← Book details So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 70

Sashe 11

So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jalila na ganin fitar Huda ta share hawayenta ranta fess!
Sannan ta mik’e ta k’arasa inda Auwal ya daskare yake k’ok’arin hada 1+1 akan alamarin da ya gudana yanzun nan dan in dai shi ba dak’ik’i bane ba tou abu na farko daya fara fahimta shine ‘Arshaad Huda yake dating!’ And tabbas bai san Jalila ba, to who…..
Muryar Jalila wadda ta k’araso yanzu ne ta katseshi jin tana cewa
“Nayi duk abunda kace, yanzu abunda nakeso da kai shine ka kawo miliyan d’aya, ragowar kuma in aiki ya kusan kammaluwa, dan..”
Shak’ar!! Da yayi mata ce ta katse mata maganar tata, cikin d’acin zuciya da k’arfi yace
“Who are you?”.

BULAMA ✍️

Cikin fushi tace “kafi kowa sanin me kayi!
Kuma ina so ka sani Allah sai ya bi ma Hudan hakkinta dan wallahi kaji na rantse ita d’in son gaskiya da tsakani da Allah take yi maka!
Amman duk da hakan zan yi k’ok’ari inga na cire mata kai a ranta!.
Sannan ga sak’o ka gayawa Abba!
‘ in duk duniya ce zata taru a kaina to ba zan yarda ba!!
Nima ina nan zuwa karb’arta, daganan in Mahaifinsa yaga dama ya kulle kaf jinsina ba wai iya danginaba!!”.
Tana gama fad’in haka ta wuce ta barshi nan, a daskare!!

Da kyar ya iya tattaro ragowar kuzarinsa ya fice shima a d’akin, saboda iya yadda yaga ta fita tana layi ya tabbatar mishi ba zata iya kai kanta ko da nan da gate ba!
Sai dai kuma, ko da ya fita d’in sai bai ganta ba bai ga alamartaba kamar wadda tayi layar zana ta b’ace!

Duddubawa ya hau yi har buildings d’in gefen emergency amman babu ita babu alamar ta!
Abun ba k’aramin sake d’aga mishi hankali yayi ba dan babu inda bai duba Mama ba amman bai ganta ba har unguwar su yaje a tunanin shi ko ta koma amma tun kafin ya k’arasa gidan ya hango ana (Baba) datsa datsa kwad’o a gidan, ya fitar da machine da alamun fita zai yi.

Sanin da yayi in dai napep ta hau to ba lalle ta rigashi isowa gidan ba ne, ya sanyashi zaman jiranta, anan cikin mota!
Sai dai almost 2 hours amman bata dawoba.

Zuwa yanzu kam hankalinshi ya kai k’ololuwar tashi!…..
…….Tun farkon had’uwar shi da Hudan yake k’ok’arin toshe duk wata hanyar da zata kawo musu matsala, yanzu haka ya ware millions zai siya musu gida, ta yadda In su Mammy sun zo ba zasu samu abun kushewa ba balle har Granpa yaji ya hana, su Abba kuwa ya san su zasu zo nema mishi aure, so gidan uncle Muhammad ba zai zama matsala ba!
Dan anan aka shirya za a had’u dan ba daban jiran
Dad d’in da suka tsaya yi ba ma to da tuni sun zo an gama magana.

Har ga Allah ba zai tab’a iya rayuwa babu Hudan ba, kwata kwata, shi baya jin ma a tarihi akwai wani mahaluk’in da ya tab’a yiwa wata kalar son da yake yiwa Huda since day 1,
gashi kuma yau Mahaifiyarta da kanta ta kalle shi tace ‘zata rabashi da ita!’

Bai ankaraba kawai yaji hawaye yana wanke mishi fuska!
Sunayen Allah ya fara ambata yanayi yana kuka, kamar k’aramin Yaro.
Da kyar ya samu zuciyar data yunk’ura mishi ta d’an lafa.

