← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 70

Sashe 55

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“Ok, Granpa.”
Sannan ya zaro wayar shi ya hau kiran Arshaad…
Har ta tsinke ba a d’auka ba, ya sake kira nan ma ba a d’auka ba, zai kira a karo na uku Granpa ya d’aga mishi hannu, yace
“Leave him”
Daga nan ya fara magana
“2 months ago!
Adama, Rukayya da Zainab
Sun yi wa wannan family d’in babban laifi wanda hakan ya kai ni ga yanke hukunci a garesu mai tsauri!

Dalilin tara ku a nan da nayi shine
Inaso In jaa muku kunne akan
‘magana ta riga ta wuce!’.
Mazajen su Adama da ita Ummi basa kusa
dan haka kai Yahaya kai ne zaka sanar da sak’ona garesu!
Banaso ko da wasa inji makamanciyar maganar nan ta sake tasowa!
Sun yi laifi an hukuntasu magana ta mutu!!
Duk kuma wanda ya k’etare umarnina ko a fuska ya nuna musu wani abun yi zai
gamu da fushina tabbas.
Su Yusuf kar suga wai basa tare da ni, muddin suka yi wani abun da bai kamata ba a matayensu to tabbas zan yanke musu hukunci mai tsanani!
Ka gaya musu hakan.

Ku kuma”
Ya juya kan su Mammy
“Wannan hukuncin da na yanke muku kuka yi going through for the past 2 months ba komai bane!
Ku k’irga azabar sau ashirin
tou tabbas ita zaku fuskanta muddin kuka bari naji wata matsala daga gareku.

Sai magana ta biyu!
Duk da Muhammad ya b’ata min rai a yanzu, hakan ba zai
saka In chanja abunda na shirya ba…
A kwanaki yayi laifi
wanda ya kai ni ga rage mishi matsayi
Auwal ma haka.
Tou yanzu Alhamdulillah naga progress da ci gaba a tare da su, dan haka ranar Monday
Auwal ba dan halin ubansa ba sai dan kwazon shi zai koma
assistant md
tunda Aslam ne md yanzu
shi kuma Muhammad ya koma matsayinshi, treasurer.

In shaa Allah
Nan da shekara d’aya za a fidda wanda ya chanchanci a malllakawa MT gaba d’aya na uk da na Abuja da na nan Kano, a tsakanin su uku.

Yahaya In Zainab ta warke ka mik’a ta gidan Mijinta inda ya k’aura ya koma, amman yanzu ka fara kai Adama tukunna ta samu ta huta, Mammy kema ki wuce d’akinki.
Allah ya bamu alheri.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e, ya shige d’akin shi.

Shiruu, d’akin ya d’auka.
Da kyar Mammmy ta iya mik’ewa dan jikinta ba energy
ta isa inda Mommy take tana zuwa kawai ta fad’a jikinta ta fashe da kuka tana cewa
“Alhamdulillah!!
Na ji dad’in ganinki a haka y’ar uwa ta, Alhamdulillah Alhamdulillah”
Mom ita ma rarrafawa
tayi inda suke, ba yabo ba fallasa ta d’an rungume Mommy kafin tace
“Alhamdulillah,
Allah ya k’ara mike lafiya”

Ba wadda Dad ya k’urawa ido irin Mammy!
A hankali yace musu “ku taso mu tafi”
kawai, ya mike.
Aaima ce taje ta kansu ta tayasu mik’ewa, dan ko kuzarin kirki babu a jikinsu!
Duk sun yi bak’i sun rame sun kod’e sun k’anjame!
Banda kuka ba abunda take yi.

Aslam tare suka tafi da Mommy kamar yanda suka zo tare.
Dad kuwa sai da ya fara kai Mammy gida ita da Aaima
tukunna ya wuce da Mom dan kaita sabon gidan da su Abba suka koma.

Side d’in Daddy ya shiga tana biye da shi a baya..
A zaune suka samu Daddyn a parlourn k’asa yana shan coffee da suit d’inshi a jikinshi ko takalmi bai cire ba da alama yanzu ma ya dawo daga aiki
dan ga suitcase d’inshi a gefe.
Sallamar Dad ce ta jawo hankalinshi gare su, mik’ewa
yayi yana d’an murmushi da muryarshi dake nuni da a matuk’ar gajiye yake yace
“Yaya ina wuni, ai da ka kirani na zo..”
Muryarshi ce ta mak’ale sakamokon ganin Mom wadda ta fito yanzu daga bayan Yayan nashi.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, yana kallanta..
Rabonshi da ita wata d’aya kenan, tun last zuwanshi da yaje tayi ta kuka ya yanke shawarar sai dai ya kira police d’in ya had’asu dan ba zai iya jurar ganinta a wannan halin ba!…
Muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, a hankali yaji tace
“Ina wuni”
Jinjina kai yayi kafin a hankali yace
“Alhamdulillah”
Sannan ya koma ya zauna ya shiga gaida Dad wanda ya nemi waje shima ya zauna.

A k’asa kan kafet Mom ta zauna tana ta sun sunkui da kai!
Tausayinta fal zuciyar Mijinta
dan ya hango tsantsar nadama da shiryuwa a matar tashi, daman chan shi ya san sharrin shaid’an ne!
Ba abunda yafi d’aga mishi hankali irin bak’i da lalacewar da tayi, in shaa Allah nan da 3 days zai shirya musu fita suje ayi mata checkup…..

Muryar Dad ce ta katseshi
jin yana cewa
“Abba ya dawo kuwa??
Inason ganinku ne tare.”

“Eh to i don’t think so but bara in kirashi”
Daddyn ya fad’a yana mai zaro wayarshi daga aljihun wandonsa.........

