Sashe 40
So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallonta tayi dariya taso kufce mata, da sauri ta hure kendir d’in ta fito ta maida k’ofar ta rufe ta wuce a ranta tana mamakin rashin hankali jahilci da rashin sanin ciwon kai irin na Umma!
Ace y’arki tana nan da ciki a chan wani gidan da baki san ko su waye ba! Amman kalli yanda ta barrarraje tana shek’a uban bacci kamar wata jaka!
Da wannan tunanin Sakina ta k’arasa d’aki ta tarar bacci yayi nasarar d’auke Hudan, daman ita bata da wuyar bacci.
Itama Sakinan bata wani dad’e ba baccin ya d’auketa cike da tunanin rashin man kai irin na Umma…inda ace su Ummu ne akace d’aya a cikin ita ko Huda bata gida ta tabbatar ko gigin yin bacci ba zasu yi ba!…..
Abunda Sakina bata sani ba
shine
Umma magani mai k’arfin tsiya ta sha, dan yau kusan kwananta uku bata iya bacci tun lokacin da Jalila ta gaya mata Huda cousin d’in Arshaad ce!
Ga kuma Mahaifinta yana son ta harma sun bar gidan kakan da shi da yayanshi duk akan Huda!
Yau kuwa da Jalila ta kirata take shaida mata irin daular da Hudan take ciki sai da ta kusa hauka!
K’arshema dishi dishi ta fara gani!
Ga zuciyarta tana ta bugawa da mugun k’arfi ga zazzab’i.
Don haka ta lallab’a taje wani Chemist a chan bakin titi babba da aka bud’e sabo!
Matar(mai chemist d’in yare mai mutunci)
Anan ne bayan an gwadata matar ta tabbatar mata da jininta ne yayi mugun hawa…dan haka ta samu ta sha magani ta rage damuwa tayi bacci..
Tun achan chemist d’in ta nemi matar ta bata maganin da zai sakata baccin dan itama tana buk’ata, saboda ta san in ta samu baccin at least zata huta da tashin hankalin da take ciki na y’an awanni, kafin kuma ta farka.
Mai chemist d’in taso ta hanata, but ganin halin da take ciki yasa kawai ta siyar mata
saboda tayi mugun tausaya mata dan a yanda jininta ya hau ita kam tama yi mamaki da ta ganta tsaye akan k’afafunta.
Hakanan ta bata ta sallameta sai faman sannu take jera mata zuciyarta cike da tausayinta, har ta tafi
a ranta tace
“Maybe halin mazan zamanin nan ne yake neman hallakata, Allah sarki mata! Allah ya baku ladan hak’uri da maza........”
Washegari da safe Umma bata samu tashi da wuri ba, har sai da Baba ya lek’a d’akinta ya tasheta tukunna saboda shima yaji shirun nata yayi yawa dan jiya yayi ta jiran ta amma yaga shiru bai ganta ba, yauma kuma gashi har ya shirya amma babu abun kari ba k’amshin shi babu alamun shi!
Ba yadda bata yi da shi ba akan ya tsaya ta d’an dafa mishi abu mai sauk’i amman ya k’i yarda a cewarshi ya makara!
Don haka tayi mishi a dawo lafiya
ya amsa ya juya ya fita.
A bakin rijiya ya hango Huda tana jan ruwa zata yi wanka saboda jiya cikin dare period d’inta yazo, gaba d’aya ya b’ata mata jikinta…
Suna had’a ido dashi gabanta ya fad’i! Dan wani irin kallon mamaki taga yana yi mata.
A hankali ta sunkuyar da kanta kafin tace
“Baba ina kwana”
Bai amsa mata ba, yace
“Me kike yi a nan?”
Tambayar tayi matuk’ar bata mamaki, dan duk tsawon zamanta da shi bai tab’a yi mata haka ba! Sai dai ya nuna tsana da kyamar ta k’iri k’iri, ko
lokacin da take boarding ma sai dai ya cewa Mama ta hanata zuwa nasa gida in an yi hutu, ita kuma Maman ta gaya musu…
Tambayar ya sake maimaitawa a d’an hassale!Don ya k’agu yaji dalilin zuwan nata sannan kuma yaji waye ya kawota.
Cikin d’an rawar jiki da murya tace
“Jiya da daddare nazo, ni da Sakina”
“Da wa kuma?
Waye ya kawoku?”
Yai mata tambayar ba alamun rahama a fuskarshi.
A hankali tace
“Abba”
“Ma shaa Allah”
Baba yace
Har yayi hanyar d’akin Mama a zuciye sai kuma taga ya juya ya fice fuuuu, ko
mashin d’insa bai tsaya d’auka ba.
Har tayi wankan ta fito duk ranta ba dad’i, dan a yanda taga Baba yau ta san ba za a kwasheta lafiya da shi ba!
Su mama da Sakina sarai sun ji duk abunda ya faru, dan
haka da ta shigo suka tambayeta “Ina yayi?” tace musu
“Waje, ba mashin”
kawai, ta fara shiri.
Mik’ewa sakina itama tayi ta je tayi wanka..
Basu samu breakfast daga Sadiya ba, itama k’osai ta siya ta ci, tunda mijinta ya riga ya fita.
Wankan itama Mama tayo ta d’an shirya, sannan ta basu kud’i dan suje su siyo musu abunda za suyi kari da shi
Y’ar tsala suka siyo ta d’ari biyu, suka tafasa ruwan Lipton suka soma karyawa…..
