Sashe 39
So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Arshaad yana zuwa k’asan, ya tarar da Aslam a tsaye jikin dispenser yana shan ruwa..
wanda jin sauk’k’owar tasa ne yasanya shi ya juyo.
Fara’ar da ya ga yana yi ne ya sanya Aslam d’in fahimtar wani abu dan haka yad’an matsoshi yana shirin yin magana yaga yayi hugging d’inshi yana wani murmushin da yake baiyyana tsantsar farin cikin da yake a ciki!
Cikin farinciki ya cika shi still yana murmushi ya d’ago ya kalleshi sannan yace
“Call me Ango! An bani mata”.
Ya fad’i hakan yana dariya.
Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e,
sannan yace “Congrats bro, i’m very happy for you.”
Cikin zolaya Arshaad yace “na yi maka wayo!
Kai ma kayi sauri ka nemo..”
Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “ka yi mini wayo kam!”
Shigowar da Auwal yayi cikin parlourn ne ya katse su.
Bai kalli kowa ba ya wuce yaje ya zauna akan d’aya daga cikin kujeraun parlourn…
Aslam ne yace masa
“Auwal ya gida”
D’an d’agowa Auwal d’in yayi ya kalleshi, har zai ce wani abu kuma sai ya d’auke kai kawai yace
“Fine” yana mai kallon hanyar staircase….
Bayan kamar 2 minutes Abba ya sauk’o.
Cikin girmamawa ya gaida Abban har da d’an rissinawa!
Da d’an mamaki Abba ya kalleshi ya amsa sannan ya wuce, su Aslam suma suka nufi hanyar wajen
ganin zasu fita yasa shima ya mik’e suka nufi mosque gaba d’ayansu.......
A dining d’in suka tarar da Hudan, Sakina Sudais da Shuraim don haka suka yi joinin d’insu su uku, banda Aslam wanda ya wuce gida daga mosque d’in don kanshi yana d’an ciwo! Shiyasa kawai ya wuce bayan ya cewa Arshaad “ya karb’a tofin ya taho dashi in sun gama”.
Babu kunya haka nan Auwal ya samu guri ya zauna dai dai gefen Sakina! Da mugun sauri tayi zumbur! Zata mik’e Hudan tayi saurin rik’ota tana nuna mata Abba da ido.
Suna shirin farawa Daddy ya shigo, yana ganinsu gaba d’aya ya cewa Abba
“Wato ka had’a kan y’ay’anka ni kuma ka manta da ni, ko?”
Dukkansu dariya suka yi kafin su shiga gaidashi one by one..
Cikin kulawa ya amsa musu yana mai cewa
“Na gaji da cin abinci ni kad’ai
daga yanzu kawai a dunga yin dinner a chan side d’ina, breakfast da lunch ku dinga yin abunku a nan, in ba haka ba shirun ai sai yayi min yawa, daga ni fa sai Auwal shima kuma in yaga dama ma sai ya kwana biyu bai yi dinner d’inba, yau kuma kalleshi ja’iri ya gudo ya barni!”.
Duk dariya aka sa sannan suka fara cin abincin cikin nishad’i…..
A zaman su Auwal ya cewa Sakina
‘Hi’
Yafi sau ashirin amman har aka tashi bata amsashi ko d’aya ba! Ko arzik’in kallo ma bai samu daga gareta ba
k’arshema juyar da kujerar tata ta yi kad’an ta karkatar da hankalinta a Huda gaba d’aya!
Wanda hakan ya sanya duk jikinshi yin sanyi dan tunda yake a rayuwarshi tun yana secondary school
mace bata tab’a yi mishi haka ba, wasu ma sune suke cewa suna sanshi, dan ko a yanzu haka kafin yace yana so sau d’aya sai ance ana sonshi sau goma!!.
Daddy ne ya fara mik’ewa sai Abba….
Auwal yana shirin yi mata (Sakina) magana tayi sauri ta mik’e ta haye sama
Hudan kuma ita da Arshaad suka koma cikin parlourn suka zauna, su Sudais ma suka yi mishi sai da safe suka tafi.
Kasa mik’ewa Auwal yayi a wajen, dan haka har Abba ya dawo ya taddashi yana nan bai tafi ba!.
Hudan daman a shirye take dan haka ta kira Sakina a waya tace “tazo su je”
Arshaad yaso yace zai je
amman kunyar Abba sai ta hanashi yin maganar, dan haka ya yi musu sai da safe ya tafi bayan ya karb’i ruwan Addu’an Mommy.
Auwal ma ganin yanata zama shi d’aya yasa ya yiwa Abban sai da safe ya tafi, bayan yaga sauk’owar Sakina.
A tare suka fito shi( Auwal ) yayi part d’insu su kuma suka wuce mota
Sakina na baya Hudan na gaba a haka har suka isa bakin k’ofar gidan Baba.
Ba Hudan ba hatta Sakina zumud’i take yi..
Cikin rawar k’afa suka fita a tare suka shige gidan.
Basu tarar da mashin d’in Baba a soro ba, da alamun bai kai ga dawowa ba.
Gidan shiruuuu, sai d’an hasken fitulu da suke hangowa ta d’akin Umma da Mama.
A hankali Huda tasa hannu ta d’an tura k’ofar kafin su shiga a tare da sallama…
Kendir d’in dake kan dressing mirrow ne ya taimaka wajen haskaka d’akin!
Tana zaune a k’asa gaban gado kan sallayarta, da charbi a hannunta, da alama bata tashi daga wuridin bayan Isha ba dan ga hijabinta ma a jikinta, a gefe guda kuma ta kunna maganin sauro yana d’an tashi da kad’an da kad’an.
D’ago fuskarta tayi ta kallesu, kafin ta maida idonta k’asa kamar bata ga kowa ba!.
