Sashe 47
So Da Buri Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana shiga ya tarar da jakankuna, bai gama tantance na waye ba! Yaji anyi tsalle anyi hugging d’inshi ta baya.
Yadda tayi masa ya riga ya san wacece dan haka ya fad’ad’a fara’ar shi ya sa hannu ya zare ta a jikinshi ya juyo da ita kafin yace “Wai ni sai yaushe za ki girma ne?”
Turo baki gaba tayi, kafin tace
“Ya Arshaad oyoyo d’in kenan?
Da fad’a za a yi min sannu da zuwa?”
Ta fad’i maganar tana hard’e hannunta a k’irji, sannan ta juya mishi baya alamun tayi fushi.
Dai dai nan Aslam ya shigo, d’an murmushi yayi da ganinsu a hakan kafin yace
“Har an fara ko?
Oya! In kin gama fushin, wuce kitchen ki had’a min black tea.
Yau duk kun gajiyar da ni da zirga zirgar airport wallahi, ga
drivers a gida kamar me amman kowa In ya dawo daga yawon sa sai yace Ni!”.
Sake turo baki Aaima tayi kafin tace “Ya Arshaad makarantar ne yawo?
Shikenan naji ba komai duk na lura bakwa murna da ganina.
Ina Mammy ne? Na duba ko ina bata nan!
Ka ce mini bata da lafiya shiyasa ta kashe wayoyinta, meyene ya sameta tana ina ?
Wallah duk hankalina a tashe yake, bafa ayi hutu ba ma na dawo!
Dad shima same yadda kuke yi haka yayi min.”
Ganin duk sun yi shiru sun kauda kai yasa ta k’arashe maganar tata a hankali tana mai cewa “kuyi min magana please”.
Aslam ne yayi k’arfin halin cewa “Aaima, kawo min tea, ki huta kici abinci daganan sai mu yi magana ko?”
Gani suka yi kawai ta fashe da kuka, cikin kukan tace
“Ya Aslam dan Allah in mutuwa Mammy tayi ku fad’a min dan Allah.”
Da sauri Arshaad ya toshe mata baki da hannunshi kafin yace
“Mammy tana nan, kinji!! Babu abunda ya sameta, in fact zuwa anjima ma zan kaiki ki ganta, kin ji?
Yanzu ki huta tukunna nima bara inyi freshening up, sai muzo ayi magana ko?”
Cikin tashin hankali tace
“Ba dai rabuwa sukayi da Dad ba, ko? Ya a....”
Cikin tsawa Aslam yace mata
“Idan kika bari na k’araso wajen nan sai na tattakaki wallahi!! Ba za ki wuce kiyi abunda akace ba?”
Ta tsorata sosai da tsawar shiyasa ta zo ta wuce sum sum ta shige kitchen d’in jikinta na karkarwa, tana matsar hawaye.
Sai da ta wuce kuma sai Aslam d’in yaga rashin kyautawarshi
“Damn it!”
Ya furta hakan chan k’asan mak’oshi, kafin a hankali
ya rintse idanunsa…
Shi kad’ai ya san me yake going through those days!
Abun har tsoro yake bashi,
shekaran jiya fa Gwaggo Asabe ya yiwa tsawa!
Abunda bai tab’a tunanin zai kwananta yi ba ko da kuwa da wasa ne.
Abunda ya kai yaji haushi da wanda bai kai ba gaba d’aya hassalashi suke yi!
Haushin kowa yake ji!
Ya tsani kowa ya tsani komai!
Baya son shiga mutane, shiyasa shi kuma yake tilastawa kanshi ya dinga shiga mutanen saboda yayi fighting abunda ke shirin hargitsa rayuwarshi!
But ko hirar minti uku ba a yi dashi ta kirki, zai fara fad’a.
A hankali yace
“Ya Allah ka yaye mini abunda yake shirin k’arasa tarwatsa rayuwata, Ya Allah ka ji k’aina.”
Kallonshi kawai Arshaad yake yi, ya dai san magana yake yi amman baya iya jiyo abinda yake fad’a.
