← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 70

Sashe 18

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ok, I’m sorry”
yana mai sake ruk’o hannunshi.
Sai da Aslam d’in ya maimaita sannan Arshaad ya juyo ya kalleshi na y’an seconds kafin yace
“Apology accepted.”

“Thankyou “
shine abinda Aslam d’in yace kafin ya d’aura da
“And about what you just saw, i’m..”
Cikin katseshi Arshaad yace
“Aslam we’re good fa, komai ya wuce, let me check on her, ta shiga toilet d’in mutumin nan barefoot kuma i don’t even know ko yana ciki dan ban ganshi a d’akin ba.”
Yana gama fad’in haka ya zare hannunshi sannan yayi cikin d’akin ya isa bak’in k’ofar toilet d’in yana cewa
“Hudan open the door, it’s me, su Abba sun tafi.”

A hankali take bud’e k’ofar tana d’an lek’owa..
Sai da ta tabbatar da shi d’inne tukunna ta k’arasa bud’ewa.

Murmushi ya d’anyi mata..
Gaba d’aya ta had’a gumi tayi zuru zuru!
A hankali yace “matsoraciya kawai”
A hankali tayi k’asa da kanta sannan ta fito, Allah ya taimaketa ba kowa a toilet d’in kuma mutumin yanada tsafta dan band’akin tass yake gashi tiles ko ina kuma a bushe. Amman dukda haka sai da Arshaad yayi amfani da ruwan butan da ya gani bayan sun fito ya zuba mata akan k’afafunta.
Suna fitowa ya cire takalminshi ya bata ta saka sannan yace “ta zo ta rakashi ya saka takalmi.”

A hankali ta fara kuka kafin tace masa “Ita wajen Mama zata je”

Gaba d’aya sai yaji wani matsanancin tausayinta ya kama shi. Shiruuu, yai yana tunanin ta yadda zai fita da ita bayan shi aka d’orawa alhakin curfew.
Dole ya lallab’ata ta d’an hak’ura ko zuwa gobe ne sai su je.

Matsowa yayi yana shirin lallashinta wayarshi ta hau k’ara, ganin sunan Sakina ya sanaya shi ce mata su k’arasa ciki akwai maganar da yake ai suyi da ita, dama. Tukunna sai ya kaita gurin Maman.

Ba tare da musu ba ta bishi suka yi hanyar shiga parlourn gidan, Aslam har zai bisu dan still ya lura Arshaad d’in is still mad, saboda da suka fito ko inda yake bai yarda ya kalla ba..
Sai kuma kawai ya chanja shawara ya juya kawai, duba da yayi ba shi kad’ai bane kuma ya lura soyayyar Mahaifiya ta rufe mishi ido, if not tayaya zai ce “ita da Mom basu da laifil!” ko kuma may be bai san story d’in gaba d’aya ba, dai.
Da wannan tunanin ya fita a gidan bayan ya yanke shawarar sai nan da 4 to 5 days haka zai nemeshi ya sake bashi hak’uri, by then ya san ya sak’k’o.....

Suna shiga parlour ya umarceta da “ta zauna akan kujera”
Bayan ta zauna shi kuma ya nufi fridge ya d’auko mata ruwa da glass cup a kan dining ya kawo.
Dama kuwa tana buk’ata hakan yasa yana zuba mata ta k’arb’a ta hau sha. Sai da ta shanye tass sannan ta ajjiye tana sauk’e ajjiyar zuciya a jejjere.

Kallonta yayi da idanuwanshi da har yanzun basu gama dawowa dede ba sannan a hankali yace
“In kara?”
Girgiza mishi kai tayi tana y’ar mitsitsiyar gyatsa kafin tace “Alhamdulillah”
Sai kuma anhankali ta mik’e tace “Bara inje wajen Aaima”
Mik’ewa shima yayi yace
“bata nan, bata dawo daga school ba tukun!
Mammy kuma tana cell!
It’s just me.”
Ya fad’i hakan yana tsareta da ido.

Saurin yin k’asa tayi da kanta, kafin a hankali tace
“Kayi hak’uri dan Allah.”
Murmushi ya d’an yi yana kallonta kawai ba tare da yace komai ba.
A hankali tace “bara in tafi, nayi tunanin Aaima tana nan ma.”
Bata jira jin me zai ce ba ta fara k’ok’arin fita tana cewa “ka d’auko takalmin naka muje mu duba Mama da wuri, ko?”.
Dede nan wayarshi ta sake ringing, ganin me kiran ne yasa shi kai mata wayar har bakin k’ofa sannan yace
“Na so muyi magana but it’s like kamar tsorona ma kikeji!
Gashi ungo, Sakina ta gaya miki, bara in d’auko takalmin nawa”
Yana gama fad’an haka ya kara mata a kunne bayan ya amsa kiran daga nan yayi hanyar part d’in nashi.

Da sallama ta amsa wayar..
Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e jin muryar Huda sannan tace
“Alhamdulillah”
Jin yanayin muryar Sakina yasa ta fahimci akwai matsala.
Cikin sanyin muryar da bata santa da shi ba taji tace
“Huda kuna Ina? bakya hawa watsapp, ba kwa amsa waya tun jiya, gamu kuma mun dawo gida bakwa nan. Ina kukaje gaba d’aya hankalin mu ya sake tashi.”
Da sauri Huda tace “Sakina Mama bata gida?
Ya naji muryar ki wani iri duk ya dishe?”
Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e, har zata fad’a mata kuma sai tayi shiru (saboda su Madu sun ce a bari a fara yin test na gawarwakin da ake expecting akwai Junaidun a ciki da jinin Baba, before ayi confirming nashi as dead )
Hakan yasa tace mata
“Ban gane ‘Mama bata gida ba’ bakwa tare? Ke kina ina?”.