Ganin babu Mama ba labarin ta, ya sanya kawai ya yanke shawarar komawa gida yayi wanka daga nan ya kira Ummu a san abunyi!
Dan in ba ruwa ya samu ya sakarwa kanshi ba baya jin kalmar ‘A’ zata iya futowa daga bakinshi a halin da yake ciki...........

BULAMA ✍️

So da Buri
Free Book
37

Kamar yadda Arshaad ya tsara, sai da ya lallab’a yayi wanka da kyar tare da hutun awa d’aya! Tukunna yaji d’an dama dama, cikin tsantsar mutuwar jiki ya lalubo wayarshi ya danna kiran Ummu.
Sai da ta kusan katsewa tukunna aka d’auka, a tunanin shi ko hayaniyar biki ne yasa ta jinkirin amsawa sai dai kuma tana d’auka yaji hayaniya da koke koke!
Cike da fargaba ya hau tambayarta, nan take gayamishi.....
....”Suna shirin shigowa Kano, wani Abokin Junaidu ya kira Baba! Bayan sun gaisa ne
yake ce mishi ‘dama ya kira ne a kan maganar Junaidu!
Wai an sake shi tun satin baya da ya wuce sai dai kuma
babu irin kalar binciken da basu yi ba amman an rasa shi!
Wajen kwana uku kenan yau.
Lokacin da aka sallameshi yayi mishi waya yace ‘zai zo gidanshi, ya d’an kimtsa tukunna ya wuce Kano, bayaso ya sanar da kowa dan surprise zai yi musu’.
Yayi ta zaman jiran nashi amma shiru! Sau daga baya yaji labarin accident da aka samu a garin guda uku ata wajajen k’iri k’iri d’in! mota biyu ta y’an kasuwa ce, d’ayar kuwa ta prisoners d’in ne
waenda aka saki sai dai kuma duk sun k’one k’urmus! Dan ko iya tantancesu ba a yi!

Yayi shiru ya tsaya bai fad’a musu ba domin yanaso yayi bincike sosai tukunna
dan shi tunanin shi yana bashi
ba lalle har da Junaidun ba
amman duk wani investigation yana tabbatar da akwai gawar Junaidun a ciki!
Shiyasa kawai ya yanke shawarar kira ya fad’a musu..’

Gashinan yanzu haka a mutuary in babu damuwa wasu a cikinsu suzo
dan ana da buk’atar su
wajen tantance gawar da kuma ragowar abubuwan da ya kamata!!’.”
(Da kyar Baba ya iya k’arasawa gida ya d’auki kud’ad’e
da atms da abun buk’ata ya mik’a Ja’afar wajen K’asimu
suka kama hanyar Lagos!
Suma su Abba Madu suna ajjiyesu a gidan Baaba Talatu ya juya shi da su Ya Jamilu.
Yanzu haka sun kama hanyar Lagos d’in.)

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Shine abunda Arshaad yayi ta maimaitawa, yana jiwo Sadiya tana ihu tana wallahi “sai tayi sharia da y’an sanda da sojojin da suka rik’e mata Yaro bayan sun gano bashi da laifin komai! Inda ace sun bari ranar su Madu sun dawo da shi ai da duk haka ba ta faru ba!
Allah ya isanta”

Baba Talatu ce ta hau yi mata fad’a, tana cewa
“Bata da tawakkali ne?
In Allah ya riga ya tsara abu dole sai ya faru! Ta daina yi mishi kururuwa da ihu…”
Amman inaaa, bata ji bata gani sai rafka kuka da kururuwar kawai take yi.

Jin yadda gidan ya hautsine ne ya sanya kawai yanke shawarar zai nemo Mama da kanshi in shaa Allah, dan haka yayiwa Ummu gaisuwa, kafin ya kashe wayar.

..............
Kusan a tare motar Abba da ta Aslam suka k’araso cikin estate d’in! Basu shiga ko wanne gida ba suka yi parking a babban parking lot d’in estate d’in kamar had’in baki.
Abba ne ya fara fitowa kafin Aslam, yana k’arasowa inda yake yace “Ka kaita wajen Gwaggo Asabe.
Zan nemaku zuwa anjima.”

