← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 66

Sashe 60

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Baya suka shiga, a wajen asibiti Fa'iza tashiga napep yabiya kud'in sannan yanufi gida dasu Ama.....
Motar tayi shiru, Uncle nata tuk'insa, Amatallah da Aysha suna d'an hira jefi-jefi akan aikin yau d'in, Uncle najinsu amma baice komaiba har suka Isa gida ana kiraye-kirayen magriba.
Fateema tafito cikin kwalliya da d'okin tarbar mijinta, amma saitaci karo dasu Ama... nafitowa a motar itada Aysha.
Kallonsu kawai tayi batace komaiba, amma taji zafi a zuciyarta. Shikansa Uncle yakula bataji dad'iba Dan fuskarta ta nuna hakan.
Su Amatallah kam ko a kwalar rigarsu, gaisheta sukai suka shige ciki abinsu suka barta da mijinta.
Cikin fara'a ya tarbeta, yafito yana fad'in "yarafa my tee!".
"Basu dawoba suda momynsu".
Fara'arsa yarage yana kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, " mtsoww nifa banason irin wannan rayuwar, shiyyasa banson wani birthday d'in banzan nan, ankira magriba amma suna gidan mutane?".
"Kayi hak'uri, wlhy nasan itama hankalinta na gida".
Baice komaiba yamik'a mata wayoyinsa, " bara naje nayi salla ni".
Tace, "adawo lafiya".
Ciki takoma abinta, bataji motsin su Amatallah ba tashige 6angarenta, dan gaskiya taji haushin ganin Amatallah da Uncle tare, ga yarinyarnan data fara zargin kodai mijinsu sonta yakeyi? yo haka kawai dan yarinya ta musulinta sai a maidata tamkar wata jininsu, (nace hummm, kardai kishi ya rufe miki ido fateema).
Su Amatallah ma basusan tanayiba, Dan suna shiga Aysha tashiga wanka, Amatallah tazauna tana sauke numfashi dajiran fitowarta itama tasamu tayi, dan tanama fashin salla ne, shiyyasa Aysha tafara shiga danta sami damar yin salla akan lokaci.

Har Uncle yadawo sallar magrib Aneesa da yara basu dawoba, ransafa yafara 6aci, bayason shirme irin wannan, yanzumma anfi k'arfinsane, wai d'iyar su shehu ce ke birthday d'in cika shekara biyu, shine Aneesa ta kaisu dan Amatallah batanan, itakuma yakamata taje d'in tunda itace k'arama kuma kamarma za'a iya cewa k'awar Zalihance.
A falon k'asa ya zauna yakira Number Aneesa amma tak'i shiga, itadai Fateema tanata had'a masa kayan bud'a baki a d'arare, dukda abin na damunta a rai, tun bayan tafiyarsa masallaci kuma itama take kiran Number Aneesa network ya hanashi wucewa.
Tsaki yaja yad'auki ruwa yanasha.
Da wayo Fateema tanufi 6angaren Amatallah. fitowarta wanka kenan itakuma tashigo, Aysha kuna na zaune inda tayi salla tana karatun alkur'ani.
"Antyn yara munga idi".
" kamarya Anty?".
"Wlhy momy naketa kira awaya tak'i shiga, kuma Abbunsu yafara fad'an rashin dawowarsu, shima yagwada wayarta tak'i shiga, narasa misuka tsayayi har dare haka?".
Amatallah tace, " mun banu, Anty Aneesa ta manta da yandama yayarda suje Birthday d'inan? bara nima na gwada kiranta to".
Amatallah ma takira tak'i shiga, tace, "bara nakira zaliha to".
''Yauwa, ni wlhy tunanin nanma bai zominba, yo dukna rud'e kirata muji........"
Maganar Fateema tamak'ale saboda sallama da Amatallah tayi alamun Zaliha ta d'aga. bayan sun gaisa taimata Happy Birthday d'in Hafsa d'in dabata hak'urin rashin zuwanta sannan tace Su Anty Aneesa fa? basu taho bane?".