Gefe guda Hudan ta koma kan kujerar dining ta zauna sannan
ta fara bawa Sakina labarin tun daga sumewar da Mama tayi jiya da safe, har kawo yanzu da take son gudowa….

To fa!! Ana wata ga wata.
Numfashi Sakina ta fesar kafin tace “With all that is goin on Hudan, congratulations!
Kin had’u da Mahaifinki finally, and baya gudunki, kamar yadda mutane suke fad’a.
But first
Maama,
so yanzu ki bani kamar 20 minutes haka za sake kira in shaa Allah.”

......Su Abba kafin su koma ciki suka tsaya shi da Daddy suka yanke shawara…suna zuwa suka sanar musu cewa
“Shi da Daddy za su bar gidan, Dad da Gramma kuma za su zauna.
Addua suka dinga yi akan Allah yasa kowa ya yarda.

Ba dan su Gramma sun so ba haka nan suna ji suna gani suka amince da tafiyar su su kad’ai, Dad yaso ace shi ne yabi Abba tunda shine Babba Amman bayan sun keb’e sai suka yi mishi bayani akan kasancewar shi babban ne yasa suka ce ya zauna a estate d’in, sannan ya taimaka ya dedeta Gramma da Granpa, kafin ya koma Abuja, dan tun a wajen meeting d’in suka fahimci iyayen nasu suna fushi da juna wanda hakan it’s not usual.
Ahaka ba dan rai yaso ba aka tsara akan gobe zasu bar estate d’in kafin a samu komai ya dedeta In Granpa ya sauk’o su dawo, Dad ne ya basu mukullin makeken mansion d’inshi wanda ke anan bayan su kad’an yace “su zauna su biyu a tare ba sai sun raba gidaje ba.” Dan ana hoping d’in daidaituwar komai soon in shaa Allah.

Daddy yayita jiran Granpa ya kirashi yace “yayi resigning, ya kawo takardun companies d’in da yake rik’e dasu sannan ya sauk’a a md d’in MT UK branch Amman ga mamakin shi sai yaji shiru, bai ce masa komai ba.........

Sakina tana katse kiran ta mik’e ta isa inda Ummu take ta jaa hannunta suka koma gefe, ganin haka yasa Shuwa itama ta iso inda suke, nan Sakina ta zayyane musu komai.

Kafin awa d’aya gaba d’aya su Kaka kowa ya hargitse a neman Mama har da Madu wanda ba kad’an ba kowa yaji dad’in yadda ya shiga cikin lamarin.
Babu inda ba a duba ba har wajen 10 amman shiru.
Ummu ce ta bada shawarar “aje asibitin malan d’in a sake bincika ta!.”

Nan d’inma ba Inda basu duba ba dan rarrabuwa ma suka yi amman shiru…

Tunda suka fito Baba yake ta maimaita magana d’aya
“Aje gidansu Abba! Shi ya tabbatar idan aka yi kwakkwaran bincike a gidan za a ganta. Ya san tabbas
Abba ne ya d’auke Maryam ya b’oyeta bashi da tantama!
A kira y’an sanda a kama Abba…waye waye.”

Su Ummu tun suna k’ok’arin fahimtar da shi har suka hak’ura suka kyaleshi kawai dan sun lura abun nashi ba na k’are bane.
Ganin dare ya lula yasa Ummu tace bara kafin su koma gida ta shiga masallacin can tayi sallar isha dan gaba d’aya ta sha’afa bata yi ba gashi lokaci ya tafi sosai, sai a lokacin Sakina itama ta tuna bata yi ba hakan yasa suka nufi famfo suka yi alwalla tare daga nan suka shiga masallacin domin gabatar da sallah…
Babu kowa a ciki sai wasu mata guda biyu a chaan k’uryar masallacin, d’ayar a zaune da Yaro a hannunta d’ayar kuma ta juya baya tana kallon bango alamun bacci ma take yi.

Cikin nutsuwa suka gabataar da sallar su suka d’ora da doguwar Adduar Allah ya baiyyana musu Mama.
Daga nan suka mik’e suka fara k’ok’arin fita.
Ummi ji tayi kawai gabanta ya yanke ya fad’i, kamar kuma ance ta juya…bata san daliliba amman taji tana buk’atar juyawan…
Matan nan na d’azu ta sake kallo still suna a yadda suke, har tana shirin juyawa idanunta suka kai kan atamfar jikin matar kwance da mayafinta, sai a yanzu ma ta lura da kayan dan sanda suka shigo kwata kwata hankalinsu baya tare dasu, gasu a gajiye.

Kusan a tare zuciyoyinsu suka buga ita da Sakina wadda itama taga atamfa da mayafin jikin Mama
Tabbas mayafin Mama ne wannan
Atamfar kuma ankon wunin kai amarya Khadijah ne.
Da sauri Sakina tace “Maamaa!” Sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tab’ata ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita.

“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare.

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
39

Da sauri Sakina tace “Mamaa” sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tattab’a ta,
ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita!
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare, dan a yadda Sakina ta juyo da ita haka ta biyo hannun Sakinan ta taho yuuu ta zube wanwar kwanciyar rigingine.

Ummu mutuwar tsaye tayi a wajen, so take ta k’arasa inda suke amman ta gagara sakamokon ganin y’ar uwartata da tayi kwance tamkar gawa!
Ta kasa tab’uka komai banda hawaye ba abunda take yi.

Sakina wadda ta rikice tanata tattab’a Maman ne ta juyo tace
“Ummu ki zo ki kamata mu mik’ata emergency..
Mama ce amman bata numfashi.”
Chapter 18 · 0% Book details