Ya kusan minti uku a tsaye yana kallonsa, kamar zai k’arasa wajenshi sai kuma ya sunkuya ya d’auki suite case d’in shi da ta fad’i garin oyoyo d’in Aaima, ya jaa trolley d’inshi ya nufi side d’insa.
Yana wucewa Aaima ta fito da tea d’in akan d’an karamin tray, ta ajjiye mishi tace
“Gashi”
Bata jira jin mai zai ce ba ta wuce sama itama don yin wanka.
Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e,
kafin yasa hannu ya d’auki cup d’in wanda yake ta uban tururi yayi sipping a hankali..
Da kyar ya iya had’iyewa sakamokon wani tururi da yake ji yana taso mishi daga k’irjinsa yana yowa sama..
He hates this!
Yana disturbing peace d’inshi,
kamar ya sa hannu ya kwakule heart d’inshi ya jefar haka yake ji…
Takaici da ya isheshi ya sanya shi d’aga cup d’in ya kafa a baki ya hau kwankwad’a yana had’iyewa da k’arfi! Ko zafin tea d’in ba ya ji saboda wanda yake ji a k’irjinsa ya ninnika na tea d’in.
Sai da yaga bayan tea d’in tukun ya hak’ura ya ajjiye cup d’in yana uban gumi, had’i da sauk’e ajiyar zuciya a jejjere.
A hankali ya jinginar da kanshi da bayanshi a jikin kujerar yana sauk’e ajjiyar zuciya still
kafin ya lumshe idanuwanshi…
Sai bayan kusan minti talatin tukun Arshaad ya fito wanda kana ganin sa ka san zance zai je. Sanye yake cikin wani had’add’en fari k’al d’in yadi d’inkin boda, yayi matuk’ar karb’ar jikinshi, ya murza sky blue d’in hula zanna bukar sai kyalli take yi, sawunshi sanye cikin farin takalmi sau ciki mai mugun kyau, sai silver agogo da ya d’aura a tsintsiyar hannunshi.
K’amshin turarenshi ne ya sanar da Aslam fitowarshi!
Dan haka ya bud’e idanuwanshi da suka yi jaa ya zuba mishi.
Suna had’a ido Arshaad ya d’auke kai ya tamke fuska yayi hanyar fita.
Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “Irin wannan tamke fuska haka! So kake idan kaje ka firgitata?”
Banza Arshaad yayi da shi ya ci gaba da tafiyar shi.
“You promised Aaima akan za kuyi magana kuma zaka kaita wajen Mammy, remember?”
Arshaad ya sake jin muryar Aslam d’in.
Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e, bayan ya tsaya cak! Ba tare da ya juyo ba dan har ya kai k’ofa.
Yafi 1 minute a hakan, kafin chaan! Ya juyo ya fara takawa zuwa inda Aslam d’in yake zaune.
A kan 3 seater yake zaune dan haka shima ya zauna a kai a gefen shi kad’an, cikin nutsuwa yace
“Are you ready to talk?”
Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “About?”
Cikin d’an b’acin rai Arshaad yace
“Ok!!
Shikenan, kaga tafiya ta.”
Ya fad’a yana mik’ewa tsaye.
A hankali Aslam yace
“Ka san dai akwai abubuwa da yawa a kaina ko?
How kake tunanin zan fahimci wanne kake nufi?”
Iska Arshaad ya furzar kafin ya komo ya zauna
sannan cikin kulawa yace
“Akan abunda yake damun ka kwana biyun nan nake so muyi magana!
Ka chanja Aslam, Abba ma sai da ya kira ya tambayeni ko akwai abunda na sani yana damunka, dan ya tambayeka kace mishi ba komai!.
Na tambayeka tun a waya kace ba komai, yanzu gani nan face to face so talk!
Ka gaya min ko menene idan na addua ne in tayaka idan kuma na taimakone in taimaka maka
I hate to see you like this!
Dan Allah ka gaya mini ko menene i promise to help.”
