Sashe 42
So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BAYAN WASU Y’AN KWANAKI.
Tun ranar da su Hudan suka koma Nasarawa gra, malaria da mura suka yi mata ram!Bata iya komai hatta karatunta ma Sakina ce ta karb’a take yi.
Gaba d’aya hankalin Abba a tashe yake, kwananta d’aya a asibiti aka sallamosu aka had’o su da nurse wadda zata dinga yi mata allurai da chanjin drip.
Shi da kansa (Abba) yake jinyar ta, da kyar yake yarda yaje yayi bacci amman da sassafe shi da Arshaad ne suke tashinsu a bacci.
Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yanda bata iya cin abinci dan ta samu lost of appetite! A rana sai a girka abinci kala nawa amman da kyar zata iya tsakular d’aya, gaba daya duk ta zabge ta rame tayi wani irin fariii!
Sai dogon hanci wanda ya sake fitowa tubarkalla, idanuwan nan daman ya lafiyar kura sun sake lumshewa kamar na mashaya.
A cikin kwana biyun nan ba Hudan ce kad’ai ta rame ba har Auwal!! Dan kwata kwata Sakina ko a waje ta ganshi to ta bar wajen kenan sai in ya tafi tukun zata koma, k’iyayyar k’iri k’iri take nuna masa babu ji babu gani.
Ranar da aka kwantar da Hudan a asibiti kuwa, da Auwal d’in yaje dubota akai rashin sa’a Sakinar ce a wajen Abba ya d’an fita ita kuma Huda tana bacci dan haka ya samu chance!
Ganin da Sakina tayi abun nashi ba na k’are bane yasa ta fito mishi a Sakinar ta ta wankeshi tass!! Sannan tace
“Ta tsaneshi, ba zata tab’a iya yin rayuwa da mazinaci mak’aryaci kuma mayaudari ba!
Ya fita a harkar ta tun kafin ta sauya mishi….”
To dai tun daga ranar ta samu ya d’an sakar mata mara, dan ita yau kusan sati d’aya ma amman bata saka shi a idontaba.
Abunda bata sani ba ashe rashin lafiya shima yayi na kwana biyu..gaba d’aya duk
ya rame, office kawai yake iya zuwa, Daddy yayi tambayar duniya har ya gaji ya kyaleshi…..
Yau Hudan ta d’an tashi jikin da sauk’i tun safe, dan yau
through out batayi amai ba kuma ta d’an ci abinci ba laifi
Abba sai murna yake yi, don haka yace “idan zata iya tazo suje k’asa suyi dinner da kowa (cikin mutane)”.
Sudais ne ya ruk’o hannunta na dama Abba kuma na hagu, Sakina sai murmushi take yi,
dan ba k’aramin burgeta suke yi ba sai wani lallab’a ta ake yi kamar kwai!
A haka suka sauk’o gwanin ban sha’awa.
Tayi tunanin a nan za suyi dinner d’in
amma sai taga sun nufi side d’in Daddy, Sakina ba dan taso ba ta bisu dan kwata kwata bata son abunda zai had’ata da Auwal, sam!.
A chan suka tarar da Aslam da Arshaad…
Basu samu Daddy a wajen dining d’inba amman an kammala jera komai.
Ba suyi 5 minutes da zama ba, su Daddy suka sauk’o shi da Auwal! Bai yi wata wata ba ya nemi kujerar dake gefen Sakina ya zauna Allah ya taimakeshi babu kowa a wajen.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana jin wata nutsuwa ta musamman….
Sakina kuwa kamar ta tashi haka taji, kawai dai ta san su Abba za su d’an iya fahimtar wani abun shiyasa ta zauna saboda itafa ko a labari bata k’aunar a sako sunanta kusa da na Auwal!
Cikin kulawa aka shiga exchanging greetings..
