← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 70

Sashe 27

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata iya rashin kunya ba amman bata san lokacin data tak’ark’are ta zabgawa Aslam wata uwar harara sannan ta murguda mishi baki ba!
A tunanin ta su Abba yake kallo dan direction d’insu taga yana kalla
amma abunda bata sani ba shine duk abunda take yi yana kallonta ta gefen idonshi.
Tunda yake a rayuwarshi bai tab’a ganin harara da murgud’a bakin da yayi matuk’ar burgeshi da bashi dariya irin wannan ba, hakan ya sanya wani sassanyan murmushin da ya dad’e bai yi ba wanzuwa akan kyakkyawar fuskarshi, wanda har sai da Hudan taji sautin murmushin tayi saurin juyowa tana kallonshi amman ga mamakinta sai taga still su Abba yaketa kallo waenda suka tsaye a setin su..
Gani tayi kamar Madu yana magana da fad’a fad’a!
Cikin takaici ta juyo tana kallon Aslam a ranta tana aiyyana “wato dan yaga ana fad’a shine yake murmushi, lallema wannan mutumin!.”

A chan wajen su Madu kuwa abu bai yi dad’i ba!
Dan tun farko da Madu ya tambayi Abba “dalilin da yasa ya d’auko Hudan lokaci guda haka?”
Abba ya k’ule!
A ganinsa dan mai yasa Madu zai yi mishi tambayar ‘dalilin d’aukar y’ar sa da yayi’ bayan shekaru da dama da yayi ba tare da ita ba!.

Daga k’arshe dai, Abba tafiya yayi ya bar wajen dan bayason yayi musu rashin kunya.

Daddy ne ya tabbatar musu da “sunje har unguwar da Hudan ta taso kuma sunji irin zaman da Huda tayi a gidan Baba, wajen mutane bakwai suka tambaya amman duk maganarsu d’aya ce! Ba abunda basu saniba a halin yanzu na irin zaman da Hudan tayi na azaba a hannun mutumin nan, har k’usar da Ja’afar ya buga mata a ciki suna da labari!”

Yace musu
“Tun jiya suke ta faman lallab’a Abba, da kyar suka samu ya hak’ura amma daa cewa yayi sai ya kulle Usman kuma yayi shariah da su!”

Daga k’arshe yace musu
“Dan haka, ko kotun da Madu yake ik’irarin zai je sai dai ya kulle kanshi da kanshi dan wannan dalili kad’ai ya isa a barma Abba custody d’in Huda!.”
Yana gama fadin haka shima yayi musu sallama cikin girmamawa ya wuce ya koma mota Auwal ya ja suka yi gaba suka barsu a wajen, daman su su Abba sun dad’e da wucewa.

Tunda suka shigo gidan Huda take bin had’add’en mansion d’in mai hawa biyu da kallo!
Har Aslam ya gama parking bata sani ba, sai da yace
“Na bud’e lock d’in, ki fita sai kin fi jin dad’in kallon!”

Tukunna ta dawo hankalinta, gaba d’aya kuma sai kunya ta lullub’eta.

A hankali tasa hannu ta bud’e ta fito, still mutane waenda suka kwashe kaya daga chan gidan sunata kai kawo, da alamun basu gama jeran ba, dan gashi har sets d’in kujeru wasu ba a shishshigar ba.
K’ofar shiga gidan biyu ne manya manya!
Kamar yadda Dad ya fad’a gidan wajen zaman mutum uku ne ma amma k’ofar farko ta gefen dama yafi girma dan wajen d’akuna sha biyar ne da faluka bakwai (shine mutum biyu zasu iya using dan hatta kitchen biyu ne)
Sai d’ayar k’ofar gefen hagu ta d’an gefe kad’an na d’auke da 7 bedrooms da 4 parlourns.

Mai girman Abba ya d’auka
Daddy kuma ya nufi d’ayar k’ofar (side d’in mutum d’aya wanda bai kai na Abba ba).

Suna shiga Hudan ta kusan daskarewa…
Dukda gidan chan estate d’in shima yana da double height ceiling amman ko rabin wannan bai kai ba, ga wata mahaukaciyar chandelier da tunda take bata tab’a tunanin akwai irinta ba, wasu irin kwayayene da suke k’ok’arin makantar da ita tsabar haske a gidan!
Waiting parlour yana a ta gefe a cikin wani d’an glass door
kafin ka k’arasa shigowa makeken main parlourn k’asa wanda girman parlourn zai iya cin set d’in manya manyan kujeru 6 ko bakwai!
Gefen dining daban, sai
wata had’add’iyar matattakalar bene doguwa da zata kaika sama.
K’aramin Kitchen d’in na ata gefen waiting parlour kana iya hango cikin shi dan bangon half ne bai kai har chan sama ba
Main kitchen d’in kuma yana ta gefen dining
Amman shi rufaffiyar k’ofa babba gareshi.
Akwai wasu k’ofofin still a cikin parlourn wanda take da tabbacin d’akuna ne.

Sama suka yi gaba d’ayan su,
Parlour ne nan ma biyu
d’aya a gefen dama d’aya a hagu masu masifar kyau, dukda basu kai na k’asan girma ba saboda double height ceiling d’in da aka yanka ya cinye kusan 1/3 d’in saman amman suma sun had’u sosai ba a magana!
pop kam kamar ka kirashi ya amsa ta jikin bango ta ceiling hatta k’afar bene shima ba
a barshi ya huta ba.

