← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 70

Sashe 30

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’an k’ura mata ido Sakina tayi….Chaan! Tace
“Yanzu sai yaushe kuma?
Anyways kinga dai 30 minutes ya baki yanzu kuwa kin kusan awa d’aya ma. Ki kunna wayarki kawai
za muyi magana.
Mai yasa kika kashe ko kwacewa akayi?”

A hankali tace
“Charger ne babu.
Amman d’azu na siya a online an kawo har na ma jona Ina so ya cika ne kafin In kunna.”

“Ok za muyi waya muje in rakaki”

Hannun ta Hudan ta ruk’o kafin tace “Sakina kina ganin Mama ba zata ji haushina ba?
Me za kice mata idan kin koma ciki?”

Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e sannan tace
“Haushin ki kam za taji, ba d’aya bama kuwa! Kuma yau Allah yasa ta bar Ummu ta rintsa dan ni ba anan zan kwana ba Baba nake jira yazo ya d’auke ni sai gobe tukun zan dawo. Amman na san yau rikici zata yi tayi, Mama ta zama mai fad’a sosai!.

Maganar da zan fad’a mata kuwa, gaskiya ce zan fad’a kawai ba wani abun ba.”

Rau rau Huda tayi da idanu.

A hankali Sakina tayi murmushi tace
“Kije ku tafi, tabbas Mama za taji ba dad’i amman kije kawai kin ji?”

A hankali ta share hawayenta ta matso ta rungume Sakina,
dai dai nan Baban su Sakina shima ya k’araso wajen.
Abba ma haka wanda tun fitowarta ya gansu ganin da yayi kamar bata ganshiba ne yasa ya fito ya k’araso inda suke tsaye.

Kusan a tare suka k’araso wajen, Baban su Sakina yana ganinshi ya gane shi ne baban Hudan dan haka yayi saurin mik’a masa hannu
(wani aiki ya tab’a had’ashi da Abban kuma ya samu alkhairi sosai!
Har gidansa ma sukaje suka yi mishi godiya. Yanata yaba alkhairin mutumin, shiyasa
da Arshaad ya rok’esa akan ‘ya rufa mishi asiri kar ya fad’awa kowa daga family d’in daya fito yet saboda gudun matsala’
Shi kuma ya yarda yayi shiru bai fad’a d’in ba
Don yaga sun san mutunci
kuma shi kanshi yana so Hudan ta had’u da Mahaifinta a samu a dedeta komai!
Amma Arshaad yace
baya nan yanzu ya tafi wani aiki kuma akwai issue har yanzu a k’asa, but a hankali a hankali za suyi settling in shaa Allah, komai ya dawo normal .
Shi kanshi a lokacin ya yarda da hakan saboda ya san wani part na case d’in su Madu da family d’in Abban…

To kuma suna k’ok’arin ganin komai ya koma normal d’in
tukun
a samu a daidai sai shi kuma
Aslam yazo yayi musu mai gaba d’aya!)....

Shima Abban kallon sani yake yi masa, sai da Baban su Sakinan ya tuna mishi ‘ya tab’a basu wani contract kwanakin baya’ Tukunna Abba ya tuna shi, Hudan kuma ta gabatar masa dashi a matsayin Baban su Sakina mijin anty d’inta.
Sake gaisawa suka yi sakina itama ta gaidashi cikin girmamawa… kallon Abban take yi tana sake maimaitawa!
Tanaji Ummu tana cewa ‘Baba kishi yake da Abba shiyasa yake yin wasu abubuwan’ tabbas kam dole Baba yayi kishi da wannan mutumin!
Dukda cewa shima Baban ba mummuna bane kuma fari ne shima amman ko makaho In ya shafa yaji ya san babu had’i kwata kwata tsakanin Abba da Baba, Abba ya tsere mishi a komai da komai..
Gashi wani abun mamaki ba zaka tab’a cewa ma ya haifi Hudan ba dan kamar wani d’an 33 haka yake, jikinsa san bai
nuna tsufa ba kamar dai Mama,
Ita kam tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin perfect match irin na Abba da Mama ba……

Da kulawa ya amsa gaisuwar tata yana tambayarta “ya school” a hankali tace “muna jiran results ne har yanzu”.