Sai da aka gama gaggaisawa tukun Daddy yace “sorry i kept you waiting, Auwal ke hunger strike kamar wani baby abincin ma wai sai naje na lallab’ashi tukunna zai yarda yazo yaci”
Murmushi Aslam yayi, Abba kuma yace
“gashi kuwa duk ka rame, what’s wrong with you?”
Yayi maganar referring to Auwal d’in.
“Nothing”
kawai ya iya cewa yana sunkuyar da kanshi k’asa.
Murmushi Abban yayi, dan kamar yad’an gano Auwal d’in amman sai ya basar kawai aka fara cin abinci.
Arshaad ke zaune a kusa da Aslam Abba kuma na ata gefenshi (sun saka shi a tsakiya) Duk su biyun suna lura da yanda yake kallon Hudan wadda ke opposite d’insu akai akai!
Gaba d’aya Arshaad sai yaji ya damu sannan bai ji dad’in hakan da Aslam d’in yake yi ba kwata kwata!
Amman sai yayi ta k’ok’arin kawar da duk wani negative thinking a kanshi.
Ita kanta (Hudan) a takure take, gashi zuciyarta ta hanata sukuni.
Loma biyu kawai Sakina ta iya yi cikin kwanciyar hankali dan tunda Auwal ya fara mata
‘Hi’
‘How are you?’
D’insa taji wani malolo ya tokare mata mak’oshi!
Bata san lokacin da ta ajjiye spoon d’inta da k’arfi ba wanda hakan ya janyo hankalin kowa kansu…
Dariya Abba yayi dan tun d’azu yanata lura da su,
cikin dariyar yace
“Ya takura miki ko?”
Da sauri tace
“Eh wallahi Abbac kace mishi....”
Kasa k’arasawa tayi sakamokon zungurinta da Hudan tayi, k’asa k’asa tace “kinga Daddy fa yanda yake kallonki, ki yi shiru”
Kallon inda Daddyn yake tayi, karaff! Taga itan yake kallo yana d’an murmushi,
gaba d’aya sai kunya ta lullub’eta tayi k’asa da kanta.
Y’ar guntuwar dariya Daddyn yayi kafin yace
“K’arasa mana Sakina…
Ace mishi ya daina takura miki ko?”
Cikin dariyan ya kalli Auwal kafin yace
“Auwal, Allah har a gama cin abincin nan kar inji ta sake kawomin k’arar ka!”
Shi dai Auwal shiru kawai yayi kamar ruwa ya cinye sa..
Arshaad kuwa dariyar mugunta yake yi mishi
a ranshi yace
“Allah mai had’i!”
Don ya tabbata Auwal sai yaci kwal ubanshi a hannun Sakina.
Daddy kuwa kallonsu yake ta yi lokaci zuwa lokaci….tabbas daman ya d’an fahimci akwai abunda yake damun Auwal kuma yake kaishi side d’in Abba! Kenan wannan Yarinyar ce, but yaga kwata kwata Yarinyar bata da interest a kansa shi kuma gashi ya fahimci tsakani da Allah Auwal d’in nasa yake son Yarinyar.
A zuciyar shi ya hau adduar ‘Allah ya karkato da hankalinta ga Auwal d’in a samu yayi aure ya bar wannan tsalle tsallen,
dan tabbas ya hango nutsuwar d’an masa a tareda Yarinyar…….
Har aka kammala, Auwal bai sake yi mata magana ba.
Sai da aka d’an tab’a hira tukunna aka watse.
Arshaad na son ya gana da Hudan amman Abba yayi kane kane!
Har d’aki suka rakasu shi da su Sudais kamar d’azu…
Sakina ce ta kawo musu tofi suka yi sallama suka tafi shi da Aslam.....
Suna shiga d’akin, suka hango wayar Hudan dake kan gado tana kyalli, da sauri Shuraim ya k’arasa yaje ya d’auko dan yanayin tafiyar tata kafin ta isa kiran zai iya tsinkewa, amman dukda hakan kafin ta kai ga amsawa kiran ya tsinke.
