← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 70

Sashe 59

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsannnin fushi ya tunkarota kamar wanda zai rufe ta da duka!
Dasauri Arshaad wanda shigowar shi kenan yanzun ya shiga gaban Mammy ya tsaya Hajiya Binta kuma taci gaba ta k’ok’arin hana Dad d’in k’arasawa inda Mammyn take!

Dukkannin k’arfin da Allah yayi mata tayi amfani dashi wajen ingije Arshaad d’in sannan kafin yayi nasarar tsaidata ta tafi gaban Dad ta tsaya! Tana mai jin wani tuk’uk’in bak’in ciki yana taso mata,
babu abunda idan ta tuna yake k’ona mata rai irin yanda taga Daddy yana ziryar zuwa wajen Adama last zuwanshi da yayi har kusan kuka taga yayi daga nan ma yace ‘ba zai iya sake ganinta a haka ba’
Tun daga ranar kuwa idan bai kirata sau d’aya ba tou zai kira sau biyu!
Amman ita ko lek’enta ko waya Dad bai tab’a yi yace a bata ba, ita tana chan tana tunanin sa ashe shi yana nan Aisha ta d’auke masa hankali!
Kalli fa sarai ya san ta dawo amman ko lek’enta bai yi ba kuma suna cikin gida d’aya, sai yanzu dan rashin kunya da tsaurin ido ya buk’aci ganinta
kuma ko alamar tambayarta ya take bai yi ba instead
ya hau wani tsattsare ido yana hucin banza..
Waennan takaicin ne suka sanya ta kasa cewa komai kawai ta zube a wajen ta fashe da wani mugun kukan bak’in ciki.

Cikin son kawar da lamarin Arshaad yace “Dad, dan Allah ka bar maganar nan, na fad’a maka ba komai fa”.

Banza Dad yayi da shi kawai ya juya ya fice! Yaso ace Mammy tayi mishi wani shirmen yau wallahi da sai ya yi mata abunda bata tab’a tsammani ba! Ya san at least zai samu peace of mind at last.

Yana fita Mammy ta mik’e!
Tunda take a rayuwar ta bata tab’a jin kishi da takaici da tashin hankali da bak’in ciki irin na yau ba!
Ta rasa dalili amma ko y’ar kissar da ta saba yiwa y’ay’an nata da Dad d’in ta kasa kuma bata jin zata iya, babu abunda take so kuma take buri irin taga ta b’atawa Dad rai ko ta samu zuciyarta ta d’anyi sanyi.
Tayi imani yanzu haka wajen Aisha zai tafi yaje ya ganta yad’an samu nutsuwa hankalinshi ya d’an kwanta alhalin ita kuma gashi ya k’unsa mata bak’in cikin da bata jin zata iya mantawa da shi har abada!
Taya zai yi mata haka?
Taya zai banzantar da ita har haka saboda Allah kamar
wata dabba?
‘Inaaa!! Ba zai yiu ba Wallahi’
Shine abunda ta fad’a ta gyara tsayuwarta tana k’ok’arin yin hanyar waje…..

Da sauri Hajiya Binta ta tareta tace
“Meye haka ne wai Mammy?
Ba a isa a fad’a miki kiji bane?
Ina za ki ji yanzun?”

Cikin kukan Mammy tace
“Kina ganin fa abubuwan da Yahaya yake yi mini
Ya gama b’ata min rai ya fice ya tafi wajen uwar gidan shi ya bar ni ni anan zuciyata ta kama da wuta kenan ko me?
Ki cikani kawai, wallahi bai isa yayi farin ciki ba, ba inda zai je yau, kullle k’ofar gidan nan zan yi sai dai mu kashe juna ni da shi a cikin gidan nan!”

