← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 70

Sashe 5

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kulawa Gwaggo Asabe ta amsa…
Har ga Allah ta dad’e bata had’u da Yarinya mai hankali da nutsuwa irin Huda ba, ga kyau tubarkallah…shiyasa lokaci guda suka saba, taji ta shiga ranta sosai!
Har k’asan zuciyarta take yiwa Aslam d’insu kwad’ayin auren Yarinyar saboda ta had’a komai ga kyau ga hankali ga nutsuwa gata y’ar uwarshi!
Sai dai kuma yadda taga Arshaad yana shige mata sosai, watak’il shi ne zai fara cewa yana sonta, dan jiya ta lura har wata y’ar hira suka tsaya yi a parlour, sai wani nan nan yake yi da ita…..
Hannu Huda ta saka tana k’ok’arin karb’ar tea flask d’in dake hannunta wanda hakan ne ya katse mata tunanin ta!
Ba musu ta sakar mata , dan itama tana jin yadda ya kusan fad’uwa.
A tare suka nufi hanyar sama, tana gaba Hudan na biye mata baya, wata hanya suka kuma d’auka bayan sun shanye stairs d’in,
nan ta sake hango wani bene,
benen suka bi suka hau, suna kaiwa k’arshe suka tarar ta wata y’ar k’ofa
A bud’e k’ofar take hakan yasa suka shige, dogon corridor ne sosai, sai k’ofofi biyu, d’aya a farko farko hanyar dama, d’ayar kuma a kusan k’arshen dogon corridor d’in ta hannun hagu,
Wadda itan taga Gwaggwon ta nufa, sai da suka iso bakin k’ofar, tukun suka tsaya!
Rik’on tray d’in Gwaggwo Asabe ta gyara sosai a hannu d’aya sanna tasa hannu tayi knocking, tukun taja ta tsaya, ta gyara ruk’on tray d’in.
Kusan minti biyu tukunna suka ji ance “come in”
Hudan ta kalla tace “tayi amfani da empty hand d’inta ta bud’e musu.”
Hakan tayi, bayan ta murd’a handle d’in a hankali ta d’an tura sai kuma ta matsawa Gwaggo Asabe don ta fara shiga..
Murmushi Gwaggon Asabe tayi sannan ta shige
Itama Hudan ta bita a baya.
Sai da ta rufe k’ofar tukun ta juyo ta fara kallon d’akin….

“Ma shaa Allah” tace, a ranta.
Ba zaka kirashi d’aki ba kuma ba zaka kirashi da parlour ba, ga set d’in kujeru har da k’aramin dining, da makekiyar tv d’in da bata tab’a ganin irin ta ba, ga kuma set d’in gado shima komai akwai,
royal, light blue da fari haka colour d’in kujeru da gadon suke, hatta pentin d’akin haka yake. Ga kuma wani glass door, wanda kana iya hango swimming pool da shuke shuke da kujerun shak’atawa.
K’auyanci ta fara, don a ranta ta hau rayawa “daman ana pool a sama? saman ma ta biyu!
Ita tunda take bata tab’a ganin d’aki mai girma sosai da kyau irin wannan ba!”……

Tunanin ta ne ya katse jin Dad yana cewa “Hudan k’araso mana ya kika tsaya a k’ofa?”.

Sai a lokacin hankalin ta ya kai kan Dad, da wata mata a zaune a gefen shi yana rik’e da hannunta.

Ji tayi kamar ta rusa kuka!! Da ta san gurinshi Gwaggo Asabe zata zo da bata biyo ta ba, kenan ita duk b’uyab da takeyi ma a banza, tunda gashi a gidanshi ma ta kwana ba tare data sani ba,
kuma yadda ya nuna it’s like ya san tana nan d’in, shikenan ta san yanzu zai kira Abba shi kuma ya hanata zuwa taga Mama.

Gwaggo Asabe ce ta katsemata tunani jin ta sake cewa “Huda k’araso mana.”

A hankali take takawa izuwa bakin gadon inda suke…

Taji Dad yana cewa
“Ashe da gaskiyar Abba, daman ya ce tana wajensu Aslam ni ban yarda ba,
sune suka kawota jiyan ko?”