Hudan tana jan Mama tana ta shige mata a hankali a hankali dai tana d’an kulata.
Suna cikin karyawa wayar Mama ta hau ringing
Ganin number Kaka, yasa ta d’auka da sauri!
ko gaisawa bai bari sun yi ba yace “ki zo yanzu nan ke da su Sakina!
Muna gidan Abban ku.”
Gabanta ne ya fad’i ras! Tana shirin yin magana ya kashe wayar…
Mik’ewa tayi ta d’au hijabinta sannan ta rarumi purse d’inta kafin tace
“Ku taso muje,
Kaka yana kira.”
Hijabansu suma suka sanya, suka fito, gaba d’ayansu.
A tsakar gidan suka tarar da Umma tana bawa Ya Ja’afar koka a baki!
Ya dalalar da wani ya zxubar da wani….
Da tsoro Hudan ta kallesu, sai kuma ta k’arasa! Sai da ta d’an rissina tukun ta gaida Umma.
Da kyar Umman ta iya amsawa
Ya jafar d’in kuwa da ta gaidashi, kallonta kawai yake tayi bakinshi na zubar da yawu da d’an ragowa ragowar kunun, ya kasa cewa komai.
Daga d’an nesa Sakina tace “ina kwana” bata jira jin amsawar su ba ta wuce tayi waje abunta.
Itama Mama d’an matsawa kad’an tayi suka gaisa sama sama kafin tace
“Ya jikin nashi?”
“Da sauk’i” Umma tace, tana wani b’ata rai irin ita an dameta d’innan…
Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace
“Bara muje Kaka yana kiranmu.”
Wannan karon banza Umman tayi da it.
Guiwa a sace suka fice daga gidan ita da Huda Umma tana jin kamar ta bisu ta shak’e su!
K’arshe dai haushin akan Ya Ja’afar aka sauk’e, dan kokon da bai sha ba kenan tace wai “yana ta b’ata mata lokaci”.
Jikinshi ta bashi tsumma ya goge, da kyar! Daganan ta mik’e ta fice ko wanka bata yi ba.
Su Mama kuma bayan sun fita ne, Hudan take tambayar “mai ya samu Ya Ja’afar?”
Sakina ce ta iya amsa mata da
“Fad’a suka yi! Nasu na y’an shaye shaye
Wani ya d’au makeken dutse ya buga mishi a kai. A haka ma ya d’anji sauk’i….”
A babban parlourn Madu suka same su dukkansu, Shuwa Baaba Talatu Madu da Kaka!
Kana ganin fuskokinsu ka san ba lafiya ba!
Dan haka su Mama suka sha jinin jikinsu suka gaidasu suka nema waje suka zazzauna.
Baaba Talatu ce tace
“Maryam yaushe Yaran nan suka zo?”
A hankali Mama tace
“Jiya da daddare”
Jingina kai tayi tukunna tace ,
“Shi Abban ne yace su kwana?”
A hankali ta girgiza kai.
D’an shiruu ne ya biyo baya kafin Kaka yace
“Maryam mun yi miki magana akan ‘ki d’in jira tukunna’ amma ko? Mai yasa kike da taurin kai ne?
Kinsan me taurin kan naki ya haifar yanzu?”
Bai jira amsar taba ya d’aura da cewa
“Kinga na farko yanzu haka Usman yana hannun hukuma!
Yanzun nan aka kamashi bayan ya wanke k’afa yaje ya kwashi y’an sanda ya kaisu wai su d’aure Abba saboda yana bin matar aure!!
Ban san dai ya aka yi ba amman reshe ya juye da mujiya, yanzu haka yana d’aure a station!
Sannan kema Abban yace ya baki minti 40 ki maida masa Yarinyar shi da hannun ki, in ba hakaba kuma to duk abunda ya biyo baya ke kika ja!
Kuma yace gaishe kin ma ta daina zuwa yi daga yau!.
Cikin kuka Mama tace
“Kaka dan Allah kar ku ce in yi abunda yake so..
Wannan wanne irin son kai ne Abba yake gwadawa?
Na ji na yarda da maganar ku da kuka ce bai san da itaba tun farko na yafe mishi wannan amman dan Allah kar ku bari ya raba mu! Kawai ni ya fita a harkar mu gaba d’aya, bama buk’atar shi.”
Murmushi Madu yayi kafin yace “Hudan kema ba kya buk’atar Mahaifinki??”
Sai da ya sake maimaita tambayar tukunna ta d’aga kanta alamar ‘eh’ sannan tace
“Zan zauna a wajen Mama”
A hankali, Madu yazo ya zauna a gefen su da kyau kafin ya fara magana
“Shikenan zamu gwada mu gani, amman idan mun yi nasara kin dawo wajen Maman naki to inaso kisan cewa
Ba a inda take zaki zauna ba sai dai ki zauna a gidana! Saboda Usman ba zai tab’a bari ki ci gaba da zama nasa a gida ba sannan na san ba zai dinga barin itama Maman naki tana zuwa inda kike ba
kwata kwata kinga kenan baki zauna da Abba ba kuma baki zauna da Mama ba!”
Cikin kuka Mama tace
“Abba dan Allah ka dai na, za ka karya mata guiwa”
Murmushi ya sake yi kafin yace
“Maryam hakan shine gaskiya!
Kuyi hak’uri, for the first time nayi miki alk’awari ban cika ba!