"Yanzu suka taho Anty Ama..... wlhy Haneefa ce yarinyar Anty Mariya ta d'auki su Ummita da Siddiqa wai suka tafi gidan k'awarta can k'asan layinmu, gashi tabar wayarta agida, munrasa yanda za'a kirata tadawo dasu, kuma babu wanda yasan gidan. ALLAH yasa Yaya baiyi fad'aba dai?".
"A'a baiyiba, tunda dai suntaho shikenan, ALLAH yakawosu lafiya".
"Eh sun taho, ya shehu mane yarakosu saboda yaran sunmata yawa gashi ba motar gidaba".
" wlhy kuwa, shikenan a gaidamin hafsa, sainazo cin cake".
Dariya zaliha tayi suka yanke wayar.
Ta fad'ama Fateema duk yanda sukayi, hamdala Fateema tayi, tace, "ALLAH ni tsoronma fita nakeyi, ran Abbunsu a 6ace yake, shirya mu tafi tare".
Ido Amatallah tazaro waje, " Anty Fatee ke kina tsoronsa bareni kuma?".
Karki damu saka kaya kedai, idan mu biyune k'ila ya sassauta.
Aysha najinsu, tayi murmushi cikeda sha'awar wannan family, ita kanta a d'azun taga fuskar Fateema ta nuna rashinjin dad'in ganin Uncle ya kawosu, amma gashi yanzu sun had'u suna magance matsalar data shafi kishiyarsu, rayuwarsu na birgeta.
Doguwar riga tasaka kawai tad'an shafa fauda tasaka turare suka fito, yana zaune inda fateema tabarsa, yad'ago ya kallesu, ransa a 6ace yake amma kwarjininsa ya shanyeshi, duk sai tsoro yakama Amatallah, ta la6e bayan Fateema tana satar kallonsa.
Kauda idonsa yayi daga kansu kawai, a d'arare Fateema tace, "kozakayi wanka tunda gasunan tahowam......"
Wata harara ya jefeta dashi wadda tasakata kame bakinta ta maida kanta k'asa.
Hakan yakuma bama Amatallah tsoro, dama Uncle ya iya fushi haka? lallai takuma yarda bayason abinda zai ta6a 'ya'yan nan nasa.......
Tunaninta ya katse saboda shigowar yara da gudu, daga Amatallah har Fateema ajiyar zuciya suka sauke, kowa yafurta alhmdllh a hankali.
Dukansu jikin Abbunsu suka fad'a suna masa oyoyo, abin mamaki sai Amatallah taga yaware yana musu dariya, Aneesa tashigo a d'an tsorace, Dan tunda taga motarsa a harabar gidan jikinta yay sanyi k'alau.
Su Amatallah duk sukai mata barka da dawowa, ta amsa tana nuna musu Uncle da ido, da hannu Fateema tamata alamar itadai tayi shiru.
Barka da gida tamasa, ya amsa kamar bata masa komaiba, (itama tasan bazaice mata komanba agabansu Ama....., saiya ke6e dagashi sai itane zataga 6ancin ransa).
Shehu yashigo d'aukeda Abubakar, zama yayi ya gaida yayansa dasu fateema, kamar babu komai sukad'an ta6a hira sannan yamusu sallama yatafi.
Shima sallar isha'i suka fito da yaran.
Baidai sha ruwaba sai bayan isha'i daya dawo yay wanka............
*_wayata tagajine, iskanci takemin, ALLAH dai yasa nasamu na k'arasa buk d'inan, shiyyasama nabar chart d'in dannayi manage, ngd da comments d'inku da addu'ar dakukema mahaifina, duk ina gani saidai babu damar amsawa, typing d'inma a wayar my Abdull nakeyinsa wani lokacin wlhy, dan wayata dana cika danne-danne saita k'ame
One luv my sweet fans
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
[1/24, 2:15 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
____________________
*_Number 38_*
____________________
A wajen shan ruwanma bai nemi kowaccensu ba, harma mai girkin kanta, tareda yaransa sukaci daganan ya zauna sauraren shirmensu.