Da kyar ya iya kai wa 2 yau a waje, duk da tarin aiyukan da suke a kanshi haka nan ya baro su birjiki! Ya dawo gida.
Yana d’aki shi kad’ai sallah kawai yake iya fita yayi…
Anya bai yi gaggawar aurar da Hudan ba kuwa?
Kar yaje garin gudun b’atawa su Yaya da Daddy rai ya cuci kanshi fa!
He just knew her
amman har ya d’auketa d’ungum ya bama wani
kuma bama a Kano kusa da shi da anytime yaso zai je ya ganta za su zauna ba!
A Uk za su zauna, sai
after 4 ko ma 5 years tukunna za su dawo!.
Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya
A ranshi ya raya zai nemi Alfarmar Arshaad akan su d’an zauna anan gidanshi for some time, ko da ace duniya za tayi mishi kallon the most selfish father ne!!
Tsaki ya jaa tunawa da yayi Arshaad d’in har ya biya mak’udan kud’i na course d’inshi da zai yi da kuma karatun da Hudan zata fara…
Yana wannan tunanin yaji kira ya shigo wayarshi..
D’auka yayi ba tare da ya kalla sunan ba ya amsa ya kara a kunnenshi, sai da Daddy yace
“Abba”
Tukun ya fahimci wanene
dan haka ya gyara zama yace
“Ina wuni, ya aiki?”
Amsawa Daddy yayi daganan yace masa “yazo ya samesu ga Dad ya zo yana son ganinsu”.

“Ok” kawai yace,
sannan ya kashe wayar ya mik’e ya fice jikinshi duk a sanyaye.

Ko mintuna hud’u cikakku bai rufa ba, ya k’arasa parlourn.
Waje ya nema ya zauna
suka sake gaisawa..
Ba tare da b’ata lokaci ba, Dad ya fad’a musu sak’on Granpa!
Shi ababa wallahi har k’asan zuciyarshi yama manta da wata halitta wai ita Ummi!
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, ya koma ya kwantar da kanshi a jikin saman kujerar
ba tare da yace da su komai ba!
Dan in ya cewa Dad zai iya yin abunda Granpa yace a yanzu dai tou gaskiya k’arya yake yi,
sai dai maybe ko in gaba.

Mom ce ta katse mishi tunanin shi ta hanyar cewa
“Abba Ina mai baka hak’uri game da kuskuren da muka aikata maka!
Bisa ga biyewa son zuciyoyinmu, ka yafe mana dan Allah.”

Shi sai a lokacin ma ya gane ita ce a wajen.

Mik’ewa kawai yayi ya cewa su Dad
“Bara inje in sha magani In d’an kwanta kaina yana min ciwo, sai da safe.”
Daga nan kawai ya nufi hanyar fita….
.....inda ace Mom ta san tunzurashi d’in da maganar ta tayi, da ba zata soma ba!
Kawai wani sabon haushin su ne ya sake lullub’e shi..
Hudan is soppose to get married at this age duk wani uba zai so hakan
amman dalilin su ya sanya har yake having second thoughts akan abunda ya san shine farin cikin ta, yakamata ace yana taya ta murna yana sopporting d’inta d’ari bisa d’ari amman because of them gashi har yana son aikata abunda za aganshi kamar selfish,
kuma ya san inba da kyar ba, su Yaya za su iya jin haushin sa wanda hakan abunda bai tab’a
faruwaba ne…

Daddy yana shirin yin magana da sauri Dad ya dakatar dashi ta hanyar d’aga mishi hannu!
Har Abba ya fice ba wanda yace komai.

Yana fita shima Dad d’in ya mik’e yayi musu sallama ya fice.

Mik’ewa Daddy yayi daga inda yake ya koma k’asa wajen Mom. Tun kafin yace wani abun ta fad’a jikinshi ta fashe da kuka tana rok’on shi akan “yayi hak’uri shi da y’an uwanshi, in shaa Allah ba zata sake ba! Sharrin shaid’an ne
dan Allah kar ya dinga kallonta da abun ya taimaka mata ya goge komai a ranshi…”

Lallashinta ya shiga yi yayi hugging d’inta yana jin tausayin ta na sake shiga zuciyarshi..
Da kyar ya samu tayi shiru daganan yace “tazo taje tayi wanka ta huta”
Dan da gani tana buk’atar ta tsaftace jikinta da kuma hutu ba na wasa ba..........

Hatta kujerun personal parlour d’inta na chan sama, sabbi dal Daddy ya saka mata
Bedroom ma ya saka mata sabbin furnitures
duk don ya dan rage mata zafi.

Har k’asa kuwa ta durk’usa ta kama k’afafunshi tayi godiya sannan ta sake bashi hak’uri.
Shi kam Daddy
tausayinta kawai yake ta ji,
yaga duk tayi sanyi ta koma kalar tausayi, sai wani nan nan yake yi da ita....

Ko da Auwal ya dawo bai san da labarin dawowarta ba, gashi kuma ranshi a mugun b’ace yake ga gajiya, dan haka direct side d’inshi ya nufa, yayi wanka yayi sallah ya bi lafiyar gado, da kyar sai da yayi da gaske tukunna hoton Sakina da Ashraff yabar idanuwanshi
sannan ya samu bacci ya d’auke shi.

Auwal yana ajjiye Arshaad ya shiga gida shima.
A mugun gajiye yake dan haka tun a hanyar shiga ya zare suite d’in shi ya rik’eta a hannu
kafin ya fara k’ok’arin zare necktie d’in! Kana ganinshi ka san bacci kawai yake buk’ata.
Ko kallon cikin parlourn bai yi ba ya nufi side d’inshi….

“Ango!!”
Yaji muryar Mammy.
Chapter 55 · 0% Book details