← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 66

Sashe 8

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jiyayi kamar ya kwashe da dariya, amma saiya gimtse, ya kalli Fateema dake tsaye har yanzu yace, "my tee... bud'emin gate to, tunda bazakuce Na gaishetanba, saina dawo".
Kanta kawai ta d'aga masa, tanufi gate tabud'e masa, harya fice yana d'aga mata hannu, tamaida tarufe sannan takoma cikin gida zuciyarta Na k'una, dajin tsanar Amatallah.
Nikam bilynku Nace, "wannan fa shine gudu a duhu masu karatu
Yana tuk'i yana dariyar abinda matan nasa sukayi, a fili yace, " dama kun kwantar da hankalinku my wife's, Muhammad bashida burin k'ara aure, koma zanyi babu yanda za'ayi Na auri 'yar cikina, Amatallah she is my daughter ".
Da wannan tunani yak'araso gidansu mahaifarsa.
A k'ofar wani gida yay parking motar, gidane irin ginin da, sai dai ko ina mulmule yake da siminti, tundaga k'ofar gidan har zuwa bangon gidan.
Yatura murfin yashiga soron gidan da sallama, karo sukaci da wani saurayi dabai wuce 30years ba.
"A ya Muhammad barka da zuwa".
" yauwa Jabeer, daga ina haka kuma? bakaje aiki bane?".
"Wlhy naje yaya, mantuwa nayi nadawo d'auka, ina yarana? duk suna lafiya dasu Aunty's?".
" lafiyarsu k'alau, ya jikin baba?".
"A alhmdllhi wlhy, yanzu haka nabaro innani nabashi kunu dayasa a dama masa".
" masha ALLAH, jiki yafara sauk'i, bara to nashiga, dan zanje Jos ne".
"Amma yaya Muhammad tafiyar yamma?".
" to yaza'ayi Jabeer, ai ranar dole sai dole, bara nashiga dai".
"To shikenan, ALLAH ya tsare hanya, a gaida mana su Yaya Ismail da iyalansa".
" insha ALLAH zasuji".
Musabaha sukayi
, shi ya shiga, shikuma yafita.
Tsakar gidan babu kowa, sai dai a share yake tas, sai kuma k'amshin girki dake fitowa daga kichin d'in tsakar gidan.
Kai tsaye d'akin baba ya nufa, tunda jabeer yace innani tanacan.
Sallama yayi a k'ofar d'akin, sai da aka bashi izinin shiga sannan yashiga da sallama.
Mahaifinsu na zaune a saman k'atuwar katifar da yake jiyya, ya jingina da filuluwan da innani ta saka masa a jikin bangon, yatsufa sosai gaskiya, duk da hadda alamun rashin lafiya data kuma fiddo tsufan nasa, danma 'ya'yansa tsaye suke Kansa wajen kulawa dashi, musamman ma Alhaji Muhammad d'in. Sai dattijuwa itakuma tana zaune a kujera 'Yar tsugunno kusadashi, itama dai babu laifi ta manyanta sosai gaskiya, sai dai jikinta yafi Na baba k'arfi, saboda lafiya da ALLAH yabata, hannunta rik'eda ludayi zata saka a kwanon shan ruwa, da alama tagama bashi kunun.
Tunda yashigo tamasa kallo d'aya saita kauda kanta gefe. baba kam murmushi yayi, idonsa akan sa..
Ya tartare malun-malun d'insa ya zauna a k'asa kusada babansa shima yana murmushi, "sannu baba, ina yini?".
Ahankali baba yace, " lafiya lau Muhammadu, ya iyalanka?".
"Lafiyarsu lau baba, ya k'arfin jiki?, duk da dai yauma naga Alhamdulillahi".
Murmushi baban yak'arayi, yace, " gaskiya ne Muhammadu, jiki kam sai dai mucigaba da godema ALLAH".
"to Alhmdllh baba, ai mu haka mukeso, ALLAH yak'ara lafiya da tsawon kwana masu amfani".
Baba ya amsa da ''amin Muhammadu".
Kallonsa ya maida ga innani data kauda kanta gefe tun d'azun, yace, " Innani ina yini".
Kuma kauda kanta tayi sannan ta amsa masa. ta tambayi iyalansa.
Shima kansa a k'asa yace duk suna lafiya.
Batace komaiba tafara yunk'urin tashi.
Da sauri yace, "innani dama zan koma jos ne wajen maganin baba, dan naga yanajin dad'insa, daganan kuma zan duba d'iyar Isma'il batada lafiya, har an kwantar da ita a asibiti ma".
Yanzu kam sosai ta kalleshi, tace, " subahanallah, badai Khadija ba?".
"Eh innani ita".
" miya sameta?".