D’an murmushi Gwaggo Asabe tayi kafin tace
“Eh jiya lokacin da ka kira ni, Arshaad bai dad’e da kawota ba, shi ya rakota.”

Hudan dake jin su duk sai taji jikinta yayi sanyi, ashe ita kad’ai take ta shirmen ta.
A hankali ta k’arasa wajen, kanta a k’asa.
Har k’asa ta durk’usa ta gaida Dad, wanda cikin tsananin son yake yiwa y’ar d’anuwan nasa yayi saurin kamo ta ya zaunar da ita a kan d’an stool d’in da yake facing d’inshi,
cikin kulawa ya amsa kafin ya hau tambayarta “ya kwanan bak’unta?”
“Alhamdulillah” kawai ta iya cewa kafin ta juya ta hau gaida matar gefen shi har sau biyu amman ba alamun zata amsa kuma ta kafeta da idanuwa!
Tana shirin sake gaidata a karo na uku ne
Dad ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an dafa Huda tukun yace
“Karki damu ba zata iya amsawa bane, amman ta fahimceki, tunda gashi tanata kallonki.”

Yana gama fad’in haka ya juya ga Gwaggo Asabe jin tana cewa “ga breakfast, watak’il taci tunda naga yanzu jikin da d’an sauk’i, ko?”
Shiru ya d’anyi kafin ya sauk’e wata ajiyar zuciya tukunna yace
“Sai addua fa, amman Alhamdulillah, ni fa da Granpa zai yarda wallahi da an hak’ura da wannan theraphy d’in, saboda duk lokacin da akaje aka yi aka dawo ni sai inga kamar abun k’aruwa ma yake yi, kwanaki fa har hira tana yi, amman yanzu kiga gaba d’aya sai a hankali, danfa baki ganta last two weeks ba
(Tym d’in da suka dawo. A Abuja), shiyasa ai na hanata dawowa nan, da kyar fa da addu’o’i tukunna abun yayi sauk’i ta dawo hakan.”

Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e kafin tace “nima dai gaskiya na dad’e da lura, magana ce kawai banaso.”

Cikin d’an fad’a Dad yace “Ai kuwa ta gama theraphy!
Dan a gaskiya, ko ance za aje, sai dai In kaita Abuja kawai muyi sati mu dawo, abu ba fad’ar Allah ba amman an maidashi kamar dole!?”

Kwalla Gwaggo Asabe ta share sannan tace
“Ai shima Granpa d’in naji yana cewa ‘daga wannan an gama’.”Cikin katseta Dad yace “ai tun last year yake cewa ‘daga wannan an gama daga wannan an gama’! Amman an kasa gamawa da gasken.”

Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e ranta duk ba dad’i da yanayin y’ar uwarta ta….
A hankali ta durk’usa ta fara serving abincin cikin mutuwar jiki.
Hudan itama duk jikinta yayi sanyi dan haka tace
“Allah ya bata lafiya”.
A hankali Dad ya d’an juya ya kalle ta sai kuma yace
“Ameen” cike da jin dad’in adduar tata.

Juyawa yayi ya kalli Mommy, gani yayi har yanzu Hudan take kallo, kamar tanaso ta tuna wani abun..
Bai gama fahimtar yanayin ta ba yaga ta d’aga hannunta sannan tayi amfani da yatsar ta manuniya wajen sai da Huda!
Gaba d’aya hankulansu kanta ya koma,
cikin rawar murya kamar ta mai koyan magana sukaji tace
“Aaa-sllam, ttanna kama ddda Aasllm d’Ina”

Ba Dad ba hatta Gwaggo Asabe sai da
gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa!!!
Rabon da Mommy ta kira sunan Aslam, tun kafin ta fad’o daga bene!

Gaba d’aya rawa jikin Dad ya d’auka, a hankali ya sa hannu ya juyo da fuskarta, ya kalli cikin idanunta sannan yace
“Kina so kiga Aslam d’in naki?”
Da sauri ta hau d’aga mishi kai, sai kuma hawaye, shaaarrrr suka zubo mata.