Aneesa tasan tanada laifi shiyyasa tak'i fitowa, Amatallah kam firarsu sukesha da Aysha hankali kwance, tasan ba itace da mijinba, abincima yana tafiya salla dama ta d'ebo musu, Fateema kam zamanta tayi itama ta sharesa.
Sauraren surutun yaran kawai yake, amma hankalinsa nakan matan nasa, yasaba ko yaushe indai yana a gida duk suna gefensa, yau kuma yalura sunma had'e masa kai sun barsa shida yaransa.....
Wayarsa dake wringing ta dawo dashi hayyacinsa, Innani yagani ajiki, da mamaki yad'aga dan saiya had'a watanni bata kirashiba inba shine ya kirataba.
A ladabce ya gaisheta, ta amsa tamkar yanda ta saba, ta d'ora da fad'in ya yaran.
"Lafiya lau suke Innani, ya baba?".
"Yayi barci, Aysha ce bata dawoba, shine abin yadameni nace bara na nemeka, danna kira warta bata zuwa".
''Kiyi hak'uri Innani, wlhy naje d'aukar Khadija saita biyomu akan idan nasha ruwa zanzo gidan saina maidota, tokuma saina iske Aneesa basu dawo daga gidan Shehu ba hankalinna yatafi can, amma yanzu zan maidota".
''Alhmdllh, dama ni damuwata kar wani Abu ya samarmin yarinya, amma tunda tanan shikenan dama kun bari saida safe kawai, tunda dare yayi har tara fa, yaushe kukazo ka koma, nifa banason yawon darennan".
" to shikenan ALLAH ya kaimu goben a gaida gwaggo".
"Zataji". ta fad'a tana yanke wayar.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yamik'e yanufi 6angaren Amatallah.
Tunkan yashigama yafara jiyo dariyarsu, yashiga falon da sallama, film ya iske suna kallo, da sauri Aysha tace, " sorry Uncle, nataso kagama?".
"A'a Innani tace ki kwana anan, amma ki kirata dantata kiranki wayar tak'i shiga".
" to Uncle".
Bedroom d'in Ama...... yashige, hakan yasata mik'ewa dole tabi bayansa, ta iskeshi a bakin gado zaune.
d'an nesa dashi ta zauna. ya kalleta fuska babu walwala, "saboda 'Yar uwarku tamin laifi kuka had'e kai kuna fushi dani?".
Ama.... ta d'an zaro ido waje, " Uncle fushi kuma?".
"Eh mana, bagashi kunbarni nida yaranaba kowacce ta dawo d'akinta".
" nidai Uncle wlhy bahaka baneba, kawaidai ganin karna bar Aysha ne ita kad'ai, amma kayi hak'uri".
Baice komaiba yamik'e ya fice, yaran yacema suje su kwanta gobe akwai school.
Duk suka amsa da to, samansa ya haye shima.
Shigowar Siddiqa da saifudden yasaka Aneesa tambayarsu ina Abbunsu?, Saifudden yace "momy yafi d'akinsa".
" umma fa?".
"Itama tana d'akinta".
Sakasu tayi suka kwanta, taima Abubakar shirin barci sannan ta d'an kuma fesa turare tafito, 6angaren Fateema taje, itama isketa tayi tanama yara shirin barci.
" Umman yara alfarma nazo nema, dan ALLAH bara naje nabama Abbunsu hak'uri, nasan lattinmu yajawomin laifi".
"Hakan yayi, dama yanzu zanje nace kozakije kibasa hak'uri, naga muduka ukun haushinmu yakeji, yatasa yaransa gaba ya share kowaccenmu".
" kuyi hak'uri, nasan nina jamuku".