Sun d’an tab’a hira da Baban Sakina daga nan sukayi exchanging numbers suka yiwa juna sallama.

Abba ya lura da yadda Huda ta shak’u sosai da Sakina dan
har suka isa mota tana waigawa tana waving d’inta kamar wata Yarinya
itama Sakinan haka dan ita kam har sai da taga fitarsu tukunna suka shige ciki don su d’auko kayanta.

Tun kafin Mama ta gama gaisawa da Babansu Sakinan ta san yanda tayi ta zulle ta gudu, daman itama k’arfin haline kawai zata yi wajen yiwa Maman bayani
kuma yanzu ga mafita Allah ya kawo mata.

Tunda suka kama hanya Hudan take tunanin abunda tayi sam bata kyauta ba! But ya kamata shima Mahaifinta ta d’an kwantar mishi da hankali tunda ga halin da yake ciki da family d’inshi….

Ya lura da ita sosai, don k’arshema har da y’ar kwalla yaga tana gogewa. Shiru yayi mata kawai…..har sun kama hanyar gida sai kuma ya juya yayi hanyar dominos.
Suna zuwa yayi parking ya shiga bai dad’e ba ya fito da Ledoji nik’i nik’i
dangin su ice cream da milk shake da pizza…..

A baya ya saka ya zagayo ya zauna yace “gashi ita da su Shuraim, in kuma sun yi bacci by the time da suka gidan sai ta sa musu nasu a fridge.”

Godiya tayi masa, daga nan
suka kama hanya, yana ta d’an
janta da hira kad’an kad’an, yace if “she’s bored gobe ta shirya Arshaad ya kaisu munjibir park”
Kamat zata ce masa a’a sai kuma tace “to” kawai.
A haka suka karasa gida.

Shi ya taya ta d’aukar kayan sai da suka isa chan sama tukunna ya ajjiye a parlour yayi hanyar d’akin shi bayan ya rarrage fitulu yana ce mata “ta duba su ta shafa musu addua idan sun yi baccin, itama tayi kafin ta kwanta.”

Kamar yanda tayi tunani, ko da taje su Shuraim d’in har sun yi bacci dan haka tasa a fridge d’in sama dan ita tsoro take ji ba zata iya sauk’a k’asa ba, a
Iyaka saman ma itakam duk a tsorace take!.
Tana jera kayan tana mamakin uban yawansu….
Ice cream d’aya ta Iya d’auka, dan gaba d’aya bata da laka a jikinta tunanin Mama take tayi..duk jikinta a sanyaye yake, ta san tayi laifi babba a Mama, bata san ma ta ya zata sake facing d’inta ba!
Cokali biyu kawai ta iya yiwa ice cream d’in duk dad’in shi amman sai ta kasa sha, da kyar ma ta iya had’iye biyun a mak’oshinta
don haka ta rufe ta saka a d’an mitsitsin fridge d’in gefen gadonta ta mik’e tayi wanka.
Tana fitowa ta rarumo waya ta danna kiran Sakina
Ita kuwa Sakina tunda suka fita tana zama a mota ta kashe wayarta ma gaba d’aya
dan wallahi ta gaji dayawa tana buk’atar isheshen bacci, in yaso duk fad’an da za ayi mata ayishi gobe!.
Shiyasa Hudan tayita kiranta amma taji a kashe…. daga k’arshe ta hak’ura tayi cilli da wayar, ta kwanta, gaba d’aya ranta ba dad’i, bata san ya Mama zata kwana ba yau! Kuka ta fara yi, ta dad’e tanayi kuma daga baya ta share hawayenta….