“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!”
Shine abunda Dad ya dinga maimaitawa, cikin kid’ima ya mik’e ya fita yana cewa “su Gwaggwon su tsaya gashi nan zuwa, kar kowa yaje koina.”

Ba ayi minti goma ba sai gashi ya turo k’ofa, rik’e da hannun Aslam Abba yana binsu a baya!
Cikin zumud’i yace “Ga Aslam d’in naki” ya fad’a yana tunkarar ta, yana cewa su Abba “komai yazo k’arshe in shaa Allah, Aslam yau da kanta ta kira sunank.........”
Razananniyar k’arar da ta fasa ce ta hanashi k’arasa maganar tashi, ta kuma rud’a duk wani wanda ke a cikin d’akin!!
Basu ida dawowa haiyyacinsu ba ta kuma sakin wata k’arar! Wadda kusan rabin estate d’in sai da aka ji!.
Cikin tsananin tashin hankali firgici kid’ima da tsoron da ya baiyyana k’arara a kwayar idanunta take nuna Aslam d’in tana kururuwa!

A kid’ime Dad wanda duk ya rud’e ya sake nufota still yana rik’e da hannun Aslam wanda ya sake shiga tsananin tashin hankali da rud’ani don shi Dad ce mishi yayi “yazo Mahaifiyarsa tana nemanshi yau da kanta!” Gashi yanzu kuma ya tarar da haka!….
K’arar da ta sake saki ne ya kid’ima su dan tafi ta ko yaushe! Sai kuma ta saki jiki rigif ta fad’i sumammiya akan gadon…..
Da sauri Aslam wanda idanuwanshi suka kad’a sukai jaa over, ya k’arasa inda take ya hau jijjigata yana kiranta amman bata motsi…….d’ago jajayen idanuwanshi yayi yana kallon Dad.
Gaba d’aya sai Dad d’in yaji tausayin su, su duka ukun ya lullub’e shi..

Abba ne yayi k’arfin halin zuwa inda suke, yad’an kura mata ido kafin ya cewa Gwaggo Asabe “ta mik’o mishi ruwa!”

A hankali yake yayyafa mata ruwan, har sun cire ran zata farka sai kuma sukaga tana motsi da idanunta alamun zata farfad’o….
A hankali Abba yad’an kalli Aslam wanda ke zaune a gefenta ya rankwafa kanta sannan ya kama hannunta gam!! Yana kallon idon da take k’ok’arin bud’ewa, alamun a kag’e yake yaga ta bud’e idanun nata!

Da kyar Abba ya tattaro courage d’in da ya iya cewa Aslam
“Aslam, ko zaka d’an je waje ko? Kar ta farka kuma ya zamana kai d’in zata fara gani.”

Da sauri yace
“No Abba, I think bata gane ni bane ba.”
Sai kuma ya kalli Dad yace “Dad da kanta ai kace ta kirani ko?”

Ganin da Dad yayi Aslam d’in na neman koma musu wani firgitachche ne ya sanya shi kawai cewa
“Kaje wajen tukunna mu gani.”
Jikinshi har wani karkarwa yake yi, sai da Dad ya sake cewa
“I’m so sorry Aslam, ita tace a kiraka but ban san me ya sake faruwa ba kuma, for now just, ka d’an jira a waje ko?”

A hankali ya cika hannun ya mik’e ba tare da ya yarda ya had’a ido da kowa ba ya fice,
Dede nan Dad ya fashe da kuka, gaba d’aya sai hankalin su Abba ya sake tashi, saboda abune wanda basu saba gani ba!
Don haka duk sai suka hau bashi hak’uri suna tausar shi, tare da adduar in shaa Allah Allah zai bata lafiya soon…

A b’angaren Dad shi kuma Aslam yake ji, da ya sani da bai yi saurin kiranshiba, gaba d’aya duk sai yaji ya tsani kanshi…..
Da kyar suka samu ya tsaida kukan ya k’arasa gurin Mommy wadda ta farka yanzun tanata faman dube dube a mugun tsorace alamun neman tsari take daga sake ganin Aslam d’in.
Chapter 5 · 0% Book details