“Ok”
Shine abinda Aslam d’in yace
sannan ya juya ya fara k’ok’arin bud’e inda Huda take zaune tana kuka har yanzun, shi kuma Abba ya juya ya nufi gidan Ummi.

Hannunta ya sake fincika bayan ya bud’e motar
ya fito da ita!!
Sannan ya zaro wayarshi ya danna kiran Gwaggo Asabe ya kara wayar a kunnenshi…

Fisge hannunta tayi da duk k’arfin ta! Sannan ta juya ta bud’e motar ta d’au wayarta tana dubawa dan ita a nata tunanin ma ta fashe ne
saboda yadda Aslam d’in ya had’a wayar da hannunta ya runtse a nasa hannunt tun lokacin da yace ‘Mama ba zata tafi da ita ba’ har sanda ya kaita mota….
Rad’ad’i da zugin da hannunta yake mata da kuma tsananin tashin hankalin da take a ciki ne suka hanata d’aukar wayar data fad’i daga hannunta tun shigar ta motar, sai yanzu Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin bata yi komai ba hakan yasa ta
rufe motar ta d’an juyo da niyyar kiran Mama.
D’an satar kallonshi tayi, ganin ya tsareta da dara daran idanuwanshi ne ya sanya ta yin k’asa da kanta sannan tace
“Ko baka ja ni ba zan bika!
Wayata kawai na d’auka”
Tayi maganar cikin muryar kuka.

Murmushin rainin wayo yayi mata, kafin yace
“Better!”
Sannan ya juya ya fara tafiya yana cewa “Gwaggon ta fito, yanada bak’uwar da zai bata, ta same shi a gate!”

Hudan kuwa wata zuciyar ce take ce mata ‘ta d’iba a guje ta fice a estate din!’ Amman kuma ta na juyawa tayi ido hud’u da sojoji har hud’u a wajen gate d’in suna zazzaune.
Wani sabon kuka ta fashe da shi kafin ta durk’ushe a wajen abun tausayi…
A hankali kuma sai ta d’ago wayar tata ta fara k’ok’arin kiran Mama tana adduar Allah yasa taga purse d’inta ta d’auka a cikin d’akin, dan
lokacin da Aslam ya jawota
purse d’in ta fad’i a k’asa.

Aslam kuwa jin da yayi kamar ba mutun a bayan shi ne ya sanya ya juyo dai dai ita kuma da d’ago kanta sukai ido biyu!
A zuciye ya taho gadan gadan yana nad’e hannun rigar shi,
Ta san me yake shirin yi hakan yasa ta mik’e da sauri, kafin ya k’araso ita tayi hanyar da taga yayi…..
Rashin kwarin jiki da kukan da taci ne yasa har yazo ya gota ta ya zamana ita take binshi a baya.

Kamar yadda suka yi a bakin Gate d’in ya tarar da Gwaggo Asabe tana jira, nuna mata Hudan kawai yayi sannan yace
“Zuwa anjima zan kiraki!”
Da mamaki tab fuskarta take kallon Hudan ganin yadda yake kallonta ne ya sata kawai jan hannunta suka shige ciki
shi kuma ya nufi gidan Mammy
a falon ta na sama ya samu doguwar kujera ya kwanta, zuciyarshi fal da tunani barkatai.
.......

A parlourn k’asa Abba ya samu Ummi tana shafa wa jan lallen da aka gama cire mata yanzu mahallabiya.
Sallamarshi ce ta katse musu k’us k’us d’in da suke yi ita da Mom wadda ake k’arasa saka mata nata lallen yanzu.
Da sauri ta d’ago jin muryar shi, su na had’a ido ta sakar mishi murmushi sannan ta mik’e ta nufe shi….
Bata damu da Mom da mai lallen da suke parlourn ba! Tana isa gareshi tayi hugging d’inshi tana mai yi masa sannu da zuwa……
Chapter 11 · 0% Book details