"Wlhy kibarma zargin kanki, kinsan halinsa dai akan yara, kijedai naji sunce yatafi 6angarensa".
" okey ina zuwa".
A bedroom ta samesa yana shirin barci, sallamarta kawai ya amsa yacigaba da abinda yakeyi.
A bakin gadon ta zauna harya kammala sannan tace, "dear!".
" uyim". yace batareda ya kalletaba.
Tace, "dan ALLAH kayi hak'uri, nasan namaka laifi tunda nasa6a lokacin dakace mu dawo, wlhy Hanifa ce ta d'auki su Ummita suka fita, gashi tabar wayarta kuma babu Wanda yasan gidan".
Kallonta yayi cikeda takaici, " amma shine kika gagara kirana ki sanarmin? inda nasan Baku tahoba aizan biya na d'akkoku kamar yanda na kaiku, saboda tsabar kin rainani shine bakiyi hakanba ko?".
Shiru tayi tana kallonsa, tama rasa ta ina zata farane, danta kula yakai mak'ura a 6acin rai.
Matsawa tayi kusadashi sosai, ta marairaice murya tamkar mai kuka, "dan ALLAH kayi hak'uri dear, wlhy ba raini bane, naga kayi azumi ne karmu shiga hak'inka, ka yafemin hakan bazai sake faruwa ba wlhy, kuma nikad'ai namaka laifin banda 'yan Uwana".
" bandasu amma kuka had'emin kai?".
"Bahaka bane wlhy dear, maybe su Baka fahimcesu bane, kayi hak'uri to".
Tausayi tabashi yanda yaga dukta damu, harda guntun hawayenta.
" shikenan na hak'ura ki kiyaye gaba, karki kuma min irin haka, inhar hakan takuma faruwa ki kirani ki sanarmin, miye amfanin wayar, dan baki ta6amin hakanba kuma yasa na hak'uran".
Cikin farinciki ta rungumeshi tana godiya, saikuma tasakeshi da Sauri tace sorry".
Murmushi kawai yayi ya d'aga mata kai, takuma masa godiya tafita.
Ganin yanda tafito ya tabbatarma Fateema komai ya daidaita, dan haka tashiga itama, (dama tasan mijinsu yanada saurin sauka afushi inhar zaka nuna masa nadamarka) saikuma tad'anji haushi, kar Aneesa tagama rurrungume mata miji tana nan. (Abin dariya masu karatu
Itama dai saida yamasa k'orafin sun had'e masa kai, hak'uri tabashi tacigaba da tattalin mijinta, shima kuma yabada kai bori ya hau.
Amatallah kam tun fitarsa tabishi da kallo, a fili tace, "ALLAH ya huci zuciyarka Uncle". daga nan tafito suka cigaba da hirarsu da Aysha, dukda lamarin Uncle d'in na caccakar mata rai haka ta danne.
*********
Washe gari
Da safe sai Amatallah taga da d'an sauk'i kamar ya sauka, hakanne yasa tasaki jikinta kad'an, amma jiya da damuwar fushin Uncle ta kwana, tsaf yalura da yanda takeyi agabansa, shareta yayi danta bashi dariya.
Koda suka gama break fast bata yarda sun jirashi akan sufita tareba, da wuri tace sutafi itada Aysha.
Lokacin daya fitoma sun dad'e da tafiya.
ALLAH yasotama ranar Aneesa ce zata kar6i girkin.
Haka rayuwar gidan take tafiya musu cikin kwanciyar hankali da annashuwa, idan kuma wani damuwar ya gifta a fuskanceta a yanda tazo.
Wata safiyar laraba kuma Nazeefa tatashi da nak'uda, Uncle mijinta yafara kira, dan haka yatafi a rikice daga kasuwa.
Nazeefa tasha wahalar haihuwarnan kafin ALLAH ya sauketa kuma, dan harma sun fara shirin mata cs. tasami d'anta namiji k'ato mai kamada babansa.