Da sauri Arshaad ya matso kusa da su ya rik’eta, wani
tsananin takaicin sa take ji hakan yasa ta juyo da sauri ta kifa masa Mari! Sai kuma ta fashe da kuka, cikin kukan
tace
“Ai kaima baka kishina
Arshaad, a tunanina ko Hudan y’ar gwal ce wallahi ba za ka so auren ta b.
Taya za ka had’ani da ita mu zama surukai!?
Ko kasan cin mutuncin nan da aka yi min shine abu mafi muni a rayuwata?.
Na fad’a na k’ara fad’a yanzu ma zan maimaita maka
‘Wallahi idan ka aureta sai na tsine maka!’.”

Arshaad bai san lokacin da ya tsugunna a wajen ba ya fashe da wani mugun kuka.

Cikin b’acin rai da kafiya Mammy tace
“Kuma ko event d’in yau da suka gaiyyaceka ban yarda ka je ba!
In kaje kuma wallahi Allah ya isa ban yafe ba!
Zan ga wa zaka zab’a tsakanin ni da ita.”

Da sauri ya mik’e yace
“Haba Mammy ya kike so inyi ne?
Ki tsaya ki saurareni kuma kin k’i..
Dad ne ya nema min aurenta Abba kuma ya bani,
idan nayi miki biyayya
su kuma bijire musu kike so in yi?”

Da sauri cikin katsesu Hajiya Binta tace
“Rukayya ban tab’a tunanin baki da hankali ba sai yau wallahi!
Ni, na fad’a miki!
Mahaifiyarmu, itama ta fad’a miki! Amma ba za ki ji ba?
Waye a cikinmu zai fad’a miki abunda zai cutar da ke?
Munce kiyi hak’uri ko?
Waennan irin y’an iskan aljanu masu shegan taurin kai kika kwaso a cell d’in ne wai?”

In banda gunjin kuka babu abunda Mammy take yi.

Cikin son su kad’aita iyaka su biyu dan ta samu damar lallashinta da fahimtar da ita Hajiya Binta ta cewa Arshaad “wuce ka tafi ka shirya ku je ku yi event d’in, idan ka dawo sai mu k’arasa”

Ai kuwa Mammy na jin haka ta tafi da gudu hanyar k’ofar fita ta tsaya tayi stretching hannunwanta sideways ta kare k’ofar tace “wallahi idan ka fita sai na tsine maka!!”

Da sauri Hajiya Binta tazo ta kama hannun tana k’ok’arin janyeta tana cewa “Arshaad zo ka wuce” a ranta tana aiyyanawa
‘Tabbas akwai abu a kan Mammy’
“Zo ka wuce nace kar ka bari tayi maka spoiling day d’inka!”
Hajiya Binta ta sake maimaitawa ganin Arshaad d’in ya k’ame a waje d’aya abun tausayi.

A hankali ya k’araso ya shiga lallab’ata, Hajiya Binta itama tana yi, amman fur!! Mammy ta yi kane kane a hanyar tana ta faman maimaita kalma d’aya
‘Idan ka fita sai na tsine maka!!’

Basu ji lokacin da akai sliding k’ofar aka shigowa ba sai dai
kawai suka ga an juyo da Mammy an wanke ta da mari!
Diff!! haka parlourn yayi tsit!
Cikin b’acin rai Maman Mammyn tace
“Yi maza kaje ga Aaima chan driver ya bata kayan da zaka saka ta kawo.
Jeka ka shirya yanzun nan za muzo mu rakaka.”

Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo yace
“Tace fa In na fita sai ta tsi..”
Cikin katseshi Maman Mammyn tace
“Nace ka fita ko!
Ta tsine makan in gani.”
A hankali yad’an kalli Mammyn yaga ta d’auke kai daga kallonshi, cikin nutsuwa yayi sliding door d’in ya bud’e ya fice, yana mai share ragowar kwallar dake kwance akan fuskarshi.

Yana fita ta fashe da kuka, cikin kukan tace
“Da wanne kuke so inji ne wai?
Ya kuke son inyi?
Wallahi ko sunan Yarinyar bana so a kira!
Ji nake yi kamar zan mutu, ku
duba fa kuga yanda yake kuka shab’e shab’e dan kawai nace ba zai aureta ba!
Idan ya aureta kuma ya kuke tunani??”