"Wlhy nima ban san dai miyake damuntaba, sai dai naje tukunna".
Daga innani har baba addu'a suka mata, sannan baba ahankali yace, " amma Muhammadu zakayi tafiyar dare ai".
Kallon agogon hannunsa yayi, "baba insha ALLAH kumin addu'a zan Isa da wuri, yanzu dana fita salla kawai zanyi Na d'auki hanya".
" to shikenan ALLAH ya tsareka, yakaika lafiya kaji".
Amin baba, ALLAH ya k'ara lafiya".
Sukace amin.
ya fiddo kud'i a aljihun babbar rigarsa, saman katifar ya d'ora, "innani ga wannan kowani Abu zai taso bana nan, insha ALLAH jibi zan dawo".
Batareda ta kalleahiba tace, " da kama bar kud'inka, dan Wanda kabada jiyama ko ta6asu ba'ayiba, munada komai agidannan, d'azuma jabeer yayo cefane mai yawa dazaiyi iya kaimu sati".
"Duk da haka a ajiye innani, ina Nazeefa da Shehu? Banji motsin suba".
"Nazeefa ta tafi gidan maijiddah, zata tayata aiki abokiyar zamantace ta haihu jiya, Shehu kam wai yatafi makaranta yace"..
"ALLAH sarki, to ALLAH ya raya, shikuma ALLAH yasa gaskiyane, tunda nasan halinsa. bara naje lokaci Na k'ara tafiya".
"Katsaya kaci abinci, naga Ramatu takusa gamawa".
Agogonsa Yakuma kalla, ya d'an kwantar da murya, " kiyi hak'uri Innani, gara naje karnayi dare, naci abincima babu dad'ewar nan."
"addu'a duk suka masa, yafita yana amsawa, zuciyarsa nak'ara masa dad'i, dajin k'aunar mahaifan nasa. salla kawai yayi ya d'auki hanya.
_______________________________
Koda d'an siyasar nan Mr Pam da jama'arsa sukaje police station sai suka nemi ganin d.p.o
Bayan ankaisu office d'insa, suka gaisa cikin mutunci, sannan ya mik'a buk'atarsa ga d.p.o nason asaki su zike, da farko d.p.o yaso ya tirje.
Amma tunda Mr Pam ya fiddo 'yan dubu-dubu bugun Abuja sai d.p.o ya waske. Mr Pam yay murmushi ganin yanda d.p.o yayi.
Ya ajiye kud'in agabansa yana fad'in "Yaya za'a banisu yalla6ai?".
" wata 'yar dariya d.p.o ya d'anyi, yasa hannu kan kud'inda Mr Pam ya ajiye, sannan yace, "yanzun kuwa".
Daga Mr Pam har yaransa biyu dake tare dashi dariya sukayi.
Duk wani ciku-ciku daya dace Mr Pam yayi, yasamu nasarar fiddo su zike.
Wad'anda tunda aka bada belinsu suka fito da k'udirin d'aukar mataki akan Amatallah da ahalinta.
Su duk zatonsu babantane yamusu shunen 'yan sanda suka kamasu.
Shiyyasa suka k'udirci ramawa..........
_(wannanfa Shine halin mafi yawan jami'an tsaron k'asar tamu. Shin tayaya za'a samu gyara? bayan masu gyaran suma suna buk'atar a gyarasu, *CIN HANCI DA RASHAWA* yazama abokin kowa a k'asarmu, kuma duk a dalilin *SIYASA KO K'ABILANCI*, zakiga d'an siyasa yayi duk wani shigi da fici wajen samun yanda yakeso, koda bai cancantaba. Zakiga ankama mai laifi awani waje, amma saboda bad'an yankin bane, ba d'an k'abilar bane sai a masa mummunan hukunci, amma idan k'abilarsa ne babba awajen, da 'yan uwansa sunzo sun mik'a sai a fiddashi, komai girman laifinsa, shiyyasa zakuga idan mutum k'abilarsa nada wani babban muk'ami awaje bayajin tsoron shiga kowanne tarko, saboda alfarmar dayake da ita, shin yaya zamu kira matsalolin k'asarnan?, *SIYASA KO K'ABILANCI!?* ne ke jagorancin lalacewarmu
?.)_
*_ya ALLAH ka gafarta ma iyayenmu
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
*_Happy Birthday Abba gana, ALLAH yak'aro shekaru masu al'barka da amfani a duniya da lahira
____________________
*_Number 5_*
____________________
Kusan 5pm ya isa garin jos, damma ba gudu yakeba, yakuma tsaya a garin Mr Ali yayi sallar la'asar, dan yana ganin kafin yashigo gari time ya shige sosai.
Chapter 8 · 0% Book details