai kun san kun wulak’anta, hak’urina ya k’are a cikin gidan nan!
Amman yanzu akwai boss d’in da ya kamata mu fara kashewa ni da kai a yau kafin komai.”
Bata jira jin me zai ce ba taci gaba
“Naji labarin za kayi aure!
Jibi ko?
To wallahi bari kaji
In dai sunana Rukayya
kuma nonona ka sha
to wallahi muddin ka auri wannan Yarinyar
ni kuma a ranar zan tsine maka......................”

“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Itace kalmar da Arshaad yake ta nanata wa a ranshi!
Ya kasa motsi ya kasa cewa komai……
A ranshi yace
“Wannan shine abunda nake gudarwa since day 1, ya zan yi
da Mammy, ya zan yi da zuciyata wadda na san muddin aka fasa aurena da Hudan tabbas tarwatsewa za tayi”.

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
51

Mammy tana gama fad’in haka ta wuce sama, haka Aaima itama ta bi bayanta
tana jin kamar an tsundumata a Aljannah!
Suka barshi shi kad’ai a tsaye.

A hankali ya nemi kujera ya zauna ya sunkuyar da kai sannan yasa hannu ya dafe kan da hannu biyu..
Yafi minti ashirin a haka, chaan! Ya ji an dafa shi,
yana d’agowa suka had’a ido da Dad.
Kallon shi Dad d’in yake yi trying to fassara yanayin da yake ciki.

Da sauri Arshaad ya mik’e tsaye ya fara k’ok’arin saita kanshi, cikin k’ok’arin danne abunda ya tokare mishi k’irji yace
“Ina wuni Dad”

Sai da Dad d’in ya d’an k’uraa mishi ido tukun yace
“Lafiya kake kuwa?”

Murmushi kawai Arshaad d’in ya k’ak’alo kafin yace
“Alhamdulillah!
All is fine na gaji ne kawai, bara inyi freshening off
in kwanta”
Ya k’arashe maganan da k’ok’arin barin wajen dan
ya lura da kallon da Dad d’in yake mishi so yake ya gane yanayinshi ne.

Har ya d’anyi gaba yaji Dad d’in yace
“Arshaad”

Tsayawa kawai yayi ba tare da ya juyo ba.

Ajiyar zuciya Dad d’in ya sauk’e kafin a hankali shi ya taka ya k’arasa inda yake ya tsaya a gaban shi yasa hannu ya dafa kafad’ar shi, cikin kulawa ya fara magana
“Son, irin haka is normal!
Most a times couple basa tashi samun matsala sai ya rage y’an kwanaki kad’an aurensu..
Ka kwantar da hankalin ka kar ka sa komai a ranka, za ku hirya soon komai ya wuce kamar bai faru ba.
Wannan duk aikin shed’an ne so karka bari yayi galaba a kanka.
Allah yayi muku albarka.”
Cikin sigar zolaya ya ci gaba da cewa
“Nan da jibi fa ka zama magidanci, a nan ne zaka fara facing real life da real issues
So garama ka shirya!
Kar ka bari small things irin haka suyi breaking naka.”

Da k’arfi Arshaad ya taune lip d’inshi na k’asa, yana jin
yadda zuciyarshi take tafarfasa!
Ba k’aramin kokawa yayi da makogwaro da harshenshi ba kafin ya samu su bashi had’in kai wajen furta kalmar
“In shaa Allah Dad, thanks a lot.”

Murmushi Dad d’in yayi kafin ya d’anyi tapping kafad’ar shi da hannunshi ke a kai
yace mishi “good night”
daga nan ya nufi hanyar side d’inshi, ya bar Arshaad tsaye a wajen…

In banda ajiyar zuciya babu abunda Arshaad yake sauk’ewa a jere a jere.
Ganin ya fara ganin duhu duhu, kar yaje ya fad’i a wajen yasa ya lallab’a ya nufi side d’inshi shima dake nan a k’asan.

Da kyar ya kai kanshi toilet
bayan ya ajjiye suite d’in hannunshi akan gadon.
Ko agogon hannunshi bai samu ya cire ba ya yana shiga toilet d’in ya sakarwa kanshin shower ta ko’ina da ruwa mai mugun sanyi!

Ya dad’e a haka kafin da kyar ya samu ya fito kayan jikinshi na d’igar ruwa..
Dai dai nan ya ji wayarsa ta hau ringing, hannu yasa a aljihu kafin ya zaro wayar k’irar iphone 13 ya kalla screen d’in!
A take damuwar da ya samu ta d’an ragu ta dawo mishi sabuwa ta sake hauhawa
sakamokon ganin mai kiran nasa..
Har ta tsinke bai d’aga ba kuma bai daina kallon screen d’inba!
Yana a yanda yake wani kiran ya sake shigowa…
A hankali hannunshi na rawa ya d’auka ya kai kunnenshi kawai yayi shiru bai ce komai ba.