Wayarta taji tana k’ara dan haka ta lallab’a ta d’auka, gabanta ne yayi wani irin mugun fad’uwa ganin sunan Ummu, sai da wayar ta kusan tsinkewa tukunna ta iya d’auka
tana karawa a kunnenta Ummu tace “kina gida ne?”
“Eh” ta bata amsa.
“Waye ya mayar da ke?”
“Abba” ta sake bata amsa.
“Daman tare kuka zo?”
“Eh!”

“Tam! Sai da safe.”

Hudan tana shirin yin magana taji kit!! A yanke kiran.

A daren ta kira layin Ummu yafi sau ashirin amman bata d’aga ba!
K’arshema dena shiga tayi.
Gaba d’aya hankalinta sai ya sake tashi, sai wajajen 2 tukunna ta samu tayi d’an baccin ta rabi da rabi,
kiran sallar farko ta farka.

Tashi tayi tayi Nafila ta jira aka kira tayi sallar Asubah…
Bata kwantaba sai da tayi azkar d’inta ta fara karatu.
Sai bayan gari ya d’anyi haske tukunnna ta d’an iya yin bacci shima nisanshi iya awa d’aya!
Wayar Sakina ta sake gwadawa tana tashi but still a kashe.
Tana zaune taji kamar ana knocking chan waje k’ofar
falo, mik’ewa tayi ta fita taje ta bud’e…
Tana bud’ewa taga ashe ragowar kayantane na jiya
aka kawo/
Cikin girmamawa maid d’in ta gaidata sanann ta hau shigo mata da kayan leda leda.
Godiya Huda tayi mata bayan ta gama, ta juya ta fita.
Ita kuma ta tura k’ofar taja kayan zuwa bedroom.

Tana gama ajjiyewa a closet
ta fito kenan ta zauna akan gado Abba ya shigo cikin jallabiya mai k’aramin hannu rik’e da hannun Sudais wanda shima yake sanye cikin kayan bacci.
Da sauri Sudais d’in yazo ya rungumeta sannan yace
“Abba just told us that you are our big sister, i’m so glad that we’ve a big sister” Ya k’arashe maganar yana sake hugging d’inta.

Murmushi tayi itama tayi hugging nashi back kafin tace
“I’m so glad to have cute brothers too.”

Da sauri ya d’ago yace “Monday idan anje school zan gayawa Ashraf da Sultan da Kareem nima nayi big sister, dariya suke yi min kullum suna tsokanata!
Yanzu kema kice Abba ya kaiki school d’inmu a sakaki a ss2 dan Allah so that i can come and see you during break time just like they do, and also....”
Abba ne ya dafa kanshi yana dariya, kafin yace
“Sudais wai har yanzu baka san ka girma ba?
Ya kamata fa ace ka daina wannan shirmen
And
Big sis ta gama secondary ai,,kar kayi mata adduar komawa baya mana. School d’in su Aaima zata tafi, ko?”
Yayi maganar yana kallonta yana murmushi.
D’an zamowa tayi ta gaidashi,
a hankali ya amsa yana mai dafa kanta yana kallon idonta da tashi d’aya ya fahimci taci kuka.

A kan Kujerar gefen gadon ya zauna yana kallonta kafin yace
“Me ya saki kuka? Mama kike son sake gani?”.
A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace “ina jin ba dad’i ne akan abunda nayi mata jiya, Ummu ta kirani nace mata mun dawo, inaga haushi suka ji dan I’ve been calling them since last night amman ba wanda ya amsa.”
Ta k’arashe maganar tana sakin kuka.

Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “A kawo miki Sakina? Ku zauna tare?”
Da sauri ta d’ago tana kallonshi, sai kuma ta hau d’aga kai tana share hawayenta.

Murmushi yayi kafin yace
“Ok, but no more crying, in ba haka ba in fasa.”
Da sauri ta cigaba da goge hawayenta, da kyar kuwa ta samu suka tsaya….
Chapter 30 · 0% Book details