Gaba d’aya jikinsu sai yayi sanyi, amman suka aro jarumta suka k’arasa inda take!
Sakina ce tayi k’arfin halin hugging d’inta kafin tace
“Mama Ina wuni ya jiki?”
“Alhamdulillah” kawai tace Maman tace mata.
Itama Hudan ta gaisheta
ta bita da “Alhamdulillah”
Sannan ta mik’e ta cire hijabin jikinta ta ninke da sallayar, ta mik’e ta haye gado ta kwanta abunta.
Duk kasa cewa komai suka yi,
d’akin ya d’auki shiruuuu.
Wajen minti goma ta tashi taje ta kashe kendir d’in ta dawo ta tofa addua ta kwanta, harda d’an jan abun rufuwa.
Sheshshek’ar kukan Huda ne ya sa Sakina kunna flash d’in wayarta!
Itama Mama jin kuka yasa ta mik’e ta zauna daga kan gadon tana kallonsu a inda suke.
A hankali Sakina ta cewa Mama
“Mama dan Allah ki yi hak’uri mana.”
Cikin katseta Maman tace
“Hak’urin me?”
Dibi dibi Sakina ta hau yi kafin ta samu damar cewa
“Naga kamar kina fushi da mu ne”
Murmushi Maman tayi kafin tace “ba fushi nake yi ba Sakina, ko kad’an bana fushi daku
Kawai kun zab’i abunda kuka ga ya dace ne
Nima kuma na zab’i wanda naga ya dace!”
Ajiyar zuciya ta (Mama) sauk’e kafin ta juya kan Huda tace
“Na san abunda kika yi ranar da kika zo duba ni a asibiti!
Dukda Ummu taso b’oyewa amman naji kuma na fahimta!
Na gode Hudan, Mahaifin ki ya fini ko?
Ba komai..
Amman abunda nake so ki fahimta shine
Tunda shi kika zab’a, to ki zauna a iya shi kad’ai kar in sake ganin k’afar ki a inda nake! In ba hakaba wallahi sai ranki ya b’aci!
Na bar masa ke!
Tunda naga a ganin ki yanzu ban dace ki zauna da ni ba, kin girma ko? Kin mallaki hankalin kanki, so bani da wani amfani a wajen ki, tunda ba abunda zan iya miki ko zan iya baki..”
Wani irin kuka Hudan ta rushe da shi, tana shirin yin magana Mama ta katseta ta hanyar cewa
“Haka ne mana, kar ki min kuka gaskiya na fad’a!
Kinyi girma ai yanzu tunda har kika iya yankewa kanki decision..”
Sakina ce tace
“Mama dan girman Allah kiyi hak’uri, wallahi kin yi misunderstanding d’in mu ne
Please Mama ki tsaya ki fahimcemu”
“Hmmmm”
Maman tace, kafin tace
“Nima kun kasa fahimta ta Sakina
ba wai haushi naji ba fa, kawai ina baku space d’in da kuke buk’ata ne, tunda gashi ta nuna min k’iri k’iri abubda ranta yake so ai kinga sai in barta in daina kutsa kaina cikin rayuwarta ko??
Ku tashi kuje dare yayi, na san yau ma yana waje yana jiranki!
And maganar zuwa kotu itama na daina yi! Tunda gashi k’iri k’iri kin riga kin zab’i abunda kikeso, so ba amfanin zuwa kotun tunda babu amfanin inje inata yak’i ni kad’ai.
Sai kuje ku yi ta rayuwarku mai dad’i cikin daula ke da Mahaifinki.”
Tana gama fad’in haka ta koma ta kwanta abunta.
Kusan 20 minutes suna bata hak’uri, amman tak’i kulasu
Sai da suka kaita bango ta tashi ta balbalesu da fad’a tace “wallahi In basu fita ba zata dake su! Su bar ganin wai sun girma.”
Mik’ewa Hudan tayi kamar zata fita, sai kuma ta koma da gudu ta je ta kanainaye Maman tace
“Ni ba inda zan je, dan Allah ki daina fushi dani haka,
ba zan sake komawa ba, anan zan zauna.”
Kasa cewa komai Mama tayi..
Suna a haka wayar Hudan ta fara ringing, har ta tsinke ba wanda yayi yunk’urin d’aukar wayar…
Sai da aka sake kira, tukunna Sakina tayi k’arfin halin d’auka ta d’an fita waje, ta fad’awa Abban halin da ake ciki
“Sai da safe” kawai yace mata, daga nan ya kashe wayar!
A chan d’aki kuwa, da kyar Mama ta d’an kulasu..
Sai da Hudan tayi mata alk’awarin ta bar zuwa gidan Abba har abada sannan ta d’an sauk’o….
Daga Hudan har Sakina, gabansu fad’uwa yake yi dan basu san ta inda zasu fara yi mata bayanin baikon Hudan da sa ranar da aka yi ba!
Chaan dare! Kowa ya kasa bacci sai juyi suke yi, Mama ta hango kendir d’in d’akin Umma a kunne, ita tama yi tunanin ko tana d’akin Baba ne tunda ita ke da girki, gudun kar ya k’are ya kama wani abun yasa ta cewa Sakina “taje ta kashe mata kendir d’in, in k’ofar a bud’e take.”
Tun daga bakin k’ofar d’akin Sakina fara jiyo gwarti!
Tsaki tayi ta d’anyi sallama kusan sau uku, jin shiru yasa ta d’an tura k’ofar ta shiga…
Kendir d’in saura kad’an ya k’are, dan ba don ta je ba ma to da babu abunda zai hanashi kama kan mudubin katakon d’akin, dan Umman bata d’aurashi akan komai ba kamar yadda taga Mama tayi ba.