Cikin sanyin muryarta yaji tace
“Ya Arshaad.”
Ajiyar zuciya ya sauk’e ya lumshe idanuwanshi da suka yi jaaa wanda hakan ya bawa hawayen da yake ta addabar zuciyarshi daman zubowa ta ido d’aya! Kafin d’ayan idon shima ya samu damar zubo da nashi hawayen...

Ajiyar zuciya kawai taji yana sauk’ewa a jejjere
Hakan yasa a d’an rud’e tace
“Ya Arshaad ka yi mini magana pls, baka da lafiya ne yanzu? Mai ya faru”

Da kyar ya iya k’arasawa bakin gadonsa ya zauna dan ya fara rawar sanyi ba kad’an ba!
Yana zama wata wawiyar atishawa ta kece mishi
wanda yasa Hudan mik’ewa daga kwancen da take, kafin tace
“Mura ko? Sorry sannu ka sha magani tou?”

Sai a sannan taji yayi magana
“Hudan!”

“Naam” tace da sauri dan daman so take taji ya furta wani abun dan shirun nashi ba k’aramin tsoratata yayi ba.
A hankali ya d’an yi tari kafin yace
“Do you love me??”

Ta d’anji kunyar tambayar amma jin yanayin shi da kuma muryarshi wata iri yasa tace
“Yes, a lot”

A hankali yace
“Say it”
Shiruu, ta d’anyi kafin a hankali yaji tace
“I love you”

Sai da yad’an lumshe idanuwansa kafin yace
“To what extent??”
Ya sake jeho mata wata tambayar.

Zuwa yanzu kam yad’an fara birkita mata lissafi hakan yasa tace
“Ya Arshaad meye ne yake damunka?”
Tayi masa tambayar kamar zata fashe da kuka.

Cikin tsare gida yace
“Just answer me!
How much??
To what extent za ki iya zuwa domin kiga mun mallaki junan mu??”

Ita dai ba abunda take fahimta daga shi zuwa yanzu, gashi
tana jin yanda numfashinshi yake seizing sama sama!
Daurewa tayi tace
“Kamar yaya?”
Dan da gasken bata fahimta ba.

Da kyar ya dedeta numfashinshi
kafin yace
“Idan Mama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura??

Sai da ya sake maimaita mata tambayar tukunna tace
“Maama ba zata tab’a cewa In hak’ura da kai ba!
Meyene ya faru na kasa gane komai”

Bai bata amsar ba
sai cewa yayi
“Idan Maama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura??”

Ta kasa fahimtar inda ya dosa,
kawai sai ta yanke shawarar ce mishi
“Ya Arshaad ai albarkar iyaye shine abinda ake buk’ata!
In basu da niyyar sakawa meye amfanin auren da za ayi babu albarka?”

Rintse idanuwansa yayi da k’arfi! Tuni numfashinshi suka fara korar juna…
She can feel it
dan haka duk sai ta sake rud’ewa ta hau kiran sunan shi
amman yak’i kulata, k’arshema
wani irin tari taji yana yi,
yayi kusan 3 minutes yana tarin Hudan tana kuka tana kiran sunanshi
amman shiru
wanda hakan har sai da ya farkar da Sakina da Khadijah amarya y’ar Anty Zainab da suke d’aki d’aya da ita
daga bacci.

Ganin yanda duk ta rud’e ne yasa Sakina ta shiga tambayarta….

Karb’ar wayar Sakina tayi
itama ta shiga kiran sunan shi
tana
“Are you there?
Are u okay??”
Amman tsit kake ji
ko tari babu.

Rikicewa suka yi…
Da kyar idea ta fad’owa Sakina
hakan yasa da sauri ta d’auki wayarta ta danna kiran Aaima!
Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna aka d’auka, cikin gigita Sakina tace
Aaima ina wuni,
sorry na tashe ki,
Ya Arshaad ne bashi da lafiya, dan Allah ko zaki gayawa Dad in yana gida a duba shi ko kuma ki tura wani wanda yake kusa….”

Shiruuu, Sakina taji anyi!
Hakan yasa ta sake cewa
“Aaima”

Ajiyar zuciya taji Aaiman ta sauk’e sannan ta fara magana
“Ki turo Hudan mana ta zo ta duba shi!
Daga nan ma sai su yi sorting out decision d’in da ya kamata su yanke..
Besides
a nan ba wanda zai kulashi saboda rashin lafiyarshi ba zamu iya yi mishi maganinta ba.
Spoiler alert!!
Bara kiji abunda na san ya jawo mishi ciwon......
Mammy ta dawo d’azu
at last ita da su Mom!
And tace masa ‘ya hak’ura da auren Huda ko kuma ta tsine mishi!’
Wannan shine abunda ya janyo mishi rashin lafiya
na riga da na sani.”
Tana gama fad’in haka ta ajjiye wayar.
Chapter 56 · 0% Book details