Hugging d’inta Mahaifiyar tata tayi tana d’an bubbuga bayanta…
Sai da ta tabbatar tayi shiru tukun cikin sigar lallashi tace
“Kiyi hak’uri Rukayya,
ke fa da kanki kikace Mijinki yana share ki! Ki duba fa ko wajen ki baya zuwa kuma da kika dawo bai nemeki ba, ko ya yi miki magana bayaga yanzun?”

Cikin sheshshekar kuka Mammy ta hau girgiza kai alamun ‘a’a’.
Ajiyar zuciya Maman nata ta sauk’e kafin tace
“Kinga ko!
Wannan ma kad’ai abu ne wanda ya kamata a tsaya a duba da kyau.
Yanda kikace Matar nan tasa ta warke, da kuma dalilin da ya sanya yake ta faman jin haushin ki wanda bamu san daliliba
yanzu shine abun a tsaya a duba a gyara bawai wannan k’aramin alhakin ba.”

Da sauri Mammy tace
“Wallahi Hajiya Hudan ba k’aramin alhaki bace ba!
Ki dubafa ki ga tun daga ranar data shigo estate d’innan nake cikin tashin hankali..”

Cikin d’an b’acin rai Maman nata tace
“To yanzu ya za ki yi?
Kinga fa wannan abun da muka san za kiyi wallahi shiyasa muka k’i mu fad’a miki maganar auren tun kina cell!
Ki tsaya ki danne zuciyarki yanda kika saba, ki fara gano matsalar da ta shiga tsakaninki da Mijinki a samu a gyara a shawo kanshi in yaso daga baya sai kiyi yadda kikeso
Amman yanzu idan kikayi yunk’urin hana auren nan, wallahi kowa bak’in ki zai gani, kuma hatta Arshaad d’in dakike ta haukar ‘kar Hudan ta janye miki shi’
Ke ce da kanki gashi kike k’ok’arin kawo matsala a tsakaninku da kanki gashi kina turashi away from you
dan
Wallahi kinji na rantse miki yadda Arshaad ya kwallafa rai akan Yarinyar nan muddin kika sake kika zama silar da ya rasata to kuwa ba zai tab’a yafe miki ba!
Kuma sai kin yi dana sani.
Ki bari ayi auren sai mu san abunyi. Yanzu kar ki fito b’aro b’aro a matsayin wadda ta hanashi aurent....”

Cikin katseta Mammy tace
“Ki kwantar da hankalinki ni na san ta inda zan b’ullo mishi yana jin maganata ai yana yi min biyayya.
Matsalar da za a samu shine
In har na bari ya aureta!
D’azu fa muka gama waya da Adama wai ashe ma k’asar za su bari gaba d’aya!
Haba dan Allah taya ba zan yi kuka ba? D’ana kwalli d’aya a duniya zata d’auke shi su tafi sai ta gama mallakeshi tukun a dawo min da fanko? Dama yanzun ma ya aka k’are?? Ballantana kuma yaje yayi spending years da ita!
Ni kawai ku kyaleni dan girman Allah, dan na tabbatar ranar da Arshaad ya aureta to ni kuma zan iya barin duniyar nan a ranar.”
Ta k’arashe tana sake fashewa da wani sabon kuka.

Cikin fad’a Maman nata tace
“Baki rabu da su Adaman nan ba har yanzu ko? Na ce miki ki tsaya ku fara shiryawa da Mijinki ki fara gano matsalar da ta shig..........”

Da sauri Mammy tace
“Matsalata da Dad, Aisha ce!
Na rigada na sani.
Ki bari kawai in fara kashe wannan boss d’in after that idan na tashi bi ta kan Aisha wallahi duk wanda ya ce zai shiga tsakani sai na had’a da shi”.

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
52

Cikin fad’a Maman nata tace
“Baki rabu da su Adaman nan ba har yanzu ko? Na ce miki ki tsaya ku fara shiryawa da Mijinki ki fara gano matsalar da ta shig..........”
Chapter 59 · 0% Book details