Gabanta ne ya fad’i ganin 20 missed calls d’in Mama akan screen d’in, tana shirin kira wani kiran ya sake shigowa….
Tana amsawa taji Maman ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Duk hankalina ya tashi na d’auka jikin naki ne ya motsa.”
Murmushi Hudan tayi tana k’arasa zama a kan gado kafin tace
“Da sauki Alhamdulillah, ai na fad’a miki na warke fa Mama ki daina d’aga hankalinki.”
Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e sannan tace “Gobe zamu zo mu dubaki ni da Ummu in shaa Allah.”
Hudan, cikin d’an zaro ido na murna tana murmushi tace “Na gode kuwa sosai Mama zan ji dad’i, sai kin zo.”
Murmushi itama Maman tayi kafin tace
“take care, kina dai shan maganinki ko? Na sanki da k’in shan magani.”
Cikin yin y’ar dariya Hudan tace
“Maama kin manta Sakina na tare dani.”
Y’ar k’aramar dariya taji itama Maman tayi kafin tace
“Hakane fa, sai mun zo goben in shaa Allah, Hajiya ma tace a gaida ke!”
A hankali Hudan tace
“kiran ki tayi? Kun shirya? Na ga rannan ma tayi miki magana a gida lokacin a gaban kowa.”
Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace
“Kirana tayi takanas Hudan dan taji jikinki da kuma yanda nake” ta k’arashe maganar tana share hawayenta.
Murmushi Hudan tayi itama kwalla ta zubo mata, kafin tace
“Alhamdulillah”
Tana share hawaye sannan tace
“Sai kun zo Mama”
Tana murmushi, itama murmushin tayi sukai sallama ta kashe wayar.
Cike da nishad’i
Abba dake tsaye a kanta yace
“Y’ar gidan Mama”
Cikin yanayin zolaya.
Cikin d’an murmushi tace
“Wai hankalinta ya kasa kwanciya gobe zata zo ta ganni” ta k’arashe maganar cike da zumud’i.
Murmushi Abban yayi sannan yace
“Allah ya kaimu goben” ya shafa kanta tukun ya juya ya fita.
“Sai da safe” Shuraim yayi mata, Sudais ma haka, yayi pecking cheek d’inta sannan ya fita.
A hankali ta kwanta ta lumshe idanunta ahaka Sakina ta shigo ta sameta. Nan take fad’a mata good news d’in!
Ta kuwa yi murna, sannan tace “Ai daman lokacin dana ce mata har a asibiti kika kwanta baki ji yanda hankalinta ya tashi ba, daman
na san ba lalle ta iya hak’ura ba, sai tazo.
Allah ya kaimu goben ya kawosu lafiya.”
A hankali Hudan tace “ameen”
tana hamma......
Tun da suka tashi da safe suke expecting d’in su Mama,
har girki suka d’anyi musu dukda rashin k’arfin jikinta
sai shirye shirye suke yi.
Suna cikin setting dining Abba ya shigo, murmushi yayi a ranshi yana yaba irin k’aunar da y’ar tasa take yi wa Maman ta.
Sai da yazo ya dafa kanta tukunna ma ta fahimci ya shigo.
Gaishesa suka yi ya amsa musu cikin kulawa kafin yace
“Suje da Linda (mai girki) ta bata kayan wankinsu da suka tara, masu wanki zasu fara.
Da mamaki yake kallonta, jin tace “Ai su kullum In suka cire kayansu a washing machine suka sakawa su wanke”
Sannan ta k’ara da cewa
“Akwai fa washing machine a toilet din nawa Abba”
Murmushi yayi ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace mata
“Na wanke inners ne wannan dota.
Next time ku tara akwai masu wanki da guga da suke yi, time to time.
Yanzu ku bata kayan ta kai musu sai a goge”
Da ‘to’ suka amsa ya wuce
Sakina ma ta kira Linda suka wuce domin ta bata kayan,
ta bar Huda anan tana ci gaba da setting dining.