A ranar daga makaranta Amatallah suka wuce itada Aysha, a can suka iskesu Fateema itada Aneesa. sunta santin baby kuwa, Amatallah harda kuka tayi a 6oye da addu'ar itama ALLAH yabata.
Uncle yazo kusan 5pm ya d'aukesu, dankar yara su dawo islamiyya basa nan, kallo d'aya yayama Ama.... yaji ajikinsa tayi kuka, dan ita koyaya tayi kuka sai manyan idanunta sun nuna. bai tambayetaba suka tafi, dama ranar girkintane, dan haka ta zauna a gaba, Aneesa da Fateema suna baya, mah-mah da Abubakar ma suna gaba wajen Amatallah.
Tausayinta yakuma kama Uncle d'in, ganin yanda taketa luguyguyta Abubakar da Mah-mah, koma saka baki a hirarsu batayi saboda yaran gaba d'aya sun d'auke hankalinta.
Suna zuwa gida mai napep d'in dake kai yara school yana isowa, ya d'akkosu daga islamiyya.
Tare suka shiga cikin gidan.
Da daddare bayan sun gama cin abinci da 'Yar hira yace yaran suje suyi shirin barci su kwanta.
Kafin yashige yaje yayma Aneesa saida safe yayma su saifufden addu'a kamar yanda yasaba yafito, itama Fateema yashiga yayma yaran addu'a.
Amatallah tagama tsaftace jikinta da baje ko wanne lungu da sak'o na jikinta da k'amshi, duk a sanyaye takeyin komai, dan rashin haihuwarnan tata na damunta, musamman yau dataga babyn Nazeefa ma. A sanyaye tashigo bedroom d'in nashi, haryama kwanta danya gaji da jiranta.
Hannu yamik'a mata alamar tazo gareshi ganin ta tsaya a bakin k'ofar.
Idonta harya cika da kwalla ta taka a hankali zuwa gaban gadon, shiya kamo hannunta yajawota tafad'o jikinsa.
Rungumeta yayi sosai, a cikin kunanenta yace, "my heartbest waya ta6amin kene?".
Ai tamkar yazugata saita rushe masa da kuka kawai.
Dama yasan za'a rina dan tund'azu batada walwala koda ana hirama.
Bai hanataba ya barta tayi kukan sosai yana shafa bayanta a hankali, alamar lallashi, saida tayi sosai sannan yad'ago kanta ya manne bakinsa kan nata kawai, yafara mata lalashin dazatafi gamsuwa dashi.
Saida hankalinsu yadawo jikinsu sannan yashiga mata kalamai masu sanyi da ratsa 6argo.
" haba my best fad'amin matsalarki please, nine Uncle nine baba nine Ammi nine miji kuma kinji?".
Kanta ta d'aga masa, murya a raunane tace, "uncle maganar haihuwarnan bata damunkane?".
Shiru yay danya rasa mima zaice mata, zuwa can yace ''ki kwantar da hankalinki khadeeja, insha ALLAH baki tare da kowacce matsala, Amma ranar Monday ki shirya saimuga doctor mana".
" Uncle inajin tsoro wlhy, inajin tsoron kar ace bazan ta6a haihuwaba........."
Da sauri yarufe bakinta, ''insha ALLAH zaki haihu, sainaga jinin brother d'ina da nawa cakud'e a waje d'aya da izinin ALLAH my best, ki d'auka komai akwai lokacinsa, watarana sai labari, kikama sani ko nayi ajiya wannan watan". yay maganar cikin tsokana yana shafa shafaffen cikinta.
Kanta takuma cusawa a k'irjinsa tana 'Yar dariya.
Yayi dariyar shima yana sumbatar Sumarta da fad'in kokefa, amma da anatamin rowar fara'arnan dake yalwata farincikina da annashuwata nima.
Kuma k'ank'amesa tayi tana fad'in kai Uncle".
"ALLAH kuwa my Dee....."
Chapter 60 · 0% Book details