← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 70

Sashe 62

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nuna halin ko In kula ya mik’e tsaye ya karkad’e farar jallabiyar dake jikinshi, kafin yace
“At least na sakata tayi mai dalili ai yanzu ba fake ba.”
Yana gama fad’in haka ya juya zai hau sama..

Da sauri Dad ya mik’e
ya sa hannu ya juyo da shi, bai yi wata wata ba ya d’auke shi da wani mahaukacin mari
dan tun lokacin daya durk’usa akan Ummi idanuwanshi suka sauk’a kan takardar saki biyun da Abba yayi mata.

Da sauri Auwal wanda ya shigo yanzun ya k’araso inda suke yana cewa
“Subahanallah, mai ya faru?
Dad wace..?”
Maganarsa ce ta katse sakamakon Idanunshi da suka kai kan fuskar Ummi,
da sauri ya durk’usa ya hau tattab’ata yana tambayar mai ya same ta?.

Cikin b’acin rai Dad yace
“Maida ita yanzunnan ko ka fuskanci fushina Yakubu!”

Da mamaki Abba yake kallonshi jin yana yin yanda Dad d’in yayi mishi magana da kuma yanda ya kira sunanshi haka!
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“I can’t Dad, I’m really sorry
Wallahi baz..”

Wani marin ya kuma sakar mishi kafin yace
“Kar ma ka rantse!
Dan ko ka rantse sai kayi azumi saboda Ummi sai ta koma d’akinta a yau wallahi!
Kaji dai na rantse.”

Bai ankara ba yaji hawaye yana zuba ta idanunshi..
Cikin kuka yace
“Dad bana son ganin fuskar matar nan, tayi ruining komai nawa saboda selfish reason d’inta!
Ba zan b’oye maka ba
wallahi Ina having second thoughts akan auren Hudan da Arshaad saboda
kwata kwata bana son yin nesa da y’ata
because i just knew her,
all because of ummi.

Ka san irin azabar da Hudan ta sha a hannun Usman kuwa?
All because of Ummi.

Ka san yadda nake jin Maryam a cikin zuciyata? Amma ba yadda na iya dole haka inaji Ina gani ta auri wani ta rayu da shi for almost 20 years!!
All because of ummi

Komai fa Yaya ita ce sila!
Itace silar ciwon zuciyana!
Itace silar bak’in cikina!
Itace silar lalacewar soyayya ta!
Haba haba dan Allah..
sannan yanzu kace In maida ita?
Gaskiya kayi hak’uri Yaya, ban tab’a maka gardama ba amman kam yau zan yi maka!.
Wallahi ko sunanta ba na son ji
kwata kwata..”
Ya k’arashe maganar cikin d’acin zuciya sannan yana gama fad’in hakan ya wuce sama ya barsu shi da Auwal wanda yake ta yayyafa wa Ummin ruwa yana son yaga ta farka.

Da kyar Dad ya iya juyowa ya kalli Auwal d’in, sannan yace
“Kamata mu kaita asibiti,
Allah yasa ba wani babban abun bane ya sameta......”

Gandun albasa
(2:30 pm)
A tsakar gidan Madu,
akayi decoration na traditional kaulu!
Wajen yayi masifar yin kyau.
Taken wak’e wak’en Shuwa Arab ne ke tashi in a very low tone.
Su Sudais da wasu Yaran sai y’an tsofaffi tsilla tsilla ne a zazzaune a kan kujerun da aka k’awata tsakar gidan da su.

Gaba d’aya y’an mata da manyan matan suna ciki,
wasu suna had’a takeaway da souvenirs wasu kuma suna shiryawa dayake mostly family ne sai na jiki sosai suka zo
dan Mama ba wani taro tayi ba
Ita dama ba wani sanin jama a ma tayi sosai ba, sai y’an unguwa da suke ta zirya tun safe waenda rabinsu duk munafurci ne yake kawosu
dan an san yau za a kawo lefe.

Umma bata da lafiya tana fama da hawan jini amman tun sassafe suka zo ita da Baaba Laraba da yayarta Hansai,
kuma wani abun mamaki tunda tazo d’in tak’i kula Mama dan wani mugun zafinta take ji, sun dai gaisa da Shuwa da Ummu
Ita kuma Mama sun gaisa da Hansai da Baabaa Laraba
amman Umma kam tama k’i bari su had’u dan tana hango ta zata kauce hanya
ko ta fad’a d’aki ta shige band’aki. Da Mama ta fahimci hakan kawai sai ta tattarata ta watsar ta shiga sabgar gabanta dan ita mamaki ma Sadiyar take bata duk tabi da d’aurawa kanta wahala
gaba d’aya a takure ma kamar ta ganta ga kuma rashin lafiyar Bp da take ta fama.

Sai da Anty Zainab ta zo tukunna ta d’an samu ta ware.
Itama Anty Zainab d’in da kyar ta iya daurewa suka gaisa da Maman wadda tayi wani irin fresh! Sannan idan ka kalleta ba zaka tab’a cewa sa’ar su bace ita da Sadiyar
Sai dai kace Antys d’inta ne
dan ba za ma ka ajjiyesu a matsayin yayunta ba!
Musammam ma Sadiya wadda ta zama kamar wata mahaukaciya kwana biyun nan!
Tun lokacin da taji labarin maganar auren Huda
har yau bata san inda nutsuwarta take ba………

Mama na gama gaisawa da Anty Zainab ta juya ta wuce abunta.
Anty Zainab kuma ta nufi wajen Umma! Nan kuwa
suka hau hassada da zagin Mama har da suna cewa wai “bazawari take nema shiyasa taci wannan uwar kwalliyar”.
Laffaya Maman ta nad’a itada Ummu, kalar laffayar ja sai blue d’in flowers,
sun yi kyau sosai dan
har d’an light makeup sai da Sakina ta tirsasa su suka tsaya aka yi musu.