Murmushi Aslam yayi kafin yace “Ba komai fa Arshaad.
Kawai matsalan Mommy ne
daga shi ba komai.
Ko kuna ganin halin da muke ciki ni da ita for years bai kai ya maidani haka ba?”
Ya k’arashe maganar
yana kafeshi da kyawawan idanuwanshi da har yanzu basu gama dawowa dai dai ba.
Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e dan ya fahimci Aslam bai shirya fad’a mishi matsalarshi ba
tunda yayi haka
kuma ya san ko ya tilasta ba sani zai yi ba…..
Yana cikin wannan tunanin Aaima ta sauk’o, ta shirya tsaf cikin abaya blue black tayi rolling, tayi masifar yin kyau.
A hankali ta k’araso inda suke tace
“Ya Arshaad muje”
Tana gama fad’in haka ta juya zata wuce Aslam ya rik’o hannunta.
Sai da ta turo baki tukun ta juyo ta kalleshi.
Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba ganin ya kama kunnenshi d’aya da hannu d’aya yayi kalar tausayi.
Zare hannun nata tayi da ke a cikin nashi kafin ta zauna tukunna tace
“Allah ya Aslam gani nayi gaba d’aya kamar haushina kake ji, tunda fa ka d’auko ni kake ta wani hantara ta, kamar irin ka tsaneni d’innan.
Ni Ina chan a skul ba ni da labarin da ya wuce naku
amman na dawo duk baku ma yi murna da ganina ba.”
Murmushi kawai Aslam d’in yayi kafin yace
“Sorry Auta.
Mun yi murna sosai.
We good?”
Murmushi ta d’anyi itama
sannan ta d’aga mishi kai alamar ‘eh’.
D’an guntun smiling Arshaad yayi tukun yace
“Aaima mun samu newest member a family d’innan!
Daughter d’in Abba.
Na san kin san labarin Anty Maryam ko?
To tanada y’a
Hudan!”
Cikin murmushi ya k’ara da cewa
“Hudan dai da kika sani”
Cikin zaro ido Aaima tace “Ma shaa Allah! Haba no wonder! Dama ba nayi ta ce maka tana kama da Abba da Ya Aslam ba kwanaki kace min a’a idonane kawai.”
Ta fad’a haka da tsantsar farin ciki kwance akan kyakkyawar fuskarta. Kafin ta tashi ta fara juyi da d’n tsalle tana cewa “Alhamdulillah nima nayi y’ar uwa! Yanzu Gramma sai ta daina yi min tsiya ta daina cemin k’anwar maza yayar maza..
Tana Ina (Hudan)?”
Sai kuma ta d’anyi jim! Tayi shiru daga baya ta zauna
tukunna tace
“Mai yasa Abba bai fad’a ba?
Tun farko?”
Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin yace
“Anan za kiji dalilin da yasa baki ga Mammy a gidan nan ba!”
….Tiryan tiryan haka ya zayyano mata abunda ya faru tun daga farko har k’arshe!…
Sharkaf haka fuskar Aaima ta jik’e da hawaye
kafin ya k’arasa bata labarin.
Yana yin shiru tace
“Mammy tana cell?
Yaya ka san inane cell kuwa?.
Ina Hudan take?
Ashe shiyasa na daina ganinta a wasapp rannan har kiran ta nayi tak’i d’auka, munafuka!!!”
Cikin b’acin rai Arshaad yace
“Watch your words, Aaima!
Ni na hanata ta fad’a miki komai, ita kuma tace ba zata iya chattn dake ba tana yi miki b’oye b’oye, shiyasa na d’auki wayoyinsu ita da Sakina nayi blocking d’inki ba tare da su kansu sun sani ba!
Na fi so sai mun had’u ido da ido tukunna in yi miki bayanin komai da kaina saboda na san haka ce zata faru!
Ku mata k’aramar kwakwalwa gareku ba zaki duba circumstances da situations ba kawai wanda yake naki shi za kiyi sopporting!
Yanzu ki nutsu tukun mu yi magana…”