Wata matattakalar suka sake bi suka hau chaan sama.
Suna hawa suka nufi side d’in su Sudais, d’akunan su da parlourn su yayi matuk’ar burgeta.
Sudais yanata murna Shuraim kuwa miskili bai ce komai ba
Sudais shi a shirmen shi ya d’auka har da Huda, dan haka ya hau tsarawa
‘Za su d’auki d’aki daya ita kuma ta d’auki d’aya, sannan ya cewa Abba “ai da anyi mata nata gadon pink ba kalar blue ba”…’

Dariya dukkansu suka yiwa shirmen shi, kafin Abba yace “a’a ita nata d’akin daban ne bara in kaita in dawo ko?”
Yana shirin fita yaji Shuraim yace
“Abba yaushe Ummin zata dawo?
Gramma tace za kaje ka d’auko ta”

A lokaci d’aya duk suka d’auke wuta..
Gaba d’aya duk sai Hudan taji ba dad’i, yadda taga Abba ya had’e rai ne yasa ta kasa cewa komai
“Bana son yawan tambaya!”
shine abunda yace daga nan ya fice daga d’akin.

Ganin haka yasa itama Hudan tayi musu sai anjima ta fice..
Tanata kallon parlourn nasu har ta fita, ta jaa musu k’ofa ta rufe.

Sai a sannan Abba yace “tazo suje ya kaita d’akinta” yana mai kama hannunta.
A gefen parlourn da suke a ciki suka shiga wani dogon corridor, k’ofar tana achan k’arshe suna isa ya sa hannu ya zura key ya murza k’ofar ta bud’u! Sanna ya jaa hannunta suka shige ciki.

Set d’in kujeru biyu ne
Peach da black, sai wani d’an k’aramin dining mai mugun kayau mai d’auke da kujeru biyu a gefe, da wata had’add’iyar tv babba mai curve.

Wucewa sukayi suka shiga bedroom a nan ta sake shiga mamaki, gadon nata pink ne mai rumfa da net a jiki (princess tent) ga wasu had’add’un resting da coffee chairs guda bibbbiyu a kusa da tvn bedroom d’in, fad’ar had’uwar d’akin kawai sai wanda ya gani! Kawai.

Still toilet d’inta ya nufa da ita don ya nuna mata…
Ta closet suka bi kafin su isa cikin toilet d’in
A nan kuwa ta saki baki, wajen wanka har uku shower da wani had’add’en jacuzzi, sai kuma wani makeken bathtub da mutum hud’u ma za su iya shiga su kwanta kamar gado
da
Showers a jikinshi ta ko ina.
Ba abunda yafi bata mamaki irin wutan pop da take gani na sama, da taga yana ratsowa ta k’asan toilet d’in toilet d’in ta ko wanne angle.

Bata gana dawowa dede ba ,
taji Abba yana cewa
“Duk abunda bai yi miki ba ki fad’a sai a chanja! Munata sauri ba a samu anyi komai a nutse ba, so if you need anything just say it sai a chanja miki ko a siyo, an d’an zab’a miki kad’an jiya
kayan suna mota mostly abaya ne da shoes da sauran y’an abubuwa, zan kawo miki tab zuwa anjima, sai kiyi shopping duk abunda kike buk’ata, in kuma a furnishing akwai abunda kikeso ki fad’a shima sai a kawo.”

Ita dai mamakine ma ya hanata yin magana, wai
A nan d’in amman still ana tambayanta ko akwai wani abun da takeso a kawo!

Girgiza kai kawai tayi, kafin tace
“Abba na gode komai yayi Allah ya k’ara Arzik’i. “

A hankali ya dafa kanta yana mai jin tsananin kaunar y’ar tashi tana ratsa ko Ina na jikinshi sannan ga tsananin tausayinta da ya hanashi sukuni!
Ji yake kamar yaje ya kama Usman yayita dukanshi har sai yaga baya numfashi tukunna ya kyaleshi!
Jiya yanda yaga rana haka yaga dare tsabar bak’in ciki…
Jin yadda zuciyarshi ta fara tafarfasa ne yasa ya kawar da tunanin yace
“Ki huta bara a kawo miki tab d’in da kayan, anyi order abinci shima na san kafin ki gama freshining up ya zama ready sai ki sauk’o muci ko?”

D’aga mishi kai kawai tayi ta kasa d’ago kanta, saboda kwallar da ta tarar mata!
Dan
tana ganin inda aka kawota a matsayin mallakinta Mama ce kawai ta fad’o mata……

A tare suka fito daga toilet d’in suka shigo d’aki.

Ganin Abba yana shirin fita yasa tunanin ta ya katse tayi saurin cewa
“Abba”

Juyowa yayi yana kallon ta.
A hankali ta k’arasa wajen da yake sanna tace
“Dan Allah Mama, mun yi waya da Sakina tace min Maman tana asibiti tun shekaran jiya”ta k’are maganan hawaye na zubowa daga idanunta.

A hankali ya kama hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace
“Zan kaiki wajenta anjima da daddare.
Ki daina kuka”
Da sauri tasa tafin hannunta tana share hawayen duka biyu.

Kallonta yayi tukunna yaci gaba
“Amman idan kinje, inaso ki yi promising d’ina zaki dawo, 30 minutes kawai za kiyi, zan
jiraki a mota!
Ku gaisa ki dubata daganan kice musu kina zuwa, in
kin fito sai mu dawo.
And karkice musu ni na kawoki”.

Da sauri ta d’ago ta kalleshi kafin tace
“To ai kamar na yaudaresu ne idan nayi hakan, kuma Mama ba zata ji dad’i ba.”

Mik’ewa yayi kafin yace
“Shine ni kuma zaki yaudareni ki tafi kik’i dawowa ko?”

Kuka ta fashe da shi….saboda daman ta san ko da ace ta yarda zata dawo d’in su Mama ba za su barta ba!.
Chapter 27 · 0% Book details