Itama Sakina laffayar ce a jikinta, amma bata nad’a ta har ka ba, instead sai tayi d’aurin Zahra Buhari da mandil a kan nata shi kuma mayafin layyafar ta nad’a a kafad’ar ta.

Amarya kuwa ta sha traditional kaya abunta!
Hatta hair style d’inta ma irin nasu aka yi mata,
daga sama ta nad’a wata had’add’iyar blue black d’in laffaya, aka yafa mata mandil akai.
Tun daga kan sark’ok’in k’afarta har na wuya da y’an kunneta da wanda ta sa a kanta na sisin gold duk na asalin gold ne!
Wanda Madu ya bata kyauta jiya da daddare, yace “tun na mahaifiyar mahaifinsa ne!
Maryam yaso bawa Allah bai yi ba.
Ashe rabon ta ne..”

D’akin isu isu ne ita da k’awaye ta, anata d’aukar hotuna
amman kallo d’aya za kayi mata ka san hankalinta baya ma gidan gaba d’aya!
Tun da gari ya waye take jin fad’uwar gaba, gashi yanzu kuma sai kiran Arshaad take yi baya d’auka…..

Shuwa ce ta shigo
ita da Baabaa Talatu sanye cikin wata rantsatsiyar milk laffaya sun yi anko su biyu suma abun su ita da Baabaa Talatun.

Basu dad’e ba wasu mata suka shigo su biyu, daga nan suka umarci Hudan da ‘ta mike
a fita da ita’
Aranta ji take kamar ta tambayesu ‘Ya arshaad ne ya zo? Sai kuma taga rashin kunya da zak’ewarta
Kuma ta tuna jiya Sakina tace mata
‘Ta bar nuna mishi ta damu sosai fa, idan ba haka ba tabar ganin wai yana sonta
Wallahi wahala zata sha....’.
Lumshe idanuwanta tayi
ta dedeta nusuwarta
sannan ta bawa Sakina wayarta ta mik’e, ta jaa
mandil d’inta ta rufe kaf fuskarta, su kuma
suka tik’eta sukayi waje.
Suma su Sakina suka take musu baya.

Hudan, so take ta yakice tunanin Arshaad a kanta amman ta kasa!
K’arshema bigewa tayi da adduar Allah yasa tana fita ta ganshi amman yanayin yanda taji an zaunar da ita a doguwar kujerar da aka k’awata domin ita da shi ne yasanya ta fahimci bai zo d’inba.

Ummu ce ta fito ta bud’e taro da addua sannan ta fara gabatar da al’ada a Huda,
A matsayin uwa.

Mama suna parlourn Madu, tun lokacin da Mommy da Aslam suka zo suka buk’aci ganinta har yanzu bata samu damar fitowa ba.

Wata distant relative d’in Shuwa wadda zata d’an girmi Shuwan kad’an ce
ta k’arasa wajen sannan
cewa Ummu “Ina uwar Angon?
Ta zo ta zauna a kusa da ke
yadda kina gamawa zata karb’a.
Sannan ba ayi welcomin Ango ba kuma ba aga shigowarsu ba besides ai dole sai yananan ma tukunna za ayi komai.
Na ga bai riga yazo ba
amman kin yi wuff kin fara abu haka bayan kuma akwai abubuwa da yawa before wannan.”

Karaf! A kunnen umma. Daman neman abun yi suke yi ita da Anty Zainab shiyasa
suka zo suka zauna a k’asa gefen kujerar Amarya. Da sauri sannan da d’an k’arfi yadda ta tabbatar kowa zai ji
Umman tace
“Eh kam tabbas!”
Sannan ta mik’e tsaye
kafin tace
“Uwar Ango! Tana Ina?
Ana buk’atar Uwar Ango a nan yanzu yanzu”
Da k’arfi ta yadda kowa ya iya jiyota tunda daman wak’ar da aka kunna a low tune yake
kuma iya murya ne kawai babu kid’a.

Da sauri Ummu tace
“Umma meye haka?
Idan kin yi min magana ba zan je In kirata baneba?
Ko hakan da kika yi kina tunanin shi zai sa ta fito?”

Still da k’arfi Umma ta sake cewa
“A’a, ai ji nayi kamar kince bata zo ba!
Gashi shima Angon shiru.
Duk da dai ni ba Shuwa bace ba amman Tabbas na asan cewa Ango da Amarya a tare ake shafa musu lalle, manshanu, da ragowan abubuwa! Dan har yau ina tuno naki, a tare aka shafa muku ke da Muhammadu wanda ya zo wurwuri
bai tsaya b’ata lokaciba,
Ita kuwa yayarki daman ba a yi mata ba
shiyasa gaba d’aya auren nata duk biyun suka tab’arb’are!
To kuwa kinga ai ba zan so auren Huda itama ya samu matsala ba ko?
Dan haka gara mu jira Angon ya zo ko nan da k’arfe taran dare ne mu masu iya jiransu ne
har sai shi da uwarshi sun zo an yi alada yadda ya kamata!”.
Ta k’arashe maganar har wani karkarwa jikinta yake yi, wanda kana gani ka san bala’ine kawai yake cinta.
Chapter 62 · 0% Book details